Showing 15001 words to 18000 words out of 21725 words

Chapter 6 - ZARGE Book Free Hausa Novels by Zahra Royal & Salma Ahmed Isa.txt

gaba da min tausar jikalle, da ma so nake na gane masu jin yaushin ana min tausa kuma na gane ki".


Ta k'are maganar tana mintsinin cinyar Amira. Amira ta janye jikinta, sannan ta miƙe riƙe da robar da take cin ramar da ita tana faɗin.


"Bari na tashi kar ki ƙarasawa saurayina ni"


"Ai sai na ƙwace saurayin naki ma! In ya so na ga ta tsiyar"


Ita dai Amira ƙin tanka mata ta yi, ta fita tana cin ramarta. Mummy ta yi dariya kawai tana firfita da muhuci, bawai dan gidan babu nepa ba, sai dan Hajiyar ba ya son iskar fanka, domin babu ta inda za ka ga gidan ka ce a ƙauye yake, domin gini aka yi mai matuƙar kyau. Sai wajejan yamma Daddy ya shigo tare da ƙannensa biyu.


"To Hajiya! Mu fa za mu kama hanya kin ga magariba ya kusa, kuma ina tsoron kwana a garin nan, bare ma na d'an zaga an san na shigo garin".


D'an nisawa Hajiya ta yi kamin ta furta kalamomin da za su yi sanadiyyar wargaza farin cikinsu gaba d'aya.


"Shi ya sa ai ban so ka nausa cikin garin nan ba har wasu su san da zuwanka. Ga shi dare ya farayi, ni kuma ba zan bari ku tafi yanzu ba gaskiya, sai dai ku bari zuwa gobe".


Daddy ya yi k'asa da kansa cikin bin umarnin Hajiyar ya ce "Shikenan Hajiya za mu kwanan zuwa gobe sai mu wuce".


Ya faɗa ba wai dan hankalinsa ya kwanta da hakan ba, dan ya san zamansa a garin haɗari ne... Su ko su Zahra daɗi suka ji, domin sun sha roƙon idan suka zo garin kan ya barsu su kwana, amma bai bari, sai yanzu da Hajiya ta faɗa, suna ta murna ba tare da sanin abin da zai biyo bayan hakan ba.


"Yawwa insha Allah ba abin da zai faru. Duk da dai a kusa-kusa damu d'in nan ana 'yan bindigar suna yawan shigowa, shi yasa abin sai a hankali".


Cikin Amira ne ya bada wata k'ara tsabar tsoro ta ce "Hajiya to miye na bada labari kuma? Kawai ki yi shiru dan Allah wallahi ni dai har kin samin tsoro, har na fara jin kamar ma kar mu kwana Wallahi".


Zahra tayi saurin cewa "To amma Hajiya kuke zaune a haka? Ku ma ai nake ganin duk masu kud'in garin sun tashi sun koma cikin birni, ke ma Wallahi kawai da yarda kika yi, idan za mu yafi mu tafi tare da ke".


Wata dak'uwa Mummy ta jefa ma Amira da Zahra, hakan ya sa ba shiri suka kama bakinsu suka yi shuru. Hajiya ta d'an yi murmushi tana cewa.


"Kyaleta kawai, ai tana da gaskiya, ni kuma gara na mutu a garin nan da kuke gani, ai da zan tashi daga cikinsa da tuni na tashi, ga ubanku nan zaune, ba yadda bai yi i da ni ba domin na koma kusa da shi nak'i, ina dai nan inda nafi wayo, muna ta kuma addu'a a kansu, kuma cikin ikon Allah abin nasu ya yi sauk'i, amma kwanakin nan dai sai Addu'a domin ba ranar banza da za'a tashi da safe ba ki ji labarin cewa sun shiga wani gari nan kusa damu ba, an kashe wani ko an d'auki wani, amma nan dai gaskiya har yanzu ba'a tab'a shigowa ba".


Ɗaya daga cikin ƙannen Daddy yace "Hajiya da za ki yarda yanzu ma zaku iya tafiya domin alamu sun nuna cewa hankalin Yaya Musa bai wani kwanta da ci gaba da zamanki a garin nan ba"


Hajiya ta girgiza kanta.


"Su dai sa tafi zuwa gobe, amma ni kam zama a garin nan yanzu na farasa"


Salma Ahmad Isah ✍️
Zahra Royal Star 🌝


_________________


Page ɗaya ya rage a free pages ɗin da muka alƙauranta... Domin ci gaba da karanta littafin ZARGE za ku biya ₦500 ta lambar wayar da za mu rubuta a ƙasa... Muna masu tabbatar muku da har yanzu ba mu yi komai ba.


5487270431
Salma Isah
Monie point


Sai ku tura shaidar biyanku ta 0813 047 9973
*ZARGE*


BY
SALMA AHMAD ISAH
&
ZAHRA ROYAL STAR


Page 07




*Ƙauyen Gyaza, Kankia Local Government, Katsina State, Nigeria.*


ZAHRA POV.


Bacci suke hani'an a wani ɗaki da aka ware musu ita da Amira, yayin da Amira ta jibga mata ƙafafunta, dan da ma can Amira mummunar kwanciya gareta, hakan yasa ma aka raba musu gado tun suna yara... Tsaki ta ja cikin magagin bacci ta kai hannu ta ture ƙafafun Amiran dake kan cinyoyinta. Amma ba a fi minti uku da yin hakan ba Amira ta sake lafta mata ƙafafun nata a karo na bayu.


Tsakin da ta ja a wannan karon ya fi wanda ta ja da farko tsayi, idonta ta buɗe tana ɓata fuska, sannan ta sake ture ƙafar Amira tana haɗawa da faɗin.


"Ke Yaya kin danneni"


Amira da ba ta san me take cewa ba cikin magagin bacci ta yi wani gwarancinta da ya so bawa Zahra dariya, dan yanzu da ace gari zai waye tace Ya Amira kin yi kaza Wallahi har ƙur'ani za ta dafa kan ba ta aikata ba. Juyi ta yi tana laluben pillow, ta ɗauko guda, sannan ta rungume tana lumshe idonta.


Sakan uku ba ta haura da lumshe idon nata ba ta ji kamar ana buga ƙofar sashen da suka sauƙa, domun tsabar girman gidan da Alhaji Musa ya gina sashi sashi aka kasa shi, na Hajiya da ban, na ƙannensa da matansu ma da ban, haka kuma ya yi nasa ma da ban. Jin ƙaran ƙwanƙwasa ƙofar a karo na biyu yasa ta buɗe idonta, kafin kuma ta tashi zaune tana mamakin jin bugun ƙofar a lokaci irin wannan.


Domin ta tabbatar da wani abu guda ta sauƙa daga kan gado, tana laluben wani dogon mayafinta data ɗaura a kanta lokacin da za ta kwanta, ta ɗauka ta ɗaure kanta, sannan ta nufi ƙofar ɗakin, sanye take da wasu pyjamas riga da wando masu santsi, duk da kalar kayan mai duhu ce bai sa kayan ya fasa sheƙi cikin duhun daren ba. Lokacin da ta buɗe ƙofar ɗakin ya yi dai-dai da sanda shi ma Daddy ya buɗe tasu ƙofar.


Kuma tana leƙowa da kanta suka haɗa ido da shi, ta fito yayin da Daddy ke mamakin rashin baccinta a lokacin, dan shi kam bai samu bacci ba, tun da ya kwanta har zuwa yanzu da ƙarfe ɗaya da mintuna ta yi.


"Zahra me ya hanaki bacci har yanzu?"


Daddy ya tambaya yana kallonta, kamin ta samu zarafin amsa masa aka kuma ƙwanƙwasa ƙofar falon, hakan yasa Daddy ya kauda batun, ya nufi ƙofar zai buɗe, sanda ita ma Mummy ta fito daga ɗakinsu tana hamma.


"Isah lafiya?"


Daddy ya tambaya lokacin da ya buɗe ƙofar ya ga ƙaninsa Isah, hasken fitilun dake waje ne ya ba shi damar ganinsa da kyau. Isah ya sharece gumi, sannan a gaggauce yace.


"Ku yi maza-maza ku fito! Domin an samu gayu sun shigo garin nan a cikin wannan daren!"


Wani irin sautin ƙulululu na tashin hankali cikin Daddy ya yi, sannan hantar cikinsa ta shiga kaɗawa, take gumi ya yanko masa, yana jin wani tashin hankali na masa sallama.


"Innalillahi wa inna ilaihirraji'un!"


Daddy ya furta bakinsa na rawa.


"Sun shigo gidan nan ne?"


Daddy ya tambaya bakinsa na rawar tashin hankali.


"A'a ba su shigo ba, shi yasa muke ƙoƙarin mu fita daga gidan kafin su shigo!"


Isah bai rufe bakinsa ba Daddy ya ji sautin harbin bindiga da kunnuwansa. Idanuwansa ya zaro waje yana innalillahi wa inna ilaihirraji'un.


"Me yake faruwa ne wai?"


Mummy dake tsaye tare da Zahra cikin rashin sanin abin da yake faruwa ta jefo musu tambayar. Amma Daddy bai amsata ba ya juyo cikin falon, ya tsaya yana kallonsu.


"Ina Amira?"


Ya tambaya gaba ɗaya ilahirin jikinsa na rawa.


"Ta... Ta na ɗaki!"


Zahra ta amsa tana haɗiyar miyau, dan ita ma ta ji tashin bindigar.


"Maza jeki ki tasota ta zo mu fita"


Da gudu Zahra ta koma ɗakinsu, sannan ta shiga tashin Amira dake bacci hankali kwance, kamar tsumma a randa.


"Amira! Ya Amira!"


Ta faɗa tana ɗaka mata duka a cinyoyinta, amma a banza man kare. Cikin tashin hankali Zahra ta cije leɓenta na ƙasa, dan gaba ɗaya ma ta rasa yanda za ta yi, ba ta taɓa sanin cewa wata rana wannan nauyin baccin na Amira sai ya kusa janyo musu halaka ba sai yau.


"Ina Amiran wai?"


Daddy da ya faɗo ɗakin ya tambaya, Zahra ta nuna masa ita.


"Ta ƙi tashi"


"Ke Amina! Amina"


"Na'am"


Aka yi sa'a wannan karon ta amsa.


"Ki tashi mu tafi"


Cewar Daddy. Da yake ba ta san wainar da ake toyawa ba sai ta yi juyi tana faɗin.


"Ina kuma za mu je cikin daren nan Daddy? Ba Hajiya tace sai gobe za mu tafi ba?"


"To Bandits ne suka shigo Gyaza!"


Ai Zahra ba ta gama rufe bakinta ba Amira ta zabura ta miƙe zaune, take jikinta ya kama rawar tsoro, hawaye kuma suka yanko mata.


"Wayyo Allahna mun shiga uku Daddy za su kashemu!" Ta faɗa bakinta da jikinta gaba ɗaya na rawar tsoro.


"Ki yi shiru kin ji? Babu abin da zai sameku! Tashi mu je"


Cewar Daddy yana kamo hannunta, kamar wata sokuwa haka ta miƙe tsaye, ya ja hannunta yayin da Zahra ma ta kama ɗayan hannun nata, tsaye suka iske Mummy da Isah a falo cikin tashin hankali, ba tare da ɓata lokaci ba suka fita daga sashen Daddy, suna tafiya a hankali kamar masu shirin yin sata.


Lokacin da suka isa babbar harabar gidan suka ji an daki babban gate da mugun ƙarfi, hakan yasa Zahra da Amira suka tsorata, suka rungume juna Amira na fashewa da kuka.


"Na shiga uku, Daddy mun mutu"


Ta faɗa jikinta na rawa, Mummy ta kamasu ta jasu cikin matan ƙannen Daddy su biyu da, da kuma Hajiya da aka tarasu a tsakar gidan. Kowa ka kalla a cikinsu hankalinsa a tashe yake, domin abu makamancin wannan bai taɓa faruwa da su ba, dan ba a taɓa shiga ƙauyen nasu ba, har gara ma ƙauyen maƙwabtansu...


Kafin su samu mafita wasu daga cikin gayun suka dirƙo ta katanga, lamarin da ya ƙara ruɗa duk wani mai jini da hankali a jika dake wurin... Musamman ma da suka nunasu da bindiga, tare da umartarsu kan su durƙushe a kan gwiwoyinsu. Abinka da wanda yake gaɓar ceton rai, babu musu suka zube a ƙasa, kowa jikinsa na rawa, ciki har da Hajiya tsohuwa, ita ko Amira har da fitsarin tsoro ta saki a wando.


Kasancewar su biyu suka dirƙo, ɗaya ya tsaya gadinsu, yayin da ɗaya ya ƙarasa ya buɗe gate ɗin da yake a kulle, sauran abokan tafiyarsu dake tsaye a waje suka shigo, kowa cikinsu riƙe da muggan makamai. Haka suka musu ƙawanya suna kallonsu.


"Ku mana shiru dan Ubanku! Kafin duk mu bi mu kasheku yanzun nan!"


Cewar wani daga cikin 'yan bindigar yana zare jajayen idanuwansa a kansu, tsawar da ya daka musu ce tasa Amira ta ƙara firgita ta ƙanƙame Zahra dake aikin kuka, amma babu sauti sai hawaye.


"Ina Alhaji Musa?"


Tun da suka ji wannan tambayar kuma suka tabbatar da cewa shikenan! Ta faru ta ƙare, da ma sun zo ne dan su kashe shi, ko su tafi da shi.


"Ba magana ake muku ba kun yi shiru!?"


Suka sake daka musu tsawa jin babu wanda ya amsa, kuma yanzun ma tsoro ya hana kowa furta komai, sai Zahra da ta fashe da kuka mai sauti tana matsawa kusa da Mummy da ita ma ke hawaye. Ganin abin nasu rainin hankali ne yasa wani cikin 'yan bindigar ya ɗaga bindigar dake hannunsa, cike da rashin imani ya ɗorata a kan Hajiya da jikinta ke rawa, ba tare da kowa ya fuskanci abin da suke son aikatawa ba suka ji ƙaran bindigar da ya harba ya tashi.


Hakan ya sa suka sake ruɗewa, ɗaya cikin matan ƙannen Daddy ta ƙwalla ƙara, yayin da Zahra ta toshe kunnenta jikinta na ƙara ƙaimi wurin rawar da yake, ita ko Amira hayyacinta ne ya shiga ƙoƙarin ƙaura daga jikinta... Take Daddy ya ɗaga hannunsa yana kuka, a lokaci guda kuma yana kallon gawar mahaifiyarsa yashe a ƙasa.


"Ni ne!.? Ni ne"


Ya furta har sau biyu.


"Wato rainin hankali ne ya sa ka yi shiru ke nan?"


Daddy ya girgiza kansa.


"Kai! Ku kama mana shi da 'ya'yansa biyu mu tafi"


Jin batun waɗan da za a ɗauka har da 'ya'yansa yasa Daddy ya haɗa hannayensa ya shiga roƙonsu.


"Dan Allah karku taɓsu! Na roƙeku da girman Allah! Dan Allah ni ku kasheni, ko ku tafi da ni!... Amma su kam ku ƙyalesu"


Har ƙasa Daddy ya kifa yana ƙoƙarin roƙonsu, amma ba su saurare shi ba suka kamo Zahra da Amira dake jikin Mummy suna kuka, cikin ƙoƙarin kare 'ya'yansa Daddy ya riƙo mutumin da ya riƙe Zahra, aiko yana juyowa ya bugawa Daddy bakin bindiga a tsakiyar kansa, yana faɗuwa ƙasa wani da ban da wanda ya daki kansa ya harbe shi har sau uku, hakan yasa Zahra da Amira suka fasa ihu tare da Mummy suka yi kansa, yayin da ita kuma Mummy ta soma yin abu kamar mai hauka, tana ihu tana riƙe ƙafar ɗaya daga cikin 'yan bindigar da ya harbi Daddy, ita ma bai yi wata-wata ba wurin harbin ƙoƙon kanta, abu goma da ashirin suka haɗu suka taranma Zahra da Amira, duk sai suka rasa me za su yi.


"Daddy! Daddy!"


Amira ta ƙira da ƙarfi tana jijjiga shi, tashin hankali bai ƙara kamasu ba sai da suka ji an ce a kashe kowa dake wurin... Ai take Amira ta yanke jiki ta faɗi, Zahra ce mai taurin ran da ta ga komai, aka yi komai a kan idonta... Amma kuma kunnuwanta gaba ɗaya sai da suka daina aiki, domin ƙaran harbe-harben da suka yi a wurin ya sa jinta ya yi nisa, ta yanda har suka saɓi Amira ita kuma suka soma janta zuwa wajen gidan ba ta sani ba. Ba wai ta mutu ba ne, ba suma ta yi ba, kuma ba haukacewa ta yi ba, kawai dai lamarin da ya faru a kan idonta ne ya kasa fita daga cikin tunaninta... Babu abin da yake maimaita kansa sai harbin da suka yi wa Daddy guda uku, da kuma wanda suka yi wa Mummy a cikin kanta.


Ba iyaka su kaɗai aka ɗauka a ƙauyen ba, har da wasu 'yan mata da maza dake ƙauyen aka haɗa, tsabar yawan 'yan bindigar a tashin farko ba ka isa ka ƙirgasu ba... Yawansu ya kai intaha, kamar 'yan rali, wasu a kan babura, wasu kuma a ƙasa, suka saka mutanen da suka ɗauko a tsakiya, waɗan da matan cikinsu suka fi yawa... 'Yan mata ire-iren Zahra da Amira sun fi yawa, amma duk da haka har da mata masu goyo da kuma tsofi waɗan da shekarunsu suka fara gazawa, kawai tafiya suke, ba tare da sunsan inda za a kaisu ba, ita dai Zahra ba ta cikin hayyacinta, domin ba ta san inda ƙafafunta suke takawa ba, tafiya kawai take saboda ta ji kowa na tafiyar.




YABINTU.


Bayan kwashe tafiya ta tsawon awanni uku da 'yan mintuna motar hayar da ta hau ta isa garin Kaduna... Kuma ba tare da wani ɓata lokaci ba ta naimi motar da za ta kaita Gusau. Lokacin da aka nuna mata motar sai da ta tsaya ƙarewa motar kallo, kafin ta shiga ciki, yayin da ake saka mata kayayyakinta a bayan motar.


Ta yi waige-waigenta ta gama, amma ba ta ga alamun akwai wani fasinja bayan ita ba, hakan bai ɗaga mata hankali ba, musamman da ta tuna cewa yanzu ta yi rabin tafiyarta. A hankali ta kalli fuskar wayarta da ta kashe tun bayan da ta shiga mota a tashar Abuja. Bawai dan tana tasammanin ƙiran wani ba, domin ta san babu yanda za ayi ƙira ya shigo wayar a rufe.


Kuma dalilin da ya sa ta rufe wayar shi ne, ba ta son Daddy, Ummanta ko Umar su san cewa a mota taho, domin ta san idan suka ji za su iya hanata, shi yasa ta rufe wayar tata, duk da ta san ba lalle ma wani cikinsu ya ƙirata ba, tun da sun ɗauka cewar ta riga ta hau jirgi ne.


Tun tana jiran cikar motar da fasinjoji kafin su ɗauki hanya har ta cire rai, domin har bayan shuɗewar awanni biyu babu fasinja ko guda da ya zo yace zai je Gusau. Ganin kamar lokaci na ƙurewa ya sa ta kalli ɗan yuniyal ɗin dake kusa da motar.


"Baba dan Allah wai babu yanda za ayi mu tafi yanzu? Na ga rana na takewa!"


Mutum biyun dake zaune kan wani benci suka dubeta, kafin ɗayan cikinsu ya furta.


"A'a 'yar nan, indai za ki biya kuɗin sauran kujerun me zai hana ku tafi yanzu!"


Tsaki ta ja, ita da ta san da wannan ma ai ba za ta ɓata lokaci har haka tana zaune ba. Dan da ma ita ba ta son takura, gara ma a kaita ita kaɗai, dan haka tace.


"Nawa ne kuɗin kujerun duka?"


Aka ƙira direban motar akai lisaffi, ta lale kuɗinsu tas ta biya. Amma kafin su tafi sai da ta naimi su mata alfarma ta samu abinci kafin su tafi. Da yake ta biyasu kuɗinsu yanda ya kamata yasa basu musa ba. Fita daga tashar ta yi, ta je ta hau agwagwa da buje in ji Zamfarawa (keke napep nake nufi🤣).


Ta je wani supermarket ta yi siyayyan kayan ciye-ciye da drinks, ta hau wata keke napep ɗin ta dawo tasha, tana dawowa ta shiga mota, da yake ita ake jira kawai sai suka kama hanya. Tafiya ce doguwa, wadda ta fara tun daga Kaduna. A hanya sun wuce ƙauyuka da garuruwa.


Tun da suka ɗauki hanya sau biyu suka tsaya, na farko sun tsaya sun sha mai a wani gidan mai, sai kuma a wani ƙauye da drivern ya sake tsayawa suka yi sallah. Sannan suka ci gaba da tafiya, hira wannan ba ta haɗata da drivern ba, sai sanda take cin cake tai masa bismillah yace alhamdulillah, ta maida hankalinta kan hanya kawai, zuciyarta da bakinta ko sun duƙufa wurin ambaton Allah da naiman kariya daga gareshi.


Har bacci sai da ta yi a motar, lokacin da ta farka kuma yamma ta yi liƙis, a nan ma sun tsaya a wani ƙaramin gari sun yi sallah, sannan suka ci gaba da tafiya. Yabintu

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login