Showing 12001 words to 14265 words out of 14265 words
Chapter 5 - MASARAUTAR ZAZZAU TRUE BOOK HAUSA NOVEL BY HAUWAU MUSA YELDU.docx
kuma haka" ya fada yana kallon su, yayin da tambayar sa tayi dai dai da bacewar da gadangaren yayi bat.
"Abeey! Hamma ne ya toromin kadangare" ta fada sanda take isa kusa dashi tare da rirrikesa.
"Ya subhanallah! wai Aman da Kabeer ba na hana abin amfani da tsafi a gidan nan ba? To kar ku sake na kara ganin hak tinda dai nan ba gidan kafirai bane" ya karashe fadin hakan ransa a matukar bace, yana mai mayarda hankalin sa wajen Jiddah
"Me kake nufi Ardo?
Mama Fulani' yar Agadaz ta fada tana kallon sa, badai so kake ka danganta Masarautar Agadaz da kafirci ba?
Ko so kake ka gayamin cewar ni da mahaifana duk kafirai ne?
Tare da' yan uwa da yayuna?
Kenan wa'Annan duk kafirai ne?
Ta fada tana mai nuna Aman,Kabeer da kuma Jiddah, domin nasan kafi kowa sanin cewar duk ni na haife su sa'annan daga jikina suka fito har suma suka gaji baiwar dana gada a wajen iyaye da kakanni na, wanda har ya baka damar kake jifana da kalmar kafirci".
" Ya salam Mommah! Me yayi zafi har haka?
Nifa sam ba haka nake nufi ba,kawai fahimta nane baki yiba, nifa ba ina nuna 'ki ko kuma kyama ta ne akan abun ba, A a kawai ina nuna masu illar amfani dashi wajen tsoratarmin da mama tane,kinsan ko da'a tabamin Mahaifiya gwanda ran kowa ya baci"
Ya karashe maganar yana shafa kan Jiddah tare da guntun murmushi akan fuskar sa.
Yayin da Mama Fulani' yar Agadaz ta sauke nannauyar ajiyar zuciya tana mai hura hancin ta, alamun dai har yanzu bata huce ba.
"Yauwa ko kefa mommah? Ya fada yana kara sakin murmushi, to kizo maza ki biyo ni a bedroom akwai magana mai mahimmanci da zamuyi" ya karashe maganar yana barin falon baki daya.
Yayin da ita kuma Mommah ta mike jiki a sanyaye ta bi bayansa.
Yayin da Aman da Kabeer suka da katarda duk wani abu da suke yi tun lokacin da ya fara kokarin cin zarafin baiwar tasu, idanuwan su sun yi jajir, domin su harga Allah suna Alfahari da baiwar da suka gada a wajen mahaifiyar tasu,tinda dai ba koya suka yiba, haka zalika ba ara suka yiba, kamar yadda basu sha komai domin samun ta ba, baiwa ce sahihiyar ta wacce suka samu a wurin Ubangiji ta hanyar gadarta a wajen mahaifiyar su.
Yayin da itama Jiddah ta kama hanya tana mai susudawa ta nufi dakinta jikinta a matukar sanya ye.
©"Masarautar Yamma "
SASHEN WAZIRI.
A misalin karfe 2 na rana, aka gama sallatar gawar Junaidiyya bintu Waziri, tare da kaita aka rufe a gidan ta na gaskiya, wanda babu shakka ko konkonto duk wani dan Adam saiya je can kamar yadda Allah (s.w.a) ya fada a cikin littafin sa mai tsarki cewar.
Kullu nafsen za ikatul mauth.
Wato ma' ana duk wani rai sai ya dandani zafin mutuwa acikin suratul (Ankabut aya ta 57 ) .
To a misalin dai dai wannan lokacin Waziri ya shiga sashen sa yana mai nufar dakinsa kai tsaye, yayin da Kilishi ta mike tana mai share hawayen ta a falon ta wanda ya cika dinkim da jama'a, sa'annan tabi bayan Waziri zuwa dakin nasa.
"Waziri!" Ta fada sanda ta shiga dakin babu ko sallama.
"Na'am Kilishi! " ya fada yana kokarin boye hawayen dake zubo masa shiyasa ya dawo cikin gidan saboda yasan wajen ba zai samu damar koka waba.
"Shin ko kanada labarin Junaidiyya ba mutuwar Allah da Annabi ce tayi ba?" Ta fada tana jan majinar hancin ta.
"Kamar ya Kilishi?"
"Kwarai kuwa Waziri, Fulani Mai Dakin Yamma tana da sa hannu a mutuwar Junaidiyya!"
Rasss gabansa yayi mummunar faduwa yayin da gumi ya fara tsattsafo masa.
"Wa ya gaya miki Kilishi?"
"Bincike nane ya tabbatar min da haka"
"Kilishi dan Allah ki rufa mana asiri, bakin ki alaikum karki bari maganar nan ta fita" ya fada yana rike bakin sa.
"Kamar ya Waziri? Ai abinda bazai taba yiyuwa ba kenan, domin kafi kowa sani Junaidiyya ita kadai ce ' ya a gareni duk fadin duniyar nan, ka ga kuwa wallahi Tallahi bazan bar jininta ya tafi a banza ba!"
"Me zaki yi? Nace me zaki yi Kilishi? Nasan kinfi kowa sanin cewar Rayuwa da mutuwa a hannun mahaliccin mu kadai suke, domin shi ke kashewa sa'annan kuma shine mai rayawa....✍️
Like Share and Comment pls🙏 Sai daku mutanen Arziki much love💃🤸♂️🤸♂️😘😘
Update group link👇👇
https://chat.whatsapp.com/GT9wHXDXR6kKEklUsof4Bv
Channel link🐽𡱨ttps://whatsapp.com/channel/0029VbApRz2LSmbf6rc13P3H
GARKUWAR AL'UMMA WRITTERS ASSOCIATION
(G.A.W.A).....✍️
___________________________
Kungiya mai Amfani da Alkalaminta tare da Basirarta da kuma tinaninta Adomin ta Fadakarda AL'UMMAR ta.
__________________________
Mallakar Sarauniyar GARKUWAR AL'UMMA👑Queen Jiddah👑
👑MASARAUTAR ZAZZAU👑
Magical love story💕
Story and written by
HAUWA'U MUSA YELDU.
Inkiya
Queen Jiddah👑
Baby nice💫
Bismillahir Rahmanir Rahim.
Kamar yadda na fara rubuta wannan littafin lafiya, Allah ka bani ikon kammala shi lafiya.
Pg 10.
"Kamar yadda babu mai talautawa da azirtawa saishi, babu mai hanawa saishi haka zalika shi kadai ne mai bayarwa, saboda haka ni nayi imani da cewar lokacin Junaidiyya ne yayi tunda ko yayi babu makawa sai ta amshi kiran mahaliccin ta, sa'annan ina mai yima ta addu'a Allah ya jikanta ya kuma gafar ta mata"
"Da kata Waziri!" Kilishi ta fada tana mike wa tsaye sa'annan ta furta.
"Na Rantse da rabbul izzati, Sai Fulani ta dandana kudarta! Sai na wulakanta ta Sa'annan sai ta kaskanta A cikin gidan Masarautar nan, Billahil Azim sai nasa ta dandana zafi da kuma radadi na rashin ' da, domin ina mai tabbatar maka da cewar bazan taba bari jinin Junaidiyya ya tafi a banza ba"
"Inna lillahi wa inna ilaihir raji' un Kilishi! Da alama So kike amana korar wulakanci a Masarautar nan"
"Ko ra? Wa ya isa duk fadin Masarautar Yamma?"
"Shin ko ka manta cewar Sarautar Waziri ga darta kayi bawai kyauta aka baka ba?
Ko ka manta cewar a wajen mahaifin ka ka gaje ta?
Yayin da shima ya gada a wajen nasa mahaifin!
Ko ka manta cewar da tunanin ka Sa'annan da duk wani abu da kayi nazari ,dashi mai Martaba ke amfani har ya yima bayinsa hukunci dashi?
Shin ko ka manta irin girman da mukamin Waziri ke dashi wanda hatta idan sarki bashi nan zaka iya maye gurbin sa harka yanke wa al'ummar sa hukunci?
Ko kuwa ka manta duk fadin Masarautar nan Mai Martaba bashi da wani abokin shawara face kai a matsayinka na Waziri?
To billahil Azim ni Kilishi diya ga Tafidan Masarautar nan wanda ya gaji sarautar Tafida a wajen mahaifin shi sa'annan shima mahaifin shi ya gada a wajen nasa mahaifin, sai na sanya Fulani Mai Dakin Yamma tayi dana sanin abinda ta aikata a gareni,sa'annan kuma na sanya ta girbi abinda ta shuka! Wannan alkawari ne na dauka"
Ta karashe maganar tana fita daga dakin ba tare da ta jira domin jin ta bakin sa ba, Yayin da shi kuma Waziri ya rinka safa da marwa a dakin, wanda daga karshe ma ya fita daga sashen baki daya yana mai nufar fada, domin amsa zaman makoki.
©"Masarautar Gabas"
Kuka yake yi wanda ke hade da gurnani, yayin da yake dawowa siffar sa ta dan Adam, sai dai kash yatsun hannayen sa harma da na kafar sa suna nan a siffar su ta dabbobi, yayin da bakinsa ke dauke da manyan hakora biyu a haurunsa na sama , wanda ya kafe iyayen nasa da jajayen idanuwan sa yana mai sauke nannauyar ajiyar zuciya.
"Subhanallah Balmaty! Me ke faruwa ne haka?"
"Modibbo nima ban sani ba, ka ga yanda abun ya zama"
"Kinga sake gwada wa muga"
Da sauri ta sake durkusa wa a gaban Hussain tana mai cake guiwowin ta akasa tare da daga hannun ta na dama a sama sa'annan ta furta.
"Kuwwatish Shadidul Huzun"
Nan take wani kyakkyawan tsuntsu ya bayyana a saman dakin yana mai sakkowa kasa da sauri sa'annan ya rikide yana mai dawowa matsakai ciyar kyakkyawar sanda yana mai fado wa acikin hannun Balmaty.
A dai dai wannan lokacin da sandar ta fado hannun ta idanuwan ta ne suka rikide suna masu dawowa launin wannan sandar wato black, launin fatar wannan tsuntsun.
Da sauri ta sake juyarda wannan sandar zuwa saitin da Hussain yake tana mai furta.
"Kuwwatish Shadeed "
Da karfi ya saki wata irin kururuwa yana mai girgiza kansa sa'annan ya bude kwayar idanuwan sa wacce ta dawo golding wato launin wannan Zakin sa'annan ya sanya su acikin na Mahaifiyar tasa, nan take wani irin haske mai tsananin sheki ya fito a idanuwan sa yana mai kai farmaki a wurin Balmaty.
Da sauri tayi baya tana mai jifa da sandar ta tare da saurin rumtse idanunta sa'annan ta sake bude su.
Yayin da Hussain yake zaunen sa kamar dai dazu hallau kuma hannayen sa da kafafuwa suna nan a siffar dabbobi.
"Inna lillahi wa inna ilaihir raji' un Balmaty" Hassan ya fada sanda ya isa wurin ta tare da rike ta, shima Modibbon da sauri ya isa wurin nata tare da Intisar harma da Jurmainatu, suna yi mata sannu.
"Modibbo hakika ina cikin tashin hankali marar misal tuwa idan har abinda nake zargi ya tabbata"
"Me kike zargi Balmaty"
mai Martaba Jibreen Jabbar bin Jafar ya fada hadi da saka hannunsa yana mai rike nata hannun yayin da fuskar sa ke fuskantar tata fuskar.
"Modibbo bazan iya warkar dashi ba! Karfin ikon dake tare dashi ya zarce nawa nesa ba kusa ba!" Ta karashe fadin hakan tana mai fashe wa da matsanancin kuka.
Yayin da Itama Intisar ta mike tana mai zuwa kusa da Mahaifiyar tata wato Mama Fulani Balmaty, ta fada jikin ta tana mai rirrike ta itama ta fashe da matsanancin kuka.
Hassan kuwa kusa da dan uwan nasa Hussain yaje tare da sanya hannu ya tabasa kasan cewar yanzu yana bisa hankalin kansa bazai cutarda kowa ba.
Mai Martaba kuwa safa da marwa ya rinka yi a dakin, daga karshe ya juyo yana fuskantar su tare da sauke nannauyar ajiyar zuciya, sa'annan ya bude baki yana mai furta.
"Hassan!"
"Na'am Dady!"
"Dauki Hussain kuje can bangaren ku, ke kuma Jurmainatu ki dauki Intisar ki mayar da ita dakin ta, ina da bukar nayi magana mai mahimmanci da Balmaty"
"An gama Ranka shi dade" Jurmainatu ta fada tana mai jan hannun Intisar, Yayin da Intisar din ta kara kankame Balmaty tana mai furta .
"Balmaty! Ni zan zauna a kusa dake, dan Allah ki gaya mata karta tafi dani" ta karashe maganar tana sake fashe wa da wani kukan.
Balmaty dake zaune tamkar butum butumi, ta motsa labbanta da kyar tana mai furta.
"Kinga 'yata Tashi kuje Allah yana tare da mu saboda haka karki damu kinji?"
Ba ta furta komai ba illa hawayen dake sake zubowa a idanun ta tana mai mike wa tsaye tare da bin bayan Jurmainatu suka bar dakin a tare.
Shima Hassan din jikin sa a matukar sanya ye ya kama hannun dan uwan nasa Hussain suna mai barin dakin tare da nufar bangaren su kai tsaye.
Yayin mai Martaba Jibreen Jabbar bin Jafar ya zauna a kusa da Mama Fulani Balmaty yana mai fuskan tarta ,sa'annan ya motsa labbansa yana mai furta.
Da gudu Dokin ke tafe a harabar Masarautar yana mai nufar sashen mai Martaba, yayin da Harun yake zaune a saman Dokin hannun sa daya rike da linza minsa yayin da dayan hannunsa ke rike da karamar sanda yana mai dan bubbuga bayan Dokin da ita.
Yayin da shima Abdul Jalal ke tafe a saman nasa Dokin yana mai nufar sashen mai Martaba, wanda isarsa sashen yayi dai dai da sau kowar Harun a saman nasa Dokin, Yana mai gyara tsayuwar sa tare da sanya hanna yensa gaba daya a aljihunsa.
Wanda yayi dai dai da lokacin da Abdul Jalal ya sauko a saman Dokin sa yana mai nufar inda Harun yake, tare da mika masa hannunsa suka yi musabaha.
"Kace kaima ka samu labarin rashin lafiyar Hussain?" Abdul Jalal ya fada fuskar sa na bayyanar da rashin jin dadin sa game da zancen.
"Hmm eh wallahi Jalal na samu labarin, Amma fa ni ba wajensa nazo ba, saboda mutumen naka sai dai kai" Harun ya karashe fadin hakan yana tabe bakinsa, kasan cewar Abdul Jalal din shine babban aboki a wajen Hussain, sa'annan shine babban' Da a wajen Hakimin Masarautar tar.
"Harun kenan, ni ina na taba ganin an nuna wa mahaifiya kiyayy kuma ace danta ake so" ya fadi maganar yana kallon Harun din.
"A a fa Jalal ni bance bana son Hussain ba, kafi kowa sanin ba shiri muke ba yanzun nan sai mu fara rikici dashi, amma tinda ka matsa muje na dubashi"
"A to da dai ya fiye maka amma ni ina na taba ganin haka" Abdul Jalal ya fadi hakan yana mai jan hannun Harun suka shiga ciki.
©"Sashen Ciroma Zubair "
"Wai Hafseena me kike yi ne tin dazu? Ba dai kuka ba?"Ta fada sanda ta ke karaso wa kusa da Hafseenar.
" Haba Hafseena! ki zama mai hakuri mana, dubi yanda kika barmin girki duk ya kone a kitchen, kinzo kina wannan kukan, bafa zai fisshe ki ba"
"Mama dan Allah kibawa baba hakuri ya barni naje na duba hamma Hussain, Hankali na bazai kwanta ba muddim banje can ba"
"Ashe kuwa zaki tabbata a cikin tashin hankali har abada,domin kuwa idan harni Zubair ni na haife ki Hafseena! to wallahi baza kije gun dan iskan fitsararren yaron nan ba" ....✍️
Like share and comment fisabilillah🙏🙏
The pg is deducated to my fans much love😘🤸♂️💃