Showing 3001 words to 6000 words out of 14265 words

Chapter 2 - MASARAUTAR ZAZZAU TRUE BOOK HAUSA NOVEL BY HAUWAU MUSA YELDU.docx

27 Aug 2025

1712

saina gaya masu, shine wai har yake cewa bazan auri hamma Harun ba, wai bazan yi Auren ba baki daya" ta karashe maganar tana sakin wani kukan.

"Ya isa haka Intisar kinji? Daina kukan karya saka maki ciwon kai, wane Akheeyn ne yace ba zaki Auri Harun ba?"

"Akheey Hussain mana, kuma hahar da harara na yayi"

"Harara fa? Tau shi kenan yanzun dai ki share hawayenki barni dashi, da kaina zanyi magana da Mai Martaba idan ya dawo daga fada, waye shi da har zai sanya Shalele kuma Kaka a wurin Mai Martaba hawaye"?.

Dan murmushi Intisar tayi tana turo baki gaba, tare da lafewa a jikin "Fulani Balmaty" tana sauke nufashi, yayin da ita kuma Fulani Balmaty take kara mamakin irin wannan rigimar ta Intisar da Hussain, da murmushi akan fuskar ta tana shafa bayan Intisar din.

Tafiya yake yi a cikin gidan Masarautar, yana tafiya yana jan zazzalallen wandan sa, ga Ear Pies sanye a kunnen sa, yayin da jajayen labbansa ke motsawa a hankali wanda ke nuni da yana jin dadin marming music din nasa.

"Hamma Hussain"!

Matashiyar yarinyar ke fada tana binsa a baya,yayin da ta kasance ta tattare kasan alkyabbar tata tare da rike ta da hannunta saboda yanda Alkyabbar tata ke ja da kasa, kasance warta gajeruwa.

Hafseena kenan 'ya ga kanin Mai Martaba "JIBREEN JABBAR BIN JAFAR" wato zubair, wanda shine ciroman yanzu a cikin MASARAUTAR GABAS.

Ganin dai da gaske bazai tsaya bane ya saka ta yin sauri tana shan gabanshi, tare da sauke numfashi wani a saman wani saka makon dan gudun da tayi.

A wani wula kance ya dago yana saukar da rikitattun idanu wansa a kanta, kana ya cije gefen lebensa yana sake jifan ta da wulakan taccen kallo.

"Hamma Hussain, barka da war haka, sannu kaji? Ya zafin ranar nan ? Tin jiya nake ta neman ka amma ban gan ka ba, kuma ma nayi ta kiran ka a waya baka daga ba, yan zumma zanje wurin Intisar ne muyi magana akan yanda baikon nata da hamma Harun zai kasan ce shine naji kamshin turaren ka naz.."..

Tass ka keji ya dauke ta da lafiyayyen mari.

Ta dago hannun ta dafe da kuma tunta ,yayin da farin da ke cikin dara daran idanunta ya maye gurbi da launin ja! Take hawaye ya fara gangara a fuskar ta yacce kasan an kunna fanfo.

" Ni Hussain Jibreen Jabbar Bin Jafar!

Kike tarewa a hanya akan wani zancen ki na banza da wofi! Saboda dakikanci? Jahilcin ma irin na mutanen farko?"

"Ti bari na baki sako zuwa ga Zubair shida ya haife ki keda Harun din"

"Ki gaya masa, kice ina mai kara tabbatar masa, kamar yadda nayi masa Alkawarin bazai taba hawa kujerar Mulkin Masarautar Gabas ba! To wllh jininsa da na mahaifi na bazai taba haduwa ba da sunan Auratayya Atsakani"....

" To fitsararre dan gidan fitsararra! Marasa Addini da tarbiyya! "

Cewar ciroma zubair yana turo katon cikin sa gaba, ya yinda yake gyara babbar rigar dake jikin sa kasan cewar yau bai daura Alkyabba a saman ta ba, a bayan sa kuma dakarun sa ne kusan guda biyar 5 sun take masa baya , yayin da biyu daga cikin su ke rike da zabga zabgan bulallai a hannun su, yayin da fuskar su kuma ta kasan ce babu annuri ko kadan atattare da ita, ballan tana kuma a saka ran samun tausayi.

Yayin da Hussain ya dago da karfi, ransa a matukar bace saka makon jin yanda Ciroma Zubair ke ko karin keta alfarmar mahaifiyar sa a bisa idonsa ba tare da wata kara ba.

Idanuwan sa a waje kamar zasu fado kasa,

Yayin da cikin su yayi jajir, ji yake kamar ya shako wuyan rigar Ciroma Zubair, ba tare da nuna damuwa ko kadan akan dakarun dake bayan sa ba , domin kuwa ko kadan basuda maraba da mata a wurin Hussain.

A dai dai lokacin da Hafseena take tsaye a wurin hallau rike da kumatunta , yayin da duk wanda ya bude baki a cikin su kalmar sa ke kara birkita mata lissafi!!.

Ganin da tayi tabbas idan ta cigaba da tsayuwa a wurin, ba zata iya hanasu kammala aika aikar da suka fara bane, ya saka ta nufar Balmaty Garden da matukar sauri hallau kuma hawaye na ci gaba da zuba a idanunta....✍️

Like share and comment pls🙏sai daku mutanen Arziki Much love😘😘🤸‍♂️😩

Group update link👇👇

: https://chat.whatsapp.com/GT9wHXDXR6kKEklUsof4Bv

Channel link👇👇

https://whatsapp.com/channel/0029VbApRz2LSmbf6rc13P3H

GARKUWAR AL'UMMA WRITTERS ASSOCIATION

(G.A.W.A)....✍️

______________________________

Kungiya mai Amfani da Alkalaminta tare da Basirarta da kuma tinaninta Adomin ta Fadakarda AL'UMMAR ta.

__________________________

Mallakar Sarauniyar GARKUWAR AL'UMMA👑Queen Jiddah👑

👑MASARAUTAR ZAZZAU👑

Magical love story💕

Story and written by

HAUWA'U MUSA YELDU.

Inkiya

Queen Jiddah👑

Baby Nice💫

Bismillahir Rahmanir rahim.

Kamar yadda na fara rubuta wannan littafi lafiya, Allah ka bani ikon kammala shi lafiya.

Wannan page din sadaukar wane ga Aunty "Faiza Almustapha Murai" ( FA'EEH BG👊) Allah ya kara miki lafiya da nisan kwana.

Pg 04.

® "MASARAUTAR AREWA".

A Babban Falor ne suke zaune, yayin da shi Yariman naku ya kasan ce sanye da tsadaddar alkyabbar sarauta a jikinsa, ga kuma karamin filo mai matukar laushi wanda ya taimaka mashi wurin kishin gidar sa.

Yayin da princess Jidda ke zaune a gefen da ta kasance tana fuskan tarsa, ga kuma fuskar ta dauke da mayalwacin murmushi, ita ma alkyabbar ce sanye a jikin ta sai dai ban bancin tata alkyabbar da tasa, bai wuce adon da take dauke dashi ba, kasan cewar ta mace.

A tsakiyar su kuma babban tire ne a jiye mai dauke da kalar abu buwan tabawa da yawa a cikin sa, kamar dai duk wani kalar abinci da ake tarbar baki dashi a kowa ce Masarauta.

" Gimbiyar Masarautar Arewa, sannan kuma mafi kyawo da haiba, wacce ta zarce duk sauran wasu gimbiyoyi dake rayuwa a cikin, sauran masarautu na nahiyar Masarautar Zazzau" Yarima Habeeb ya katse shurun nasu yana mai furta hakan.

Murmushi ta sakar masa wanda ke tafiya da hankalin duk wanda a kewa irin sa.

"Zolaya koh"? Ta fada tana kallon sa.

" ko kusa, wannan babu zolaya a cikin sa, domin kuwa duk wanda yaga zabuwa to ki tabbatar da zanen ta ya ganta, sa'annan kuma ke dawisu ce wacce a koda yaushe launin ki sabon sheki yake sake wa. Kamar yadda ki keda daukar ido a duk lokacin da kika bayyana a cikin dubbannin al'umma, domin irin kune fa hausa wa, ke cewa koda kudin ka sai da rabon ka" ya karashe maganar yana kanne mata idonsa daya.

"Mai Martaba na barka da zuwa ya hanya"?

Ta fada tana dariya kasa kasa.

" yayi maki kyau" ya fada tare da watsa mata harara kasa kasa, shima yana murmushi.

"Taum hanya Alhamdullah, kuma mun samu tarba ta musamman daga wajen Mai Martaba, yanzu abu daya ya rage".

" Me nene"? Ta fada tana kallonsa ganin alamun bashi da niyar kara sawa.

"To sarkin son jin labari, ba komai ne ba fa, kawai abinda ya rage shine haduwar gemu da gemu, wato mai Martaban mu da naku, su ya rage su tsaida lokaci , da Alama sai naje na saka masa kuka dan bashi da alamar daukar abinnan serious"...

" kai hamma Habeeb! Kuka sai kace karamin yaro?".

"Eh naji kome zaki fada dai sai nayi"

Aiko dariyar da bata shirya ba ta kubuce mata, harda rike ciki tare da daukar 'karamin filo ta jefesa dashi.

"Haba Jiddah! Meye kuma na dariyar ?" Ya fada yana kallon ta.

Cikin dakikun da basu gaza uku 3 ba launin Fuskar ta ya sauya, dariyarta ta bace bat, kana farin dake cikin dara daran idanunta ya maye gurbi da launin ja! Yayin da ta 'kafesa da rinannun idanunta wa 'yanda basu da maraba da gauta.

"Me ya faru Jiddah? Ko na miki wani abun ne?" Ya fada adan tsorace yana kallon ta.

"Habeeb !"

"Na'am Jiddah na"

"Wane kalar so! Kake yimin ne? Yaya adadin 'kauna ta yake a cikin zuciyar ka?"

"Hmm Jiddah ! Ina yi miki so! Wanda ni kaina bazan iya kiyasta shi ba , ina sonki fiye da rayuwa ta! Sonki nake fiye da kaina! Kamar yadda masu ilimin kimiyya suka yi analysis suka gaji ba tare da sun iya gane yawan adadin Taurarin da ke fitowa a sararin samaniya ba, domin kuwa bincike ya tabbatar da a ko wace rana sababbi ne ke fitowa, wanda har yanzu aka kasa kayyade adadin su. To kamar haka ne sonki yake tsiruwa a zuciya ta da kuma ruhina, ba tare da na iya gano adadin sa ba! Sanin kanki ne a duk lokacin da karamar bishiya ta kasan ce shuke a tsakiyar rana ba tare da ruwan sama na samun ta ba, kuma ba a samu wanda zai sanya mata wa'yannan ruwan ba, cikin kankanin lokaci zata bushe ta kanjame sa'annan kuma ta lalace! Wanda daga karshe rayuwar da ke dashe a jikin ko wace bishiya zata fita daga jikinta. To kamar haka ne a wajena! Domin ni kaina na sani idan na wayi gari babu ke a kusa dani to tabbas rayuwa ta zata zo karsh"....

" ya isa haka hamma na! " ta fada hawaye na fita a idanunta suna gangarawa a kumatunta.

"Na sani wallahi na sani, nasan kana 'kauna ta kuma nima haka, sai dai tsoro na keji jikina yana bani tabbas zaka barni ! Ji nake kamar za'a shiga tsakani na da kai, a koda yaushe fargaba ta kenan yayin da soyayyar ka ke sake mamaye duk wata jijiya dake gudana a cikin jinin jikina!".

Sai ya samu kansa da kasa tanka mata, domin babu shakka shima yayi wannan tinanin, yayin da idanuwan sa suka hasko masa Zulaihat wacce yayi kicibis da ita, a cikin Masarautar tasu lokacin da zai zo nan, shi kansa yasani a yanda ya wula kanta ta dole zata bawa Mama Fulani Mai Dakin Yamma labari wanda kuwa Allah kadai yasan hukun cin da zai biyo baya.

©" Masarautar Gabas"

A cikin Balmaty Garden.

Yayin da Mama Fulani Balmaty! Ta kasan ce zaune a saman wannan cafet din, Intisar kwance a jikin ta, Hassan kuwa zaune a gefensu kasan cewar daga masallacin Juma'a yake, sannan a duk lokacin da ya dawo masallaci wurin Mahaifitar tasa yake fara zuwa. A za gaye dasu kuma hallau wa'yannan Bayin ne .

"Balmaty yarinyar nan fa dada sangar cewa take kara yi, ki duba kiga ko su Aboy da Akheel basa wannan shashan ci, ni ina ga fa maganar Akheey Hussain gaskiya ce, Auren nan nata da an dan jinkirta sa harta dan kara girma"..

" hmm Balmaty kina jinsa ko?" Ta fada tana tashi zaune da matukar sauri.

"Kinga 'ya ta kyalesa zo kiyi kwanciyar ki, Hassan ka fitarmin a ido na rufe tun kan na saba maka, koshi Hussain din jiransa nake ai ina nan zai zo ya sameni"

"Hmm ba dani ba Balmaty nayi shiru Allah ya huci zuciyar ki, ya fada yana rike bakin sa"

" to da dai ya fiye maka, yawwa Hassan dazun Hakimi ya same ni akan maganar wa'yannan dawakan da akayi wa su Aboy da Akheel order dai sai ka same sa asan yanda za ayi".

"To shi kenan Ranki shi dade Insha Allah"

Dai dai misalin wannan lokacin Hafseena ta iso tana zubewa a gaban Fulani Balmaty.

"Subhanallah Hafseena ! Mene ne?"

"Mama Fulani Balmaty, ham.m.a Hus.s.a.in da mahaifi na Zub..ba.ir. "

Sai ta kasa karasa maganar saka makon ambaliya da hawaye ke mata a fuska.

"Ki natsu mana Hafseena! Me Hussain din yayi masa?"

Kasa furta komai tayi illa hanyar farfajiyar Masarautar da kawai take nunawa da hannunta, hallau kuma hawaye na zuba a fuskarta.A firgice ko wannen su ya mike suna mai nufar wurin da matukar sauri, yau ko tafiyar sarautar ba'a samu mai yi a cikin su ba.

Yayin da Ciroma Zubair yake tsaye a gaban Hussain, kana ko wannen su yana fitar da huci, idanuwan su sun kada sunyi jajur kamar gauta, daidai lokacin da Hussain ya daga hannunsa na dama a sama yana mai furta .

"Huznul Shadidul Kuwwa"

Sana diyyar haka wani jibgegen Zaki ya bayyana a sararin samaniya, ya rinka ratsa gajimare da gira gizai yana mai sakkowa kasa da matsanan cin sauri, hakoran sa a waje yayin da ya barbaje gashin jikinsa yana mai kuka irin na Zakuna, sa'annan ya rikide zuwa tsuntsu daga tsuntsu ya dawo matsa kaiciyar kyakkyawar sanda yana mai fadowa a cikin hannun da Hussain ya daga a sama.

A dai dai lokacin da wannan sandar ta shiga hannun sa idanuwan sa ne suka rikide zuwa launin wannan sandar, wato ruwan zuma launin fatar wannan Zakin.

Hannun sa ya sake juyawa zuwa saitin da Zubair yake, yana mai furta wannan kalma wato "Kuwwatish Shadeed!!"......

" la Hussain ! Yaharimukas Ti'imali Bissihri Inda Halatil Gadabi!"

"A a Hussain! Na haramta maka amfani da tsafi a lokacin da kake cikin fushi!"

Fadar Mama Fulani Balmaty kenan lokacin da suka iso wurin.

Yayin da Zubair yake a firgice idanuwan sa a warwaje, saboda shi har ga Allah bai zata hatsa bibancin yaron ya kai nan ba, kenan shima ya gaji tsafin a wurin mahaifiyar sa? Kasan cewar ta Ba' indiya ya tambaya a zuciyar sa....✍️

Like share and Comment pls🙏mutanen Arziki much love💃🤸‍♂️😘😘💃

Update group link👇👇

: https://chat.whatsapp.com/GT9wHXDXR6kKEklUsof4Bv

Channel link👇👇

https://whatsapp.com/channel/0029VbApRz2LSmbf6rc13P3H

GARKUWAR AL'UMMA WRITTERS ASSOCIATION

(G.A.W.A)...✍️

___________________________

Kungiya mai Amfani da Alkalaminta tare da Basirarta da kuma tinaninta Adomin ta Fadakarda AL'UMMAR ta.

___________________________

Mallakar Sarauniyar GARKUWAR AL'UMMA👑Queen Jiddah👑.

👑MASARAUTAR ZAZZAU👑

Magical love story💕

Story and written by

HAUWA'U MUSA YELDU.

Inkiya

Queen Jiddah👑

Baby Nice💫

Bismillahir Rahmanir Rahim.

Kamar yadda na fara rubuta wannan littafin lafiya, Allah ka bani ikon kammala shi lafiya.

Pg 05.

Yayin da ya gyara tsayuwar sa cikin karfin

hali da kuma jarumtar da ya ara ya sanya wa kansa, yana mai fur ta.

"Aikin banza aikin wofi, ni za' a yiwa karyar larabci? To anyi walkiya kuma ta haska na ganki, domin ke ba balarabiya bace sannan rayuwa da ki kayi a garin larabawan da har ki ke tinka ho da yaren su ke da 'ya 'yanki bai hana ku sa'bon Ubangiji ba, kuna tsafi! Abin da Allah da Manzon sa suka hana"....

Zubair Yaka rashe maganar yana mai boyewa da sauri a bayan da karansa, saka makon farmakin da Hussain ya sake kai masa....

" Bafa nason shashanci Hussain! Duk abinda zai fada a wurin nan karka sake ka kai masa farmaki domin shi din kanen mahaifin ka ne"

" Bitarajjak Ummi! "

"Ina rokon ki mama!"

" La Yamna' u Halaka Hazash Shaitan"

" ina rokon ki karki haneni na illata wannan shaida nin"....

"Ga shaida niyar nan a gaban ka! Ita ta haife ka harka zama ka surgumin shaidanin kai ma! Duk Masarautar nan ba' a taba samun wanda ya hau karagal Mulki ya zauna da mace daya ba, sai yayana duk saboda hatsabi banci da tsafi irin na uwark".....

" Kuwwatish Shadidul Huznu!"

"La Hussain" Balmaty ta fada tana kara rike sandar tasa wacce kanta ke fitar da hayaki.

" A a Balmaty dan Allah ki sake ni"

"Bitarajjak"

" Ina rokon ki"

"Ki bari koda azaba daya ce na gana masa"

"Yalla! Yalla Hussain!"

Ta fada tana jan hannun sa a firgice ganin halittarsa ta fara sauya wa, yayin da ko wane sashe na jikinsa ke fitar da tsiron gashi wanda yayi kala da na dabbobi! Dabbobin ma jarum taccen Zaki!!

Idanuwan sa kuwa sake rinewa suka yi zuwa golden, suna mai nuni da tabbas zai iya rikidewa ya dawo Bijimin Zaki nan da wasu dakiku.

®"Masarautar Arewa"

A misalin wannan lokaci da kowane Bawa ke zauna wa domin ya huta, haka ma tsofaffi da kananan yara suke namen wurin kwanciya, wanda Hausawa kewa la'kabi da dare! Wato mahutar bawa.

Hallau kuma duk wata dabba ke deman wurin da ta buya, yayin da tsuntsaye ke dakatar da kukan su, suna masu lafewa a bisa bishiyoyi wa' yanda ke dauke da gidajen su, Sa' inda reshunan itacen ke motsawa saka makon iskan da ke kadawa a sararin samaniya.

To kamar haka ne ita ma take kwance a saman tsadadden gadonta mai kama da gari guda, kayan bacci ne sanye a jikin ta yayin da tayi rigin gine idanuwan ta kuwa suna kafe a saman silin na dakin, zaka rantse da Allah kirga shi take yi bayan gangar jikin ta ne kawai a dakin, amma ruhinta da kwakwal warta suna waje na daban.

"Jiddah! Ina yi miki so! Wanda ni kaina bazan iya kiyas tashi ba! Sanki nake fiye da kaina! Ina sanki fiye da rayuwa ta!"

Ta rumtse idanunta da sauri, tana dafe kanta dake dan sara mata,. Saka makon yanda kalaman sa ke mata amsa kuwwa a kunnu wanta, ta bude fararen dara daran idanuwan ta, wa' yanda suka maye gurbi da launin ja! Tana mai furzar da zazzafan huci a bakin ta, yayin da fargaba da tsoro suka sake dabai baye zuciyar ta, hakan ya haifar da wan zuwar zafafan ruwa a cikin kwayar idanun ta, sai hakan ya bayyanar da ruwan suna masu gan garowa a kumatin ta, wanda yayi dai dai da turo kofar dakin nata da Mama Fulani ' Yar Agadaz tayi, tana mai yin sallama.

Sai tayi saurin goge fuskar tata tana mi kewa zaune tare da amsar sallamar Mahaifiyar tata.

"Subhanallah! Jiddah mene ne? Meya same ki?" Ta fada tana hayewa kan gadon tare da rike gimbiya Jiddah.

"Ba komai mommah! Daman zazzabi nake ji sannan kai na yana ciwo" ta fada tana dafe da gefen kan nata.

" A a Jiddah! Bamu saba ' yar haka dake ba kuma karki bari mu fara daga yau, meke damun ki? Jikina ya bani cewar ba kalau kike ba, dole akwai wani abu, gayamin ko

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login