Showing 9001 words to 12000 words out of 14265 words

Chapter 4 - MASARAUTAR ZAZZAU TRUE BOOK HAUSA NOVEL BY HAUWAU MUSA YELDU.docx

27 Aug 2025

1556

Habibu Usman Umar Bin Ubaidullah keda ita bissalam".



Magatakarda ya nade takarda bayan ya gama karanta wasikar.

"Allahu akbar " gaba daya mutanen fadar suka furta suna murmushi, sa'annan sarkin zagi ya bude bakin sa yana mai furta.

"Gaba dai gaba dai sarkin Yamma! Jikan Ubaidullah, sun buga da kai sun barka yau ga adilin sarki a gaban mu, uba ga Yarima Habeeb sarkin gobe, miji ga jajirtacciyar mace kuma jinin sarauta da mulki gaba da baya wato Mama Fulani Mai Dakin Yamma! Yau ina gwanin wani ga nawa! Yau ina za muje nemawa Yarima Habeeb mata duk fadin Masarautun dake nahiyar Masarautar zazzau a hanamu aiko basu bamu ba domin ilimi da nagartar yaron, ya zama dole su bamu domin Nasaba da Asali gamida mutuncin da wannan Masarautar ta yamma ke dashi"

Murmushi bayyane a fuskar Mai Martaba ya daga wa sarki zagi hannu Alamun ya isa haka.

"Wanbai!"

"Na' am Ranka shi dade" wanbai ya fada yana kallon Mai Martaba tare da rissina wa.

"Ya akayi banga Waziri a wurin nan ba? Naso ace yana wurin nan yaji wannan daddadan Albishir din da aka aiko mana" mai Martaba ya fada yana kallon wanbai.

"Ranka shi dade ai Waziri yana bangaren sa duk yau ma bai shigo fada ba, saka makon yanda jikin 'yar wurin sa Junaidiyya da ya tsanan ta"

"Inna lillahi wa inna ilaihir raji' un" Waziri lafiya?. Wanbai ya fada saka makon ganin yanda Waziri ya fado wurin babu ko sallama bare kuma neman iso.

"Ina kuwa lafiya Wanbai! Allah yayi wa Junaidiyya cikawa yanzun nan!"

"Inna lillahi wa inna ilaihir raji' un" gaba daya mutanen fadar suka furta suna masu girgiza kansu, yayin da mai Martaba ya mike a tsaye yana mai fita fadar da matukar sauri, a wajen fadar ya taradda wasu daga cikin fadawan sa aikuwa da sauri suka zube agabansa suna masu gaidashi, ba tare da ya kula su ba ya wuce zuwa sashen sa ransa a matukar bace.

A sashen na mai Martaba kuwa Mama Fulani Mai Dakin Yamma ce zaune a wani kata faren falor yayin da Fauziyya ta kasance kwance a kusa da ita, ta daura kanta a saman cinyar Fulani Mai Dakin Yamma. Yayin da ta turo bakin ta a gaba sa'annan ta yatsina fuskar ta tana mai furta.

"Ammi!"

"Na'am Fauziyya!"

"Ammi dazu naje gun hamma Habeeb ina ta masa magana ya shareni daga karshe ma ya koroni ya rufa kofarsa, wai zan saka masa ciwon kai, yanzu fisabilillah Ammi! Ni zan saka masa ciwon kai? Dubeni fa kiga girma na, yau dinnna fa na cika shekara goma sha shida harda wata uku aiko na girma ko Ammi? "Ta karashe maganar tana ware 'yan yatsunta wai ala dole girga shekarun takeyi, wanda ke nuni da akwai kuruciya sosai a tattare da ita.

" hmm kinga auta ta kyalesa karki kara zuwa wajen sa kuma ballan tana ya sauke miki haushin"

"Haushin me Ammi?"

"Hmm barsa kawai Fauziyya yanzu muka fara nida shi inhar bazai bar wannan yarinyar ba"

"Lah Ammi badai aunty Jiddah ba? Kin gan ta kuwa ? Masha Allah she's so beuriful! "

"Rufemin baki Fauziyya! Ni ban wani tambeki kyaunta ba" Mama Fulani Mai Dakin Yamma ta fada tana yatsina fuska sai kace wacce taga ka shi.

"Allah Ammi tana da kyau!"

"Zan fa balla miki mari! Fauziyya! Oya tashin min a jiki"

"Am sory Ammi!"

"Tashi nace, zaki tashi ko sai ranki ya baci?"

"Fulani! Fulani! Fulani! "

Mai Martaba usman Umar Bin Ubaidullah ke fada yana shigo wa falon ransa a matukar bace.

"Lafiya dai kake kwalamin wannan kiran?"

Ta fada sanda take tashi tsaye itama tana jifansa da wulakantaccen kallo yayin da Fauziyya ke tsaye a gaban su ta kafesa da idanuwan ta, tana jiran mazai fito daga bakinsa kuma a wannan karon.

'Fulani! "

"Na am Mai Martaba!"

"Fulani! Allah ya yiwa Junaidiyya' yar wajen Waziri cikawa yanzun nan"

"To sai me Ranka shi dade? Ko kanaso kace min naje na dawo mata da numfashin tane? Bayan kuma kasan Allah ne mai kashewa da kuma rayawa" ta karashe maganar tana watsa masa harara....✍️

Like share and Comment pls🙏🙏

Update group link👇👇

: https://chat.whatsapp.com/GT9wHXDXR6kKEklUsof4Bv

Channel link👇👇

https://whatsapp.com/channel/0029VbApRz2LSmbf6rc13P3H

GARKUWAR AL'UMMA WRITTERS ASSOCIATION

(G.A.W.A)...✍️

_________________________ ____

Kungiya mai Amfani da Alkalaminta tare da Basirarta da kuma tinaninta Adomin ta Fadakarda AL'UMMAR ta.

___________________________

Mallakar Sarauniyar GARKUWAR AL'UMMA👑Queen Jiddah👑.

👑MASARAUTAR ZAZZAU👑

Magical love story💕

Story and written by

HAUWA'U MUSA YELDU.

Inkiya

Queen Jiddah👑

Babi Nice💫

Bismillahir Rahmanir Rahim.

Kamar yadda na fara rubuta wannan littafin lafiya, Allah ka bani ikon kammala shi lafiya.

Pg 08.

"Fulani! Ki yi rantsuwa da Ubangijin sammai da kassai bakwai, cewar babu hannunki a mutuwar Junaidiyya!"

" wallahi! Tallahi! Ina mai rantsuwa da Ubangijin al' arshi ni na sanya aka kasheta!'

"Inna lillahi wa inna ilaihir raji' un, Fulani! Why? Meyasa Fulani?" Ya fada yana girgiza kansa a dai dai lokacin da idanuwan sa suka rine suka yi jajir.

"Hmm lallai Mai Martaba! Ni kake tambaya meyasa? To bari na fada maka da manyan baki ta yanda zaka fahimta" ta fada tana daga kanta sama hannunta rike da kugu tana karka dashi.

"Ka dubeni da kyau mai Martaba nayi maka kama da sakar karun matan nan, wa' yanda ake hadawa da wata mace da sunan kishiya? To inaso kasani yanzu aka fara mutuwa a Masarautar nan muddim baka canza kudirin ka ba!"

"Fulani! Anya kuwa akwai digon imani a cikin wannan 'kahon zuciyar taki?

Mutuwa kike kira tsirarar ta ba tare da wani shakku ba?

Yanzu ke a ganin ki kinyi wa Junaidiyya da iyayen ta Adalci da wannan hukun cin da kika dauka?

Ko kina tinanin iyayen ta zasu yafe miki idan har suka samu labarin ke ce silar mutuwar Junaidiyya?"

"Junaidiyya? Junaidiyya fa kace?

Ai ba Junaidiyya ba kawai, ina so ka saka a zuciyar ka da kuma tinanin ka muddim ka sake neman wata ya mace a cikin gida da wajen Masarautar nan da sunan Aure to billahil Azim sunan ta Gawa!"

"Kai conki Fulani! Allah ya waddaran irin wannan zuciyar taki"

"Ba ka ga komai ba wallahi Mai Martaba! Kardai ka manta shekaru biyu da suka wuce 'yar Ciroma ta fara mutuwa wato Jamilah!

Sa'annan kuma maimunatu diyar Galadima!

Haka kuma murjanatu diyar sarkin nadi!

Yanzu kuma Junaidiyya diyar Waziri!

Saboda haka muzuba dani dakai dan halak ka fasa!

Idan har baza ka gaji ba? Nima ko bazan gaji ba!"

"Fulani kar ki bari son zuciya ya kaiki ga aikin dana sani"

"Kai dai zan gaya wa haka, Karka bari son zuciya ya kaika ga aikin dana sani"

"Dana sani Fulani? Ni me nayi na dana sani?"

"Me kayi ? Tambaya ma kake kenan?

Me na rageka dashi Ranka shi dade?

Me na rageka dashi a Masarautar nan?"

"Kar fa ka manta 'ya' ya maza har uku na haifa maka, Ni na haifi Habeeb sa'annan na haifi shamsu, ga kuma Rasheed! Sai kuma 'yar autar su Fauziyya gata nan tsaye a gaban ka, to me kuma ya rage wanda kake nema?"

"Ina so kasani koda ace ban haifi 'da namiji a Masarautar ba, to wallahi! Tallahi kai kayi kadan kace zaka hadani kishi da wata macen domin jinin dake yawo a jikina na mulki da sarauta ne gaba da baya, ba wai talauci da kaskanci ba!" Ta karashe maganar tana barin falon ranta a matukar bace.

Yayin da Fauziyya ke tsaye a gaban Mai Martaba tun lokacin da suka fara sa' in sar tasu hawaye na zuba a idanun ta, ba wai hawaye na takaicin abinda mahaifiyar ta ta aikata take yi ba, A a hawaye take yi na jin cewar wai mahaifin tane zai karawa Ammin ta kishiya.

Yayin da shi kuma mai Martaba ya kara so kusa da ita yana mai sanya hannun sa tare da janta ya sanya ta ajikin sa, yana mai shafa bayan ta.

"Mene ne Mama na?"

Ya furta yana jan numfashi tare da furzar da zazzafan huci daga bakinsa.

"Abbah !"

"Na'am Fauziyya!"

"Abbah! Da gaske kishiya zaka yiwa Amminmu?"

Ya rumtse idanun sa da sauri sa'annan ya bude su lokacin da suka fara sauya launi suna dawo wa jajir, saka makon furucin da yaji yana fito wa daga bakin karamar ' yar tasa sannan kuma yana mai kasa furta komai.

"Abbah! Nima bana son kishiya! Kuma bana son kayiwa Ammi, ka ji?"

Baid furta komai ba illa kawai kansa da ya daga bata alamun yaji.

"To shi kenan mama na kukan ya isa haka kinji"

ya fada da kyar dan son ya kwantar mata da hankali saka makon ganin yanda ta bi ta firgice.

Domin a bayyane yake karara cewar itama ta gaji bakar zuciyar a wurin mahaifiyar ta, ya fada a cikin zuciyar sa yana mai kara nazartar yanayin yarinyar.

"Sashen Habeeb"

Zaune yake a saman makeken gadon nasa yayin da hannunsa yake dafe da kansa, a gefe daya kuma kalaman abar kunar sa ne ke yi masa zarya a cikin zuciyar sa, yayin da dayan kefen kuma kalaman mahaifiyar sa ke sake birkita masa lissafi.

Kenan da gaske Jiddah take yi za'a raba shi da ita?

Meyasa beyi wannan tinanin ba tin farko?

Meyasa Amminsa ke so ta dakatar da farin cikin sa?

Da alama dai rayuwar sa na gab da kai karshe a duniyar nan!

Domin shi kansa ya sani idan babu Jiddah a kusa dashi to shi ba komai bane face Masarautar da bata da sarki a cikin ta sa'annan kuma bata da wani jagora!

"Kai lafiyar ka kuwa?"

Habeeb ya fada yana kallon kanin nasa Rasheed, saka makon ganin yanda ya banko kofa da karfi kamar zai karya ta, sa'annan ya fado cikin dakin babu ko sallama ballan tana neman iso.

"Hamma Habeeb! Albishirin ka?"

"Hmm Rasheed kenan, yanzu a ganin ka har akwai wani albishir da zaka nufa toni dashi Dan Allah?, ina a wannan halin ko kunya baka jiba?"

"Hamma Habeeb Allah mahaifin Jiddah ya baka auren ta!"

"Kai Rasheed da gaske?" Ya fada yana dirowa daga kan gadon.



"Eh wallahi yanzun nan Magatakarda ke gayamin dana hadu dashi ya fito daga fada! Allah sarki ashe harda rasuwa akayi,harma za ayi jana' iza idan gari ya waye tinda maraice tariga tayi"

"Subhanallah! Waya rasu kuma?"

"Hmm Junaidiyya' yar wurin Waziri" ya fada yana tabe bakinsa domin shin can dama auren nata da mahaifin su bai kwanta masa ba.

"Tau Allah ya jikanta da rahama ashe Allah baiyi ta shigo gidan nan amatsayin matar Abbah ba!"

"Uhm to Allah yasa hakan shine Alkhairy" Rasheed ya fada yana danna wayar sa.

"Tau naji Albishir kuma zan bayar da goro, sai ka bani waje zanyi waya da my princess"

"Oh oh Hamma nima fa auren nan zanyi gaskiya"

"Kai bana son shirme fita ka bani waje, duka duka shekarun naka guda nawa suke?"

"Tau na barka lafiya a gaisar min da Aunty na" ya fada yana murmushi tare da barin dakin ya ja kofa.

Habeeb kuma girgiza kansa kawai yayi tare da daukar waya yana kokarin lalubar numbar Gimbiyar sa.

®"Masarautar Gabas"

"Fasbeer Balmaty! Inna laha ma'as sabireen wayu hibbu nahum"

"Kiyi hakuri Balmaty! Allah yana tare da masu hakuri kuma yana son su" mai Martaba jibreen Jabbar bin Jafar ya fada hadi da daura tattausan hannun sa a fuskar ta yana mai share mata hawaye, sai dai bai ko kai ga jaye hannun sa ba wasu ruwan hawayen suka sake zubowa a fuskar ta ta.

"Me zanyi modibbo? Hankali na a matukar tashe yake, ji nake tamkar banyi wa Hussain adalci ba, wannan halittar a jikin sa take amma nice mai jin zafi da radadin a zuciya ta, modibbo ya zanyi? Shin kana ganin zan karya Alkawarin da na daukar wa mahalicci na, A domin samun lafiyar yarona? Kaina a matukar kulle yake ina bukatar daukin ka a wannan karon, wannan jarabawar tafin girma bazan iya cinye ta ba Modibbo!" Ta karashe maganar tana mai fashewa da matsanancin kuka.

"Balmaty!"

Mai Martaba ya fada yana mai jawota tare da sanya ta ajikin sa, ka na ya daura hannunsa a gadon bayan ta tare da fara dan bubbuga sa kadan, sa'annan ya cije gefen lebensa yana mai furzar da zazzafan huci daga bakinsa, hallau kuma idanuwansa a matukar jajir.

"Hakika shi addinin musulunci sauki ne dashi Balmaty! Domin kuwa kamar yadda yazo acikin hadisin manzon Allah (s.a.w) cewar"

"La 'da' ati li makhlukina fi ma'asiyatil khaliki ma' ana"

"Ba'a yiwa abokin halitta 'da'a a wurin sa'bawa mahalicci, Haka kuma sanin kan kine Allah baya yafe laifin da ke tsakanin bayin sa har sai idan bawan ne ya yafe da kansa"

"To kamar haka ne wannan ma domin a halin yanzu Warakar Hussain a hannun ki yake, meyasa baza kiyi tinanin dalilin da ya sanya Allah (s.w.a) ya zabeki a cikin dubbanin bayinsa sa'annan ya damka miki wannan ikon a hanninki ba? Karfa ki manta duk duniyar nan Allah bai yi halitta mai dumbun daraja kamar dan Adam ba, sa'annan ya saukar da aya acikin Al'qur ani mai girma yana mai fadar,

" Walakad karram na bani adama......"

"Cewar hakika lallai ni na karrama dan Adam, har zuwa karshen ayar ....✍️

Like share and comment pls🙏🙏

Domin neman Karin bayani ko kuma shiga cikin group dinmu sai a tintibi wannan layin...✍️

08145999600.

Update group link👇👇

: https://chat.whatsapp.com/GT9wHXDXR6kKEklUsof4Bv

Channel link👇👇

https://whatsapp.com/channel/0029VbApRz2LSmbf6rc13P3H

GARKUWAR AL'UMMA WRITTERS ASSOCIATION

(G.A W.A)...✍️

___________________________

Kungiya mai Amfani da Alkalaminta tare da Basirarta da kuma tinaninta Adomin ta Fadakarda AL'UMMAR ta.

___________________________

Mallakar Sarauniyar GARKUWAR AL'UMMA👑Queen Jiddah👑.

👑MASARAUTAR ZAZZAU👑

Magical love story💕

Story and written by

HAUWA'U MUSA YELDU.

Inkiya

Queen Jiddah👑

Baby Nice💫

Bismillahir Rahmanir Rahim.

Kamar yadda na fara rubuta wannan littafin lafiya, Allah ka bani ikon kammala shi lafiya.

Pg 09.

"Wacce ba akan komai take magana ba face dumbun daraja da kuma kima irin na dan Adam" ya karashe maganar yana mai dan numfasawa kadan sa'annan ya cigaba da fadin.

"Yanzu ya kike tinanin makomar ki zata kasan ce a wajen Ubangiji? idan har kika ki amfani da baiwar da ya baki har hakan ya zama sana diyyar salwantar rayuwar daya daga cikin bayinsa, kuma dan Adam"

Sai ta sami kanta da jin natsuwa game da zancen nasa,sa'annan ta dago da jajayen idanuwan ta da suka jike sharkaf da hawaye tana mai sanya su acikin nasa, yayin da shi kuma mai Martaba ya jinjina mata kansa alamun tabbaci akan zancen nasa.

"Kenan Modibbo zan iya warkar dashi yanzu ?" Ta fada tana kallon sa jikin ta a matukar sanyaye.

"Kwarai kuwa Balmaty! A matsayi na na mijinki ina mai umurtar ki daki warkar dashi yanzun nan"

"Taum Modibbo!" Tafa da tana nufar wajen da Hussain yake a daure da matukar sauri.

®"Masarautar Arewa"

Yayin da hannunta daya ke rike da wani bangare na benen, tana mai sakkowa a saman steps din fuskar ta dauke da mayalwacin murmushi, kana kuma ta mayarda duban ta ga yaran nata maza wa'yanda suka kasance twins wato Aman da Kabeer, tana mai sake fadada fara'ar fuskar ta, duka duka baza su wuce sa'annin Habeeb da Hussain ba wato kimanin shekara talatin da dan dauri kenan.

"Mommah! Barka da fitowa" suka fada a tare yayin da suke sake jin kaunar mahaifiyar tasu na ninkuwa a zukatansu.

"Yawwa Aman Da Kabeer! Ina fatan dai ba wata matsala?" Mama Fulani' yar Agadaz ta fada tana mai sake sakin wani murmushin.

"A a mommah! Ba wata matsala", Aman ya fada yana kallon ta.

" Eh mommah muna wani aiki ne to shine muka zo nan mudan duba wani abun" shima Kabeer din ya fada yana mai mayarda hankalin sa kan wata babbar laptop dake gaban sa.

"Tau shi kenan, Allah ya taimaka" ta fada sanda take zama asaman three seter wato kujerar zaman mutum uku, tare da daura kafar ta daya akan daya tana mai mayarda hankalin itama akan dalleliyar wayar ta,kirar iphone 15 promax.

"Mommah! Mommah!"

Jiddah ke fada tana sauko wa asaman down stair din falorn da matukar sauri, har harde kafafu take yi, yayin da hannun ta ke rike da wayarta fuskar nan tata dauke da mayalwacin murmushi kamar gonar auduga.

"Na'am Jiddah na" mommah ta fada tana kallon autar tata itama fuskar ta dauke da murmushi.

"Mommah! Ta fada tana sauke numfashi wani a saman wani, lokacin da ta zauna a kusa da Mama Fulani' yar Agadaz tana mai daura kanta a saman kafadar ta.

" Jiddah na! gayamin wane daddadan labari kika samo haka?"

"Hmm mommah kenan, wannan shirmammar me zata samo kuwa banda shirmen da ta saba, Kabeer ya fada yana tabe bakinsa sa'annan ya mayarda hankalin sa kan laptop din sa.

" Mommah! Kinji sa ko?"

"Rabu dashi gayamin mene ne?"

"Mommah! Yanzu Hamma na ya kirani kuma yamin Albishir wai Abeey ya tura wasika a Masarautar su cewar ya amince zai bayar da Aure na ga Hamma Habeeb!" Ta karashe maganar tana saka tafin hannun ta biyu tare da rufe fuskar ta,Sa'annan ta lafe a jikin mommah.

"Mommah kinsan Allah? Yarinyar nan bata da kunya" Aman ya fada yana rike bakin sa.

"To ka fadi kaima, da nine sai ace wani abun" Kabeer ya fada yana sake tabe bakinsa.

"Eh to kome zaku fadi ba ruwana, zanyi dai Aure na bar ku har kun fara furfura ba mata, Mommah kije ki nemo wa wa'Annan gorayen ma ta, kona nema masu a cikin hadimai na"

Ta karashe maganar tana zaro harshen ta waje tare da yi masu gwalo.

"Kinga dubi nan wajen, Kabeer ya fada sanda yake fitarda babbar yatsarsa manuniya a waje yana nuna kusa da ita, nan take sai ga Jibgegen kadangare ya bayyana a kusa da kafafunta yana mai kokarin hayewa jikin ta.

" wayyo Allah na Mommah " ta fada tana rumtse idanunta tare da fasa uban ihu tana kara rike momman.

Wanda yayi dai dai da shigo war mai Martaba Habibu Bin Ibraheem Khairullah cikin falon.

"Kai! Mene ne

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login