Showing 6001 words to 9000 words out of 14265 words

Chapter 3 - MASARAUTAR ZAZZAU TRUE BOOK HAUSA NOVEL BY HAUWAU MUSA YELDU.docx

27 Aug 2025

1561

mene ne ina jinki, just feel free ni mahaifiyar kice duk duniyar nan baki da kamata".

Da sauri ta fada jikin Mama Fulani' Yar Agadaz tana mai sa hannu ta rufe bakin ta, saka makon kukan da ya kubuce mata wanda take ta kokarin dannewa.

"Mommah!"

"Na' am ' ya ta!"

"Mommah zuciya ta!Ciwo take min, kirji na zafi, Numfashi na shudewa yake yi, Mommah! Mutuwa zanyi!"

"Subhanallah Jiddah! Daina fada kinji? Mutuwa ba zata rabani dake yanzu ba"

"Mommah! Hamma na! Habeeb dina!"

"Me ya samu Habeeb din? Ina ce dazu yabar Masarautar nan kuma lafiya lau"

"Mommah! Rabani za suyi dashi kuma ina son sa!"

"Ya isa haka mana Jiddah! Waye zai rabaku? Gayamin ina jinki"

"Mahaifiyar sa Mommah! Kuma ma da akwai wacce zata aura masa"

"Inji wa Jiddah? Bafa nason shirmen banza ina ce harda tsarabar kayaki yazo Masarautar nan, wanda kafin agama shigo dasu saida aka kwashe dakiku kusan dari! Kuma yace daga mahaifiyar sa"

" Eh Amma ba ita ta basa ba kawai fada yayi, na gani a Mafarki na kuma kinsan dai ban taba mafarki a gidan nan bai zama gaskiya ba! Lokacin da kike dauke da cikin Aboy da Akheel bani na gaya miki twins zaki haifa ba? Kuma maza, to wallahi wannan ma na gani kuma ba ma so daya ba."

"Ok naji yanzun dai ki saurare ni kiji, ni mahaifiyar ki Fulani' Yar Agadaz! Ina mai daukar miki alkawarin cewar saikin Auri Habeeb! Idan kuwa baki aure saba to ki dauka dama can ba shine mijin da aka rubuta miki a littafin ki na Lauhil Mahfuz ba! Kwanta kiyi bacci bara naje na binci ka."

"Tau Mommah! Sai da safe"

"Allah ya tashe mu lafiya" ta fada sanda take fita daga dakin tare da jan kofa.

Yayin da Gimbiya Jiddah! Take jin zuciyar ta wasai, domin tasan tinda har Mommah tace zata aikata to fa tabbas zata aikata din.

©"Masarautar Yamma"

"Wallahi Tallahi! Habeeb! Ka bani kunya da mamaki, ban taba saka ran samun haka daga wajenka ba, Zulaihat ! Fa? Yanzu Zulaihat! Zaka yiwa wannan wulakan cin? A yau Da ba nina haife ka ba to da babu a binda zai hana na kira ka da Kaskan tacce!".

Da sauri ya rumtse idanun sa saka makon yanda mummu nar kalmar Kaskan tacce ta ratsa kunnu wansa.

" A tunani na koda ace bana raye kai mai kare Martaba da kimar Zulaihat ne, A matsayin ta na ' ya ta! ' yar 'yar uwa ta, sai gashi kai da kanka kake zubar da mutuncin ta a gaban Hadimai da Dakarai har suna samun abin tsegumi duk saboda bare! Barer ma Wulakan tacciya! wata aba wai Jiddah! Kaji suna dan Allah, sai kace a gidan kaskan tattu!"

Dan sauri ya bude kwayar idanuwan sa wacce ya rufe ta tun lokacin da ta fara magana sai gashi kalmar Kaskan tatta! Ya sake yi masa amsa kuwwa a kunnu wa, ya sake dago wa da sauri yana mai jefa jajayen idanuwan sa wa' yanda suka rine da launin ja, a cikin na Mahaifiyar tasa.

Yayin da yake jin tsana da kiyayyar Zulaihat sun sake dabai baye ilahirin zuciyar sa...

"Lallai Habeeb ! Rainin harya kai can ina magana ka mayar dani kamar wata zararra wato nayi haukar tawa na gama kana sau raro ko?".

" Ammi ! Dan Allah kiyi hakuri, insha Allah zan ki yaye nan gaba" ya fada da kyar saka makon bala' in sarawar da kansa ke masa.

"Habeeb ! Wallahi kaji na rantse sai ka Auri Zulaihat! Muddin nina haife ka"

"Inna lillahi wa inna ilaihir raji' un" ya fada yana girgiza kansa idanun sa a rufe.

"Kwarai kuwa da gaske in har zaka auri waccan Ballagazar to kuwa ya zama dole ka hada su su duka ka Aura! Saboda gida bai koshi ba, ba za a kaiwa dawa ba".

" Ta shi ka bani wuri"

"Na barki lafiya ranki shi dade Allah ya huci zuciyar ki" ya fada sanda ya mike jiri na dibar sa ya bar dakin.

" Sha sha sha! Banza! Bakin Sakarai! Ta fada itama tana mike wa ta nufi bayan sashen ta....✍️

Update group link👇👇

https://chat.whatsapp.com/GT9wHXDXR6kKEklUsof4Bv

Channel link👇👇

https://whatsapp.com/channel/0029VbApRz2LSmbf6rc13P3H

GARKUWAR AL'UMMA WRITTERS ASSOCIATION

(G.A.W.A)...✍️

____________________________

Kungiya mai Amfani da Alkalaminta tare da Basirarta da kuma tinaninta Adomin ta Fadakarda AL'UMMAR ta.

___________________________

Mallakar Sarauniyar GARKUWAR AL'UMMA👑 Queen Jiddah👑

👑MASARAUTAR ZAZZAU👑

Magical love story💕

Story and written by

HAUWA'U MUSA YELDU.

Inkiya

Queen Jiddah👑

Baby Nice💫

Bismillahir Rahmanir Rahim.

Kamar yadda na fara rubuta wannan littafin lafiya, Allah ka bani ikon kammala shi lafiya.

Pg 06.

"Sha sha sha! Banza! Bakin sakarai!"

Ta fada itama tana mike wa tsaye ta nufi bayan sashen ta.

Da sauri ta rinka taka steps din benen bayan sashen nata harta kai can tsololuwa tana mai hayewa saman dakunan.

Yayin da take tsinkar duk wani abu dake gudana a Masarautar tare da kai da ko mowar da bayi da hadimai gamida da karai keyi.

Tana tsaye a saman dakunan, yayin da t juya tana mai fuskan tar Yamma.

"Gabbarjannara!" Ta fada a tsawace yayin da idanuwan ta suka rine suke yi jajir, tafin hannun ta da hagu kuwa yake a bude yana fuskantar Yamma.

Nan take Jibgegen DRA_GON! Ya bayyana a wurin yana mai lilo da hika hikansa a iska, sa' annan ya karkada shirgegiyar Jelarsa, dake can baya tare da juyarda katon kansa wanda ke dauke da munanan hakora, sa'annan sai ga Bakar wuta ta bayyana a cikin sa yana mai busa ta a ko wane gefe, tare da sake russunar da kansa a gaban Mama Fulani Mai Dakin Yamma!.

"GabbarJannara! Me ake ciki gameda aikin da na saka ka?"

Da sauri wannan Dra_Gon din yayi baya kadan sa'annan ya dawo a dai dai gabanta yana mai girgiza kansa alamar bai samo komai ba!

"Huzzannal Zag zaba!"

Ta fada tana mai daga hannun ta a sama tare da watsa masa azababben dafi a jikinsa!.

Ya fadi da sauri a kasa yana mai gurnani tare da mulkako a saka, sa'annan ya sake da gowa yana mai rissina wa a gaban ta.

"Na baka nan da yini uku 3! Ka tabbatar ka zomin da abinda nake son ji idan ba haka ba to Bakar Azaba ta tabbata a gareka!".

" Izhab Ilaina Bissur' a"

"Maza ka bacemin daga wurin nan" Ta fada tana mai nuna masa hanya.

Nan take ya bace bat kamar wani abu mai kama dashi bai taba wanzuwa a wurin ba.

Yayin da Mama Fulani Mai Dakin Yamma! Tayi saurin koma wa hanyar da ta fito da sauri sauri kamar dazu, ranta a matukar bace.

©"Masarautar Gabas"

"Balmaty dan Allah kiyi wani abu ni ina son Akheey dina, bana son na rasa shi".

Intisar ta fadi hakan cikin kuka sanda ta rusuna a kasa tana mai rike kafafun Balmaty.

Yayin da Hassan ke zirga zirga a dakin hanna yensa goye a bayansa ransa a matukar bace, saka makon ganin halinda dan uwansa Hussain ke ciki.

" Balmaty! "

"Na 'am Intisar!"

Ta fada tana furzar da iska abakin ta yayin da idanuwan ta suka kada suka yi jajir.

Dai dai lokacin da Hussain ya sake wata irin hargowa yana mai karasa rikidewa ya dawo Jibgegen Bijimin Zaki!.

Sa' annan ya tankwashe kafafunta na gaba yana mai tsayar da kafafunsa na baya tare da bude kafadun sa sa' annan ya barbaje gashin jikinsa yana hargowa da gurnani gamida kukan zakuna! Wanda ya sanya ilahirin dakin Amsawa, sa'annan kuma ya koma ya lafe a bango yana mai fitoda zara zaran hakoran bakinsa, ga wasu hawaye da yake fitarwa a idanun sa na zaki, saka makon daure sa da Balmaty tayi da igiyar tsafi.

"Balmaty wallahi idan baki masa magani ba zanje kusa dashi sai dai idan zai kashe ni ya kashe ni".....

Tasss kakeji ta dauke ta da lafiyayyen mari.

" wallahi Intisar bana son shashanci! Kuma karki sake na sake jin bakin ki anan wurin"...

"Uhm.. Hmm ni wallahi Balmaty bazan yarda ba idan wani abu ya sami Akheey dina!"..

" wai bakin nan naki bazai mutu bane Nikam?" Ta fada tana shirin sake zabga mata wani marin...

"A a Ranki shi dade, Allah ya huci zuciyar ki, kuruciya ke damunta don Allah ki mata afuwa" Jurmainatu ta fada tana mai sadda kanta kasa, wato hadima kuma babbar amintacciya a wurin Mama Fulani Balmaty.

Ba tare da ta furta komai ba ta juya ga Hussain tana mai sauke nannauyar ajiyar zuciya, ta tabbatar da cewar yana matukar shan wahala a wannan halittar da yake sai dai babu abinda zata iyayi masa akai.

"Ranki shi dade!"

"Na' am Jurmainatu!" Balmaty ta fada tana kallon ta.

"Ranki shi dade ina ganin akwai kamshin gaskiya a zancen Intisar!, me zai hana kiyi amfani da abinda kika gada awurin iyaye da kakanni wurin yiwa Yarima Hussain magani, a gani na kamar hakan zai fi da abarsa yanashan wannan wahalar".

" Hmm Jurmainatu! Kenan ko kadan bazan iya yiwa Hussain komai ba game da wannan al'amarin, sai dai ina so ki sani wannan halittar ajikinsa kawai take amma ni ke jin radadi da zafin"...

"Balmaty! Dan Allah ki taimaki rayuwar dan uwana, karki bari wannan mummunan abun ya illata shi" Hassan yafada yana hade hannayensa biyu waje daya alamun roko, yayin da idanuwan sa ke fitar da hawaye.

"A a Hassan bazan iya ba"

"Meyasa Balmaty? Meyasa bazaki warkar dashi ba? Bayan makarin wannan abun yana hannunki"

" Hmm Hassan! Bazan yiba domin na daukar wa mahalacci na Al'kawarin bazan sake saba masa ba"

"Balmaty yanzu warkar da Akheey Hussain din shine sabawa mahalicci?"

"Kwarai kuwa Intisar! Domin 'Karfin ikon da zanyi amfani dashi shine sabon ubangiji! Kunfi kowa sanin cewar Allah da manzon sa sunyi hani akan hakan, koshi Hussain din ba yanda zanyi dashi akan haka domin da ina da iko to wallahi daga yanzu bazai sake amfani da karfin iko ba, duk da cewar daga waje na ya gajeshi!".

" Inna lillahi wa inna ilaihir raji' un! Hussain! Abin har ya tsanan ta haka?" Mai Martaba yafa da yana mai nufar wurin Hussain din.

"A a modibbo! karka je kusa dashi saboda zai iya illata ka!"

"Illata ni fa kika ce Balmaty? Ko kin manta ni din Mahaifin sa ne?"

" A a modibbo! ba manta wa nayi ba, amma ina so kasani Ni kadai ce zan iya zuwa kusa dashi ba tare da ya iya yimin wani abun ba,koni kuwa saboda makarin abinda ke tare dashi a wajena yake shiyasa".

"A a ke kuwa Balmaty! Me yasa ki ka barsa yana ta shan wahala bayan makarin abinda ke jikin sa yana hannun ki?" Kyakkyawan dattijon yafada sanda yake rike da sandar sa ta sarauta kana kuma yana gyara tsayuwa sa, yayin da kafafun sa ke sanye da kyawawan tsadaddin takalmin sarauta, jikin sa kuwa Alkyabba ce baka yayin da kananan kayan dake kasan alkyabbar tasa suka kasance farare wato kalar takalmin sa.

"Na barsa yana shan wahala kamar ya? Modibbo!" Balmaty ta fada tana kallon sa.

"Haba Balmaty! Tin kan nazo ya kamata ace kin magance komai ai, ko kuwa?"

"Haba modibbo! Me kake cewa ne haka? Bayan a gaban na kone duk wani abu na tsafi dana gada daga wajen iyaye na! Tin a kasa mai tsarki, bayan doguwar nasihar da na sha tare da kuma sanin hukun Ubangiji akan duk wani mahaluki daya mutu yana mai aikata tsafi!, sannan yanzu kake cewa nayi hakan ko so kake na kasance cikin wa' yanda Azabar Ubangiji zata tabbata a garesu Ranar gobe kiyama?" Ta karashe maganar tana durkushe wa akan tiles din dakin, yayin da ta fashe da matsanancin kuka.

Mai Martaba Jibreen Jabbar bin Jafar! Ya sauke nannauyar ajiyar zuciya yana mai furzar da zazzafan iska daga bakin sa, sa'annan ya juwa izuwa saitin da Hassan yake, tsaye yake kansa soke a bangon dakin yayin da hannayen sa suka kasance goye a bayan sa, sai kuma Intisar wacce tayi lamo a jikin Jurmainatu tana tsiya yarda hawaye a idanun ta, ga kuma Hussain wanda ya kafe su da rinannun idanunsa wanda ga shi ya kasance zagaye da fuskar tasa, wanda hatta Mai Martaba saida ya tsorata da ganinsa a wannan halittar, ai kuwa da sauri ya sake juyowa wurin Balmaty yana mai soke guiwo winsa a kasa sa'annan ya furta.

®" Masarautar Arewa"

Tafiya Mama Fulani' yar Agadaz keyi, jikinta a matukar sanya ye yayin da kalaman Jiddah! Ke sake yimata amsa kuwwa a cikin kunnuwa.

Mommah! Mutuwa zanyi! Mommah! Akwai wacce zata aura masa! Mommah! Ina son sa!.

" Inna lillahi wa inna ilaihir raji' un" ta fada tana dafe kanta dai dai lokacin da ta isa bedroom din ta tana turo kofa, sa'annan ta murza key, tsakiyar dakin nata da take a tsaye mai kama da gari guda, ga ado na sarauta a kowane lungu da sakon dakin, da kuma kaya da aka zuba wanda daga gani kasan ba karamin kudi aka kashe a wajen ba, tako biyar zuwa shida tayi ta isa ga bangon dakin,sa'annan tasaka hannu tana mai yaye labulen wurin saiga kofa ta bayyana a wajen....✍️

Like share and Comment pls🙏sai daku mutanen Arziki much love😘😘🤸‍♂️💃

Update group link👇👇

https://chat.whatsapp.com/GT9wHXDXR6kKEklUsof4Bv

Channel link👇👇

https://whatsapp.com/channel/0029VbApRz2LSmbf6rc13P3H

GARKUWAR AL'UMMA WRITTERS ASSOCIATION

(G.A.W.A)...✍️

___________________________

Kungiya mai Amfani da Alkalaminta tare da Basirarta da kuma tinaninta Adomin ta Fadakarda AL'UMMAR ta.

____________________________

Mallakar Sarauniyar GARKUWAR AL'UMMA👑 Queen Jiddah👑

𤑍ASARAUTAR ZAZZAU👑

Magical love story💕

Story and written by

HAUWA'U MUSA YELDU.

Ikiya

Queen Jiddah👑

Baby Nice💫

Bismillahir Rahmanir Rahim.

Kamar yadda na fara rubuta wannan littafin lafiya, Allah ka bani ikon kammala shi lafiya.

Pg 07.

Ta saka kanta tana mai kutsawa cikin wurin,sai gashi ta bulle a cikin wata doguwar hanya wacce take dauke da matatta kalai a cikin ta, ta rinka taka steps din tana mai ratsa wurin sai gashi ta sake bullewa cikin wani jeji mai matukar girma, ga kuma manya manyan bishiyoyi sai kuma tsuntsaye wa'yanda ke shawagi a sama.

Da hanzari ta isa wurin wata bishiya mai shegen girma, ga kuma wani katon kogo a kasanta mai matukar zurfi, tayi saurin jan burki sanda ta karasa kusa da bishiyar kana ta furzar da iska daga bakin ta, sa'annan ta rumtse idanunta, ta sake bude su da sauri bayan sun sauya launi suna masu dawowa launin wannan bishiyar wato green! Ta daga labbanta dakyar lokacin da zuciyar ta ke tsanan ta bugawa, jikin ta kuwa yana famar yin rawa ta furta.

"Ya Hazal A'karabu IKhrij Ilaina Bissur'a"

"Ya ke wannan kunamar inaso ki fito a wurin nan da gaggawa"

Sannu a hankali bishiyar nan ta fara motsawa, yayin da reshunan ta suka rinka juyawa kana wannan kogon ya fara budewa yana mai kara girma da zurfi, sai ga wata Jibgegiyar kunama ta fito, yayin da launin jikinta ya kasance green wato launin kwayar idanun Mama Fulani' Yar Agadaz! Hallau kuma launin wannan bishiyar.

Yayin da take tafiya sannu a hankali kana duk inda ta taka sai tabar sawunta wanda ke dauke da halittar jikinta, kwayar idanuwan ta manya manya yayin da suka kasance guda uku 3 , wato bayan normally irin na sauran dabbobi tana da karin daya a saman goshinta ga kuma kafafu da hannayenta kusan guda Arba' in wanda suke da matukar girma da tsawo wanda banda dahin azaba babu abinda ke cikin su.

Haka kunamar ta iso kusada Fulani' yar Agadaz tana mai kwanta wa kasa wanwas kamar mushe ta gaida ita.

"A a Sadejinnabar! Ba wannan nake buka ta ba" Fulani' yar Agadaz ta fada tana kallon kunamar.

Yayin da kunamar ta juya baya tana tafiya sa'annan ta sake dawowa tana lankwasa har ta karaso gabanta, kana kuma ta 'kafeta ta idanuwan ta tana mai kifkif tasu, alamun me kike da bukata.

"So nake kije Masarautar Yamma! Ki binci komin wane hali Masarautar take ciki? Yaya goben ' ya ta zai kasance acikin wannan Masarautar?"

"Sadejinnabar! " ta sake ambatar sunan wannan kunamar tana kallon ta.

"Kinsa Duhun dare shike bayyanar da Hasken taurari! To ina so nasan su waye boyayyin taurarin wannan Masarauta! Shin mene ne gaskiyar zance akan Mafarkin da Jiddah tayi? Na baki nan da yini uku 3 ina so ki zomin da cikakkiyar amsar tambayoyin nan".

Ta karashe maganar tana mai juyawa ba tare da tajira cewar wannan kunamar ba.

Yayin da wannan kunamar tarinka tafiya sannu a hankali har ta isa wurin wannan katon kogon tana mai shige wa ciki, sa'annan wannan kogon ya koma yana mai rufewa ruf kamar wani abu mai kama da wannan kunamar bai taba fitowa daga cikin shi ba.

®" Masarautar Yamma "

A cikin fadar Mai Martaba "Usman Umar Bin Ubaidullah".

Yayin da shi Mai Martaban yake zaune a saman kujerar mulkinsa! Kana kuma da karai biyu a gefe da gefensa rike da fayafai suna masa fifita.

A gaban sa kuwa Galadima ne da Ciroma Sai wanbai zaune a gefen daman sa, yayin da Tafida da magatakarda, matawalle sai Sarkin zagi ke zaune a gefen hagun sa. Yayin da Magatakarda ke zaune a durkushe gaban Mai Martaba da wasika rike a hannunsa .

" Hattara dai Magatakarda!" Sarkin zagi yafada yana kallon Magatakarda.

"Mai Martaba ya baka izini da ka gaggauta bude wannan wasikar sa'annan ka karanta muna ita domin musan Abinda ta kunsa" Sarkin zagi ya sake furta hakan yana mai kallon Magatakarda.

Yayin da shi kuma Magatakarda ya gyara zaman sa yana mai sake Russuna wa a gaban Mai Martaba yafara karan ta wasikar Kamar Haka.

"Ni Mai Martaba Habibu Bin Ibraheem Khairullah! Wanda "Masarautar Arewa" ke karkashin mulki da kuma iko na! Ina mai yiwa Usman Umar Bin Ubaidullah! Wato Mai Martaban Masarautar Yamma! Albishir dace war na yarda kuma na am

inta game da wasikar da katuro min akan kulla alaka ta auratayya tsakanin 'ya' yanmu, saka makon nasaba da kuma tarbiyyarda yaron ka

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login