Showing 15001 words to 17850 words out of 17850 words
Chapter 6 - ZUCIYA DA KWANJI 3 by MAIMUNA I SANI BELI .pdf
ya kwashe ni,ina farkawa na kira
wayoyinsa na
ji su a kashe,kafin in tunanin wani abu
wannan'yar hargitsin ta shigo min da
hauka...."
Tana maganar wayarta a kunne amma har
yanzu
wayoyin a rufer,sai kawai ta sauke wayar
tana
ambaton innalillahi. Duk suka yi cirko cirko
kafin
fatima tsaiwar ta gagareta ta nemi guri ta
zauna
tana mayar da numfashi,sadiya ta shiga
kame
kamen. "Mun shiga uku! Shi kuwa abu turab
ina
ya tsaya?" Duk a kule suke da ita,saboda
haka
babu wanda ya bi ta kanta,cikin jimami
fatima ta
dubi hindatu ta ce. "Kuma da gidansu ya je
ba?
Hindatu ta girgiza kai a sanyaye. "Ko karfe
goma
zai kai a gidansu sai ya yi waya ya sanar
fadima,wallahi na tsorata a wannan lamari
da ran
dan adam ya koma tamkar kiyashi. Jikin
fatima
ya kara daukar bari,cikinta ya wani hargitse
tamakar za ta haife shi yanzu. Hindau ta
hada
tausayin fatima da kokarin ba za ta daina
na, sai
fatima ce cikin numfarfashi ta ce. "Ki kira
gidansu
ki ji, ko wani abun ya. Kai shi ya tsayar da
shi".
Cikin awa daya sai ga zauren ya kauraye
kowa a
gidan su abdullahi,hankali ya tashi
musamman
na malam da ya wuni da takaicin abdullahi
ya
saba umarni da ya yi masa na zuwa ya same
shi.
Dan haka ya shiga rudani matuka gaya, yake
kuma shakkar idan ba wani abu ya smai
abdullahi. A hanyarsa ta amsa kiransa ba.
Amma
duk da haka,haka ya dinga tausar su fatima
daya
bayan daya yana kwantanta musu hakuri da
yin
abin da ya kamata wato yin alwala a
durkusa
gaban Allah a kai masa kuka. Sadiya ce ma
ya
dora da tambayar ta. "Wani abu ya kara
hada ku
ne kafin ya fito?" Nan. Da nan ta ci laya
cikin
fargaba. "Wallahi malam ni tun jiyan ban
kara
sanya shi a idona ba". Cikin rarashi malam
ya ce.
"To shi ke nan kar ki damu,in Allah ya so zai
takaita,maza a tafi a sanar da Allah mu
jira
safiya". Suma shirin barin hindatu a dakin
ta,
hindatu na kuka tana komai amma ta bi
sadiya
da kulli. "Ki dauki kayan ta'addancin naki
ki tafi
da shi ba kin sami me kashe miki shi, sai ki
zauna ki yi gadin duniyar". Jikin sadiya a
sulabe
ta sunkuya ta dauki galan din kananzir
dinta tana
cewa. "Ni fa hindau bacin rai ne kawai ya
sani
fadar haka, amma da da gaske wutar na so
babbaka musu me zai kawo ni shawara da
ke?
Cikin kuka hindatu ta ce. "To Allah yana
kyale
azzalumao ne? Ai tunda kika furta za ki iya
sadiya, wa ya sani ma ko ke kika yi hayar
aka
sace shi...." Sadiya dai da ta ga babu sarki
sai
Allah sai ta wuce ta kyale hindatu,sai dai
maganar hindatu ta karshe ta jefa fatima
wani
tunanin daban mai alakar batan abdullahi
da
Alh,har ta je dakinta zuciyarta na bugawa
fat fat!
Shi ya sa ma da ta yi alwalar sallar ta gagare
ta,
ta fara karatun kur'ani hankalinta ya kasu
gidaje
barkatai. Karfe biyu da rabi ta mike ta nufi
dakin
hindatu ta kwankwasa mata kofa, sannan ta
tura
ta shiga ba tare da ta jira iso ba. Ta sami
hindatu
cikin sujjada, ta dan jima tana jiranta
ganin za ta
jima jiranta Kawai sai ta dauki wayarta da
ke
ajiye kan kujera tana cewa. "Wayarki zan
ara". Ta
juya ta fice zuwa nata dakin. Ta zauna cikin
jarumta da kokarin tsayar da bugun zuciya
ta
daddana lambobin wayar Alh da ke
kwanyarta.
1 · Like · React · Report · May 20, 2015
Amierah S-Man
Zuciya d kwanji 3
37
Wayar ta jima tana ringing har ta tsake.ba
ta
hakura ba ta sake jarrabawa, sai tana dab
da
katsewa,aka daga, mace mai alamun maye
ko
gigin bacci ta amsa da gurbaracciyar hausa.
"Wa
ke magana?" Numfashin fatima ya shiga
sassarfa
saboda haka bakinta ya hau rawa ta ce. "Ko
na
yi kuskuren ne? Alh sulaiman nake nema".
Matar
ta yi tsaki ta ce. "Dan ki yi masa me....
Karamar'yar iska?...." Da sauri fatima ta
cire
wayar daga kunnenta ta katshe,saboda haka
da
ta gama sallallaminta sai ta mayar kunnenta
da
zummar kwantar da murya matar ta hada ta
da
Alh. Ta ce mata. "Ki yi hakuri kanwarsa ce".
Sai
kuma ta ji muryar Alh na cewa. "Wace ce ke
magana?" Nan take wata jarumta ta
mamaye ko
ina a gabobinta na fili da na boye,ta yi
gwauro
numfashi cikin dacin rai ta ce. "Fatima ce"
Nan
da nan ya diririce ya shiga sambatu. "Zara'u
barka da dare... Ya ya kike.... Wallahi......
Wallahi
Allah a wajen mitin muke.... Abokiyar. Aiki
....
Sakatariya ta ce mary ta amsa wayar...."
Fadima
ta yi gyaran murya ta tare shi muryarta a
tsaurare. "Eh babu laifi ai, wai an yiwa'yan
biki
duka har an karya uwar amarya". Ya kuma
debi
rawar murya,yana dariya. "To fatima
wannan
hausar ai sai ki bidiye ni... Ya ya kike dan
Allah?"
Ta sauke numfashin takaici ta nisa ta ce.
"Lafiya
kalau amma ta mahaukaci, nima nawa
abokin aiki
ne aka samu matsala, Abdullahi ne tunda ya
fita
da safe bai shigo gida ba shi yasa na kira ka
in ji
ko kana da masaniya a kan bacewar sa?" Ya
yi
kasake yanayin muryarta ne yasa ya rasa
wanda
zai zaba ya gasa wajen gamsar da ita, da
gaskiya
ne ko da karya? Ya kamata ya fara sanin
inda ta
dosa kafin ya bayyana kansa. "Ban gane fa
abin
da kike nufi ba fadima, aiki kika fara ban
sani ba,
kuma me zai hadani da abokin aikinki cikin
wannan daren fadima? Amma duk da haka
na yi
mruna da kiran da kika yi min, barki da
wayar
ne?" Ta yi tsaki cikin sikewa. "Dan kana tare
da
taka abokiyar aikin ne a yanzu kake
mantawa da
nawa abokin aikin,gwari gwari Abdullahi ne
ba a
gani ba tun da safe, tambaya daya na yi
maka da
nake son amsarta. Shin kana da masaniya a
kan
batan abdullahi ko babu? Kai tsaye ya amsa.
"Ai
fatima na ji ne kamar kina maganar fada
fada,
yanzu don Allah batan Abdullahi ba abin
dariayarmu bane? Ya ya kike son mayar da
dariyarmu kuka? "Ai ba na son yin kuka ko
dariya
a duhu,ya ya zan yi kuka ko dariya cikin
abin da
ban waye ba? Ka fada min inda hannunka a
batan abdullahi sai in yi dariyar da za ta
dore ko
kuma in saka rai watau rasa aikin wannan ta
kusa da kai ya kusa kamawa,dan na ga
alama
kai kadai kake so ka yi ta tara abokan aiki
nawa
abokin aikin ya tsuke maka ido". Da wannan
maganar tata ya fahimci inda ta dosa,
fatima ba
ta bayansa Abdullahi ya yi nasara a
zuciyarta.
Saboda haka yanzu hatsari ne ya ce mata shi
ya
sa aka farauce abdullahi duk da akwai kila
wakalan ta goyi bayansa kop kuma ta kware
masa bayan. Wannan ya sa ya shiga magana
cikin muryar rarashi kuma rarrabe. "Bani
bane...
Sam ba. Ni bane... Yanzu fatima ba ki yarda
cewa matar nan abokiyar aikina ba ce....?
Na ga
kamar kina yi mana wani zargi daban......."
Ta
tare shi, "to Allah ya bamu alkairi,kar ka ce
za ka
kira wannan lambar domin ta kanwar innata
ce.
Shima ya yi saurin tare numfashinta. "Au
fatima
dama dan kawai ki tambaye ni abdullahi
kika kira
ni?" Wani takaici ya kara tokare mata
makoshi,ta
hadiye da kyar ta ce. "Ba kawai ba ne, idan
dai
tare da hankali nake tafiya bai kyauta na
kiraka
cikin daren nan ba alhalin na san kana tare
da
abokan aiki. Mu kwana lafiya. Ta kashe
wayar,karon farko kuma ta ji ya kamata ta
yi
kukan rashin abdullahi da rashin sanin
takamaiman halin da yake ciki. Ta fara
kukan
sosai,da alama hadawa take da na dan
cikinta
tana yi musu tare. Saboda yadda ta ke
jin,in Allah
ya karbi ran abdullahi ba ta tsammanin
akwai
wanda zai yi nasara sama da abin da ke
cikinta.
Wasu kalamansa na daren jiya suka dinga
dawowa zuciyarta suna kuma ba ta hawayen
da
basu ba ta a jiyan ba. "Idan kuma nine ba
na tare
da alkairi duk taurin kaina sai ki ga ya
kashe miki
ni ki huta....." Wannan kalmar tasa ta fi
komai
tsaya mata a rai. ***************
***************
************ Sati guda ke nan babu
abdullahi
babu labarin sa.tun hankalin na tashi har
fukafukansu suka zube kasa. Suka daina
yunkurin
da kashin kai kadai. Gidan ya koma kamar
wani
gidan makoki saboda dangi da 'yan zuwa
jaje,
haka nan matan gidan. Duk sun jeme kamar
masu takabar gaske,musamman fatima da
dawuwa ta hade mata da rauni, dama akwai
kaya
kayar mutane domin kannen momi. Tun
samun
labarin batan abdullahi da suka zo mata
jaje sai
suka zauna tare da ita. Duk wata kafa ta
cigiya
da gurin zaton samun abdullahi a mace ko a
raye
babu inda dangi da abokan arziki abdullahi
basu
saka kafa ba, amma babu abdullahi saboda
haka
aka dage da addu'a kurum Tun kwana hudu
da
boye abdullahi Allaj ya so sanin matsayin
fatina a
batan Abdullahi ko a shirin sake rayuwarsu
tare.
A katafaren falonsa yana tsaye rike da
tambula
yana kurbar lemo,kafarsa kan tebur ya dubi
laila
da ke zaune a kujera tana danne danne a
wayarta
ya ajiye tambulan sannan ya dan bugi
teburin ya
ce. "Laila na budewa abdullahi kwanjina ya
kama
ta ni san matsayin fatima cikin abin da na
yi.
Laila ba a son ranta ta ajiye wayar ta ba, ta
dago
ta dube shi,dan haka ta kasa cewa komai. Ya
dan
ware ido ya ce. "Ba ki ji batun da na yi ba
ko? Ta
yi saurin gyara zama tana gyada kai. "Ina
tunanin
ta hanyar da za a sanar mata ne" Ya tare
ta cikin
daurer gira. "Ai ke ya kamata ki je ki sanar
mata,
Amma sai ki yi hakan cikin dabara,sai kin
fara
gane inda ta sanya gaba,dan ni kam na
fara
sanya shakku a kan yadda nake mata kallon
ta
hade kai da abdullahi sun ci amanata". Laila
ta
muskuta tana hadiye mugun takaici da ya
dami
ranta,fuskarta kuma na kokarin basarwa ta
ce.
"Ka manta fatima ta yanke amintar da ke
tsanainmu? Ina ganin da kyar za ta yarda
ta
saurare ni". Ya kara daure fuska yana
kallonta.
"Me yasa kika sake hakan ta fari? Kamar
fa ina
tufka ne kina warwarewa, ko me. Zai shiga
tsakaninku ai sai ki hadiye shi, mai son dan
tsuntsu ba shi yake binsa da jifa ba. Ga shi
kuma
ina biyanki ba aikin banza kike min ba".
Laila sai
ta rasa abin cewa, amma dan ta fara yanke
kauna da al'amarin wannan kidahumin
mutumin
da yake kasa damuwa da abin da ya kamata
a
damu a dau mataki. Kamar ya san abin da
take
rayawa a ranta,ya zage ya ci gaba da
masifa.
"Tun rannan kike isa ta da lissafin
laifuffukanta,
ta bi abdullahi tana tsoron abdullahi, tana
da
ciki... Duk kin bi kin cika kwakwalwata da
lissafin
masifa iri iri.... Kuma ina shuka kina
tonewa. To
yanzu sai ki gaya min abin da za a yi in ba a
je
an sanar mata ba" Laila ta jima kasake
kafin ta
kada kai ta ce. "Shi ke nan yau zan je da
yamma.
Sai dai tayar motata na da matsala, don sai
an
duna min ita mts! Na fi son ma canja
wata". Ba
tare da ya canja fuska ba ya zira hannu
aljihu ya
debo kudi babu ko kirga ya mika mata. Ya sa
kai
ya wuce,ita kuma ya barta da binsa da kallo
har
ya bace, sannan ta yi kwafa murya kasa
kasa ta
ce. "Matsiyaci kawai babban na
Like · React · Report · May 20, 2015
Amierah S-Man
Zuciya d kwanji 3
38
******************************
*********** Tun
ranar litinin din da abdullahi suka yi da
sagiru za
a je kotu shigar da karar barazanar da
abdullahi
ke samu daga alh,da kuma shigar masa gida
da
alh ya yi sau biyu. Tun safiyar litinin din
sagiru ke
zuba ido ganin abdullahi amma shiru, ya bi
wayarsa nan ma babu labari. Har yamma
yana
jiransa bai ganshi ba, kuma babi shi a waya.
Bai
taba kawo wani abu mara dadi ba, ayyuka
kuma
suka kwashe masa hankali bai kara tunawa
ba
sai da abdullahi ya yi kwana goma a bace.
Ranar
suka hadu da alh a traffi light, kawai sai ya
dauke kan motarsa ya nufi gidan abdullahi.
A can
kuma ya tara da bakin labari. Saboda haka
ya
dawo gida hankali a tashe. Da zurfafa
tunanin
abin yi. ******************************
**********
Sai da abdullahi ya yi sati uku a kulle sannan
a
ka san inda yake, da taimakon sagir wanda
ya
sako yayyen abdullahi biyu cikin aikin da
tuntubar
juna yadda lamuran ke tafiya. Sai dai a
zahiri ya
boye musu maganar Alh, dan ya dade da
sanin
abdullahi cikin ririta maganar nan ba ya so
asiri
ya fasu, saboda haka a dabarance ya
gudanar da
binciken. ******************************
************ Karo na biyar da kuwa ya je
gidan yi
musu jaje ya nemi kebewa da fatima daga
idon
su momi da yaran da suka je da su,
fuskarsa a
daure ya dubi fatima ya ce. "Fatima kun
hada
baki ke da alh kun salwantar da abdullahi
ko?"
Fatima ta zaro ido cikin kara tsananta
tashin
hankali ta fara girgiza kai lokacin da hawaye
ya
fara fita a idonta, bakinta na rawa ta debo
kare
kanta amma sai ya tare ta cikin fusji. "Babu
abin
da za ki fada min in yarda fadima,a tsahon
rayuwarki gurina babu irin tarbiyar arzikin
da ban
baki ba, ke kuma kin jure tsawon rayuwar
take
kina aiwatar da munannan halayen da kika
zabawar kanki. Na fahimce ki baki tattare
da
komai sai jin kai da daukar kowa ba a bakin
komai ba. Ba ke kika zabi auren alh ba tun
farko
tabbas na sani,kuma haka kika rayi da alh
shekaru goma kina nuna adawarki da auren
dole
da na yi miki wanda Allah ne shaidata. Ba ki
da
niyyar sharri a cikin hada ki aure da Alh
abin da
ya fi daure min kai shi ne, Allah ya cika miki
burinki Alh ya sake ki,mune na farkon taya
ki
murna saboda dalilai biyu. Fargabar yadda
zan
tarar da ubangijina idan na cutar da ke a
cikin
aura miki wanda ranki ba ya so, sannan da
jin
takaicin yadda Alh ya yi miki sakin
wulakanci,na
kuma bi ba'asi ya fada min abin da ransa ke
so.
Wai amma daga baya dan bani na haife ki
ba,
kuma dan ki ci gaba da tabbatar min ke
kishiyar
abin da nake so kike so sai kika dawo Ah kike
so.
Kuma dan watsewa lalacewa da yiwa kai
tanadin
karkon kifi,sai kika hada son da neman
kangarewa ubangijinki, har da hawa turbar
kisa
ko ma kun kashe din... Dan na tabbatar in
na
rantse ba zan yi kaffara ba da hannunku
cikin
batan abdullahi...." ....Yanzu ta sami tare
shi
cikin ballewa da kuka... "Kawu wallahi ko
akuya
ba za a iya hada kai dani a kashe ba bare
abdullahi, kawu duk sharrance sharrancen
mutane. Ne ban ga abin da na kasa a cikin
gidan
nan ba da ake min kallon ba aure na shigo
cikinsa ba Yadda duk abdullahi ya so haka
yake
juya ni,ku san shekarata daya a gidan nan
in
kirga fita ta za ai da kayr za a hada
goma,shi ma
ga kafarsa ga tawa. Wayoyina sun lalace ko
da
kun bani da hanyar sadarewa kawu ina zann
ga
Alh har mu shirya wannan danyen aikin? Na
rantse maka da Allah babu ruwana". Kawu
ya
mike ba tare da fuskarsa ta nuna gamsuwa
ba
yana cewa. "Na rantse miki da Allah fadima
babu
abin da za ki fada min na yarda da ke,
kuma ki
bude kunne ki ji ni da kyau. In da hannunku
cikin
batan abdullahi ki gagauta yin motsi dan ya
samu'yanci saboda bata lokacinki kawai za ki
yi,
ni dai ni zan daura miki aure to wallahi ba
zan
aura miki Alh ba. Kuma ko abdullahi ya
bayyana
in kika so aurensa,to sai dai ki nemi wani
uban
bani ba, wannan alkawari ne na daukarwa
kaina
har na rubuta wasiyyarsa a aiwatar da shi
bayan
mutuwa ta,wai ma idan za ku shirya na bar
duniya nima..." Bai saurari uzurinta ba ya
mike
ya bar mata gurin,ya barta da wani
matsanancin
kuka cike da ciwon zuciya. Bakin ciki da
fargabar
da take ji a halin yanzu ba ta taba cin karo
da
irinta a duniyarta ba, ta taka sahun barawo
saboda haka babu wanda zai yarda ya yi
mata
uzuri. Amma duk da haka. Ina za ta kai
zargin
kisan kai? Kisan kan ma na mijina,kuma
suna
danta ko yarta? Wai ma da me za ta ji? Ta
yi
kuka kamar za ta mutu har sai da ta
tabbatar
dole ta taimaki kanta da abin da ke
cikinta,tunda
basu da me taimako babu da me saurarensu
bare
mai yi musu uzuri. Alhamdulillahi! A nan zan
dakata,sai mun hadu a ZUCIYA DA KWANJ 4...... Amierah S Man Mai COPY N PASTE
Compelled by hauwee jidderh abdulkadir AKA mss jidderh