Showing 9001 words to 12000 words out of 17850 words
Chapter 4 - ZUCIYA DA KWANJI 3 by MAIMUNA I SANI BELI .pdf
shi a nutse ta ce. "Wannan
fa ba
wani abin tashin hankali bane na fada maka
ne
dan ka tsawatar masa,na ga ita kanta
fadima ba
ta son ziyarar tasa. Rannan da ya zo tare
da
matarsa wallahi kasa zaman dakin ta yi sai a
bayan na same ta ta rafka tagumi. Yau kuwa
kamar tana da masaniyar shine kofarta a
rufe ya
yi bugum duniyar nan ta ki budewa. Abin da
ya
kara tsoratani shine, wasu basawa da suke
tako
masa baya, abun babu kyau gani
wallahi,kamar a
film ko a garin arna. Abdullahi ya sauke
wata
gwauruwar ajiyar zuciya wadda ba ta rage
masa
ko dingo bakin ciki ba, amma dai ta soke
masa
kashio saba'in na kullacin fadima. Ya dinga
gyada kai wanda ya taimaka masa hadiye
sassarfar numfashinsa.ya ce. "Kin tabbatar
sau
biyu ya taba zuwa? "Gaskiya sau biyun na ga
zuwan sa,ina kuma kara karfafa maka
gwiwar
cewa ba da goyon bayan fatima yake zuwan
ba,na ga hakan a idonta". Ya katse ta. "Ya
ya aka
yi kika san ba da son ranta ya zo ba?" Ta
ce,"yau
dai na fada maka ta ki bude kofar ta,ranar
da ya
fara zuwa kuma tsakiyar rana na tarar da
ita a
bayan nake mata maganar ya ya ta yi baki
za ta
barsu ta dawo nan? Sai ta ce min ai ta
sallame
su mijin kawarta ne basu saba ba kawar ta
akwo
mata shi nan, dan haka ta fito ta barsu...."
Nan
ma ya kuma tare ta. "Kin taba ganin kawar
tata?"
Kai tsaye ta amsa. "Wannan lailan ce wadda
ta
same ni a dakin fatima kwanaki da na je
duba
ta,nima a nan na santa" Zumbur abdullahi
ya
mike cikin fushi da barin jiki kamar wanda
ake
kadawa gangi,hindatu kanta sai da ta
tsorata ta
taso tana rike shia gigice. "Abu turab ka
shiga
cikin hankalinka,wallahi ba na tsammanin
yarinyar
nan tana da laifi,iyakar iyarwarta ta nuna
ba ta
so, kar ka je ka yi.
Like · React · Report · May 19, 2015
Amierah S-Man
Zuciya d kwanji 3
Mata abin da bai kamata ba Abu turab". Ya
yi
suguri yana kallon ta cikin rashin hayyaci, a
sanyaye ya ce. "Cewa aka yi miki zan je in
rufe ta
da duka?" Ta yi saurin girgiza kai. "Ka yi
fadan
da ya wuce hankali ne bai dace ba,duk da
ka turje
min ba ta da ciki,amma ba a son masu ciki
da
bacin rai kar ka je ka sanya jininta ya hau
duk
mu shiga wani hali. Ya kalli hannunsa ta
rirrike
sannan ya dagha kai ya dube ta ya ce.
"Fishina
na me zuwa gurinta ne,ita iyakacin in yi
mata
fadan kin sanar dani zuwansa na farko. Ni
da za
ki yi min wani taimako ma da kin birgeni
wallahi,duk ranar da kika ga wannan
yarinyar laila
a gidan nan,to ki saurain buga min waya ki
sanar
dani". Ta saki hannunsa tana murmushi ba
tare
da ta tanka ba. Ya wuce ko jakarsa bai
daika ba
ya nufi dakin fatima". Kila ta yi zaton alh
ne dan
Abdullahi ya jima yana kwankwasa kofar sao
da
ya hada da kiran sunanta sannan ta taso ta
bude. Fuskarsa babu annuri ya dube ta sama
da
kasantana sanye da doguwar rigar shadda
ruwan
hoda,kanta sanye da makalalleb fari hijab
mai
duwatsu,fuskarya da idanunta a kode suke
alamr
ku yanzu ciki kuka take. Da ta dubu fuskarsa
da
irin haushin fushin fuskar sai ta ji kamar ta
zube
a wajen saboda tsabar tsorata.ba wai na
zargin
ya san Alh ya zo gidanta ba sai na rashin
samun
damar kudurinta a yanzu. Bayan fitar Alh
babu
irin taunanin da ba ta yi ba, a ciki har da
yanke
shawarar snar da abdullahi da bakinta
gudun abin
da ka iya zuwa ya dawo. Ta tsani zargi a
rayuwarta, musamman mummuna irin
wannan.
Idan kuma Alh ya ci gaba da fado mata
gida,to
sunanta yana dab da baci, kuma ya dore da
baci
har abada,domin ubangiji ne kawai zai
wanke ta.
A karshe kuna kila ya yi uku babu abdullahi
ya
sake ta, kawu ya hana ta auren Alh,kila ma
a
rasa mai auren ta ,ga kuma mutuncinta ya
kwaranye. To amma ta ina za ta sanar da
Abdullahi? Me za ta ce masa? Duk abin da
za ta
ce dai ya hada kafada da cewa, ta hakura
za ta
zauna da shi abin da kuma take kyashin
fada ke
nan. To yanzu da ya shigo fuskarsa a
murtuke ta
ina ta ga sararin sanar masa? Sai kawai ta
juya
a sanyaye jiri na kwasarta ta nemi kujera
da
zauna ta rafka tagumi hannu biyu kanta a
kasa.
Ya karasa tsakiyar falon cikin zafin rai ya
dora
kafa daya kan tebur ya dafe da gwiwar
hannu
yana kare mata kallo. Da kakkausar murya
ya ce.
"Fatima kkin bani mamaki wallahi, duk inda
nake
hangen karantar ki ashe kin kere nan" Ta
dago
cikin tashin hankali iri iri ta dube shi,ita ma
jikinta
ya dauki bari,dan ta san amsar daya ce ya
san
Alh ya zo gidansa. Bakinta ya dinga rawa
tana
dubansa a raunane. "Abdul.... Abdul..... Me
na
yi?" Sai ga hawaye sharr! Ya kara gintse
fuska ya
ce. "Wato da na hanaki fita yau shine kika yi
ma
sa waya ya zo gida ya same ki? Sai gata a
tsaye,kuma da alam ba ta cikin azancinta
sosai.
Hannunta sai karkarwa yake ta koma
hannunsa
ta ja shi kujera tana cewa. "Ka zauna mu yi
magana a zaune ,ina na ce maka za ni,wa
na kira
a waya? Ina na ga wayar da zan kira?" Ya
zauna
a kujera ita kuma ta zauna a gabansa tana
rike
da kafafuwansa cikin. Hawaye tana kallon sa
kai
tsaye. Barin jikin da take ne ya sa ma ya
rasa ta
inda zai kwaso jidalin da ya shirya mata,
yau
fatima ce da zuwa ta rike shi kuma a lokacin
da
yake tuhumarta da laifi? Abin da ya ji a
ransa
tausayi ne ko so, abin da kawai ya sani shine
ba
zai hana shi ya tuhume ta in ya ga ba dai
dai ba.
Ya kara tara gira ya ce. "Kar ki raina min
wayo
fadima, na ga fitar Alh daga gidan nan,
wannan
katon abu ne da hankali ba zai dauka ba a
garin
maguzuwa muke da wannan zai zama ado?
Na
rantse miki da Allah ba zan yarda ba. Ta
runtse
ido tare da sauke ajiyar zuciya kamar za ta
shide,hawaye sai jerangiya kafar abdullahi
tana
cewa. "Ka dage sai ka kirkiro min laifi ko
abdul?
Tun safe kake nema na da jidali shine yanzu
za
ka zo min da wannan maganar.... Wai me ya
sa
baka son zaman lafiya don Allah?" Lkawai
sai ya
ture ta ya mike yana bala'I "Eh kwarai kina
neman ki binne ni da yaudara ko? Ina miki
maganar kan kawo min kato gida kina min
maganar in zauna in shanye baki ki dore da
shararu shine zaman lafiya..... Ba ki da
hankali
wallahi sai na yi maganin ku idan shine
shugaban
kasa a kasar nan wallahi na rantse sai na bi
hakki keta min hakkin da ya yi...." Ya sa kai
zai
fice yana ta faman bala'I,ta biyo shi tama
faman
shan gabansa. "To ka saurare ni
mana....yanzu
don Allah ba za ka tsaya ka ji ta bakina ba?
Abdul idan ka yi abin da ya bata min suna
kai
mai zai jibince ka wallahi duk ysiya doke a ce
matarka,kuma uwar danka,ko na bar duniya
za
aiya kallon ka kai da danka da abin da aks
zargina da shi... Ka daure ka saurare ni don
Allah..." Da a ce babu ciwon shigowar Alh
gidansa dole ne ma maganganun fatima su
faranta masa rai,amma da yake a
dugunzume
hankalinsa yake,kawai sai ya fincike ta a
jikinsa
ya wuce,yana jiyota ta rushe da wani
matsanancin kuka. Ko dakinsa bai kalla ba
ya
kuma ficewa ya fizge mota sai gidan
abokinsa
sagiru. Sagiru na ganinsa haka ya san lallai
babu
lafiya,suna zama ya fara tambayarsa. "Ina
fatan
lafiya? Ya dago a birkice. "Dole mu nemi
shigar
da karar nan gobe sagiru, turbar da Alh ya
canja
hakuri na ba zai taba iya lamunta ba". A
sanyaye
sagiru ya ce.
1 · Like · React · Report · May 19, 2015
Amierah S-Man
Zuciya d kwanji 3
"Ikon Allah me ya faru?" Abdullahi ya yi
kwafa ya
ce,"bariki ya shirya mayar min da
gida,ranan ya je
yau ma ya koma da yake shi tuni an zare
masa
hankali. Cike da mamaki sagiru ya ce.
"Subhanallahi! To me yake zuwa yi, kuma me
ne
ne alakarsa da wadda yake zuwa wajenta?
Abin
da ya kamata mu fara sani ke nan". Cikin
jimamai da rauni Abdullahi ya kwashe masa
labari.sagiru ya dade cikin tunani kafin ya
sami
bakin magana. "Kana ganin babu yardar
fatima
yake zuwa?" Kai tsaye Abudllahi ya amsa "
Ba
zan iya tabbatarwa ba ,amma dai ina da
mafi
rinjayen zan yi hukunci shine babu
yardarta,na
san ta da kyau, tana da gudun abin kunya"
Sagiru
ya dinga gyada kai tsawon wani lokaci
sannan ya
nisa ya ce. "Ba wani abu ne yasa nake jan
kafa a
kai maganar nan kotu ba, sai ta baka damar
ka
sasanta da matarka kar ayi badi babu rai ta
kware maka baya a kotu, amma tunda abin
ya zo
da haka ranar litinin zan kai batun kotu..."
Abdullahi ya tare shi. "Litinin tayi min nisa
sagiru,akwai kwana uku a tsakanin wanda
Alh zai
iya waiwayo kafa ya zo min gida". Sagiru ya
ce.
"To haka dai zamu hakura abdullahi,ka ga
ai gobe
ma jama'a ce,kawai sai ka kafa gadi a
gidan
babu shiga babu fita,da za ka dau shawarata
ma
sai ka sassauta mata nuna damuwarka,dan
kar
ka samar da gurbin da za ta ji babu matsala
dan
ta rabu da kai. Suka dan taba hira duk a
kan
batun sannan suka rabu. Yana komawa gida
a
dakinsa ya tarar da sadiya zaune da
katuwar jaka
a gabanta,sanye kuma da hijabi da karamar
jaka
purse a hannunta,fuskarta kunshe da jadali
iri iri.
Ya yi fuska yana tsaki kasa kasa da ji a
ransa
duk wannan numfashin da take yi na dadi
ne,
babu wanda a neman ta rasa,kuma babu
wanda
yake neman ta,illa tsabar samun dama. Ya
dauke
kai ya wuce daki bayan ya yi mata sallama a
ciki,yana shiga dakin sai gata a bayansa.
Suka yi
cirko cirko suna kallon juna fuska ba annuri.
Ya
motsa baki da kyar ya ce. "Lafiya?" A
tunzure ta
ce. "Ban sani ba! Wallahi yau ba ka isa ba
sai ka
bani takarda ta a tafi gidanmu, bana sonla
bana
kaunar zama da kai, in kuma na zauna da
kai din
Allah ya tsine min". "Ai ba sai kin yi ta
maimaitawa ba sadiya, ai ban taba ganin me
kakan tsinuwar ALlah irin ki ba. To an ki a
baki
takardar sai ki yi abin da za ki yi,in kuma
kin
tsayar da wanda za ku haifi taron duniyar
nan da
sai ya karbar miki". "Wallahi ba ka isa ba,ko
me
za ka fada ka fada amma wallahi yau sai ka
sake
ni,na fada din muguntarka sai ka sake ni na
je na
auri mai sona,kuma wanda zan haihu da
shi....."
Haba,ya kara zuwa wuya,dan kalmar ta auri
wanin nan ba karamin ciwo take masa a zuci
ba.ya sa hanun ya doke hannunta dake rike
da
kwalarsa ya yi baya, sannan ya dube ta.
Lallai
jikinki ke kaikayi,kin san Allah na rantse
idan kika
kuma cin kwalata sai na fasa miki jiki,kuma
an ki
a sake ki,ki kai ni kara na fada miki in na ji
wuya
sai in sake ki. Ko ban ba ki wannan shawarar
ba
tuni? Samun'ya'ya ai ba a yi daha kwance
kai ni
kotu da ki yi hannun jari ne......" Kawai sai
ta
takura ta dora hannun aka ta rushe masa
da
kuka,shi kuma da zuciyarsa ke famab tukuki
ya
nuna ko a jikinsa da ita a tsakar gida ya
dawo
dakinsa ya rufe. Dole gudun tona kai a
wajen
kishiyoyi ta dauki kukanta ta yi daki kamar
ta
hadiye zuciya ta mutu.ta gaji da kiyayyar da
abu
turab ke nuna mata amma tana ganun
asarar
barin gidan nasa Ya dinga sheka ruwan sanyi
a
jikinsa dan zaton zai iya ratsa zuciyarsa ya
sanyaya ta,amma kamar turi. Yana wankan
yana
gumi. Bayan ya hakura da kwara ruwan ya
fito
ya sanya jallabiya ya nemi guri ya zauna
zuciyarsa na ta zuga shi daukar waya ya kira
Alh
ya yi masa wankin babban masaki. Amma
wata
zuciyar ta dinga hana shidaukar doka a
hannun a
karshe da kyar ya fi karfin zuciyarsa ya bige
da
daukar kur'ani ya fara karatu har zuwa sha
daya
na dare. Zuwa lokacin zuciyarsa ta samu
sarari
sosai, ko ba ta watsar da komai ba ta watsr
da
Alh da zargin yi masa ta'addaci, ta watsar
da
sadiya da kayan masifarta,sai ta bar masa
fatima
da kalamanta cikin kuka da rauni.
".......abdul
idan ka yi abin da zai taba min suna kai ma
zai
jibance ka wallahi,duk tsiya dole a ce
matarka,
kuma uwar danka,ko na bar duniya za aiya
kallon
ka kai da danka da abin da ake zargina da
shi....
Ka daure ka saurare ni Don Allah". Gaba
daya sai
yanzu take cika shi da tausayi,musamman
da ya
tuno maganar Hindatu. "Duk da ka turje
min ba
ta da ciki,amma ba a son masu ciki da bacin
rai,
kar ka je ka sanya jininta ya hau duk mu
shiga
uku. Sai yanzu ya dinga hango lokacin da ya
bangajeta ta fadi tana wani kuka mai tsuma
zuciya,nan take kwalla ta dinga cika masa
ido,ya
tabbatar cikin wannan matsanancin kukan
za ta
kwana ,kila gobe su tashi bau kalau. Ya dube
yana sake saken zuci, sai da ya tabbatar
babu
mafitar da ta wuce ya je ya kwantar da
hankalinta domin ceton ranta,ya kuma samu
ya
hutar da tasa zuciyar daga radadin
tausayinta. Ya
mike zuwa widow ya hango dakunnanta
tarwai da
haske,har yanzu idonta biyu ke nan shaidar
ba ta
cikin kwanciyar hankali. Bai yi shawara da
kowa
ba ya fitop ya tunkari dakinta,yana murza
handle
sai ya ji kofar a bude,ya tura ya shiga
jikinsa a
sanyaye ya tarar da ita zaune a falo kmar
gunki
ta zurfafa tunani,fuskarta cike da hawaye.
Ya
tsaya daga bayan kujera ya dafa majinginin
kujerar yana kare mata kallo ta dago kai
saroro
tana kallonm sa cikin ajiyar zuciya. A
tsorace
take da shigowar sa,sai dai fuskarta take
bayyana
tsoron ba. Ya yi kokari dai daita muryarsa
ya ce.
"Kukan me kike?"
1 · Like · React · Report · May 19, 2015
Amierah S-Man
Zuciya d kwanji 3
Ta fara kokarin goge hawaye suna dada
turowa,amma ta kasa cewa komai. Ya zagaya
ya
isa gabanta yana kallon ta rungume da
hannu,ya
sasauta murya ya ce. "Anya fadima za ki
bar
numfashinmu ni da ke ya huta kuwa? Da
sauri ta
ware ido tana masa kallonm rashin fahimtar
inda
batunsa ya dosa, rashin tabbas kuma ya
hana ta
tankawa. Ya daulo coffee table ya ajiye
gabanta
ya zauna,a tausashe ya ce. "Haba fadina ki
bar
zuciyata ta hada da radadin kaunarki da
take
fama da shi kawai mana, ki kyale ta da
tarkacen
kananan abubuwan da bai kamata a ce sun
taka
kara ba bare su karya Ba ta fahimce shi
ba,kuma
a tsorace take da shi,ba ta ma so ta ce ba ta
fahimce shin ba,kawai sai ta canja layin
maganar
cikin sarkewar murya gauraye da kuka ta ce.
"Abdul duniyar na ta ishe ni na rantse gara
kawai
na barta ba huta,babu abin da ke cikin
rayuwar
nan ban da tashin hankali". Ta fara kuka
sosai
kuma ta fara jikinsa dan tana tsammanin
samun
sanyin zuciya. Shima ya tareta,tarbar da ke
bayayyana kololuwar kaunarsa gareta. Ya
kasa
cewa komai saboda yadda makogwaronsa ya
cushe da tausayin ta kuma kaunarta,kaunar
da ta
wuce zuma zaki,kuma ta wuce madaci a daci
da
wahalar da zuciya,saboda yakin yada
manufa da
na daidaita mata sahu. Idan da a ce a filin
duniyar nan za a sauke masa dawainiyar
komai
bayan bautar Allah,to da dawainiyar fadima
a
sonta da yi mata hidima kadai sun isar wa
ruhinsa dadi da daci kamar daci irin na
wannan
lokacin da ganin zubar hawayenta kawai. Ya
dago ta ya dinga share mata hawaye yana
girgiza
mata kai har ta samu nutsuwa,ya mayar da
ita
wajen zamanta sannan ya mike ya tsaya a
gabanta rungume da hannu. "Me ne ne ya
dame
ki fadima?" Ya fada cikin siriryar murya ba
tare
da ya hakkake ya kamata ya yi mata
wannan
tambayar ba. Ta kara kurawa fuskarsa ido
tamkar zai bace mata,cikin rawar murya ta
ce.
"Nima ban sani ba abdul" Ya yi saurin
tsugunawa
a gabanta ya dafa gwiwowinta.A tausashe ya
ce.
"Ni na sani na kuma baki dama zan saurare
ki,
fada min abin da kike son fada min dazu,
na yi
miki alkawarin zan fahimce ki". Ta kamo
hannunsa ta damke cikin nata,wasu tawagar
kwalla suka biyo kumatunta,ta hau rawar
murya
ce masa. "Wallahi abdul bani da wata alaka
da
Alh da zan kira shi gidanka, bani da
waya,bani da
wani mai waya a kusa dani ta ina zan kira
shi
don Allah?" Za ta kuma fashewa da kuka ya
rufe
mata baki,ya murmushi dan ya karfafa
mata
gwiaw ba wai dan yana jin murmushin ba ya
ce.
"Amma dai kin yarda ya zo ko?" Ta yi
saurin
gyada kai,ya ce. "Yau ya fara zuwa. A
sanyaye ta
girgiza kai ta ce. "Ya zo rannan. Ya kara
tausasa
murya ya ce. "To bani labari ko kadan
ne,me ya
zo yi rannan da yau,kuma me kuka yi? Ta
kuma
cin laya cikin kallonsa kai tsaye. "Wallahi
kawai
ina zaune da hantsi ranar litinin din nan da
lahadi
da muka je gidan su kawui,sai gasu sun shigo
falon nan shi da laila,na kidima da na
gansu, ina
tsaye a can ya gama yi min surutai, na ga
ma ba
zan iya jurewa ba na fice na bar dakin,har
sai da
suka gaji suka fita suka tafi. Tun daga