Showing 6001 words to 9000 words out of 17850 words

Chapter 3 - ZUCIYA DA KWANJI 3 by MAIMUNA I SANI BELI .pdf

fridge,ta
kawowa sadiya nata har gabanta , sannan ta yi
musu bankwana ta fice. Dakin ya dauki shiru,shi
yana duban agogo fatima a ransa, ita kuma ta
rasa ta inda ta debo korafin da ta dankaro,mai
hali ai ba ya fasa halinsa.Sai da ta ga ya fara hammar karya sannan ta
muskuta ta ce. "Abu Turab na ce ka sallame ni
in
ba ka filin gidanka ka ki,yanzu fisabilillahi
wannan
wulakancin da janyo rainin da me ya yi kama?
Jiya girkina ne ka dauki amaryarka kun
fice,yau
girkina ne ka dawo ka nemi hindatu,duk da
wadannan ba a isa laifin da zan yi korafi ba ko
basu isa abin da zan yanke kauna da kasancewa
ta matar are a gidan nan ba?" Kai tsaye cikin
tura
haushi ya amsa mata. "Sun isa mana,shi yasa ai

da kika nuna kin gaji tafiya za ki yi na goya
miki
baya, ni bakon sauki ne ba na matsawa mutum
abin da bai yi niyya ba. Wannan shine ba kuma
na son dogon surutu,idan kuma dakin kike so in
fita in bar miki,duk babu matsala sai in fita in
bar
miki". Bai ma jira cewar tata ba ya mike,ya fice
daga falon,kai tsaye kuma ya doshi dakin
fatima.
Babu ita a falo dan haka ya doshi dakin
kwana.tana kwance kan gado ta rufe rabin
jikinta
da bargo rigingine tana kallon sama idonta a
bushe babu alamun shirin bacci. Shigarsa ya sa
ta juyo ta kalle shi, fuskarta babu yabo babu
fallasa, amma a zahiri dai boyewa ta yi. Cike
take
da fargabar abin da zai faru tsakaninsu idan ya
tsinci labarin zuwan Alh cikin gidansa Amma
ganin fuskarsa a sake sai da ta sauke wata
boyayyar ajiyar zuciya ta ci gaba da kallon sa
saroro,yana ta faman bin dakin da kallo amma
a
boye zaren da zai ja ta yake nemowa. Rashin

samowar ya sa shi bigewa da kiran sunanta a
tausashe. "Fatima" Ba ta da niyyar
amsawa,amma ta yunkura ta tashi zaune,ta
kuma janyo hularta tasa. Ya dauko stool ya
ajiye
a gabanta ya zauna yana kare mata kallo, ita
kuma duk ta daure fuska dan tsabar samun
gari,
ya kamo hannunta ya rike cikin nasa ya lalubo
idonta suka kalli juna. "Fatima ya ya jikin? Ta
kawar da kai tana 'yan numfashi wanda ke
nuna
fishi da barcin rai. Ta motsa bakinta amma
harshenta ya kasa furuci,sai kawai ta zubawa
hannayensu dake harde ido,zuciyarta na sauke
mata duk wata daukaka da take ji cikin
ranta,kowa ya juya mata baya matakin kuma
ya
gagare ta dauka. Abdullahi da take rainawa ya
zame mata kadangaren bakin tulu. Ya katse
tunaninta da cewa,"wai me ya faru? Na ga duk
jikinki a sanyaye, hala jikin ne". Ta dago ido
kwalkwal ta dube shi. "Shekaranjiya ma na
wanke
kafa na je dakinka a kansa". Ya yi kasake

alamar
tunani,sannan ya girgiza kai a nutse ya ce. "Na
manta,Allah ya sa dai ba bata miki rai ba yi ba".
Ta zare hannunta daga nasa cikin cije lebe ta
fara
janye jiki. "Shi ke nan sai ka tashi ka bani
guri,idan ka tuna ka dawo..." Ya tare ta yana
dawo da ita,a tausashe ya ce. "Wallahi da gaske
na manta, mantuwar tawa kuma tana da dalilai
na wasu rudani da na sami kaina,ki tuna min
zan
karni laifin in bayar da hakuri. Ta runtse ido ta
bude ta ce. "Idan akwai abin da ke mugun
bakanta min rai bai wuce bai wuce a rataye ni
ba,
laifi na yi ai bai kamata ka dauke mafarka
ba,sai
ka zo ka tuhume ni kawai,amma kai na ga baka
da makami sai na ka nunawa matanka zaman
dole kake dani,in a ce na gaske ne kuma zai min
abin nema tsahon rayuwata ban san zaman
kunci
da takura ba,kuma duk wahala ba zan fara su a
gidan nan ba". Ya yi murmushin da ke nuna
rashin damuwar korafin da muhimmanci yana

cewa. "Haba na fa fada miki akwai abubuwan da
ke damuna suke kuma hanani sukuni,amma
raina
ya yarda duk abin da zan yi gare ki ba ya hada
nasaba da niyya ko tanadin cin fuska. Ni da
nake
so gidana ya zame miki aljannar duniya fatima
yaushe zan yarda a kirkiri abin da zai cushe
ranki
dani? Amma ki yi hakuri da abin da ya faru ba
zan kuma ba". Ta yi shiru tana ci gaba da kallon
hannunsu a tare,ita kanta ba za ta iya
tantance
abin da ya dami zuciyarta yanzu ba, amma dai
sam ba ta jin dadin zuciyar. "Ya ya jikin ki?"
Ya
kuma tambaya a nutse.ta motsa baki a
yangance
ta ce. "Da sauki". Ya ci gaba da kallon ta,kafin
ya
sauke numfashi ya ce. "Magungunan da kike sha
sun kare ne? Nan ma ta kasa amsawa saboda
takaicin papalolon da likita ya yi mata akan
maganin,yanzu ita ba ita ba ita ba, ba gara ma
tun farko ya sanar da ita zai zubar mata da

cikin
ba, in ba ta nemi wani mai zubar mata ba a kalla
ta shirya zama da cikin kar ta yi dakon banza ya
zo ya bare a lokacin da ya gama nuna kai. Bai
damu da shirunta ba, ya saki hannunta ya isa
dirowa da take ajiye magnugunan ya debo
ragowar zuciyarsa duk ta dakude da tunanin
hanyar da zai bi ya mayar da ita wajen likita a
gobe. Saboda sati daya ya bayar ta koma
asibiti,ya san ba za ta bishi su je asibiti ba ya yi
gangancin barinta,kila idan yasa kafa ya fita
ita
ma ta sa kafa ta fitan,wakalila abin da ba a so
ya
faru in ta tadda likita. Ya dawo da magungunan
ya same ta. "Ina fatan kin ci abinci?" A kiyane
ta
ce. "Ai ka kawo min abin da zan ci". Ya janye
mata bargon kafarta ya dago ta yana dariya.
"Wai da gaske baki ci komai ba? Kin san kuma
kina da matsala ko? In za ki amince min ma
gobe
ya kyauta mu je asibiti". Nan da nan ta gintse
fuska. "Ni babu inda za ni..." Ya yi suguri yana
kallon ta musamman cikinta,har sai da ya ja

baya
yana kare mata kallo,kafin ya dubi tsakiyar
idonta
ya ce. "Asibitin da zamu je shima likitan ya iya
zubar da ciki,idan baki gamsu ya duba ki dan
dorewar lafiyarki da ta abin da ke cikinki ba, sai
ki
nemi ya cire mi ciki. Duk babu matsala a gurina
ba sai kin haifa min 'ya'ya zan ci gaba da rike
auren ki ba fatima. In kai ki a zubar miki da ciki
da kaina ya fi ki bi kawarki da ba za ta iya boye
sirrinki ba, ni kuwa zan boye do na saka kaina
zama da ke". Ya wuce kai tsaye cikin nutsuwa ya
fice daga dakin ya barta da kallonsa
galala,wani
irin tashin hankali na yi mata kururuwa a
kwakwalwa. Maganar cikin nan ita ce mafi
girman abin da ya fito yake son tilasta mata
zama da Abdullahi,abin da kuma zai zame mata
ne kaico shine zama da shi din a gabar da ya
gama kwashe damarta har yake neman mayar
da
ita ba komai ba.Zuciya d kwanji 3
Washe garin ranar bai yi niyyar zuwa
gurin aiki ba gudun kar ya fita ta sa kafa ta

fita,amma da ya nemi dama a office sai
aka ki
lamunce masa. Dole ya tuna mata baya
domin
bude kofar kashedi,wato zuwa dakinta yi
mata
aikace aikace da girki karin kumallo,tanadin
ruwan wanka,ya sa ta tayi wanka ta kuma
karya
kumallo a gabansa,ya hjada kayan wankinta
zai
fita dasu,sannan ya dube ta ya ce. "Kina
tune da
dokar da na kafa miki ta hana ki fita? Har
na
fada miki waccan fitar taki ta karshe
kwalbar
hakuri ne ta fashe,to har yau ban sami wata
ba
bare in fara zubi,idan kika kuskura kika fita
duk
abin da ya biyo baya kar ki yi kuka dani".
Ta dire
tambula din data gama shan magni,ta yi
wani

mugun daure gira. "Mene ne karshen abin
da za
ka yi idan na fita? Ka fada min idan ya yi
min
kadan in fada maka ka kara,dan kullum
kalma
daya nake ji a bakinka ita ce zan yi kuka da
kai...... Haba na gaji ka ji ko? Nima tawa
kwalbar
hakurin ta kare ban ga zan iya wannan irin
rikon
kauyen da kake min kwado,zan iya gabin
damar
na zauna in kuma ki bin dokokinka babu
yadda za
ka yi dani, karkari ka dan mataki ko wanne
iri ka
dauka ina maraba da shi...... Sai kawai ya
saki
baki yana kallon ta, ta ba shi mamaki
matuka
gaya, rabon da ya ga irin wannan tsiwar a
idonta
idan bai manta ba tun kafin aurensu. Yanzu
da ta

yi ya tabbatar wata kwabarsa ce ta shirya yin
ruwa,in ya canka dai dai tsauri matakin da
yake
dauka a kanta ya fara,shi ya sa tsake son
nuna
halin dangin gwandam,akwai bukatar ya
canja
taku ke nan. Wannan ne ya sa bai ji zafin
abin da
ta yi din sosai ba, ya yi mata duban tsab
sannan
ya ce. "Haka kika ce? Shi ke nan tunda wai
wai
kike ji ina baki shawarar yau ki sa kafa ki
fita in
ya so sai kawai ki ga abin da zan yi din". Ta
yi
baya ta kwanta a kujera tare da jan wani
katon
tsaki,ransa ya. Sosa matuka,ya juma yana
kallon
ta cike da takaici,amma sai ya sami kansa
da
tausaya murya ya ce. "Yau ni kike wa tsaki
fatima?" Ta yi turus! Idanunwanta cike da

nadama ta dago tana kallon sa,ita ma ranta
bai
yi dadi ba da tsakin da ta yi. Sai dai ya fito
ne ba
tare da ta shirya masa ba, ta yi nadama a
zuci,
amma harshenta ba zai iya furta masa abin
da ya
kamata ba wato ban hakuri. Saboda haka
suka
gaji da kallon juna shi ya rausaya kai ba
tare da
ya ce komai ba ya fice. ***************
******************************
***************
************************* Tana ji tana
gani ta
hakura da fitar,ko banza tana tsoron
hukuncin da
bai furta ba da wanda take danganta shi da
kunnen kawu a cikin halin da take ciki na
bukatar
farfado da darajarta a wajen
kawun,darajar laifin
da bai kai wannan ba ya zuba. Sun ci gaba

da
wannan takun sakar, haduwa su babu dadi
sosai,wanda ba wani abu ne ya janyo hakan
ba
sai ita da ta raina yadda yake taraiyarta a
yanzu,shi kuma ya dage a kan wannan silef
din
da ya hawo. Yana ji a ransa aski ne ya zo
gaban
goshi,ya kamata a bar fatima ta san zaki da
madaci a matsayinta na mai bi ba wadda
ake bi
ba. Idan zaman su na baya yana da uzuri a
cike,ta tabbatar uzurin dab yake da
karewa,in
kuma ya kare ba a samar da kafar toshewa
ba to
zai iya rusa doguwar lafiyar da aka shawo.
Ma'abar shine,idan bai bar fatima ta tsaya
da
kafarta ba a lokacin da watanta ce da
hakkinsan,
ba ta iya hasala komai a cikin gidanta sai an
yi
mata, ba a fada mata magana wadda ranta

ba
zai so ba,ba ta nema ta rasa da sauransu.
To
lallai akwai matsala,duk da ya san matakin
da
yake dauka yana komar da soyayyarsa baya
a
zuciyarta,amma yana ganin gara hakan a
kan ya
zabi wanda watarana zai sa gaba da yau
soyayyar ta tankwabe. Ina kuwa wannan ne
in ta
ilimantu sai ta boye certificate a
akwatu,randa
duk aikinsa ya zo ta dako ta karkada. Irin
wannan matakin ya dauka a kan sadiya,ko
ma
wanda ya fi shi tsauri,dan ya lura da kyau
kan
sadiya ya fi na fadima hayaki,duk sinadarin
da za
a zuba dan hana shi ya kamata a zuba mai
zafi.
Tun daga ranar da suka yi rigimar nan ya
fita

hanyarta,ya yiwa dakinta yaji,in ta zo nasa
ya
daure fuska,karkari idan akwai bukatun ci
da
masarufi ya yi mata waya murya a cushe ya
ce
ta zo dakinsa ta karba. Wani lokacin ta zo
wani
lokacin ta yi zuciya ta ki zuwa. A 'yan
wannan
kwananki sadiya ta yi lakwas,duk ta fige ta
rame,
daga zaman daki sai kuka. Su kansu mutan
gidan sun sam$i lafiya,har ma suke mamaki
sadiyan ce ta zama haka? Musamman
Hindatu
da shi kansa abdullahi. To dole ne ya yi
mamaki,ita da kullum ba ta da kwanjin da
ya
wuce gurin a sake ta, amma an ba ta damar
tafiya ta like.lallai dama wargi guri yake
samu.
Ranar da fatima za ta fita girki da safe
yana ta
shirin fita aiki, fatima na ta faman kumbure

kumbure,ya lura da ita amma sai ya share
ta. Da
ya ci gaba da satar kallon ta ya lura da
yatsinar
da take ne ya fahimci kamar ba ta da
lafiya,dan
haka ya dan dora mata ido. "Lafiyarki
kuwa?" Ta
fanshe gizagon da take da galla masa
harara. "Ya
kamata in tambaye ka matsayin gidan nan a
waje
na, idan kurkuku ne me zai hana ka siypo
karaf
kan kafawa kofofin nan" Ya yi dariya ya ci
gaba
da saka safarsa,ya dinga girgiza kai sannan
ya
daga ya dube ta. "Ina tsammanin na taba
sanar
da ke ba a daure masoyi ko? Illa iyaka idan
ya
fiye rigima sai ayi masa saki talala ta ci ashe
ba
za ta ci ba". Ta shaki hanci kamar za ta zub

da
hawaye ta ce. "Ina tsammanin ba da baki
kawai
ka kafeni a gidan nan ba abdul, watakila
wani
siddabarun ka yi min. Mts! Na rantse da
Allah na
gaji,auren ka ni dai ba amfaneni da komai
ba sai
ma tarin koma bayan da ya jaza min. Ba
kudi
babu 'yan uwa,sai in shafe sati ban ga wani
nawa
ba, ni kuma ka toshe min hanyar fita.kawai
ka
ganni da farin jinina ka goga min bakin
jini....."
Har yanzu dariya yake yana kallon ta,ya ce.
"Ba
ki yi karya ba, ba da baki kawai na kafe ki
ba,na
fadawa Allah ya tsare min ke,ya kuma amshi
rokona...." Ta katse shi saboda tsabar
kuncin da
zuciyarta ke mata. "Ka san akwai hisabi

tsaknin
mata da mazan da ke tilasta mata zama
dasu ba
tare da son ransu ba?" Ya yi kasake yana
kallon
ta, sai ya tuno abin da zai sa ya kashe
bakinta
yanzu ya ce. "Ai shari'a sabanin tunanin ce,
kuma
yanzu tsakani da Allah ba ki ji kunyar cewa
aurena bai amfane ki da komai ba? Ki
shekara
talati da uku a duniya babu dan kai Allah ya
baki
a gidana amma ki juyar da wannan
karamcin? Shi
ke nan in ke baki ga abun arzikina ba in kika
haihu duniya za ta gani". Ta tura baki ta
zakuro
dankwali goshi sannan ta juya masa keya,sai
daiKamar yadda ya yi zato ba ta iya tankawa
ba. Ya
mike cikin dariya ya fizge dankwalin nata
yane
cewa. "Yau da dare nan dama a ce tare

muke,na
fara gundura da wannan zaman doya da
manjar
namu nima fadima,ya kamata in yi wani
abu,kema ya kamata ki daure ki saurare ni
in kika
akwantar da hankalinki ko ba kyasona akwai
fatan in kika haihi ki sammin wani abu daga
soyayyar bebinmu duk da na san ba ki yi
farin ciki
da ko zuwanta duniya ba" Kawai sai ta tashi
za
ta bar masa dakin,ya yi sauri riko hannunta
ya
juyo da ita. Da murya kasa kasa ya ce. "Ki
min
wata lafarma guda daya fadima,idan kin
kasa
bude min wata kofar so a zuciyarki,don Allah
ki ji
kaina ki budewa dana ko yata da ke cikin
ki,ba su
da wani gata sai ni da ke da ubangiji ya
sammana jin kansu,ke kuma kin fini kusanci
dasu

saboda haka ko me za su zama hotonki ne,ki
min
wannan alfarmar ko bayan raina,har na
tashi a
tutar maho cikin kaunar da na yi miki kin
ji?"
Yanzu duk jikinta ya yi sanyi,da alama
maganganunsa sun sami matsuguni a
zuciyarta,
kuma ko ba su yi tasiri a yanzu ba akwai
alamun
za su yi a gaba. Ganin haka yasa ya kara
tausasa murya yana kara shishihe mata. Ya
ce.
"Kin ji fatima"? Ta yi kus! Ko motsi ta
kasa,hakan
ya ba shi damar juya ta yadda ya so,har
dan
kansa ya cikata yana mata sallama a
danyaye.
******************************
***************
******************************
********* Da
yammaci yana shigowa layinsu motar Alh na

fita
daha layin,da Alh kwance a gidan baya
direbansa
na ja. Wata muguwar tsarguwa ta kidama
masa
numfashi,ya karasa gidansa cikin zakuwa da
ci
da zuci,kuma kai tsaye ya shiga kwankwasa
kofar
Hindatu. Sadiya ta dinga lekensa cike da
wani
mugun takaici,yadda take ji zuciyarta
kamar ana
babbakawa,ta tabbatar in ba ta babbake
ba,to
tana dab da zugata ta babbaka Abdullahi da
matan da yake kaiwa darare da ranakunta.
Hindatu ta zo ta bude kofar ta ture ta ya
wuce
ciki yana mita. "Me ya faru da ranar nan
kika
garkame kofa?" Ta biyo shi jikinta na bari ta
zauna tana cewa. "Wanka zan yi na rufe
kofar,wani abu ne ya faru yanzu da ya
sanyani

rufe kofar,duk sai na dan tsorata wallahi"
"A
kagauce ya ce. "Me ya faru? Ta yi saurin
basarwa wanda ba ta sa ya kasa gane tana
boye
masa wani abu na. Ta ce. "Babu komai" Ya
jima
kasake sannan ya samo abin cewa. "Mun yi
baki
a gidan nan ne yanzu? Na ci karo da wasu
maza
suna fita". Ganin ya ranfo ya sa ta ga gara
ma
kawai ta fada din. Allah ya sani ba gulma ta
yi
ba. Ta muskuta ta ce. "Ai sune suka bani
tsoro,babban mutum ya dinga ziyarar gidan
mace
wai da sunan kawar matarsa....." Abdullahi
ya ji
kamar ta buga masa buhun siminti,bai
fahimci
komai a maganarta ba, kuma bai bari ta
dire ba
ya katse ta... "Subhanallahi, wane nr haka,

wajen
wa yake zuwa?" Ta dube shi a nutse ta ce.
"Wajen amarya ya zo, inda ta birge ni ma
ita
kanta ba ta kaunar zuwan nasa". Jarumtar
Abdullahi ce kawai ta boye tashin hankalin da
yake ciki,kila da sai ya suma a gurin,amma
haka
ya ci gaba da numfashi kafin ya daure ya
ce.
"Dama ya saba zuwa?" Hindatu ta tattara
dukkan
hankalinta gare

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login