Showing 1 words to 3000 words out of 17850 words

Chapter 1 - ZUCIYA DA KWANJI 3 by MAIMUNA I SANI BELI .pdf

ZUCIYA DA KWANJI part 3
"Ba dai a kafa za ki koma ba? Da kalaman da
Abdullahi ya kori shirun da ke tsakaninsu da
laila
ke nan, alhalin sun jera tafiya tare tamkar
wasu
saurayi da budurwa da ke son lallai duniya ta
san
da su. Laila ta dube shi ta kawar da kai ta ci
gaba da tafiyarta,dukkan tsoronsa da shakku a
kan abin da ya zo mata da shi wanda zuciyarta
ke ta faman kokawa da su fuskarta ta binne. To
dazu sun ci kashi a kan juna ita da matarsa bai
tsuke ba bare ta gane bayan da ya goya,nata da
ta yi masa gatan sanar da shi halin da matarsa
take ciki,ko kuma na matarsa wadda wata kila
godi din goshinta yake dusashe dukkan
laifukanta. Kamar Abdullahi ya san abin da
laila
ke sakawa a ranta, ya fara maganar da yake
nufin warware mata kullin. "Gaskiya Alh bai
kyauta miki ba, ya dauko ki gari ya kanshin
dahuwa ya zo nan ya watsar da ke ba tare da kin
yi laifin komai ba?" Nan ma ta yi masa shiru
dan

gane fahintarsa mugun dan zafin kai ne, kansa
tsakiyar hayaki yake, shirunsa ne kuma ya ba
shi
damar yin dariya ya dora. "Sai na tausaya miki
wallahi,don akwai alamun aljihun baya yake da
ke, ke kuma kika gagice har kike tsammanin
karanki ne ya kai tsaiko da kike iya mallakar yi
kafada da ita. Amma dai Alh ya birge ni
wallahi,yana ganin fatima sai ya manta da
laila,
abin da ya yi ya kara tabbatar min fatima na da
kima da daraja cikin rayuwar mutum biyu,wato
ni
da Alh wadanda dukkan mu zamu iya mutuwa a
kanta bare karamin alhaki mu kashe wani dan
mu
tsere da ita. Cikin sumewa da rashin karfin
gwiwa
laila ta dube shi da neman takaitawa kanta
takaicin da yake guma mata. Ta ce, "ni za ka
akashe ka nan?" Ya yi saurin tarar
numfashinta.
"Laila me kika yi min da zan kashe ki? Wai ina
nuna miki darajar fatima da ta yi miki nisa ne,
duk yadda za ki kirkirar mata aibu ki hada da

nata ba za ki iya canja ta a fuskarmu da
zukatanmu ba. Ki daina wahalar da kanki bata
ta
da maganar zubar min da ciki ko nunawa Alh na
dauko ta min fito....... Ki canza wata hanyar ta
tade kafarta... Wani abu ne ni mai dadi a
gurina,a
saukake kin karawa kwanjina karfi". Yanzu
laila
ta tattaro karfin hankalin duniya ta dorawa
zuciyarta,shine ma ta sami karfin halin tare shi
a
zafafe. "Yaro bari murna karaka ya kama zaki,
abin da tunanin ka rasa me gaya maka ke nan,
wato yadda kuruciya da takaicin aljihu yake
zuga
ka kake kumburi da zaton za ka iya neman
komai
ka samu. To bari ka ji in ma ka dade kana cin
irin wadannan nasarorin a rayuwarka,a
shawarce
ka yanke kauna a kan fatima". Har cikin ransa
bai
ji ciwon furucinta ba, cikin dariya ya ce. "Ko?
Wannan shawarar taki ta karbu, in dai a jiye ne

ba a aikace ba. Him! Mu ajiye wannan maganar
guri guda,yanzu me kike nufi? Gidanku ko
gidan
Alh ki dora daga inda kika tsaya?. In can din za
ki ga sakona,ki fada masa taitayin da ya yi min
tayin in shiga ni bani da shi, idan kuma a
gidansu
ake rabawa to ya yo min guzurinsa". Bai jira
cewarta ba ya tsaya kokarin tsallaka titi wajen
wani mai nama,ya siyo sannan ya tsallako dai
dai
lokacin da laila ta sami a dai dai ta sahu ta
dage,
shi kuma ya wuce motarsa kai tsaye inda ya bar
fatima. Fatima ta yi saurin sauke kai cikin wani
matsannancin bugun zuciya,dukkan dokinta ya
tafi ga son sanin abin da abdul ya tattauna da
maci amana laila. Ta kasa yarda son ta sani din
ba shi da dalili, musamman da ta ji mugun zafi
kebewar laila da abdul fiye da ganin da ta yi
mata da Alh. Sai dai gogan nata sai ya share ta,
fuskar sa a daure ya tashi motar suka bar
wajen.
Har suka je gida babu wanda ya yi da
wani,fatima cike da fargabar fushinsa da

matakin
da zai iya dauka a kanta,shi kuma da burgar
fishin wofi dan fahimtar fishin nasa ya sami
leda
a kwali a sha'aninta, sai ko damun sadiya da ya
tsaya masa a rai, girkinta ne ya dauki fatima
suka kai dare,gari banza ma sadiya ke takama
da
haddar masifa an fita da fatima ballantana
tanar
girkinta? Sai dai kawai ya toshe kunne yau.
Yana
dan hucisa yana komai ya raka ta dakinta,ya
tanadar mata ruwan wanka da ruwan tea,ya
ajiye
mata namanta ya fita babu ko sai da safe. Ta
jima tana kallon kofar dakin da ya fice cikin
wani
mugun kunan zuciya,wannan wace irin masifa
ce?
Anya kuwa ba suratul yusufa ya rubuceta ya
shanye ba,ta ke ba ta yajin tsoronsa haka?
1 · Like · React · Report · May 18, 2015
Amierah S-Man
Zuciya d kwanji 3

A rayuwarta da Alh ta tabbatar ko ido da ido ya
kamata ta zubar masa da ciki ba za ta damu ba,
in bai yi wasa ba na sai dai reshe ya juye da
mujiya. Amma ga Abdul a fayan yana ta faman
hure mata hanci,haba! Wannan karkon kifin
har
yaushe. Bayan ya bawa Hindatu nata kason,
suka
yiwa juna asuba ta gari, sannan ya hau dukan
kofar sadiya,cikin sake. Saken zuci har yanzu
bai
samo dabarar kwatar kai a cikin zafin kan da
sadiya za ta yi masa ba. Ya haure mintuna goma
yana rankwashin kofar sannan sadiya ta zo ta
bude, fuskarta duk ta kode da kuka, sai dai
tana
dauke da tashin hankali iri iri suka yi nazarin
juna
na 'yan sakanni. Sannan ya fara kokarin shiga
kofar da ta babbake. Muryarta cakude da bacin
rai ta ce. "Ka koma kawai inda ka fito". Ya tare
ta da muryar rarrashi. "Haba sadiya,sai ki kore
ni
ba ki ji uzurina ba, ki dinga sara kina duban
bakin

gatari sadiya....' Nan da nan ta ci laya cikin
bacin rai. "Wallahi ba za ka shiga ba, idan kuwa
ka matsa sai ka shiga na rantse da Allah sai dai
ni in fita in bar maka dakin. Na gaji da rainin
hankalin da kake min, idan ba ka kaunar zama
dani uban wani ya matsa maka sai ka zauna
dani? Saboda tsabar rainin wayo ku kwana tare
ku wuni tare,kana ganin lokacinta ya kusa
karewa
ka kwashe ta kun fice ku shigo min tsakar dare
ka zo kuma ka tofe ni da yawu,wato ga 'yar
iska....." Tun da ta ambaci uban wani Abdullahi
ya dauke annurin fuskarsa ya kallon kawai,sai
da
ya fahimci dab take da tura masa ashar sannan
ya tare ta a fadace. "Shiga cikin hayyacinki
sadiya,idan kika zage ni fasa miki baki zan yi a
banza wallahi...." Ta ja da baya a firgice tana
shafa bakinta tamkar ya fasa mata shi din. Ta.
Shige girgiza kai cikin hawaye saboda tsabar
kuncin zuciya,gaba daya zuciyar ta ta babu
dadi,dukkan filinta ya cushe da takaici da
tsanar
Abdullahi dan haka. Babu kyautatawa ko duba
nadama a cikin kalaman da ta nannade a

harshenta. "Dan ka fasa min baki ba zan ji zafi
ba
Abu Turab! Abin da yake min zafi shine. Ci gaba
da zama da makiyina, sai dai kar ka manta
Allah
ba azzalumin sarki bane, duk yadda kake jin
mugunta da zalunci in ya so sai ya matsa maka
ka saki aure na ko muguntarka ta hana ka in
dai
rabon in ga dan kaina ya yunkuro sai ka sake ni
na bar gidanka....." Tamkar ta kwana masa
ruwan zafi ya ji maganar ta fita ta haifi dan
kanta, tunda yake da sadiya ba ta taba
bakanta
masa rai irin yau ba, shima kuma bai taba sanin
yana da hakuri ba kamar yau, dan ya yi kasake
ne yana kallon ta da jiye maganganunta a zuci
masu shegen kaifin anka juriya, duk kuma a
tsammaninta amana')anzi take. Abin mamaki
tana diga aya sai ya bige da mika mata ledar
hannunsa ba tare da iya ce mata kanzil na,ya
juya ya wuce dakinsa. Yana ta kokawar hadiye
fishi da bacin rai cikin hidimominsa na wanka,
cin
nama da kallon labarai. Amma tunuwansa sun

zo
anma raba daidai dasu a kan sadiya da fatima.
Ya kamata sadiya ta fi tsaya masa a rai domin
ita ta yi abin da ya fi munana masa wato ci
masa
fuska,duk da ta yine dan tana ganin an
bakanta
mata kuma shima ya kamata ya yi mata uzuri ko
saboda wannan. Amma da yake dukkan
sharafin
zuciyarsa akan fatima ta ke sai ya tattara
sadiya
da bacin ranta ya watsa su gefe,ya fara ji da
na
fatina tare da cikinta da ya ke jikinta wanda
shi
kadai ma ya isa zama raddi a cikin abin da
sadiya ta yi masa yanzu. Da sanyin safiya ya yi
shirin fita ba tare da ya leja dakin kowa ba,
sadiya dai ko jansa aka yi dan kai shi dakinta
zai
tirje. Hindatu kuma dama zuwan auzinawa da
tashinsu ta dauki zuwansa gaishe ta matukar ba
tambayar unguwarta ce ta motsa ba, fatima ce
yake zuwa dakinta da radin kai dan kuma yana

da abubuwan yi a dakin,amma a yau duk ya
dauki
hutunsu saboda tauna tsakuwar da ya fahimci
tana tsorata aya(tsorata fadima) Ya fito rike
da
jaka zai fita,a tsakar gida ya yi karo da sadiya
tana ta faman jan katuwar jaka mai nuna
alamun
za ta daka barkono. Ya tsaya tsam fuskarsa a
bace yana duban ta da kyau,ita kuma ta yi kicin
kicin tana ta faman hura hanci. Ya kawar da
kai
ya sake duban ta har ta dan gifta shi, sannan
ya
gyara murya ya ce. "Wannan dai dai ne, kin yi
abin da kika fi cancantarsa,Allah ya ba da
sa'a".
Kirjinta ya fara wani mugun dukan uku
uku,kafafunta suka fara neman tika ta da
kasa
saboda karkarwa,saboda tashin hankali. Amma
hakan bai hana ta karfin hali irin na mace ba ta
danne tashin hankalinta ta ce. "Dole in tafi
inda
nake da kima, dan kuwa ba zan zauna ka lakaba

min ciwon zuciya ba....." Ya tare ta,"Ai ban
hana
ki tafiya ba, ko kin ji na hana ki? Birgewar ki
ma
n gani a tafiyar,domin ita ta fi dacewa da ke.
Abu
daya zan tuna miki shine muguntata ta kin
sakin
ki, saboda kar ki fita ki sami wani ki aura ku
haifi
taron arfa. Saboda haka abin da za ki yi yanzu
in
yaji ne dan in sake ki kin batawa kanki lokaci,in
kuma kin yi dan in zo biko ne na rantse miki da
Allah ko dandanmalin kofar gidanku ba zan
taka
ba,kuma babu wanda zai je da yawuna.
Shawarar
da zan baki daya ce, daga nan ki zarce kotu ki
kai kara ta, wata kila Alkali ya yi nasarar raba
mu
ya ba ki damar auren wanda za ku haifi rabin
duniya". Bai jira cewarta ba ya sa kai ya fice
abinsa yana zabga mita.
Like · React · Report · May 18, 2015

Amierah S-Man
Zuciya d kwanji 3
Duk wani azanci da kokarin boye sirri ya
kubucewa sadiya,kawai sai ta takura ta rushe da
kuka. Kukanta ne ya janyo hankalin Hindatu
da ke
ta aikace aikacen ta, ya wanda ya farkar da
fatima wadda ta yi kusan ... Zaune saboda.
Zulumi. A hanzarce ta kai ido kan agogo, kuma
da sauri ta nufi windo ta fara labe,cike da
fargabar tsoronta haushin Abdullahi ya fara
zuga
shi duka, idan haka ne ta ina za ta tare shi? Ta
san nata dukan zai iya nunka na kowa. Amma
sabanin haka sai ta ga Hindatu ta fito cikin
rudu
ta ce. "Assha! Sadiya me ya faru haka?" Sadiya
ta kara barkewa da kuka,da sauri Hindatu ta
kama hannunta ta ja ta dakinta,suka zauna
sannan cikin jimamami hindatu ta ce. "Me ya yi
zafi da girmanki da komai sadiya za ki kwashi
yaji ki je ki tashi hankalin iyayenki?" Sadiya ta
dago da idanunwata wadanda suka sha murzar
goge hawaye ta dubi hindatu,cike da kuncin
zuciya ta ce. "Kin san Allah in dai na sa kafa

na
bar gidan nan na barshi ke nan har abada ba
zan
kuma dawo masa ba. Haba! Na gaji da cin kashin
da yake min a cikin gidan nan,kuma shi ma ya
nuna ya gaji da kallon gilmawata mafi a'ala
kawai mu hakura da juna... Ko da yake ai aikin
gama ya gama,ya ce ma na bar masa gidansa".
A gaba daya maganar sadiya Hindatu ba ta sami
abin dorarawa ba, saboda ta san sadiya da ririta
laifi, abdullahi kuma da share korafi. Ta gaji da
kallon sadiyan a hagunce ta nisa ta ce, "Ni
wannan wulakancin da kike ta kirari sadiya
wallahi ban ganshi a Abu Turab ba, sai dai babu
mamaki na san ki da girmama burika,burinki ne
kawai ya zarce na iyakar kulawar da ya iya ba
ki,
wadda kike rainawa take kuma kankare miki a
gashe. Kin kasa kwantar da hankaliki ki kalli
Abu
Turab kamar sauran maza, wanda ake basu
damar auren mace sama da daya. Sannan aka
raba musu soyayyar matan mizani
mizani,soyayyar wata take fin wata yawa a
zukatansu,amma aka hore su da adalci,kin kasa

dubawa da kyau yadda Abu Turab ke
kwatantawa,rainuwarki ce kawai ta yi yawa take
son tunzuraki,ci da karfi kuma dan ragon
azanci a
inda aka fi naki karfin". Sadiya ta tsayar da
sharar hawayen da take ta faman yi ta dubi
hindatu cike da zargi,murya a kausashe ta ce.
"Wallahi ba zan yi zaman borarci ba, sai dai in
bar wannan matsiyacin gidan mai kama da
duhun
daji,kowa bakin hali da son kansa ya yi masa
yawa dan kawai Allah ya yi maka bakin fadar
gaskiya in ka fada a kore". Hindatu na jin
wannan
kan mai uwa da wabin sai ta karkade hannu ta
mike tana cewa. "Shi ke nan sai kawai ki je ki yi
abin da ranki ya raya miki,nima karambani na
ya
kai ni..." Sadiya ta figi jakarta fii! Ta fice
daga
dakin,sai ka rantse da Allah ko kafa sai ta je
gidansu,saboda tsabar fishi Amma tana fitowa
tsakar gidan sai ta dogare, ta kara rushewa da
kuka, kunnenta kuma ya dinga kwaso mata
muryar Abu Turab yana gasa mata bakaken

maganganunsa. "Ai ban hana ki tafiya ba,ko kin
ji
na hanaki? Birgiwarki ma na gani a tafiya
domin
ita ta fi dacewa da ke...." Tunda take a
rayuwarta
ba ta taba cin karo da kalmar da ta fi wannan
daci ba a zuciyarta, amma sai ta yi mata wani
aiki na bala'in tsoro da shakkar Abdullahi ya
sake
ta, sakin da take nema tuni na barazana ne,
yanzu da yake neman tabbatar mata da shi ko
fita dukkan hanyar ta sai ta ji babu abin da ya
fi
wannan bakin ciki a duniyarta. Ba ta yi shawara
da kowa ba ta ja jaka ta shige dakinta ta banko
kofa ta fada kujera ta hau rusa kuka. Har rana
ta
fara dagawa gidan tsit! Kowa tasa tana fisshe
shi.sadiya kuka fatima,hindatu ce dai babu
abin
da ya shafi farcenta.taba nade a kujera tana
shan
kallon cikin nishadi,wannan fa shine kowa da
kiwon da ya karbe shi. Da kyar sha biyu ta wuce

fatima ta lallaba kicin ta samarwa kanta ruwan
zafi,ta dawo falo cikin hawaye shabe shabe. Ta
zauna tana sha. Abubuwa ne da yawa suke
lugude a zuciuyarta! Duk na jiyyar da zuciya
kuma, nisanb da suke neman yiwa juna ita da
Alh,laila a cikin sha'aninta da Alh. Tsattsauran
matakin da suka dauka a kanta. Sai mafi komai
jiyar da ciwo wato zama da Abdullahi,musam
man
zaman doya da manja irin wanda ya kirkirar
musu
kwanan nan,sai cikin da ya matsa mata zama
da
shi da makomarsa a duniyar,wato a rayuwar
gidan Abdullahi ko a ta gidan Alh. Wasu
magangani da kunnuwanta ke kwaso mata a
tsakar gida,suka sa ta wani mugun bugib
zuciya.ba ta san lokacin da ta tashi tsauye da
kofin shayi a hannu ba. Ko daga bacci ta farka
za
ta iya shaida muryar wadanda ta jiyo a tsakar
gida suna gaisawa da hindatu,muryar
la'annanyar
laila ce da oga Alh. Ko mafarki ne, muryoyinsi
da

take jiyowa a tsakar gidan abdullahi ya kamata
a
kira mafarkin wani rudu,bare a tabbatar ido
farke
ne. Ta yi dira dira ta watsar da kofin hade da
ruwan shayin cikinsa,ta doshi kofar fita sai ga
shi
sun riga ta shigowa falon,kai tsaye babu ko
kankanuwar shakka a idanunwan su. Alh
sulaiman sanye da farar riga shit mai dogon
hannu da bakin wando, idonsa sanye da bakin
gilas,shigar da ta ke son kwatanta mizanin
yawan
rashin mutumcin da ya gwado ya taho gidan.
Domin a iyakar saninta da shi a cikin gidan
nigeria da wahala ka ganshi a waje cikin
kananan
kaya. Duk su ukun suka yi cirko cirko a tsakiyar
falon,suna kallon ta hankalinta kwance,ita
kuma
tana kallon su shigen a zare,ta nuna wannan
da
yatsa ta nuna wancan,bakinta ya kasa fitar da
furuci. Cike da murmushi da nuna hain ko ni
kula

Alh ya tunkari kujera ya zauna yana ce mata.
"Fatima babu barka da zuwa ? Ta yi baya tana
kara nesanta tsakaninsu,ciki nuna rudewa ta
ce.
Alh wanne ta'adancin ne ya kawo ka gidan
Abdullahi?" Kai tsaye ya amsa mata da fuskar
mara nuna shakka. "Dan ina tsoron ya tarar
dani
cikin gidan hakan ya janyo min zaman gidan
kaso,ko kuma dan ina tsaoron idan zargi ya
shiga
zuciyarsa ya sake ki? To bari ki ji, idan gidan
kaso ne bana tsoro sa, wanda nake ciki yanzu
saboda rashinki ya fi shi komai,in kuma sakin ne
ai kinga ruwa ta sha, dama abin da muke ma
yaki
ke nan. Laila ma ta karasa ta nemi gurin zama
ta
zauna tana kokarin kawar da mugun kallonm da
fatima ke mata. Fatima ta hada su duka tana
musu kallon da idan fassara shi za a yi za a
samo ma'anonin barkatai,sannan ta yi
murmushi
karfin hali tana duban Alh. "Yanzu me ka zo
yi?"

Ya yi saurin nuna mata kujera.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login