Showing 18001 words to 19791 words out of 19791 words

Chapter 7 - Sanadin Boko Book 4 end complete by Halima Abdullahi k Mashi .txt

kuka, ya zauna ya jawoni jikinsa yana lallashi na,
wai in fada masa meke damuna?
Na ce nifa banga al'adata ba, ya ce ban gane ba? Na
ce ina da ciki ne fa gashi kuma ban yaye su Hussaini
ba.
Sai naji ya hau fadin Alhamdulillah, Allah ya amshi
addu'ata, don Allah wannan karon ma don Allah twins,
na harare shi banfa yaye yarana ba.
Ya ce goben nan za a yaye su, na ce tab! Wata ashin
da uku fa zasu yi. Ya ce "in basu yi kani ba ba?"
Na ce ni dai zanje a bani magani." Ya fita ya ce "Me
kika ce?" Nan take ya hada girar sama da ta kasa.
"To shike nan kije ki cire" ya fita washe gari na tsi da
amai, na sheka shi har na gaji.
Nayi ta kuka karshe na kira Rahma na fada mata, ta ce
lallai Hafsat samun guri, ni yanzun dakyar na samu
Allah ya bani kinsan dai yawon asibitin da nayi. Amma
yanzun don Allah yayi maki kyauta shen zaki butulce?
To kiyi kokari ki batawa mijinki rai. Sai ta kashe
wayarta. Ina kwance jikina zazzabi yaran nata kuka ko
wanka ban masu ba.
Ranar shine yayi masu wanka ya shrya su, sannan ya
zuba su cikin mota da abincin su, sai gidan Dada ya ce
mamansu bata da lafiya ina ga ma yaye su za a yi, ta
ce me yake damunta?
Kai tsaye ya ce ciki ne, tana can tana tana ta kuka ma.
Ni dai na kawo su zan kawo kayansu. Dada ta ce to
Allah ya bata lafiya.
Gidana ya dawo yayi ta lallashi na.
"Haba Hafsat, ke da nike kallonki mai ilimi da sanin
yakamata? Bai dace kiyi irin wannan tunanin na jahilai
ba.
Kinsan matsayinki a gurina? Duk yanda kike tunanin
matsayinki ya wuce haka a gurina.
Kada ki zubar da kimar ki a idona, ina alfahari dake,
kuma yayin da kike haifa min 'ya'ya lokacin ne nake
kara so da kaunarki."
Kunya ta kamani, lallai naso nayi wauta. Yanda mijina
ke nuna min baikamata inyi masa haka ba.
Ni da na kasance mai bada shawara ba girmana bane
in yi haka, don haka sai nace kayi hakuri Mr Cool.
Tausayin yaran ne."
Ya ce "yanzun ma kayansu zaki hada suna gurin Daada,
mu kuma sai muyi rainon wannan ko?
Na ce ya zaka kaima Daada aiki, kasan fa barna suke
dashi." Ya rike tafin hannu na ya ce "ni suka biyo Dada
ta ce lokacin da ina yaro nayi barna, ai kin san kuma ga
Ummi ga Rukayya ina kaisu kowacce ta zabi nata, na
ce Allah ya raya su."
Fadi taji cewa an yaye twins sai ta zargo ko ciki ne
dani, don haka hankalinta ya tashi.
Har gida sai gata da yake bata taba zuwa ba, tayi ta
bin ko ina da kallo, sannan daga bisani muka gaisa.
Na ce "Maman Nana yaune kika taba zuwa gidana."
Ta ce "to bama zama ko nazo kina gurin aiki, nima
haka." Na ce "Amma koda dare?" Ta ce "da dare kowa
ya gaji, yanzun dai ba gashi nazo ba."
Na ce to na gode" ta ce "can naga su husaini a gidan
Daada, wai an yaye su, na ce me ya jawo maki yaye
yanzu?"
Na ce Abban su ne ya kwashe su ya kaisu. Ta tabe
baki lallai sweet heart shine lokacin da zan yaye Nana
ya hau yayi ta fada.
Na ce to ai kinga ita mace ce, dole ya tausaya mata, ta
ce kodai kin sake kunsar wani cikin ne?
Na ce to inma hakan ne meye aibu tunda mijina na so?
Ta ce kedai fadi gaskiya, kina son kiyi ki cika gida da
yara saboda kiyi gado."
Ta mike tsaye, "kiyi haihuwarki a sannu dan mu
mungaji kudi, so kinga banda matsalar su.
Na ce gaskiya ne baki da matsalar kudi, shi yasa na
ganki zaune a gida bakya zuwa aiki, sannan suna nan
cike da daki a gidanki sai dai ki bude ki diba.
Ta ce "inma kina yi min ba'a ne nasan dai na fiki." Ta
fita fuuu, na ce "sauka lafiya."
Tare muka je asibiti dashi, inda likita ya gwada ni ya
tabbatar cikina wata uku. Kuma lfy lau, sai murna gurin
mijina.
Munje Umara tare harda ita, haka nan aikin hajji lokacin
cikina ya tsufa.
Mun dawo bada jimawa ba ba haihu, 'yar budurwa mai
kyau, tamkar inyi tsalle don murna.
Ina son 'yar budurwa, itama anyi sha'ani, don lokacin
Abubakar ya kara zama (Don).
Yarinya taci sunan Daada, Abubakar yace ya yarda in
kana taimako Allah yana taimakonka.
Budi ta ko ina, sai yanzun na binciki kudin account
dina, lallai kudi wawaye ne, in da zaka tara su zasu
taru, don haka na kuduri niyar yin abinda zanyi dasu.
Kaduna naje yawon arba'in, na dauki babana na kaishi
aka yi masa hoton fita, wato international passport.
Lokacin aikin hajji kuma na biya masa. Abubakar ya
fara min fada wai yana cikin lissafinshi a bana zai biya
masu.
Na ce yayi hakuri alkawari na dauka, SANADIN BOKO
sai na kaishi makkah.
Ya ce "Allah ya biya ki" shi kuwa baba da na fada
masa na biya masa kujera da kudin aikina sai ya sa
kuka.
Ya ce gashi SANADIN BOKON nan da nayi ta tsana
zanje daki Allah, inda ban taba zaton zuwa ba.
Ki yafe ni Hafsa, tuni na gane boko ba dukka ta ba ce
illah, tana da amfani."
Ya ci gaba da cewa Hafsa na gane hakan ne ta hanyar
taimako da wata likita mace tayi ta mun lokacin da na
kwanta a asibiti.
In shaa Allah su Ummi zasu yi karatun boko, dama dai
na addini wajibi ne, zan bisu da addu'a Allah ya tsare
su yasa su sami ilimi mai amfani. Ya raba su da sharrin
ko hadarin da ke cikin boko, na ce ameen Baba. Ya ce
in da zaki yi adalci Innar ki ya dace da wannan kujerar,
don ita ce tasha wuyar iliminki."
Na ce "ita ma Abubakar ya bata kujerarta da Yayana
Umar, kai nidai na gode Allah da nasha wahala yanzu
kuma ina cikin gata.
Wata rana na matsawa Abubakar muje katsina ina son
in sami labrn yaron dr Hindu da yake munsha zuwa
gidan nasu lokacin tana raye. Sai ban sha wahalar gano
gidan sosai ba.
Cikin sa'a ma yaron an kawo shi hutu. Duk sunyi girma,
naji dadin ganin su, na karbi adireshin dinsu na Abuja.
Nasha alwashin zuwan sannan nayi masu kyauta mai
tsoka.
A kwana na biyu na nemo Asabe tayi aure da yaranta
biyar. Sai dai gaskiya basu dashi, na taimaka mata
sosai. Ta ce min tana son zuwa gurin yarta tana tsoro,
na ce zanje mata.
Wata rana munje Kano Rahma ce tayi haihuwa ta biyu
muka je, daga nan ta tambayi inda zan sami hajiya
Mairo,
Da dare naje gidan bayan isha'I cikin shiga ta alfarma
da dankareriyar motar mijina.
Da kima ta marabce ni domin tasan daga ganina taga
matar gwaska, falon alfarma ta kaini muka gaisa bayan
an cika teburin gabana da kayan shaye shaye.
Ta ce ban gane ki ba, na eh baza ki gane ni ba daga
Yola nake, ni 'yar uwar Asabe ce wadda ta taba maki
aiki kuma take da da tare da danki mai sunanki, shine
nazo na ganta."
Ta ce Allah sarki sai ta soma kuka, na ce "lfy? Ta ce ai
dan tilon dan nawa tuni ya mutu, tunda ya dawo daga
kasar waje ba lfy inda yaje karatun boko."
Na zaro ido "shima sanadin bokon ya rasa ransa?" Ta
ce wallahi yar nan can abokai suka bashi wata kwaya
mai karfi yasha. Tunda ya kwanta tashin da bai yi ba
kenan sai a kiyama." Na ce tabdijam, yanzu ina ita
takwarar taki?
Ta daga waya ta kira wata tace jeki ki kira min Ummi,
ta dube ni yanzu ita nake gani naji dadi.
Kinga da na salwantar da yarinyar nan da nafi haka
bakin ciki."yarinyar ta shigo cikin kayan bacci, mai kyau
da ita, girmanta bai wuce na shadad ba, na rungume ta
ina murna.
Na ce Allah ya albarkace ki. Hajiya ta ce ameen, na
dubi haji kada a barta ba ilimin addini, domin inda
addini, boko bazai batar da bawa ba sai wanda ya batar
da kansa.
Ta ce haka ne 'yar nan ai naga darasi, in sha Allah
yarinyar nan zan mata tarbiya irin ta addini,na ce Allah
ya sa.
Na kawo kudi na bata na ce ki sayi sweet sannan na
amshi lambobin wayar su na ce zan ba mamanta. Nima
zan dinga kira muna gaisawa, ta ce don Allah ki kaima
uwar tata don ta zo ta ganta. Na ce in shaa Allahu
*****************
Rayuwata ta zama abin sha'awa a idon wadanda zuka
kyamace ni da. Duk wanda na sani taimakonsa nake yi.
Mun sami daukaka ta fannoni da dama, 'yan uwana
suna hutawa a dalilina.
Abubakar yasa na bar aiki na koma makarantar jami'ar
Yola, hatta kishiyar mamana sai da Abubakar ya bata
kujera.




Zaharaddeen Shomar
whatsapp 08168575100


Sabadin BOKO 4-08
Posted by ANaM Dorayi on 05:28 AM, 29-Sep-15
Under: SANADIN BOKO
Taimako kuwa a danginsa duk me son wani abu da ya
same ni an gama.
Fadi ta sakar min ragamar uwar gidanci, kuma na rike,
'yan uwanshi tamkar nawa na rike su.
Iyayenshi kuwa tamkar su suka haife ni. Bikin Rukayya
ya taso, ta zo ta same ni, ta ce "Aunty dan Allah ki ce
ma Hamma kayan kicin dina ina son a sayo min a
Dubai."
Na ce "an gama" ta ce "Na gode" guri aunty Fadi ta
soma zuwa, ta ce duk kayan kicin din kasar nan zan ce
sai waje?"
Na ce kada ki damu zamu je"
Da asuba ni da shi muna kwance cikin bargo ranar
asabar ce bashi da aiki, nima ba makaranta.
Na ce "Ga biki na zuwa Mr Cool me muka shirya ne?
Ya ce to ya za a yi?"
Na ce zamu je Dubai sayen kayan kicin" ya ce keda wa?"
Tunda kinga aiki yamin yawa yanzun?"
Na ce "zamu da Rukayya da Ummi" ya ce "To yaushe?"
Na ce zamu shrya"
Na yaye baby na gurin Daada na bar su muka tafi
Dubai.Mun yo sayayya ta gani ta fada Daada sai shimin
albarka take, biki kuwa nice uwar biki, hatta Daada dani
take shawara, matan Usman da umar ma suna bina a
matsayin matar wan mijinsu.
Fadi sai ta koma baya a wajen bikin.
Mun kaita Abuja, dan Baffa na abuja ta aura, Ummi kuma
Kabir take so kanin Hashim, Umminmu tazo bikin Aliyun
su abubakar ya ce yaga mata. Su Daada suka ce koba
'yar uwata ba indan na santa to sukam sun amince.
Nidai murmushi nayi tare da godewa Allah.
Ina kicin ina hada Zuma ta amfanin kaina Abubakar ya
shigo, the only yaufa zamu fita ne. Zuwa ina? na
tambaye shi.
Hutu na samu na wata daya zmu tafi Abuja, daga nan mu
wuce England"
Na ce "kana dai sane bani kadai ba ce ko?
Ya rke kugu, to nidai dake zani, na ce a'a kayi kuri'a
kuma in tafiya ta fado kaina saudiyya zamu.
Ya ce "to shike nan, yanzun ya zanyi da maganar kuri'ar?
Kayi rubutu a cikin takarda guda daya sauran kuma ba
rubutu ka bamu mu zaba, wanda ya dau mai rubutu tafi
dashi zaa yi. Kuma kayi tskani da Allah, da ya samu Fadi
sai ta ce ita ba inda zata tabar aikinta.
Saudiyya muka yada zango, muyi soyayya muje ka'aba
munyi addu'a. Nidai yanzu duk abinda nake so a duniya
na samu, saura lahira kawai nake rokon Allah ya bamu,
kasa Aljanna ita ce makomarmu gaba daya da dukkan
musulmi. Ameeen
TAMMAT BI-HAMDULLAH!
Taku har kullum
Halima Abdullahi K/Mashi.
********************************
Alhamdulillahi
dukkan gogiya ta tabbata ga Allah madaukakin sarki da
ya bamu ikon kammala wannan littafi SANADIN BOKO,
tsira da Amincin Allah su kara tabbata ga Shugabamu
Annabi Muhammad SAW, Allah yasa mu amfana da
darasin da yake ciki.
Godiya ta musamman ga marubuciyar wannan littafi
Halima Abdullahi K/Mashi
Inna godiya ga dunbin mabiyana ta blog,pls kidinga
kokarin yin comment ta yanda lallai zanfagimci muna
tare


Zaharaddeen Shomar
whatsapp 08168575100

5
6
7

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login