Showing 3001 words to 6000 words out of 19791 words
Chapter 2 - Sanadin Boko Book 4 end complete by Halima Abdullahi k Mashi .txt
ba gaske bane.tace ina ce son yara ne yasaka
yin haka toh ai shi kenan.Munnir yace nidai nasan dana
ne kuma xan ta bin diddigi har sai na samo shi.Daddy
yace in kaje ka janyo rigima kaga dan wani kace naka ne
kai xaka kwana ci.mom tace kai dai ka barshi ya san
nashine ta kalli munnir kabi diddigi xamu dauko
lauyoyi.Munnir yace yauwa mom danAllah ki sayamin
donko nasan cewa yaron nan nawa ne.tace kada ka
damu kaidai kabi komai a sannu.ya mike ya fita daddy
na kara jaddda musu cewa shi fa ba ruwansa.
Kasan cewar ban samu bacci ba sai ya xamana na
makara, nayi sallah tare da shirya shadad. kaxar jiya na
bashi da milk din yaci.sai ga yayan su Rahma yayi
sallama na saka hijabi na fita muka gaisa,yace shadad ya
fito xai kai su makaranta shi da yayan sa dama mama
tace min shi ke kaisu,duk da cewa ba makarantar su
dayaba.muka gaisa suka tafi na shigo na gama yan gyare
gyare na nayi wanka.ankon bikin rahma nasa ya shigo da
sallamarshi hannuwansa dauke da ledoji farrera guda
biyu.na fito da sauri na amshi tare da cewa sannu xuwa
yace yauwa sai ya sake fita dauke da buhun shinkafa ya
shigo.haka ya dinga shigo da kaya ina ta masa sannu da
xuwa har ya gama.na shimfida mishi tabarma a ciki ya
xauna na gaishe shi ya amsa.ya amsa ba yabo ba fallasa
nace mai xaka ci in maka ya dubeni ido cikin ido yace
am ok.ya kalli agogo yace jirgin karfe goma xan bi xuwa
yola,na kalli agogon bango karfe 8.na dubeshi wani
sonshi ke fisgata kamar in sa kaina a jikinsa.kamshinsa
mai sanyin dadi ya karade ko ina acikin dakin, muryarshi
ta kaseni.""ki duba abubuwan dana kawo in akwai abinda
kike bukata babu sai ki gayamin.Bansan me yasa
muryata ta dishe ba nace ko ban duba nasan abundaka
siyo sunyi.Allah ya kara budi nagode.yasa hannu cikin
aljihu ya kirga kudi naira dubu 10 ya bani.ki riqe wannan
bani no mai adaidaitar da yake kaiku makaranta na
dauko wayata na dauki lambar tare da mika mishi harda
wayar ya amsa tare da dubawa.ya kirashi ya amsa .ce
masa yayi yana jiransa an nan gidana yace toh.na sake
cewa kodai indomie xan dafa ma yace a'aah.ya fito da
wayarshi daga aljihusa tana ruri tare da karawa a kunne
yace sweet honey. gabana das ya fadi tabbas fadi ce na
mike na fita raina daure naje in kwashe kayan daya
xubamin.dana gama na xauna waje kan kujera ina son in
tuno abin da abubakar yayi min me yake nufi dani?
tamkar in bar gidan saboda bakin ciki yanda suke hira da
daria.duk da cewa yarensu suke yi sai turanci jifa jifa
sunkusa minti ashirin sannan suka yi sallama.wayata
dana baro a dakin sai ta shiga ruri ya dauka ashe dan
mai adaidaita sahun ne ya iso don haka ya mike yace
yana xuwa.ta gabana ya fice,kusan mintin 5 sannan yace
ni xan wuce.na ce saboda anagutsirrkah dole kace xaka
tafi ,ko kuma ince ka kosa xaka tafi daga wurin
maqiyarka.yayi dan murmushi hakan ne"ya cigaba da
cewa ni xan tafi kamar yanda nace kuma ba xan cemiki
ga randa xan dawo bah sai san da na samu sukuni.haka
nan kuma bayan mkrnt ban laminta aje ko ina ba sai an
nemi ixini in sani.maganarshita fako ta kona mun rai wai
hakan ne kenan ni makiyarsa ce,na dago na dubeshi "wai
mai nayi maka ne kake son kuntata wa rayuwata?tun
daga ranar dana sake ganin kah na rasa sukunina,meye
nufinka dani? :kuka ya subuce min yace "au da ke baki
san kinyi wani abu ba ?to duk ba wannan ba ni me na
miki.kince mkrnt na dawo dake na baki abinci na baki
kudin cefane, na daukin nauyin dake a kanki na dawo
dake.me kike so bayan haka?ya sake matsowa kusa dani
tare da sausauta murya "fadamin in kina da wata
mastalar?nayi shiru ina son tuna me xance?sai ince baka
sakar min fuska kuma baka saurarena ?kai gaskiya in
nayi haka ba da kai ne...ya katseni dake nake nace
akwai sauran matsala?na dube shi ka fini sani.ya sake
matsowa ya ce kuntatawar da nake miki ?nace da ban
hadu da kai ba hankalina a kwance.yace saboda ba ki
sona koh?haushi ya sake cika ni ,son shi ya cika ni ya
hanani sakat sannan ga abubuwan da suke biyo
baya,amma xai ce wani bana son shi.bansan sanda nace
eh!ai tuni nace bana sonka mai yasa ka tursasamin har
sai da ka aureni.ya xura min ido.nayi laifi dana raba ki
da rayuwar kangi da gantalin bin maxan d akike yi?na
mike tsaye ni kada kamin sharri baka ganin a dandi
ba.yayi yar daria yace yaro yaro ne koh ba da kanki kika
fadamin cewa ke karuwace a nan gidan ba a wurin nan
bah.kila ma dan gidan baya magana ne daya
shaideni,nalumshe ido ckn takaici na ce magan xarar
bunu na nufi daki shikuma in jin fitarshi.nayi kuka mai
isata sannan nace laifina nake nina kashe kaina.shi
kuma a cikin jirgi yayi jugum gani yake ya xalunce ta, bai
dace ya ringa jefa mata magana ba in yai la'akari da ya
fa aureta. :Saidai har yanxu yana takaicin kasancewarta
karuwa ce ada bai san adadin maxan da ta kwana dasu
ba.Don haka kyankyaminta yake yi in ya ganta sai ya
tuna lkcn da take gayamasa ita karuwa ce.sai yaji
haushin ta.sai dai duk wannan bai hana sonta yayi
anbaliya a cikin xuciyarsa ba.ni kam haka nayini da
takaici,washegari haka na bufi makrnt tare da yi wa
Sa'adatu suleiman godia.na samu duk tayi min test
dina.nan suka yi tamin tsokana wai daga xuwa daurin
aure sai na bi miji yola nabarsu da katin walima.daria
kawai nayi tare da basu hkr.sam bana xuwa ko ina sai
mkrnt.daidai da gidan su rahma bana shiga sai dai in
aika shadad yace in gaishe da maama.in nayi abincin
marmari sai in aika mata koh in ina dawowa daga
makarnt sai in siya mata goro in aikamata dashi
:Rahma ma ta gaji da tambayata yaushe xanxo sai gata
rannar wata lahadi.itace ma na ba wa dinkunana na ce
taje dasu ayi min, tace inxo muyi mgn da telan, nace
rahma Abubakar ya hanani xuwa ko ina inba mkrnt ba.ta
ce toh"xamuyi magana ta waya in yaso sai in baki no
telan nace toh!!nagode.tunda ya tafi sai daya kwana
biyu sannan ya kirani ,gaisawa kawai muka yi yace in
bashi shadad su gaisa na bashi suka yi ta surutun su
hardai na tashi naje nayi sallar isha'i sannan suka yi
sallama.shadad ya dube ni Anty kinsan me?nace a'aa
yace Uncle yace wai da ina da ina kike xuwa bayan
mkrnt nace babu koh gidan su maman rahma ma kin
dena xuwa.sai yace ki ringa xuwa kina gaisheta.wai
kuma ince miki sai da safe ,kuma in muna son wani abu
ki fada mashi ta txt.nace shadad tashi kasa kayan
bacci,ka kwanta "cikin xuciyata kuwa nace koda xaya
kirani ba xan cemi shi bamu da komai bah koda ba mu
dashi.:Kullum xai kirani daidai wannan lkc wato bayan
sallar isha kenan,tsakaninmu gaisuwa.kuma xai ce in
bashi shadad suyi mgn a waya ,wani lkcn ma kwanciyata
nake yi in sharesu inyi bacci na.kwatsam ranar wata
juma'a a lkcn muna tsakiyar jarabawa na dawo a gajiye
ga tarin gajiya don kullum karatun dare nakeyi.na watsa
ruwan sanyi,bacci nake ji baxan iya girki ba don haka
gari na jikawa shadad da madara na rufe gida na
kwanta.banyi nisa cikin bacci ba anji shadad yana
jijjigani .Anty a buga gida inje in bude?Anty? da kyar na
amsa.shadad danAllah ka barni inyi bacci.Anty ana fa
buga gida inje in buda.nace jeka shadad.naci gaba da
baccina.ya taka kujera yaje ya bude nan take ya dane
Uncle dinshi suka shigo tare.nayi dai-dai kan katifa na
dura kaina kan filo tsakiyar kafa funa na saka filo a
tsakiya.sanya nake da farar singlet sai wani siket dina
mai fadi ,tsawon shi daidai gwiwata,ya tsura min ido
lallai hafsat nada durin jiki mai kyau ,kuma daga ganin
fatarta xaiyi laushi.shadad ya soma girgixa kafata Anty
tashi ga Uncle anty,a firgice natshi don har ckn kaina naji
kiran.idanuna jajir nake kallon shadad "menene?ba nace
ka daina tashi na ba ya nunamin Abubakar dake tsaye ya
kafe ni da ido.da sauri naja hijabina na rufe jikina sannan
nace sannu daxuwa "ya lumshe ido tare da amsawa a
ckn wata sarkarkiyyar murya.naja xani na daura sannan
na shimfida mashi tabarma na dauki hulata na saka na
nufi kitchen.dama naxo da kankarar pure water saboda
xafin kano kullum nakan xo da kankara in saka cikin
kula.da dauko nikarkiyar shinkafa ta wanda na samata
kayn kamshi,na tace na saka mata flavour mai kamshin
kwakwa naje fa kankara ckn jug.na dora kan tire da kofi
naxo na dire a gabanshi.:na tsiyaya masa ckn cup na aje
masa,sannan nace "me xa'a dafa maka?ya dube ni ki
barshi.Ban san dalilli ba, sai kurrum naga hawaye sun
cika idona, idanuna suna kallon cikin nashi nace in maka
fruit?ya cigaba da kallon idona, nima ban dauke nawa
idon ba.hawayen idona suna sauka a hnkl.Shadad ya
katse mu Anty kiyi mishi fruit Uncle da dadi nima xan
sha.yayi yar ajiyar xuciya, sannan ya dauke idonshi daga
kaina ya maida gun shadad, yace xaka sha da gaske?
Shadad ckn xumudi yace xan sha nayi murmushi kadan
sannan ya dauki kofin jus din kunun shinkafar ya
kurba.sai naga ya hade rai, ya hadiye jus din da
kyar.sannan yace wannan fa?haka yake ba sugar.kinsan
bakina yasa ba da xaki.nan da nan sai na tuna ashe
sabar sauri ne yasa ni ban saka sugar,lemon tsami
ba,don haka sai na saka tare da suga da na zuba masa
sai naga ya hau sha. Na kira Shadad na aike shi siyan
fanta gidan Maman Yusra. Na yanka abarba, gwanda da
kankana, bayan na wanke su na 6are ayaba sai na yanka
dabn saboda kada tayi baki, in taji sanyi. Na matsa
lemun zaki,shadad ya kawo min fanta mai sanyi na zuba
mishi a plate mai zurfi tare da cokali. Sannan na kawo
ayabar na zuba,shadad ma na zuba mishi. Nasha mmk,
kafin wani lkc ya gama da shi, Sai naji sanyi a zuciyata,
farin ciki ya cika ta, dama haka mace ke ji a duk lkcn da
mijinta yaci duk wani abu da ta sarrafa? Lallai kuwa zan
dinga kirkirar abubuwa don na birge shi dasu. Ya katse
min tunani da cewa, Zan iya shiga bayanki? Ina son yin
sallah,don bn sami Jumma'a ba. Na dube shi a raunane,
Me zai hana? sai dai ko in kana kyama, don namu na
talakawa ne. Ya mike ba tare da ya ce kala ba, ya nufi
bayina,duk da cewa bayin na gargajiya ne, amma wanke
yake tsaf, ba zarni ko karni ko ko wari. Khamshin
sabulun wabka ne kawai sai ko na omon wankin bayi. Ya
fito yayi alwala. Tuni na shimfida masa darduma, don
haka ya tada sallah, ni kuma na fada wanka ko da na zo
ya idar. Shadad ya kwaso masa takardun mkrntrsa yana
dubuwa, na dire tsakiyar katifa ban cire hijabin ba na
murtsuka mai bayan na basu baya. Da zan sa kaya sai
na diba na fita waje ya bini da ido har na fita,sai da na
saka kayan na zauna kan kujera ina daura dankwali. Na
kalli madubi,masha Allah! Nayi kyau, daya ne daga cikin
dinkunan da na bawa Rahma na saka, riga ne da siket na
leshi mai ruwan dorawa da ratsin baki. Na koma kan
katifar ina saka turare, na kalle shi shima ni yake kallo.
A duk lkcn da idanunmu suka sarke basa son daukewa
daga barin kallon juna. Yanzun haka mun kasa ko
kiftawa,shadad ya kalle ni ya kalle shi, sam bamu sani
ba, sai dariyarshi muka ji sannan ya ce...Uncel ashe
kuma kun iya kallon kuda?" shine yayi saurin janye
idanunshi, ya dubi Shadad. Me ka ce? Shadad ya ce, Irin
kallon kudan da yaran ajinmu suke yi, wai kada a kyafta
ido.. Ni kam lumshe ido nayi, bn so shadad ya katse mu
ba, domin ina karanta abubuwa da dama a cikin
yalwatattun idanunshi., Jikana a mace naja filo na sulale
na kwanta, Jim kadan na jiwo wayata sbd jin shigowar
text. Na kalle shi, sbd ganin lambr shi ce mai dauke da
sakon,shima ya dan kalle ni sannan ya maida kanshi ga
Shadad. Na bude sakon,cewa ya yi "KIN YI KYAU."
Murmushi ya su6uce min,dadi mara misltuwa ya rufe ni.
A hankali na dago kai na kalle shi, shima ya dan saci
kallona, sannan ya dauke kai tamkar ba shi ba. Na dinga
kallon kyakkyawar fuskarshi, Shadad na ta krt, bana
zaton ma Uncel din yana tare da shi, don waya yake
dannanwa. Wani sakon ya shigo wai "KALLON FA NA
NAWA NE? na kuma dubn shi, sannan na rubuta cewa.
KALLON SO NE.na tura mishi,ya dago muka hada ido.
Nayi saurin sunkuyar dakai. Ya mike tare da cewa,
"Shadad zo muje." Na dube shi, Ina za ku?" ya ce, Tadi
gurin budurwata." Na tsuke fuska,ya ce "Shadad zaka
gurin Antyn nan me baka ice ream?" Da gudu yasa
takalmi "Za ni Uncel, zata bani da wannan biskt din mai
dadi?" Gabana ya fadi, ko dai gaske ne? nayi shiru raina
6ace . Abubakar yayi murmushi mai sauti, cikin jin dadi
ya ce Zata baka. Suka fice. Na rasa me ke min dadi,
Rahma ta kira ni tana min tsiya,wai miji ya dawo in dai
kokarta in shawo kanshi. Cikin yanayin tausayi na ce,
"Uhm! Wane shawo kai? Mu2min da ke nemn wani
auran? Rahma ta ce, Daina fada min wannan
zancen,tsokanarki kawai yake yi, duka-duka yaushe aka
yi abin? Amma kada in katse ki, menene dalilin da yasa
kika fadi haka?" Na ce, "Tun kafin yace yana sona ina jin
shi yana cewa za shi tadi, su fita shi da Shadad. To yau
ma yana ce ma Shadad za shi gurin Aunty yaro ya hau
murna, har da cewa za'a bashi irin wannan biskit din mai
dadi!" Rahma ta ce, "Kika sani ko wata mai sai da kayan
kanti ce da suke sayayya yake ce mata AUNTY?" Ta ci
gaba, "Ke ko bama haka ba Abubakar ba zai tarki wani
aure yamzun ba, kiyi aiki da hankali mana. Kishi ya rufe
miki ido, baki ga ko ke baki soma cin amarcin ba?" Na yi
murmushi na ce, "Ni ko da har naji haushi." Ta ce, "Don
Allah kiyi amfani da matantakarki ki fizgi mijinki." Na ce,
"To Rahma duk na kasa gane mishi ne, amma yau da
sauki tun da har yaba kwalliyata ya yi." Rahma ta ce, "Ki
yi wadda tafi ta kafin ya dawo, ki ajiye duk wani taurin
kai ko shariya da jan aji, ki zuba basirarki ki samu ki
kwato shi gare ki." Na ce, to na gode.
Dambun shinkafa na mishi wanda na cuda shi da nama,
karas da kabeji gami da koren wake. Gida ya dime da
kamshi, na hada mishi jus din kokumba da abarba da
kwakwa, na nike su a blender na tace, na saka kankara
da flavour. Bayan na kammala na je na tsala wanka tare
da yin Sallar Magriba, nayi shafa, wata jar atamfa (java)
na saka mai fulawa blue, na gyare gidan tsaf na yi
shimfida a tsakar gida na jera masa, na kunna masa
turaren wuta ko ina ya dauki kamshi.Shi da Shadad
kawai suke 'yan zantukansu, ko nace yake taya shi
shirme. Kusan goma saura ta ce, "To Madam ni zan tafi
na kwanta." Muka yi masa rakiya, na yi Sallar Isha'i tare
da Shafa'i da wutiri na kwanta, zan soma addu'a sai naji
shigowar sako, wanda na zata shine wato Abubakar. Na
bude, cewa yayi, "Ban taba cika ciki irin na yau ba,
abincinki yayi dadi, zan zo in miki kyauta kuma ina son ki
zabi abin da zan baki." Na yi murmushi na lumshe ido,
zuciyata tana wassafo burina, na rubuta cewa, "Duk abin
da ka zaba min da zaka barni ma sai in ce yaba min din
da kayi ma kyaute ce a gurina." Da ya karanta sai ya ji
dadin lafazin, don haka sai ya sake rubuto cewa, "In sai
miki turare? Ko in canza miki waya? Ko kin fi son in
canza miki wani gida kafo mai tsarin zamani? Don
lafazinki yasa naji cewa dole ne ma in miki kyauta." Na
yi shiru ina nazari, wato Abubakar yana so na dinga nuna
kulawa gare shi, in ko haka ne zan yi ta nuna kulawata a
gurinsa, sai na rubuta cewa, "Duk wannan basu yi min
ba, tunda kace in zaba aba abu daya nake so, ka yarje
min in fada?" Da sauri amsarsa ta shigo ya ce, "Eh, fadi."
"Son ka da kulawarka kurum nake so, in zan samu sun fi
duk wani abu na kawa ko na dadi da zaka bani." Ya yi
shiru yana maimaita zantukan, sai kurun na ji kira, na
daga tare da yin sallama kasa yanda ko wani na kusa da
ni ba zaya ji ba, ya amsa min sallama shima cikin wani
sauti mai nuna cewa muryata ta ratsa shi ya ce,
"Hafsah!" Cikin wani irin sauti ya kirani, har yatsana naji
nima nace, "Sadiq!" Ya ci gaba, "Ni naki ne, sona ke
kadai yake naci, kuma zan kula dake, wannan kawai kike
so?" Na saki ajiyar zuciya, "Wannan kawai shine burina,
na gode." Ya ce, "Nima na gode. Ki yi bacci..........
Zaharaddeen Shomar
whatsapp 08168575100
Sanadin Boko 4-03
Posted by ANaM Dorayi on 06:39 PM, 28-Sep-15
Under: SANADIN BOKO
Ki yi bacci mai dadi tare da yin mafarkina." Na ce,
"Kullum cikin yin mafarkina ni ke, ina sonka sosai." Na
kashe wayar don jin nauyin furucina, na dauki filo na
rungume na lumshe ido ina tuno fuskarshi.
Shima a nashe gefen ma filon ya manna a kirji yana jin
dadi. Nan take kuma sai wata zuciyar ta ce masa,
"Yanzu kai saboda yarinyar da ta tabbatar maka da cewa
ita karuwa ce ka ke wannan?" Nan take kuma sai ya saki
tsaki tare da yin jifa da filon, zuciyarshi ta ci gaba da
wassafo mishi cewa, "Ba wani son da take maka, wanda
take so shi daya ne, tunda har ta bashi kanta. Kila ma
da zai dawo yanzun da ta nemi ka barta ta koma
gurinshi." Take ya nemi farin cikinsa ya rasa.
Lokuta da dama wannan tunanin ke sa shi jin haushin
Hafsah.......
A zato na zai shigo da wuri, don haka na shirya masa
abin kari, sai ga sakon shi ya shigo, "Madam ki yi hakuri,
kila ki zaci zan shigo, zan duba ma Dada wasu daga
cikin (super market) dinta. Idan mun gama da wuri zan
zo da wuri, in bamu gama ba ki dubi hanyata da rana.
Ina fata kina cikin koshin lafiya?" Lallai Abubakar zai
cika alkawarinsa na kula da ni, to nima Insha Allah zan
kula da shi. Na bashi amsa da cewa, "Lafiya lau (Hayate)
rayuwata, Allah ya sa ka gama abubuwan da zaka yi
lafiya, ya kawo min kai cikin kwanciyar hankali."..
Duk da cewa har Abubakar ya bar Kano babu wata
mu'amala ta auratayya da ta hada mu, ban damu ba
saboda ya nuna kulawarsa gare ni. Ya bani kudi, ya
canza min waya zuwa (BB), ya kara min abinci. Haka
nan ko da ya tafi ya kan kira ni sau 3 a kullum, nima
kullum na ke kiran Mahaifanshi da safe in gaishe su,
haka nan Lamido da Matanshi kullum sai na kira su cikin
girmamawa na gaishe su har muka kammala Jarabawa.
Lokacin yayi tafiya zuwa India akan harkokinsa, na ce
mishi, "Tunda muna hutu har da Shadad ina son inje
Kaduna da Funtuwa da Malumfashi." Ya ce shi kam bai
yarda in je Kaduna ba, amma in je Funtuwa gurin Inna in
kwana 2, Malumfashi kwana 2. Sagir zai sani jirgi in
wuce Yola. Na ce masa, "To na gode." Don na lura baya
son gayya.
Washegari Sagir ya zo ya bani kudi dubu talatin, wai inyi
tsaraba