Showing 12001 words to 15000 words out of 19791 words

Chapter 5 - Sanadin Boko Book 4 end complete by Halima Abdullahi k Mashi .txt

Kano. zaman sati 2 a camp ko ni na
san na yi missing din gwarzon masoya, Abubakar
Sadiq.
Fadima ta dubi Rukayya, "Kin san Allah ni zan kai karar
Hamma gurin Abba, sam baya cin abincina sai na
Hafsa. Don gulma har nan zaki ga ta yo ta aiko mishi
da shi, kenan ya fada mata cewa ban iya girki ba."
Rukayya ta ce, "Ai Hamma ta riga ta gama da shi, ke
har su Daada ma in kinji yanda suke yabonta? In ta yo
abinci ta kawo ma Abba kiga su Ummi har ma Daada
din sai suyi ta yabonta." Ta ce, "To gurin Lamido
zanje." Rukayya ta ce, "Kin ji ma inda zaki fi jin dadin
kai karanki, kuma zaya ci musu daga shi har ita. Dama
ai ba son auren yake ba, kila ma yana kushe auren."
Cikin zumudi Fadima ta ce, "Anjuma zan je."
Ta shigo gidan da sallamarta suka gaisa da mutan
gidan, tsoffin suna mata tsiyar cewa sun kwace miji. Ta
shiga gurin Lamido, bayan sun gaisa ta ce dama ta
kawo karan Hamma ne. Lamido ya gyara zama ya ce,
"Tun kafin aje ko'ina har an soma matsala? To me ya
faru?" Ta ce, "Baya cin abincina, ranar da yake gidana
sai ya aika nan a karba mishi abinci fa, kuma in nayi
magana sai ya ce ta fini iya girki. Shi ne ni na gaji da
wannan maganar." Can ya ce, "Shikenan?" Ta ce, "Eh."
Ya ce, "To yanzun ina Baban nawa?" Ta ce, "Yana cikin
gari." Lamido ya kira shi a waya ya ce ya zo yana
nemanshi. Kusan minti 30 sannan ya iso Lamido ya ce
masa, "Daga ina?" Bai ji mamakin ganin Fadi ba.
Lamido ya karanta mishi laifukan da ta fada, sannan ya
tambaye shi ko haka ne? Abubakar ya ce, "Haka ne."
Lamido ya ce, "Don me to baka son cin abincin nata?"
Abubakar ya ce, "Don bata iya ba, kuma don na amso a
gurin Hafsat wadda ta iya bana zaton na yi laifi.
Saboda Manzon Rahma (S.A.W) yana amso abinci a
gurin Nana Safiyya ya ci in yana dakin kowacce daga
cikin matanshi. Don haka ni Sunna na yi." Ta ce,
"Amma shi bai yi wulakanci ba." Lamido ya ce, "To naji
yanzun dai sai kiyi kokari ki gyara." Abubakar ya ce,
"Abin da in riga ta dawo wa kullum sai na fa jira ta ta
dawo sannan ta min abincin. Ita kuma Hafsah ko ina
zata sai tayi min abincin ta bari in dai tana gari, amma
ita wannan sai son jiki." Lamido ya ce, "Ka yi hakuri
tashi ka je abinka.Bayan fitar Abubakar Lamido ya ce,
"Ke Fadima abin da zan fada miki, kin ga bakuwar
yarinyar nan? To ta fiki hankali. Tun yaushe rabonki da
gidan nan da sunan ki zo gaishe mu? Ita kuwa ko bata
garin nan ta kira mu ta gaishe mu a waya. Girkinmu
daban ga girmama mutane, don haka ki nutsu ki zauna
lafiya. Ba zan 'kita ba don tana bare, dama ai mugun iri
ake tsoro." Fadima dai ta tashi jiki babu kwari ta tafi
gida, zuciyarta cike da haushin Hafsah, wato ta zo zata
siye dangi? Ta ja wani Uban tsaki.
Allah cikin ikonsa mun gama CAMP sai dai Abubakar
ya ce zai yi duk yanda zai yi a barni a Yola, ba zan
kara nisa da shi ba. Daga baya ma ya ce in na gama
bazan yi aiki ba, ni dai ina jin shi ban ce komai ba.
Allah ya taimaka da ya shiga ya fita sai ko aka barni a
Yola, ni kaina nayi murna don bana son inyi nisa da
mijina, Shadad ya dawo Yola shima Abubakar ya canza
masa Makaranta mai kyau, duk da cewa Iyayenshi suna
ta turo kudi wai na karatunshi. Dad har Yola ya zo
kuma ya sanar da abokinshi Mai Martaba Baban su
Hashim cewa Shadad jikan shi ne, don haka yaron bai
da matsala ko cikin gida, gashi da farin jini.
Cikin haka ne FADIMA TA SOMA LAULAYIN NAN, naga
rawar kai wurin Abubakar da 'yan uwansa, ganin haka
nima na soma zuwa kullum ina dubata, sai ta tsiri cewa
wai turarena na sata amai, in daina zuwa. Abubakar ya
ce, "Fadima ta ce bata son turarenki ki daina zuwa
kawai." Allah yasan na ji haushi, amma sai na share
saboda sanin halin Abubakar shi mutum ne sak babu
kwane-kwane a tsarin shi, baya rufa-rufa ko kara
zance, yanda aka fade ta haka yake daukenta, shi yasa
na sha wahala lokacin da na ce mishi ni karuwa ce, har
sai da ya zo ya ji komai da kunnanshi na samu sukuni.
To yanda Fadima ta ce haka zai fada gaskiya
tsagwaronta yake yi ba ruwanshi, don haka na ce, "Shi
kenan, na ringa kiranta a waya muna gaisawa." Ya ce,
"Hakan zai fi." Daga baya sai ta tsiro cewa ita ba zata
iya bacci ba sai in yana gurinta, Ya ce to bari ya same
ni. Ina kwance na dawo daga gurin aiki wata makaranta
aka turani ta 'yan mata nake koyarwa. Na yi abinci na
gama nayi wanka na kwanta, ya zauna na tashi na
mishi sannu da zuwa, na dire mishi abinci. Yana ci ya
ce, "The only, ina son ki yiwa Fadima taimako daya."
Na ce, "Na me?" Ya ce, "Bata samun bacci don
Rukayya ta fada min cewa zaune suke kwana. To tana
son in dinga kwana gurinta har ta dan
murmure."Zancen ya bani mamaki, sannan na fahimci
cewa makirci ne, amma sai na ce, "Ba komai." Ya ce,
"Dama na san ki baki da matsala." Da dare kuwa ya
tafi, haka-haka har sati uku. Sai dai fa in yana da
matsala ya yi min sammako ko kuma in ina gurin aiki
ya zo ya dauko ni daga baya ya dawo da ni. Ban taba
nuna mishi damuwata ba.
Lamido ya kira shi ya ce, "Ubana an fada min baka
kwana a gidan nan ko?" Ya ce, "Eh, saboda bata samun
bacci ne in bana na." Lamido ya yi murmushi sannan
ya ce, "An fada min kuma tana zuwa hurin aiki ko?"
Abubakar ya ce, "Eh, ai matsalar tata da dare ne."
Lamido ya ce, "To, daga yau na hana, kowacce ka
dinga kwana gidanta a ranar kwananta, kanta aka soma
ciki? An ce ta samu sauki ba shike nan ba?" Abubakar
ya ce, "Shi kenan." Har na soma bacci na ji kwankwasa
kofa, na zo na ce, "Wane ne?" Ya ce, "Ki bude." Na
bude na ganshi na ce, "A'a baka tafi ba?" Ya ce, "Ke ce
kika fada ma Lamido cewa Fadima ta ji sauki amma
ban daina zuwa ba ko?" Na ce, "A'a bani ba ce." Ya ce,
"To wanene?" Na ce, "Ka tambaye shi." Ya ce, "To ni
bana son kai kara, don ban soma zuwa ba sai da
izininki." Na ce, "To gaskiya ba ni bace." Ya ce, "In ma
ke ce din ai yana zuwa kanki, tunda an ce ai haka ciki
ke yi muku." Na yi masa shiru don haushi.
Abinda bai sani ba nima lokacin ina manne da nawa
cikin wata biyu, ina kuma laulayina sai dai bai yarda ni
ba, sai dai amai kuma nafi yin shi da rana, kuma ban
fasa komai ba.
Azumi ya kusanto ya zo ya same ni wai in zo muje
gidan Fadi, zai yi wata shawara, na ce to..........
Cikinta ya fito, amma yanda take tike kugu gami da
turo cikin ko watan haihuwarta ne sai haka, tana yi da
kyar take daga kafa, a dole ga mai ciki shi kuma
kallonta yake yana murmushi, ni sai suka ma bani
dariya. Ya kamata ta zauna yana yi mata sannu, ita ko
sai faman cije-cijen lebe take, na yi 'yar dariya nace,
"Maman twins an fito?" Ta ce, "Umm na fito." Muka
gaisa ya ce, "Dama saboda zuwan azumi ne ina son in
bada sadaka wa kuke ga ya dace in ba?" Fadima ta
dube shi, "Kawai honey ka bamu mana, ni ga ma
sayayyar da ke gabana na kayan baby." Ya dubeni, "Ke
fa?" Na ce, "Ka kai Masallaci ko ka samu mabukata ka
basu tunda Alhamdulillah mu muna cikin wadata." Ya yi
murmushi, "To dama nima tunanina kenan, don haka
zan bai wa masu bukata Zakka, sadaka kuma zan baku
ku bada, ko cikin family dinku ko nawa."ta zobaro baki,
"Kenan shawarata bata yi ba?" Ya ce, "Eh." Ta yunkura,
"To ai da ba'a kirani ba." Ya ce, "Hakkinki na baki da ba
sai na zo ba din, don nasan ita zata iya bani shawara
ta masu ilmi." Kudi ya zube min dubu dari uku da dari
biyar, wai in raba ma masu bukata. A zatonshi zan tafi
da shi gidanmu ne in raba ma dangina, sai na
tambayeshi zuwa kasuwa ya yarda. Ni da Ummi muka
je. Shinkafa kawai na lodo da taliya sai kuma zannuwa,
Ummi ta ce, "Aunty me zaki yi da shi?" Na ce,
"Sadaka." Ta ce, "Don Allah akwai wasu dangin su
Daada dake can wata ruga talakawa ne, jiya ma Abba
ya aika musu da gero da sugar na kunun azumin." Na
ce, "To." Daada din naje na samu na ce, "Sadaka zan
raba ta abinci saboda neman falalar wannan wata, to
ina so in cire na dangi na can Ruga shine nake so ki
cire musu nasu sai na ba makota sauran." Ta ji dadi
sosai, tayi ta shi min albarka, duk da ta san cewa shi
ne ya bamu kudin, ta ce min ya shawarceta, ita ce ma
tace yayi shawara da mu, ta ce ya ban kai dangina ba?
Na ce, "Da ku da dangina Daada ai duk daya ne ba
wani bambanci." Ta ce, "Allah ya shi min albarka. Ta
cire musu sannan na saka 'yan samarin gida mua yi ta
mika wa makotanmu wadanda ke da karamin karfi.
Dama kananan buhuna ne. Lamido har kofata ya zo
yayi min godiya tare da shi min albarka. Abubakar
kuwa da ya dawo ya ga makota na ta mai godiya tare
da addu'a sai kuwa kanshi ya daure, da yai zaton geron
da Lamido ya raba ne, sai da ya je gurin Lamidon shi
ne ya bashi labarin abin da nayi sannan ya ce, "Ka rike
matarka hannu 2, don ka samu macen da babu irinta
cikin yaranmu, Allah ya azurta ku da Yara masu
albarka." Abubakar rungume ni yayi tare da min godiya
na ce, "Allah shi ne abin godiya." Ashe zakkar shi can
ya kai ma su Babana bayan ya dibar ma Innarmu.
Shima bai fada min ba sai da Ya Umar ya kira ni ya
fada min wai mijina ya kawo wa Baba zakkar kudi naira
miliyan 2, Inna dubu dari biyar, in masa godiya sannan
yana son mu yi shawarar abinda za'a siya. Na ce,
"Yaya Umar ku nemi dan madaidaicin gida ka sai ma
Baba kawai." Ya ce, "Nima haka na ce, kuma shima
Baba zai so hakan. Allah ya saka masa da alheri." Na
ce, "Amin.
Kuka na saka da muka gama wayar, ban san ko kukan
me nake yi ba, na farin ciki ne? na son mijina ne? na
barin iyayena baya ne? Oho. Inna ma ta kirani ta ce in
masa godiya na ce to.
Da ya dawo kuka na sa tare da rungume shi, ya rude
ya firgice yana tambayata, "Me ya faru D Only? Wa ya
taba ki?" Na ce, "Ba kowa, na gode da taimakon da ka
yiwa Iyayena, Allah ya saka makada alkhairi, Allah ya
kara budi, ya tsare ka daga dukkan sharrin abin ki, ya
kuma bani ikon binka sau da kafa." Ya shafa kaina,
"Amin Masoyiyata, game da batun Zakka kuwa ba sai
kin min godiya ba hakki ne na Allah na cire." Na ce,
"To da ka cire din da kaga dama ai wani zaaka ba." Ya
ce, "To shike nan." Da dare muna kwance ya ce, "Wai
ya za'ayi da sayan kayan Sallanku? Kudin zan baku
kuje kasuwa ku siyo?" Na ce, "A'a da kai zamu je
saboda ka zaba mana son ranka." Ya ce, "Bari sai na ji
ra'ayin Fadima." Ya janyo wayarsa ya kirata, "Sweet
heart." Ta amsa da, "Na'am Sweet honey." Ina jin
muryarta, don ina jikinsa ya ce, "Gobe zaku shirya ne
mu shiga kasuwa tunda bani da aiki?" Ta ce, "To, daga
nan sai mu siyo kayan Babys din tunda an ce mace da
namiji ne?" Ya ce, "To sai ki shirya zamu shigo wuraren
11am saboda kada ki sha rana ko?" Ta ce, "To Honey
sai kun zo." Ya ce, "Yauwa, ki shafa min Babys." Suna
yin sallama na kankame shi, "Yan biyu zamu samu?" Ya
ce, "Eh, dazun da ta dawo asibiti take fada min wai an
ce 'yan biyu ne mace da namiji." Na ce, "Kai na yi farin
ciki, ina son twins shi ne baka min albishir ba?" Ya ce,
"Na same ki kina kuka yaya zan tuna da maganar 'yan
biyu?" Na ce, "Allah ya sauke mana ita lafiya." Ya ce,
"Amin, kema Allah ya baki ina son in ga kin haihu, duk
wannan dina har yanzun ba ciki, ko dai zamu je asibiti
ne?" Na ce, "Haba dai, duka yaushe aka yi abin? Ko fa
shekara banyi ba." Ya ce, "Don Allah ki daina zancan
nan, yara nake so sosai, yanzun kin ga zan fara da biyu
na zo daidai da Kanina Usman, in kin haihu ko da daya
ne kin ga na fishi ko? Balle ma kema biyun zan baki."
Na ce, "Oh! Kai ne ma kake badawa?" Ya ce, "Allah ne
zai bani ni kuma in baki." Na ce, "Dama kun gaji 'yan
biyu ne?" Ya ce, "A family ni zan fara, shi yasa kowa ke
doki, jiya kinga yanda 'yan uwa ke murna?" Na ce, "Ai
abin so ne, Allah ya bamu masu albarka." Har zuciyata
na taya shi murnna.
Katon super market muka shiga, gefen zannuwa, lesuka
da shaddoji zuwa yaduka, ya ce mu zaba, na ce, "A'a
ka zabo mana." Sai cewa Fadima ta yi, "Ni zan zabi
abina." Na ce, "To ni ka zabo min." Duk wanda ya miko
min ko bata kamfanin ba amsa nake in ce yayi kyau. Ya
ce, "To dama atamfa ce nake da irin wadda nike so,
amma sauran zabi." Da muka gama sai na zabar wa
Ummi atamfa da Shadda da leshi Rukayya ma haka.
Daada kuwa yawan namu na daukar mata, ya bini da
kallo itama haka ya ce, "Wannan fa?" Na ce, "Na su
Daada ne, ta ce, "Su Daada ne za'a sai ma kaya?" Ya
ce, "Shi ne ai, su Daada da ke da super market zuwa fa
zasu yi kawai su zaba...........".......




Zaharaddeen Shomar
whatsapp 08168575100




Sanadin Boko 4-06
Posted by ANaM Dorayi on 05:20 AM, 29-Sep-15
Under: SANADIN BOKO
Na ce, "Za ka biya ko in biya?" Na fada cikin daure
fuska, ya ce, "A'a zan biya in basu amsa ba sai kin san
yanda zaki yi da su." Fadima ta ce, "Neman gindin
zama." Ban ko kalle ta ba shima bai ce komai ba. Da
muka isa gurin da ta sai Shaddoji da Yaduka sai na dibar
ma Abba, ya ce, "Dama kin daina wahala na fa san ba
zasu amsa ba." Don haushi ban kuma tanka su ba, don
Fadi sai dariya take yi, ban fasa dibar musu ba, har
turaruka na dibarma Abba, su kuma kayan shafa. Ita
kuma muna zuwa gurin kayan Babys nan tayi ta jida,
kowanne bibbiyu ni ko nayi ta taya ta. Da muka je gurin
takalma da jaka na zaba musu. Da zai sai nashi na zaba
ma Abba har huluna ya ce, "Ke baki san lambar takalma
ka kina ta diba har da hula." Na ce, "Ido ba mudu ba ya
san kima." Ita kuma ta ce, "In da rabon ka tafka asarar
kudi ai shi kena." Ni sai na sharesu kawai na ci gaba da
lamurana.Mun dawo gida cike da lodin kaya, but din
mota shake, kujerar baya shake, da kyar na dan samu
gurin rabawa. Dama hakima ta gaje gidan gaba, ita muka
soma saukewa sannan muka wuce gida. Muka yi ta jidar
kaya zuwa ciki, har lokacin fuskata daure saboda yanda
yayi ta gwasale ni, don kawai na ce ya sayawa Iyayenshi
kaya. Ba gidan zai sha ruwa ba yau, don haka ina yin
sallah na kwanta sai bacci, ban san lokacin da ya tafi ba
ma ni. Sai da ya dawo Asham sannan ya biyo gurina, ya
samu ina sallar Asham din nima, ya zauna yana kallona.
Na idar na gama addu'a ya taya ni shafawa na dube shi,
"Sannu da zuwa." Ya ce, "Yauwa, na zo ne inga ko kin
huce, naga yau an yi bacci an share ni." Na ce, "Ai bani
fushi da kai Mr Cool." Ya yi murmushi na ce, "To yanzun
dai sai na dauko maka ka kai musu." Ya ce, "Sai dai ki
zo muje tare, dan kuwa ba za'a sace min gwiwa ni daya
ba.Na mike na dauko hijabi zan sa ya ce, "Zo nan." Na
zo ya dubeni sama da kasa, "Wai wanna kibar fa? Sama
da kasa duk kin cika?" Na shafi kumatunshi na ce, "Ka
iya kiwo ne." Na mika mishi ledar dan in bagarar da
maganar, "Ga wannan mu je." Ni kaina na san cewa na yi
kiba, cikina a kirji da hips ya tsaya, marata ba me cewa
ina da cikin wata biyar da 'yan kwanaki. Duk a falo muka
same su suna kallon Tafsir din Sheikh Amin Daurawa, na
zube na gaishe da Daada da Abba, Ummi da murna ta
hawo jikina, Daada na mata fada da fillanci. Rukayya ta
tabe baki ta gaisheni a dakile. Abba ya ce, "Daga gida ku
ke?" Na ce, Eh! Ya ce, "To sai ki basu." Na ciro ledar
Daada na yunkura naje gabanta na ce, "Gashi in ji shi."
Dama bana iya kiran sunanshi a gaban Iyayenshi. Ta ce,
"Me muka samu?" Na ce, "Kayan sallah ne ba yawa." Na
mika ma Ummi da na Rukayya sai suka hau murna,
Rukayya ta daga kai ta ce, "Hamma ya aka yi kasan
kalolin da muke so? Ni komai ja Ummi komai pink." Ya
kalleni, Daada ma sai murna take yi tana fadin, "Allah ya
shi maka albarka ya baka zuri'a ta gari wadanda suma
zasu fita hakkinka." Ya dube ni na kauda kai ina fadin,
"Amin Daada." Na mika ma Abba nashi wanda ke
kallonmu yana dariya tare da fadin, "Masha Allah." Ya
ce, "Har da ni? Ikon Allah Abubakar an yi hankali." Muka
sa dariya. Bayan an nutsu ya ce, "Wato Hamma abin da
yasa kaji na ce ashe kayi hankali shi ne, ka sani duk
kudinmu muna da hakki a kanka, kuma na gode Allah ya
kara budi." Muka ce Amin. Ya ce, "Ni fa da har ba zan
sai muku ba naga kuna saidawa." Daada ta ce, "Don
muna saidawa shi kenan bazaka fita hakkinmu ba?" Ya
kalle ni, nayi maza na kauda kai don bana son ya ce
nice. Abba ya ce, "Bari Usman ya zo ya kai ma telana
su, don da su zan je Idi in Allah yasa mun kai lokacin."
Haka suka yi ta shi mishi albarka, tare da yi masa fatan
samun zuri'a tagari. Da zamu tafi Rukayya har mota,
Rukayya ta ce, "Hamma Allah ya kawo mana 'yan biyu
lafiya..." Muka ce Amin. Har lokacin wani gani-gani take
min suka juya. Ko nisa ba suyi ba ya wani kankame ni ya
rungumeni ya ce, "Na gode D Only, na gode da sani a
hanya da kika yi, ni a zatona tunda iyayena suna dashi
fiye da ni ba sai nayi musu wata hidima na sai dai in ma
danginsu marasa shi daga ciki." Na ce, "Ko sune suke
kera kudi wajibi ne ka basu hakkinsu, yi musu biyayya na
san kana yi, yi musu alheri kai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login