Showing 3001 words to 6000 words out of 13538 words

Chapter 2 - KARUWAN CIKIN GIDA OUM YASMEEN.pdf

10 May 2025

4019

jikan bambaline shi cikin sauri yace '' ummi lafiya naga kina ɗawafi...,
Altab ba dole kaga ina ɗawafi ba Wallahi lamarin dagin mahaifin Jawad ya ishe ni dole muyi fito
na fito da su haba wannan wacce irin jaraba ce su barmin ɗana ba ruwan su dashi.
zama yayi yace '' ummi kenan Allah ya kyauta amma dai lokacin da kika tafi kikai fushin zuciya
wa ya rike miki shi ni wallahi duk irin wa'yannan abubuwan dama zaki gane ki dena saka kanki

a ciki..,
ji tayi tamkar ya zuba mata wuta a fusa tace '' lallai altab sai yau na kara tabbatarwa shaye
shayen da kake yi ya ta ɓa maka kwakwalwar ka fice ka bani guri wanda baya kishin kan'sa..,
tashi yayi yana sosa sumar kansa da ta sha gyara yace '' kudin hannu na sun ƙare me zan
samu ne...,
Ubanka za ka samu altab, wallahi nagaji nagaji ka nemi sana'a ka fara yi kudina bana shalholiya
bane bana tara matan banza bane idan ka yi zuciya ka tafi ka nema a, duk wani abu da kake yi
a guest house ina sane dakai wallahi ka guji ranar da zan faɗawa jawad.
altab yace '' to shikkenan kar Allah ya saka ki bayar wallahi ba zaki ƙi gani ba tun da haka kika
ce zan ɗin gima miki babban aiki na bar ƙasar badai kin fara tsanata ba dan ina faɗa miki
gaskiya da kuma munafukai da suke wure miki kunne any way dake da su za ku gani yasin
daga nan zuwa karshen shekarar nan kowa zai ga abin da zai faru da shi.., EPISODE 2
Dan Allah altab karka fasa abin da kayi niya me ka mai dani banki ko me kullum kace na baka
kuɗi to wallahi zan kirawo JAWAD ya zo ya raba ni dakai da me zan ji..
be ce mata ƙala ba ya wuce yana cewa za dai ki gani har su munafukan naki..
Dafa kan'ta tayi tace '' altab ni kake faɗawa haka..,
fita yayi yana sakar fito zama tayi tamkar wacce ruwan sama ya jiƙa ta bata san yadda za tayi
da altab ba yana neman ya gagare ta , da sauri ta tashi cikin sauri ta sau stair case shiga
bedroom din ta , tayi da sauri ta bude wata loka wani key ta dauko ta ma yar ta rufe fitowa a
hankali take saukowa saboda jin alamun kamar akwai baki a ƙasa aikuwa ilai Hajiya rukayya ce
haɗe rai tayi ta zauna tare da ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya akan kilishi tace '' Hajiya rukayya nasan
tun jiya sakona ya isa kunne ki amma me yasaka sai ya zu kika zo..?,
Wani murmushi Hajiya rukayya tayi tace
"It's only now that I got the time"
Ummi hannunta ta ɗun kule waje ɗaya tace '' okay yayi kyau zaki iya tafiya na riga da na gama
so yanzu bani da bukatar ki, daman kwaɗayi ya kawo ku kowa ya san kuɗa gurin kwaɗayi yake
mutuwa..,
What ni kike faɗawa haka...? ya cutar min da yarinyar ki dinga faɗa min haka lallai ma Hajiya
bilki good yayi kyau tun da haka kika ce kuje ku ɗa Allah dakin ya kusan kashe min ya' ki dinga
faɗa min haka..
da sauri ummi ta ɗago tace '' to kima godewa Allah da be nakasa ta ba in banda iskanci duk
wani abu ai tayi shi a waje ta shigo da yan iska cikin gidan sa ta tunda tunanin ba zai iya yi mata
komai ba saboda gata yar gwal suna mai shaye shaye wannan wacce irin rayuwa ce..,
dariya Hajiya rukayya tayi tace '' da yar tawa da ɗan naki ai dan jumane da yar jummai sittin ce
take dukan saba'in..,
wani kallo tayi mata tace '' dan haka dole ya je ya samo yar mutunci ya aura...,
wata uwar buɗa Hajiya rukayya ta saki tace '' wallahi karya kike baki isa ki canza ayar Allah ba
Ubangiji ne yace Az-zāninī laa yankihu illā zāniyatan aw mushrikatan, waz-zāniyatu laa
yankihuhā illā zānin aw mushrik; wa hurrima dhālika 'alal-mu’minīn wallahi, you're lying The
relationship between Altab and Samha hasn't even started. No one has the right to enter this
house,,
Haka kika ce ga hanya nan zo maza ki barmin gida na tun kafin na ci miki mutunci...

Cewar ummi
tashi Hajiya rukayya tayi tace '' au cin mutuncin na nawa kuma ɗan haka ina me sheda miki tun
da sheɗanin dan ki ya lalata min ya' to wallahi zama yanzu suka fara shi, duk ba shi ya cutar
min da yar tawa ba mene be koya mata ba , itama rashin jin ta ga samari nan nawa suka fito
suka ce za su aure ta daman dole zaman su ya zamo da zargi saboda an riga tun a waje an
lalata zamantakewa ba ta yadda za ayi a cikin gida ta ginu wallahi ko yawo kike yi a kan dutsai
tsirara altab be isa ya zaki samha ba shi da ita mutu karaba talmin kaza da kike cewa son abin
duniya mu kayi ke da ba kya so ki zubar dashi a ƙasa ban da rainin da kukai mana kuna ganin
mu talakawa ne , amma har kya budi baki, ki faɗa min haka kamar yadda kike son ɗakin haka
nake son ya'ta in ban da rainin hankali har mu zaki kalla kice son abin duniya ya rufe mana ido
Hajiya bilki kin manta amintar da take tsakanin mu kin rufa idon ki, kin ci min mutunci bayan kice
kika zo kina lallaɓani akan auren nan shima haka to wallahi ba ku isa ku mai damin yata ba
bazzawara..,
cije lips din tayi ji take tamkar ta shaƙe ta har Hajiya rukayya ta fita bata ce komai ba ji tayi
kamar tayi cille da wayar ta da sauri ta dauki key da mukullin da ɗazu ta fito da shi ta fita daga
cikin part din ta cikin sauri take komai har ta isa part din altab shiga gate ɗin farko tayi sannan ta
bi ta wata kofa nan ne ta shiga ainin farfajiyar gidan ga motar altab a ajiye a parking space kai
ta gyaɗa da alama yana cikin gidan,
tura kofar parlour sa tayi jin kiɗa na tashi tamkar a shahararren club din america..
jirine ya kusan kwasar ta dafe kan'ta tayi da yake juya mata a gurin ta sulale a ƙasa numfashin
ta na kaiwa yana kawowa da sauri ya ƙaraso gurin ta.
ɗago mai hannu tayi tace '' basai ka taɓani ba zan iya tashi...,
dafa bango tayi dakyar tana tafiya limshe danuwanta, tayi da suka cika da kwalla bata so ta
zubarwa da altab hawaye domin hawayen ta masifa ne a rayuwar'sa biyota yayi tace '' wallahi
tun kafin ranka ya ɓaci ka kawshe matan da kakawo cikin gidan nan ban da iskanci da
wulakanci gidan auren ka zaka kawo mata kuna shaye shaye.., to shikkenan ummi zan kwashe su amma bazan je na tawo da matata..
da sauri ta juyo jin zancen da ya furta anya kuwa kan'sa ƙalau lallai, ɗazu ma da ta mara mai
baya dan dai Hajiya rukayya ta nuna mata rashin mutunci ne amma ko dukan da yayi wa samha
bata ji dad'i ba duk da itama da laifin ta idan mace za tayi aure komai barin sa take yi a waje ta
shigo gidan mijin ta da kyakkyawar niya amma ita bata san wannan ba ta dinga tara matan
banza kuma bata kunyar wani ya gani suna shaye shaye ajiyar zuciya ta sauke tace '' ga hanya
nan tafi wallahi yan uwanta sun shirya tsaf kana zuwa zasu kama ka haka kurum ka kama yar
mutane ka naɗa mata duka ita , duk abin da ake aikatawa me take maka..? wallahi ko da wasa
kar na kara ji ka saka hannu ka daki yar mutane mace da kake gani daraja ne da ita..,
shiru yayi har ta gama zancen ta , ta fita da sauri hany ta biyo bayan sa tace '' Man what is
happening..?,
shafa gefen fuskar'ta yayi yace '' no bakomai ke da su mufee ku tafi zan neme ku ko wacce ta
turo account number din'ta..,
da sauri ta riƙe mai hannu tamkar za ta shiga jikin sa tana mai wani irin kallo tace '' amma didn't
you say we would spend the night here today? How many of us are even here?,,
matsar da ita yayi daga jikin sa yace '' Please hany kuyi abin da nace kafin raina ya ɓaci idan
kuka kika ce ba in da ki tafi wallahi sai na farfasa miki jiki da duka ba ku ga abin da take shirin

faruwa ba oh da ba mahaifiyar ki bace shine ba abin da ya dame ki to duk iskancina ina son
mahaifiyata bana so na rasa ta..,
bata ce komai ba ta juya ta bar gurin samin su mufee tayi suna zaune sun yi ɗare ɗare akan
gadon sa suna busa shisha tace '' maman My man ta bashi umarni ya fitar damu daga cikin
gidan nan ku taso mu tafi yace ko wacce ta turo mai account number din'ta...,
ransu be so ba suka tashi suka bar gidan bama suyi mai sallama ba..

*OSOKORO........*
*STUDY ROOM....*

tunda ya shiga yake aikin office da ya tarar mai kwana biyu da yake yayi busy ba ya ƙasar sai
yanzu ya samu yake rage wa kan'sa ne ya dauki chaji gaba ki ɗaya wayoyinsa ya kashe su,
yana bukatar hutu da kaɗaici domin yayi aikin sa ba kuskure..
ji yayi an yi knocking kofar sa yasan wace dafa goshin sa yayi yace '' abu ɗe yake..,
jin haka da sauri ta murɗa handle din ta shigo zama tayi akan ɗaya daga cikin kujerun da suke
study room din tace '' ummi ce ta bugo duk layin ka a kashe yake ce maka..,
ajiyar zuciya ya sauke shi ya amshi wayar tare da karawa a kunne yace '' Assalamu alaiki ummi
barka da yamma...,
JAWAD riƙe gaisuwar ka bana so bana so wallahi ai baka mai dani mutum ba wayancan
Mutanen da na raba ka dasu sune mutane har ka iya zuwa yola baka zo gurina ba ina matsayin
mahaifiyar ka , ka kyauta dole suyi min abin da suka ga dama su nuna min ban isa da kai ba sai
su, suka isa dakai ban ce maka ba , na rabaka da duk ahalin ɗan buzu musamman ma Hajiya
farida bani da wata wacce na tsana sama da ita dan haka kai gaggawar mai da mata da yar ta ,
wallahi wallahi wallahi JAWAD idan ka sake kayi abin da na ke zargi to bani ba kai ban da
iskanci tun wuri ka rabu da ita mana to wallahi alkali mudassir ya taro abin da yafi karfin sa
domin duk abin da yake faruwa ina sane wato za su fage da guzuma su harbi karsana ko to
sunci karya bakai ba jinin Hajiya farida da Alhaji Sharif..,
kifa kansa yayi akan table rasa ina zai saka kan'sa yayi anya kuwa Mahaifiyarsa, tana tsoron
Ubangijin'ta me wannan baiwar Allah tayi mata tun da ya taso be san dadin uwa ba , watan sa
takwas ita da mahaifinsa suka rubu dan haka bata tafi dashi ba ta bar shi ba ruwanta ya mutu
ko yayi rai sai bayan ya kammala digree dinsa na farko yana shirin tafiya egypt ƙaro karatu ta
bayyana be rayu da ita ba , tun daga bayannara ta zuwa yanzu kullum cikin saka shi take a
damuwa da farko da ta bayyana yaji dadi be taɓa zaton ba hajiya ce mahaifiyar sa ba suma
haka su NAJLAH sai a lokacin suka san me yake faruwa ajiyar zuciya ya sauke yace '' ummi
insha'Allahu zan kiyaye duk abin da kika shinfiɗa min wallahi bawai haka kurum naje yola ba a'a
na can na sauka gobe nake so na zo mu gaisa..,
kashe wayar tayi saboda ai ta riga da ta isar da sakon'ta miƙa wa jawaher yayi,
amsa tayi tace '' amma sweet lafiya ko ba wani abu ne ya faru ba..?,
bece mata komai ba ya nuna mata hanyar fita sum sum ta fice tana danne dariyar ta ,
ci gaba yayi da aikin sa bayan ya gama ya tashi ya fito ba kowa a parlour kai tsaye bedroom din
sa ya nufa tana kwance tana waya tana ganin sa ta katsai wayar tace '' badai la gama ba ?
Amma kuwa idan haka ne kayi saurin gamawa...,
zama yayi bakin gado yace '' eh na gama kije kice NAJLAH ta haɗa min coffee..,

tashi tayi tana cewa to an gama oga kiss tayi mai a kumatu tace Allah ya bar min kai ya
makantar da idon yan mata akan ka...,
dan murmushi yayi mata yace '' amin...,
da sauri ta dawo ta zauna riƙe hannun sa tayi tace '' idan har hasashena ya faɗa min gaskiya
kamar akwai abin da yake damun ka amma kaki sanar min idan ma tafiyar ce baka so nayi sai
na fasa shikkenan magana ta ƙare amma wannan haɗa ran ban saba da shi ba kullum na fiso
mu ɗore cikin so da kaunar juna da fahimtar juna shekara biyu da auren mu bamu taɓa samin
matsala ba kar yanzu akan tafiyar nan mu samu beb idan haka ne ni wallahi na hakura ma da
nayi tunani ko wani abu ummi ta faɗa maka da na kuma ƙara wani tunanin sa naga ita uwa ce
me son farin cikin ɗan ta ba za ta taɓa faɗa maka abin da zai saka lokaci kali lan ba ka shiga
cikin damuwa , ina kyautata zaton nice sanadin komai,
saukowa tayi ƙasa ta damƙe hannuwansa idanuwan'ta ya taru da kwalla fal sakin hannuwansa
tayi ta haɗe hannuwanta biyu alamar ban hakuri ta ci gaba da cewa.
Dan Allah ka yafe min mijina bana so ka kwana kana fushi da ni bana so na zama sillar bakin
cikin ka , ka dawo daga tafiya kamata yayi na faran ta maka be kama ta na bakan ta maka ba...
Kwantar da kan'ta tayi yasha kan'ta yayi yayin da wani sanyi yake ratsa zuciyar'sa hakika
annabi yayi gaskiya da yace idan namiji ya dace da mace ta gari to kamar ya samu rabin addini
ne yana kaunar jawaher yana son ta fiye da son da yake wa kan'sa baya iya kallon ko wacce
mace a matsayin mace , Hakika jawaher rabin jikin'sa ce.. cikin daddaɗan sauti yace '' wallahi
baki yi min komai ba idan ma kwai na yafe miki sweet stress ne yayi min yawa ina bukatar hutu
amma ni baki min komai ba jeki, ki faɗa mata , ta haɗa min kafin na fito daga wanka..
Hmmm ku biyoni dan jin wanne darasi wannan labarin ya kunsa
# KURUWAN CIKIN GIDA
EPISODE 3
Ɗago idanuwan'ta tayi cike tab da hawaye share mata yayi yace '' bana so na ganki cikin
damuwa..,
Murmushi tayi ta tashi, ta karasa share hawayen ta , fita kai tsaye bedroom din NAJLAH ta
shiga turawa tayi ba tare da tayi sallama ba , tana kwance wayar ta na hannun ta taɓe baki tayi
ta kalle tace '' sweet yace ki haɗa mai coffee..,
ajiye wayar hannun ta , tayi bata ce mata komai ba ta miƙe ganin haka ita mata fita, tana shiga
tarar dashi tayi ya shiga wanka zama tayi tana charting da wayar ta fitowa yayi yana tsane jikin
sa batare da ya kalli inda take ba yace '' kin faɗa mata..?,
ajiye wayar ta , tayi tace '' na faɗa mata amma bata ce min komai ba bama ta kalli inda nake ba
balle nasan taji me na faɗa..,
ajiye towel din hannun sa yayi ya fita a hankali yake saukowa cikin nutsuwa kamar ba sauri
yake ba yana sauka kai tsaye bedroom din NAJLAH ya nufa murɗa handle din kofar yayi da
sauri ta dago tare da ja da baya tun da take dashi a rayuwar'ta bata , taɓa ganin sa acikin
makamancin wannan yanayi ba ko exercise zai yi da dogon wando yake tafiya balle wannan
daga shi sai towel a ɗaure a kugu lallai auren da yaya yayi ya mai dashi wani iri,
ƙasa tayi da kan'ta tace '' yanzu zan kawo maka..,
okay ita da kikai mata shiru kenan raina ta kika yi..?,
ya jefo mata wannan tambayar bata , taɓa tunanin jin wata magana makamancin haka abakin
sa ba. turi ƙaramin bakin ta , tayi tace '' nace mata to..,

karya kenan take miki..?
da sauri ta ɗago kwallah har ta fara taruwa a idanuwanta ja da baya tayi tana sauke ajiyar
zuciya ganin ya matso kusa da ita tamkar zai shige jikin ta da sauri ta, tashi tace '' bara naje na
duba kar ya gaji da tafasa..,
ratsawa tayi zata wuce riƙe hannunta yayi da sauri ta juyo anya kuwa yaya Jawad lafiyar sa
qalau ko kallon ta ya ke kamar jawaher ta shiga uku da sauri ta saka ɗaya hannun nata , zata
cire hannunta da ya riƙe wani irin shock yaji ajikin sa da sauri ya cika mata hannu kasa koda
motsi yayi dakyar ya iya ɗaga kafar sa ina yaga abin ba zai yiwu ba hannun sa ya saka ya
kashe switch din fitilar dakin a gigice ta ɗago da kan'ta sai dai kafin ta gama tantance wanne
yanayi take ciki ya hanka ɗata kan gadon ta yunkurawa tayi zata fita aguje amma ina be bata
damar haka ba , domin ya danne ta kuka ta sakar mai , sosai ta shiga kici niyar kwace kanta
amma ina ya ƙi bata damar haka.
ji tayi an buga mata pillowcase agigice ta , tashi tana zabga uban gumi ganin shine gaban tane
ya faɗi tunowa da tayi da abin da ta gani a cikin mafarkin ta , da sauri ta ja baya gaban ta na
faɗuwa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login