Showing 1 words to 3000 words out of 13799 words
Chapter 1 - WANI DARE Free book Na MUJAHEEDAH MATAR MLM AMMIEYN KHAUSAR.pdf
*WANI DARE Free book*
_RUBUTA LABARI DA TSARAWA MUJAHEEDAH MATAR MALAM, AMMIEYN
KHAUSAR.. HEEDAH HYDAR OSTHMAN...._
```MARUBUCIYAR.... 1-FAHAT HOT LOVE, 2-RAUNIN MACCE... 3-SAINA KASHE MIJINA..
4-SO SIRRIN ZUCIYA.. 5- ZUCIYAR NAMIJI.. 6- SILAR ƊA NAMIJI..7- BARRISTER
KHALEEL..8-AKAN PRE_WEEDING PICTURE'S..9-MAIZAMAN KANTA"PAID BOOK"
10-BAƘIN KISHI"PAID BOOK" 12-ABBAKAR SARAKIEY"PAID BOOK" 13-DORCTOR
HEESHAM.. 14- *TAƘAMA PAID BOOK* ALL MY WRITE'S MUJAHEEDAH MATAR
MALAM... AMMIEYN KHAUSAR.. HEEDAH HAYDAR OSTHMAN....```
```Godiya ga Allah maɗaukakin sarki daya sake bani ikon rubuta wannan sabon littafin nawa
maitaken *WANI DARE* Inaroƙon Allah daya yafemun kura kuranda zansamu ciki inda nayi
daidai kuma Allah kaban ladansa, Ameen... Allh kabawa ƙasata NIGERI'A ZAMAN LAFIYA
DA ARZIKI MAI AMFANI DA SHUWAGABANNI NAGARI AMEEN....```
_Kafin tafiyar tayi nisa ina neman Afuwarku Readers masoyana Akan dik inda zanyi kuskure,
Wannan labarin ƙirƙirarrene nayi Amfani da fasahata haɗida kwakwalwata kawai dan kawo
muna Abunda zamu Amfana banyishi dancin zarafin wani ko wata ba inma da gaske ke haka
kike toni bansani ba kawai nayi Amfani da ƙwaƙwalwatane nayi labarin dan faɗakarwa da
ilimantar da Al'umma, Kada kumanta dika littafaina ba satar fasaha ko kwaikwayar labarin wani
ko wata dika nawane na ƙashin kaina, then bana labari dan saka nishaɗi kawai inayine dan
muƙaru dama faɗakar da Al'umma.. KADA KUƊAUKA SAKA BATSA ALABARI ƊAUKAKA NE
KO SAMUN AL'UMMA WANNAN DIKA MAIDA KAI BAYANE WLLH DAN DIK ABUNDA KIKA
RUBUTA TO DOLE KITSAYU GABAN UBANGIJI DAMA KOWA DA KOWA RANAR GOBE
ƘIYAMA KIFAƊE ABUNDA KIKA RUBUTA DAMA DALILINKI NARUBUTA HAKAN, ALLAH
KASA MUDACE ALLAH KABAMU IKON RUBUTA ALKHAIRI AMEEN..... BARKA DA
SABUWAR SHEKAR MUSULINCI ALL_
*SUNDAY 31/7/2022 JULLY*
*BISMILLAHI RAHMANI RAHEEM*
…………… Wani kyakykyawan guy nahanga wanda bazai haura shekara 35 saje da ɗan
ƙaramin gemu ya ƙawata fuskarshi kansa ɗauke da sanyayyar suma baƙa silik, chaculate
colour ne amma dai ya haɗu fans.
Ahankali ya turo ƙofar palourn yashigo, ƙarema palourn kallon yayi yana nan yarda yabarshi
kan yaje sallar Assubah, ɗan tsaki yaja tareda nufan step step ɗin dake ɗakin bayan yagama
haurawa naga ɗakuna kusan 3 Amma ɗayan yafita daban 2 ne dai Ajere, Ahankali ya murɗa
handle ɗin ɗakin Yashiga, kallo nabi dakin yahaɗu gaskiya yaji komai, can ƙarshen gadon ya
hangota kwance dik tawani duƙunƙune cikin blanket ɗin,.
Ƙarasowa yayi tare da saka hannu yaɗan kawarda dogon gashinta daya rufe fuskarta, ƙuramata
ido yayi naɗan wani lokaci, nikaina kallonta nake itakanta chaculate colour ce maikyau fuskar
nan tata tayi fayau.,
Duƙoda kansa yayi Tareda huramata iskan bakinsa,
Ɗan motsawa tayi Amma still bata tashiba,
Sake huramata iskan yayi, Ahankali tabuɗe idanuwanta tazubasu tar Akan fuskarsa wanda
yanayinsa yayi daban dabazaka iyagano fushi yake ko fara'aba, Sake masa murmushi tayi tare
da faɗin "Dama Safiya tawaye sosai haka Ashe,"
Miƙewa yayi yanufe gaban Mirro yana taje sumar kansa Yace,"Olmost 7:30 dear amma ko
wankan tsalki bakiyi ba balantana sallah da haɗamun break fast, Akoda yaushe ina ƙoƙarin
nuna miki mahimmancin Sallah da ibada dazama cikin tsalki amma kullum kasa dulmiya kanki
ruwa kike Bansan meyasa ba, danayi ƙorafi kice saboda cikin ne gashi yanzu bacikin kuma ba
ɗa ba jika amma still baki sauyaba sannan Abun mamaki bama haka kike ba bansan meya
maidaki haka ba," Yaƙarasa maganar yaɗa ɗan dafe kaisa haɗida barin ɗakin dan doguwar
maganar nan datayi hartasashi ciwon kai, dama haka bayason doguwar magana Amma Ayanzu
kullum sai Humaira tasaka shi,.
Da sauri tamiƙe tare da lalabar ƙaramin towel ɗinta dake wurin taɗaura tafaɗa towel Agurguje
tayi wanka taɗauro Alwala tafito ta tayarda sallah, bayan tagama tagyara ɗakin sannan takoma
nata ɗakin ta gyara tasaka doguwar rigar materi'al ɗinta, batawani yi kwalliya ba Amma tayi
kyau fitowa tayi Amma wayam bayanan taduba ko ina bayanan tasan tabbas yatafi Office ne
dama lokuta da dama idan har taɓatamasa rai yakan horata dabarin gidan da ƙincin Abincinta,
zama tayi ɗaya dagacikin manyan kujerun ɗakin tazabga tagumi tunani tafara itadai iyasaninta
batasan ta da wannan halin ba Amma *WANI DARE☠️* Yasata sauyawa haka nantake,
ganin tinanin bazai tsinana mata komai ba yasa ta miƙe taje taɗaura girki bata jima ba ta
kammala, wani wankan tasake tareda sabon shiri gaban madubi tadawo bayan tasaka earpice
Akunnuwant tana sauraren waƙa, ɗaukar sarƙa tajeyi kan madubi ɗago kanda zatayi kawai
saitaci karo dawata mummunar halitta cikin madubin tasaka fararen kaya amma batada fuska
saidai kana iya ganin zanen inda fuskar tata take bakinta na Waje sai jini yake fita,. Wata irin
ƙara tasake tare da ja baya jikake kaffffff.....………………………………………………… …
*KOMAI YAFARU DA MAIRA WATO HUMAIRA? BANSANI BA AYANZU DAN ZANƊAN HUTA
AMMA DAN SANIN KUKASANCE DANI MUJAHEEDAH MATAR MALAM AMMIEYN
KHAUSAR... DANJIN CIGABAN LABARIN, BAZANCIGABA BA SAINAGA COMMENTS OVER
DAN SHINE ƘWARIN GUYWATA TINDA FREE NE TO KU ANTAYO COMMENT DA SHARHI
INBASU TO BACIGABA*
_COMMENTS SHARE FISABILILLAH_
_BASEERATA ITACE ARZIKINA_
WhatsApp number 07064904617 or call 07031012948
*WANI DARE Free book* *️6&10*
_RUBUTA LABARI DA TSARAWA MUJAHEEDAH MATAR MALAM, AMMIEYN
KHAUSAR.. HEEDAH HYDAR OSTHMAN...._
```MARUBUCIYAR.... 1-FAHAT HOT LOVE, 2-RAUNIN MACCE... 3-SAINA KASHE MIJINA..
4-SO SIRRIN ZUCIYA.. 5- ZUCIYAR NAMIJI.. 6- SILAR ƊA NAMIJI..7- BARRISTER
KHALEEL..8-AKAN PRE_WEEDING PICTURE'S..9-MAIZAMAN KANTA"PAID BOOK"
10-BAƘIN KISHI"PAID BOOK" 12-ABBAKAR SARAKIEY"PAID BOOK" 13-DORCTOR
HEESHAM.. 14- *TAƘAMA PAID BOOK* 15, _WANI DARE FREE BOOK_ ALL MY WRITE'S
MUJAHEEDAH MATAR MALAM... AMMIEYN KHAUSAR.. HEEDAH HAYDAR
OSTHMAN....```
*NASA DAUKAR GA MASOYANA MASOYA LITTAFINA KAWAI*
…………Shigowarshi gidan kenan tin A parking space yaji ihun nata cikin sauri yafito ko
parking baigama ba yanufo cikin, koda yazo tayi baya zata faɗi cikin hanzari yataro ta, tafaɗo
jikinsa, kiran sunanta yafara yana ɗan shafa fuskarta Amma shuru, hakan yasa yakwantar da ita
kan gado ya ɗauko ruwa masu sanyi yazuba Ahannunsa yaɗan shafamata Afuska, dogon
numfashi taja kafin Ahankali taware idanuwanta kansa, harzata sake wani ihun ganin shine
yasa tafaɗa ƙirjinsa tana kuka,.
"Colm down, faɗamun meke damunki meya faru ne,?"
Saida taɗan tsagaita kukan sannan tace ,"Haka kawai fa naga wata mummunar halitta
cikin madubinnan wllh,"
"Cikin madubi kuma,?"
"Eh wllh cikin naganta ko fuska batada amma tanada baki kuma Abakin jini ke fita," tana
magana tana nuna masa madubin har lokacin fuskarta ba ɓoye Aƙirjinsa bata duba gurin ba,.
Maida kallonsa gun madubin yayi cike da mamaki Amma baiga komai ba shikam,
Cikin kwantar da hankali Yace,"Kinga kawai kintsorata ne amma bakomai kitashi kawai,"
yana maganar yana shafa bayanta Alamar lallashi,.
"Wllh gaskiya nake gayama maka deen naganta,"
Ɗanshuru yayi naɗan wani lokaci yana karantar yanayinta eh kam yes A tsorace take ko
suman tsorone yasumar da ita, kenan Ana nufin gidan nasa nada iska ne Aljanu ko dai Ajikinta
suke ko kuma me,?
Kukan da tasake sake masa ne tareda ƙanƙamesa tana faɗin subar ɗakin shine yadawo dashi
Hayyacinsa,.
Cikin kulawa yace "ɗago,"
"Um ni tsoro nakeji," tayi maganar cikin muryar shagwaɓa tana ƙara narkewa jikinsa,
"Amma ba ina nan ba, to tsoro name kuma? nace ki ɗauko ki kalleni," ya ƙarasa maganar
cikin Muryar kasa.,
Jin muryarsa Ahakan yasa taɗan ɗago ƙaɗan amma still tana riƙe dashi,
Kallonsa take shima haka, kafin Yace ,"da kikaga Abun kinyi Addu'a kuwa,"
Sunkuyarda kanta tayi dan tasan intaci gaba da kallonsa yanzu yagano har ƙiɗa take
saurare lokacin,.
Ganin bata Ansaba kuma ta sunkuyarda kai hakan yabashi tabbacin batayi ba, Cikin takaici
Yace, "Kinga ni ba, danme bazaki riƙa gane gane ba? kinwatsar da ibada, baki Askar baki
sallah kan lokaci muddin bana gidan koma inanan sainasha daga kina wasa da ibada Maira
haka kawai cikin *WANI DARE* Dik kinsauya bansan dalili ba,"
Kanta Aƙasa tace "Kayi haƙuri zangyara insha Allah, yanzu muje kayi wanka kaci Abinci,"
Ajiyar Zuciya kawai yasauke yana yarabata da jikinsa yafice, binbayansa tayi itama tana ɗan
tinani tinane tinanenta...
***********((())))******
Zaune nahango wata ƴarbudurwa dabazata haura 22 years ba itada ƙawayenta biyu sai
fira suke suna ƙyaƙyata dariya, Sham "Bakida imani" cewar ɗaya daga cikin ƴanmatan
"Anga yamiki ina yafiya ne? kuma gashi sai ruwanmu yatsinke Abakin kaba, ba ita wasa da
ibada ba, ai wllh batama fara ganin tashin hankalin ba,"
Dariya suke sake gaba ɗayansu tare da tafawa,
"Kiji tsoron Allah Shamsiyya kidaina wahalar da baiwar Allah nan haka koma nace bayin
Allah nan dan har mijinta kina wahalarwa, waike bakima tsoron hakke harfa rabata da ɗan
cikinta kikayi why Sham me humaira ta tare muku Arayuwa ne kuke son ganin bayanta sama da
shekaru dan Allah kubarta haka,"
Keeeee!!! Zee nuna muna tsoron Allah zakiyi? kodan kinga kinsan sirrinmu kikeson wasa
dashi? to wllh bari kiji kindai sai halin ƙungiyarmu muddin Ogerh juju yasan cewa kinsan hakan
kuma kina wannan maganar wllh rasa ranki zakiyi to dan haka ina shawartarki daki kama
bakinki baruwanki kindaiƙi mu da ƙungiyarmu so baruwanki da dik Abunda zamuyi inko kekiji
bakyaƙi gani ba wllh," Sham taƙarasa maganar cikin masifa.
Meery Tace,"Wai ita gani take kamar tafi ƙarfinmu shiyasa take faɗamuna Abinda taga
dama kisani komai yawan ibadarki da tsoron Allah ki wllh cikin *WANI DARE* Ma iya maganinki,
kamar yarda mukayi maganin Humaira cikin *WANI DARE* Kema ma iya wllh,"
Hunm Sanin halinsu darashin imaninsu Yasa tace,"Allah shiryeku ni gobe zanbar garin ma
Amma kusani kamai nisan dare gari zai waye, cikin *WANI DARE* Allah zai sakawa Maira,
nabarku lafiya,. miƙewa tayi tabar gurin.
Sham Taja tsaki tace ,"wllh badan inajin ƙaunar Zee Araina ba wllh dasai naga bayanta
cikin *WANI DARE* Amma muje zuwa inƙere nayawo zabo na yawo dole suhaɗe watarana,
Maira tabijire mana kuma tayi sa'ar samun hand some saimu barta?,"
"Never dole tayita ganin masifu Akowanne lokaci domun ba'a taɓamu Akwana lafiya dik wandan
yaci tuwo damu to miya yasha, tabbas *WANI DARE* Nazuwa da zamu ƙara gigitata," cewar
meery cikin gurɓatarciyar hausarta dama ita ba musulma bace....…………………………………
*TABBBAH SARƘAƘIYA NIKAINA NAKASA GANO ME MA'ANAR WANI DARE☠️ YAKE
NUFI, AMMA SANNU AHANKALI ZAN FAYYACEWA MAKARANTA KOMAI INDAI MUNA TARE
COMMENT KAWAI NAKE BUƘATA.....*
*COMMENTS AND SHARE FISABILILLAH*
_BASEERATA ITACE ARZIKINA_
WhatsApp number 07064904617 or call 07031012948
*WANI DARE Free book* *️11&15*
_RUBUTA LABARI DA TSARAWA MUJAHEEDAH MATAR MALAM, AMMIEYN
KHAUSAR.. HEEDAH HYDAR OSTHMAN...._
```MARUBUCIYAR.... 1-FAHAT HOT LOVE, 2-RAUNIN MACCE... 3-SAINA KASHE MIJINA..
4-SO SIRRIN ZUCIYA.. 5- ZUCIYAR NAMIJI.. 6- SILAR ƊA NAMIJI..7- BARRISTER
KHALEEL..8-AKAN PRE_WEEDING PICTURE'S..9-MAIZAMAN KANTA"PAID BOOK"
10-BAƘIN KISHI"PAID BOOK" 12-ABBAKAR SARAKIEY"PAID BOOK" 13-DORCTOR
HEESHAM.. 14- *TAƘAMA PAID BOOK* 15, _WANI DARE FREE BOOK_ ALL MY WRITE'S
MUJAHEEDAH MATAR MALAM... AMMIEYN KHAUSAR.. HEEDAH HAYDAR
OSTHMAN....```
*NASA DAUKAR GA MASOYANA MASOYA LITTAFINA KAWAI*
Fitowarsa daga wanka kenan tashigo ɗakin kasancewar yau week ba aiki, tsane
jikinsa yake da towel ɗin hannunsa ɗayan kuma yana ɗaure A west ɗinsa, Shigowa tayi da
sallama haɗida matsowa kusa dashi tana ɗan jingina bayanta kan nasa bayan, wani iri yakeji
amma baimata magana ba yasanta da shegen son jiki dama, janyo man tayi tafara shafamasa
kan lallausar fatarsa Ahankalin take bin ko ina najinkinsa da shafa man, shikuwa dik jikinsa
yasake wata kasa kefaman dirar masa, juyo da ita gabansa yayi suna fuskantar juna Ahankali
yafurta ,"Plzz kidaina inajin wani iri ne," yaƙarasa maganar ya raba jikinsu,.
Sarai tagane nufinsa bawai baison sex da itabane kawai shi mutum ne dakomai nasa yake
kan tsari gashi sam baison bari najasa jikinsa , yayi wanka baison tasake maidashi ruwa ne,.
Kwaɓe fuska tayi cikin shagwaɓa tace "Meyasa Ayanzu kadaina bani haƙƙena duka? yanzu
saiwani guduna kake kamar dodo to inkai baka buƙatata ni ina buƙatarka, inacikin hali na......,"
Ƙararrawar gida tanuna Alamar baƙo yazo tafara rura gakuma nocking da Aketayi daɗan ƙarfi
kuma ƙararrawar saifaman daddanata Ake ba sassautawa shine dalilin ƙatse mata maganarta,
tamiƙe tana share hawayen da suke ƙoƙarin zubomata tabar ɗakin.,
Ajiyar zuciya yasauke yanajin dik bai kyautaba Akan Abunda yamata gashi hartana zubda
hawaye saboda shi kuma bayan yayi Alƙawarin share hawayenta, to amma meye Ammafanin
sex basamun yara?????? tanbayar da zuciyarsa taje fomasa kenan, wadda take yanayinsa
yaɗan sauya, Shirinsa kawai yaƙarasa yaji yanason barin gidan dika ma yau yafasa wuni A
gida.,
Ƙara saita kanta tayi kafin tabuɗe ƙofar, tsofafin mate ɗinta ƙawayenta na school.
Ƙwalalo ido tayi tana musu kallon mamaki dan rabonta dasu sama da shekara 13 kenan
tinkan tayi Aure wai yau sune gidanta, cikin jindaɗi tace , "Shamsiyya Meery You are welcome,
kune Agidana yau? baku manta daniba Ashe long time," taƙarasa maganar tana musu iso cikin
palourn,.
Sukuwa sai biyarta suke da idanuwa haɗida bin ƙasaitaccen palourn, gaba ɗaya Maira
tasauya musu tayi ƙiba ga haske ka sihirtaccen kyau data ƙara Allah yasa dai baciki ne da
itaba, kai ina bama shibane dan dashine da tuni sungano sun Aikashi inda suka Aika na farko,
wannan zuwan nasuma sunzo ne dansu Aje wani maganin Agidan dakuma ganin ya nata
yanayin yake, dika Azuciyar ta take maganar sham kenan.
Tanata rawar jiki dasu ita Adole ga mate ɗinta sunzo Kayan drinks tazube gabansu da
fruits,
Aiko suka hauci da sha suna mata dabara dan gano wasu Abubuwan saidai bata sauya ba
yarda take Ada haryanzu haka take dik wayanka bazakaji sirrinta ba balantana kuma na mijinta,
ko ɓarinda tayi bata bari suka sani ba,
Firar school taɗauko ku musu suka fara firar sunata shewa da ɗaga murya,.
Fitowa yayi tindaga nesa yaƙare musu kallo kuma saiyaga dikansu basu masaba haka kawai
yaji gabansa yafaɗi yaji baiyarda dasu ba, Sanye ɗayan take cikin riga da wando waɗanda
basuma rufe cibiyarta b balantana wandon yakai koda gwiwa ne kanta ɗauke da gashin
Attachmenta mai kala 2 tawani sakeshi har bayanta kamar wata dodadniya haka yaganta,
ɗayan itace da kayan Arziki wai dan wani figaggiyar doguwar rigace ta Atamfa wadda tayi
bala'in kamata kana iya hango ya musasshen ƙirjinta daya kwanta wanda zai tabbatar maka
itaɗin karuwace inko bahaka ba to baƙaramar bazawara bace, sai ɗan ƙaramin gyale data Aza
saman kanta bako ɗankwali,.
(HAHHHHHHHHHH NIKO NACE SEEP DIK TSABAR JIN HAUSHINTA NE HAKA HARDA
KIRANTA BAZAWARA)
Ƙarasowa palourn yayi baiko dube inda suke ba Yace,"Zanfita wani uzuri yakamani kimin
Afuwa dear kasance war yau ranarki ce amma zanfita dole ce zata fiddani, idan kina buƙatar
wani Abu ki kirani," yaƙarasa maganar yana ƙoƙarin barin palourn.
Tinda yake maganar suke satar kallonsu bama kamar meery ita sam bata zata haka yake ba
lokaci ɗaya taji wata muguwar Sha'awarsa tafisgeta,..
Taɓangaren Shamsiyya ma haka saidai itakam Abunda tafi Ayyanawa