Showing 6001 words to 9000 words out of 18801 words

Chapter 3 - INGARMAN NAMIJI Book 2 Complete by Autar Alheri .txt

12 Jan 2025

3978

d'aya..Ahmad nazaune Yana kallan pic d'indayayiwa safnah yaji mutun kusanshi d'agowa yayi suka hada Ido da likitannan yasakar Masa murmushi tareda yimai sannu shima mayar Masa martani yayi batareda yace komaiba..shiko yashiga had'a na,urorin dake wurin.


Abangaren yazeed ma hakene Amma shi idanuwansa arufe suke shiyasa Dr basuce Masa komaiba shima dudda yaji mutun kusanshi besa yabud'e idanuwanshi ba yanaso ne yaga iya gudun ruwansu..




Shiko sadeeq zaune yake Yana kallansu har suka k'araso wurinshi sannu suka Masa dakai kawai ya,amsa Yana kallansu har sukagama jona na,urorinsu kallan sadeeq d'ayan yayi yace"kwanta ko abokina.."nakwanta Kuma kamar Yaya?"no zamuyima wani gwaji ne karkadamu dadynku yace dukanku amuku.."okay kawai yace tareda kwanciya dudda cewa yafahimci manufarsu tundashima likitane Amma behanasuyin aikinsuba..Yana kwantawa d'ayan yak'araso yad'ora Masa wani abun a Mara Yana dannawa Yana kallan computer Amma bega wata matsalar ba ajiye abun yayi yajuya yana kallan abokin aikinshi sukayi wata maganar kana yasake juyowa gun sadeeq hannu yad'ora akan wandonshi yafara konce igiyar Dan d'inkin hausa ne ajikinshi na shadda ido sadeeq yazaro tareda barin abunda yakeyi Yana kallansu cikin mmki ganin sun kwace igiyar suna k'ok'arin janye boxes d'inshi ne yasa,shi mik'ewa bashiri Yana fad'ar Kan ubancan mizakuyimun? minene hakan fyad'e zakumun kome?"no y'allabai wanne fyad'e Kuma za,aduba lpyr ku nefa.




Ahmad kuwa da,ake fad'ar yakwanta yak'i Yana tambayar mizesa yakwanta kamar saukar mashi haka yaji maganar sadeeq Ido yazaro tareda dirowa yanafad'ar mee?uwarme zakumana? Dubiya akanme?


Bawanda sukasami damar amsawa amsa sabida gabaki d'aya sunshiga tsoron yanayinsu ganin zaratan samari agabansu suna tuhumarsu kowanne ido sun juye kamar Wanda kefagen yak'i..




Yazeed kuwa dashi tind'azu beyi maganaba Kuma be bud'e idonshiba ga likitocin tsaye akanshi Amma sunkasa yimasa magana yakwanta sudubashi sabida kwarjinin dayayimusu bud'e idonshi yayi yanabin kowa dake wurin da kallo Jin anfad'i kalmar fyad'e.."mikuke nufi dakawomunan wurin? mikukama biyayyena? Akanme zakuyi managwaji? Uban Waye yasakaku bincikarmu?"ubankane yajiyo muryar Nene dake shigowa room d'in Dr databawasu nabiye da,ita abaya.."nace ubankane marar kunya har nice zansa ayi maku Abu kuzo kunayiwa mutane Rashin kunya eyeee to nice Nan nasaka adubamin lbyr ku domin inada tabbacin bakuda wada tacciyar lpy ajikinku Kuma kusani aure za,amuku cikin makon,nan sabida hakan doline atantace lpyr ku adoraku akan magani gudun Kar,acutarda yaran mutane ad'aukosu akawo muku kuzo kuzuba musu Ido kuna kallo kamar majigi tinda ba,abunda zaku iya tsinana musu hakan kukeso ayiko? Tobadaniba banshiryawa kallan abun kunya azuri,ataba bani,baganin talallab'on jelar y'an maza ahhh bazanga Wannan takaicinba acikin zuri,ata kaf kune kawai kukazo ahaka Kuma da,izzini memana ruwa da k'ank'ara sekun koma cikakken maza(INGARMAN DOKI)yadda zakuyi kyakkyawar sukuwa acikin gonakinku..takarashe zancen tana murmushi..sudai gaba d'aya gaskiya tayi masu yawa sunma kasa cewa komai inba kalloba ba,abunda sukebinta dashi tinani sukeyi aransu Wai sune za,ayiwa binciken lpyr mazan taka lallai ma hohuwarnan tagama dasu wlh.. sadeeq ne ya kyalkyace da dariya danshi abunma dariya yabashi kana yace "towai ke Nene wayacemiki muba lafiyayyu bane? Dahar Kika yanke Mana Wannan hukuncin tonon silili zakimana kome?"yo Ina lpy anan ainatakene afad'amun babufa🤷🏽‍♀️kungani Kuma inada tabbaci akan hakan.."tofa🤔 Allah kintabbatar dazancenki kenan? Kwarai kuwa sabida hakan maza kugyara adubaku..kamun sadeeq yayi magana yaji yazeed yafara maganar cikin fishi da takaicin tsohuwar yake fad'ar "bawanda zezauna d'akin Nan adubashi miyasa kebazaki duba dakankiba tinda aike muharramarmu ce kece Kika haifi iyayenmu sekizo kiduba kowa dakanki daganan seki samu amsar dakikeso base kinkawomu wasu k'arti sudubamuba Dan wlh Allah sedai kisaka sud'auki rayuwata ba Dan,iskan dazeganemun suturar da Allah yayimun Amma inke kesan kigani to dakaina Zan,iya nuna Miki Amma tinda kince kinada tabbacin muba lafiyayyu bane toko zakiga lpy ta ganin idanki wlh Wannan alkawari ne..Yana kaiwanan yafigi hannun Ahmad datund'azu yakebin Nene dakallon mmki danshi yamakasa cewakomai..ahakan sukafice sadeeq nabiyedasu abaya..Nene kuwa kuka tasaka tace yazeed yazageta Tass sabida ba,itace tahaifeshiba to wlh kozasu mutu se andaura musu aure jebi Tama fasabari semako nanda kwana biyu za,ayishi insha Allah..dady kuwa da Dr hak'uri kawai suke Bata dakyar suka samu tadena kukan suka tafi Koda sukazo mota bawanda yace Mata komai acikinsu itama batabitakansuba harsuka Isa gida sabida tanada matakin dazata d'auka musu aranta kumazata aiwatardashi domin shine kawai maganinsu...






Ahakan suka wuni ranar kowada abunda yake sak'awa aransa yayinda safnah kuwa tinranar dasukayi artabo da sumayya Basu sake had'uwaba Kuma tin bayan yin rigimar da kwana d'aya takejin matsala ak'ugunta inda tabagu domin dakyar taketashi tsaye Amma Bata gayawa big mom ba..to yaudai abun ya faskara domin kotashin takasayi tinsafe big mom keneman tafito Amma Tak'i Kuma Tak'igayamata batada lpy..


Kiran sallar azahar ne akeyi ko,Ina Amma safnah naji takasa tashi har aka,idar ganin takasa Koda juyawane yasanya tafara kuka ahakan big mom tashigo tasameta arud'e take tambayarta Mike damunta "mi,akamiki doter? Wani abun kikesone? Kobakida lpy? Duk atare big mom kemata tambayar cikin tashin hankali duk tarud'e..cikin kuka tashiga gayawa big mom abunda kedamunta Kuma bazata iya tashiba.."innalililahi wa innailaihiraji un tinyoshene bakida lpy doter miyajimaki ciwo? "Tinranarda Wannan tazo takadani wurin yakemun ciwo.."Ash,shakuwa bara nakira abbenku nagaya Masa se akaiki hospital adubaki..kaitad'agawa big mom tana goge hawayen dasuka Bata Mata fuska itako big mom fita tayi dantakira abbe tagaya Masa Mike faruwa..wayarta tad'auka tashiga Kiran abbe Amma Bata shiga gajiya yayida Kiran tafita..


Tana fitowa tahad'uda dady dakuma Ahmad da sadeeq cikin sauri tanufesu tareda gayamusu abunda kedamun safnah sabida akaita hospital.."subhanallah aiba,abarin mutin daciwohaka anty Zara jeki fitoda,ita akaita hospital..cewar dady yayinda Ahmad yakejin kamar zuciyar sa zatafito waje sabida tashin hankali jiyakeyi kamar yaturesu yaje yaganta Amma bahalin yinhakan..maganar big mom ce takatsemasa tinanin dayake tanafad'ar aibazata iya fitowaba domin ak'ugu ne taji cinwon.."ohh to yaza,ayikenan?"gaskiya sedai ad'aukota..ok to badamuwa jekishiryata se yayunta su d'aukota ko.."okay to shikenan tafad'a tareda komawa ciki..shiko sadeeq pert d'insu yakowa yace yayi mantuwa Kuma yayi hakanne Dan karya d'aukota hakan kuwa bakaramun dad'i yayiwa Ahmad ba..suna,nan tsaye big mom tadawo tace suzo tashiryata.."ah aikuwa sadeeq yashiga ciki kozaka iya d'aukota Ahmad.."eh Zan,iya dady yafad'a cikin sauri kamar mejiran ayimasa tambayar Dan yabada amsa.."okay to kuje kad'aukota mutafi.


Wucewa sukayi ciki shida big mom suna shiga tanuna Masa inda safnah take itako tawuce bedroom d'inta dan tad'auko abunda zata bukata kamun sudawo..shiga dakin yayi da sallamah d'oke abakinsa tanakwance taji muryar danaza tab'a tantawa da,itaba k'ara runtse mayatattun idanuwanta tayi tareda k'ank'ame jikinta..shiko Ahmad duk'owayayi Dede kunnenta yace bakida lpy shine baki gayawa ruhinkiba? Yatambaya tareda hura Mata iskar bakinshi kunneta dominshi duk lokacin da yaganta tofa rayuwar dasukeyi amafalki ganinta yakeyi kamar gaske.."yasalamm tafad'a cikin ranta domin wani sihirtaccen abu takeji nakaiwa jinin jikinta ziyara..shiko Ahmad ganin batayi magana ba yasashi sak'alo hannushi ta wuyanta da kafad'arta d'aya Kuma yasawoshi ta kasan kafafunta kana yatallabota gaba d'aya wani mugun shock dukansu biyun sukaji alokacinda jikinsu yahad'u wuri d'aya seda dukansu suka lumshe dara daran idanuwansu suna sauke numfashi ahakanli kamun yajuya yafara tafiya da,ita mak'ale ajikinshi yatsurawa kyakkyawar fuskarta ido Yana kallo koduban gabansa bayayi.


Ahakan sukafito big mom naganinsu itama takaraso wurin sukafita tare tunda daga nesa dady yahangosu tafe kallansu kawai yayi tareda zagayawa yabud'e musu motar Ahmad yakwantar da,ita big mom tashiga shima Ahmad yashiga dedenan sadeeq yak'araso shiga shima yayi suka wuce hospital d'in.


Acanma Ahmad ne yad'auketa zuwa room d'in daza,adubata bayan yafitone Dr yak'araso zeshiga d'akin..tareshi Ahmad yayi yahanashi yashiga yana fad'ar"mizakayi aciki? "Zandubatane.."no Akira Dr mace tadubata.."ayya sorry sr ba Dr mace anan domin macen dakenan yanzu batanan tad'anyi tafiya sezuwa jibi zata dawo insha Allah badamuwa nizan dubata.."kaizaka duba matar tawa? Yafad'a tareda zaro ido Kamar ze shak'ure Dr d'in..akuma Dede Wannan lokacin dady yak'araso kalmar matarda Ahmad yafad'a se a kunnenshi cikin mmki yake kallan Ahmad da kishi yabayyana k'arara k'wayar idonshi..sadeeq ma kallan tuhumar yakebin Ahmad dashi kamun yace "haba biyayye kabari yayi aikinshi Mana kagafa tanajin jiki yafad'a dansan tabbatar da zarginsa..Aiko ya hayyak'o sama damasifa Kamar yaci Babu "Taya zakace nabarshi biyayye ak'ugufa taji ciwo zanbarshi yatab'ata ai wlh bazeyuba aibananne kad'ai hospital ba yafad'a tareda fad'awa dak'in yad'aukota yafito kotakan dady dake kiranshi bebiba Dan bema jishiba..shiko sadeeq da kallo yabishi Yana K'ara tabbatar da zarginsa..yayinda dady yashiga bawa Dr hak'uri kana sukabi bayanshi suna Isa wurin Yana tada motar cikin sauri sadeeq yak'araso wurin yaname fad'ar tafiya zakayi kabarmu kome? Ahmad kana cikin hankalinka kuwa? Yatambaya Yana kallansa bece Masa komai haka dady yashigo Yana Jin sadeeq nayiwa Ahmad masifa akan beyi dedeba Amma shima Yi yayi kamar bejisuba..


Wata hospital yanufa da,ita suna zuwa akakarb'eta kamar yadda yabuk'aya Dr mace ce tadubata ansha famada ita Kamun asamu akayimata gyaran kuka Kan tasha tana Kiran huri kamar ranta zefita huri kawai take fad'a cikin fitar hayyaci domin batamasan abunda kefita daka bakintaba ahakan aka k'arasa gyaran suka koma gida..washegari tunda safe Abba yad'aukesu safnah da sumayya zekaisu wurin wani babban malamin addini dake bayadda temako....












Autar alheri ✍️✍️




29 & 30


__suna fitowa shida sumayya yabud'e Mata mota tashiga kana ya K'ira abbe yafito Masada safnah to abbe yace kana yagayawa big mom taje d'akin safnah takirata suka fito hannunta abbe yakama sukafita Koda abbe yaga sumayya zaune amotar kallan Abba dake tsaye yanajiransu yayi kana yace "konad'auko mota semutafi da safnah a motata kaiseka tafida sumayya domin inaga bazasu had'u wuri d'aya ba.."eh hakane gaskiya nama manta wlh to kazo da,ita bara muwuce..okay gamunan yafad'a tareda nufar motarshi da ita shikuma Abba yafigi tashi sukafice shida sumayya.


Abangaren su yazeed kuwa zaune suke a perlonsu Sameer na nunamusu sak'on da,aka turomai akan binciken dasuka sakasu bayan duk sundubane yazeed yace "waya turo Wannan text d'in Sameer? "Wlh Nima bansan kowayeba Yaya Kuma nayi k'ok'arin Kiran layin Amma akashe yake.."okay kabani contact d'in koma Waye yanada masaniya sosai akan abunda mukesan sani Kuma yasanda muna Wannan binciken abunda bamu saniba yanzu shine Wannan dayaturo sakon kodai acikinsu yake yanaso D'ana Mana tarkone kokuwa acikin manyan k'asar ne dabasada hannu acikin kungiyar Kuma basada ikon magana suka zabi tema kamana tawannan fannin.."koma dai yayane Wannan abun zetemaka Mana sosai akan muradinmu Kuma kotarkone suka D'ana ba,abunda zasu,iya da izzinin ubangiji cewar Ahmad.."hakane gaskiya badamuwa Sameer tashikaje zamu nemeku insha Allah sadeeq yafad'a Yana d'aukar coffee d'in dake gabanshi yanasha..tashi Sameer yayi yafita yayinda sadeeq yamarda dubanshiga Ahmad yanafad'ar.




Acan gun memagani kuwa tuni Abba ya,Isa dady ma yazo bayan sun gaisane abba kewa mlm bayanin abunda ketafedasu tareda nuna mishi safnah yak'ara dacewa d'ayar na mota domin basa had'uwa wuri d'aya.."Allah sarki ai bakomai kushigo da,aita ba,abun zasu iya,aNan insha Allah.."okay to baranashiko da,ita cewar abbe yanabarin wurin bayan minti 2 segashi yadawo da sumayya yazaunarda ita..


Kallansu mlm yayi kana yace "yasunanki y'ata yafad'a Yana kallan sumayya dake rabon Ido Dan ita batasan miyasa aka kawota nanba.."sumayya tafad'a cikin dadd'an muryarta.."Masha Allah kefa Yasunanki? yatambayi safnah.." safnah itama tafad'a cikin dadd'an muryarta..Masha Allah badamuwa insha Allah komai zezodasuk'i Allah yayikumu albarka.."ameen y rabbil alameen 🤲 suka amsa atare kana mlm yakalli abbe yace mayardasu mota badamuwa..okay abbe yace tareda tashi yamayardasu yadawo.


Kallansu mlm yayi kana yace"magana ta gaskiya alhaji yaranku dukkansu akwai matsala ataredasu.."hakane mlm muma munsanda hakan shiyasa mukazonan.."to shikenan badamuwa insha Allah komai zezodasuk'i ita Wannan yarinyar safnah akwai sihiri me had'arin gaske atareda ita domin akwai mugun tsafi cikin jikinta Wanda bak'ak'en aljanu kegadi Kuma wlh ba,abunda zeraba tsafinnan dajikinta se mijin aurenta yak'araso Maganar Yana kallan Abba..,cikin mmki abbe yace mijin aurenta Kuma kamar Yaya? "Shakka Babu mujin aurenta domin muddin batayi aureba to tsafin bazebar jikintaba sabida makarin Wannan asirin shine ketawar budurcinta duk lokacin da mijinta yakwanta da,ita to ranar zata rabida Wannan lalurar abunda yasa kukaji nace mujin aure kuma shine idan wani namujin yakusanceta batareda aureba to abun baze tab'a barin jikintaba har abada kodako tayi auren daga baya. Nisawa yayi tareda kurb'an ruwan dake gabanshi kana yacigabada cewa hikimar matsafan nasaka Wannan abun amatsayin makarin tsafinsu kuwa shine banamujin daze iya aurenta da Wannan masifar dake fita daga jikinta kodako wani yayi gangancin aurenta to azabar damace ke fuskanta lokacin rabuwada budurcinta zesaka tabud'e inadanuwanta akan mijin yayinda aikata hakan kuma kawo karshen rayuwar mijinne idan Kuma yamutu tawannan hanyar to ba shakka tsafin dake jikinta zek'ara k'arfi atak'aice dai anfisan duk namijin daya aureta to komi zasuyi afarkon had'uwarsu har yagama abunda zeyi da,ita karta bud'e idanuwanta Wannan shine kawai mafita akan ciwon ta wlh ko,Ina kukaje kud'inku kawai za,aci Wannan abun bazebar jikintaba seta Wannan hanyar.."innalililahi wa innailaihiraji un shine kawai abunda su Abba kefad'a yayinda gumi yawanke musu duka jikinsu cikin jimami da tashin hankali daya kasa b'oyuwa akan fuskarsu abba yace shikenan mlm mgd Sosai kuma insha Allah zamusan abunyi sedai baka gayamana d'ayar ba ko,ita nata bawata matsalar ne? "Ah,ah gaskiya ita nata shedanu ne kawai ko fad'an dakukaga sunayi tsakanin su nata mutanen ne basa jittuwa damasu tsaron sihirin jikin waccan shine kawai dalili..Amma ita zamu iya Bata temako insha Allah sedai bawai nace zasu rabuda itaba ,ah,ah gaskiya abune mematukar wahala sabida d'an sarkine atareda ita


Itama Abu d'aya ne ze,iya nisantata dasu shima bawai suraboba ah,ah ze nisanceta dai sosai shine aure muddin tana tareda wani namujin to zenisancete domin bayason tarayya da,ita dawani namujin yanada zafin kishi sosai bak'incikin ganin namuji tareda ita zesa yanisanta da,ita.."to ai tanada aure mlm cewar abba..tanada aure? "Eh tanada aure sedai inaga har yau mijin betab'a kusantar taba.."toko in hakane kugaya Masa yayi gaggawar kunsatarta domin yin hakanne zamu gane inzebari tayi zaman aure ko akasin hakan sedai Allah yasa mujin nada illimin addini domin shine zebashi damar mallakarta nahar abada.."eh to gaskiya idan ilimi yanadashi Kuma insha Allah zamuyi k'ok'arin yin hakan cewar abba.."to allah yasa mudace yanzu barana hada muku maganin dazasuyi anfani insha Allah zetamaka musu sosai Allah yashiga cikin lamarin yabasu lpy me amfani.."ameen y rabbil izzati suka amsa atare kana hayad'a musu magungunna Dana Sumayya Dana safnah yabaso godiya sukayimai sosai tareda alkairi meyawa kana sukayimai sallamah suka tafi tinani fal ransu...




*(Tofa 🤔 Ashe su titeee manyan matane bamusaniba to allah yabada zama lpy kowaye Wannan me sa,ar ohoabo🙄)*




Ab'angaren su yazeed kuwa


Kallon Ahmad sadeeq yayi tarada cewa "biyayye inaso muyi magana pls.." okay inajinka miyafaru ne? "Bakomai kawai inaso muyi magana akan Wannan yarinyar naso mutambayeka tin bayanzuba sabida Rashin samun lakaci yasa bamu samu mun zauna free ba.


Wai Dan Allah Ina kasanta?


Miye had'inka da,ita?


Miyasa kad'aukota dudda kaga matsalar dake tareda ita? Baka gudun tacutarda wani cikin ahlinka? Yanzu ko abunda yafaru last time be,isheka isharaba idan da ace sumayya batada nata fasin jojin yakake ganin za,ayi? Mikake tinanin zefaru?


Dudda hakan bamu fita Wannan rud'aninba kuma Sega wani kak'ara bijirowa dashi kana fadar Wai matarka ko,Aina tazan matarka Ohoo.. yak'arasa zancen Yana kallan Ahmad d'in daya d'ago shima Yana kallansu domin yazeed ma yadena abunda yakeyi yanasan Jin amsarda Ahmad zebada.


Murmushi kawai yayi kana yace"bansantaba biyayye Kuma shakka Babu ba,abunda Zan iya b'oye muku Amma kusani had'uwatada Wannan yarinyar Zan iya zewa had'ine daga Allah domin tin bansanta ba bankuma San Ina zangantaba Allah yake nunamun fuskarta amafalki kala inad'aukar abun bakomai ba harna fara D'ora ayar tambaya akan lamarin domin duk lokacin dazan kwanta senayi mafalkinta seda nashafe fiyeda 3 years Ina Wannan mafalkin Kuma bafashi muddin Zan kwanta bacci senayishi Kuma tin acikin mafalkin nafara santa bantab'a mafalkin wata maceba aduniya se ita Kuma abunda kefaruwa tsakanina da,ita ganinshi nakeyi Kamar azahiri biyayye wlh Allah inasanta Kuma San dabantab'a tinanin akwai macen da zanyiwashiba.


Zancen Mata kuma dakaji nace tabbas matatace abadini Kuma inafatar tazan hakan azahiri domin bantab'a yimata wani kalloba inba matataba Dan Allah biyayye kutausayamun kutayani San abunda nakeso wlh idan narasata zaku,iya rasani please biyayye na yak'arasa zancen Yana saukowa tareda Dora kanshi acinyar yazeed Yana zubda k'walla domin yafi kusadashi..cikin mutuwar jiki yazeed yafara shafa sumar kansa tareda bubuga bayansa yana fad'ar" it's okay biyayye karka damu insha Allah zamu tayaka San abunda kakeso Kuma zamu tayakada addu,a Allah yazab'a maka abun yafi alkairi atsakaninku.."insha Allah zamu tayaka Ahmad karka damu Allah yasa hakan shine mafi alkhairi cewar sadeeq..da ameen suka amsa kana sadeeq yasake kallan Ahmad cikin tsokana yace ayya ashedai mafarkin yarjejine akeyi shiyasa ke kurma ihu wayyyo dadiii yafad'a Yana kwaikwayon Ahmad..filon kujera Ahmad yad'auka yawulka Masa Yana fad'ar ohh saurarana ma kakeyi kenan Dan sa,Ido kawai aikinka kenai ai kaiwama yasan mizakayi..shidai yazeed murmushi kawai yayi yana kallansu.."niwai mizanyi kuwa ni wlh barakaji ingayama ko azahiri mace Bata Isa tasakani ihuba balle amafalki ni wlh kaga Wannan yafad'a Yana d'auko coffee dake gabanshi yaci gabada cewa yafimun mace domin shi idan nasha nakanji nishad'i da jindad'i Amma mace inba ciwon kaiba micece.."ohh really 🤨? Cewar Ahmad.. "Yerh.."yayi kyau zamugani kuwa Niko Ina gayama se mace tasaka ka kukan dad'i bama iya ihuba..k'yalk'yacewa da dariya sadeeq yayi yanafad'ar Aiko da,aiki agabanka domin kila ko uwar wadda zata,iyayin hakan Babu aduniya balle ita.."ok yy kyau zamu gani kajidai miyace ko biyayye? Ahmad yatambayi yazeed.. murmushi yayi kana yace to ai gaskiya yafad'a biyayye mace ai matsala ce.."ok duk hakan zakuce bakinku d'aya kenan yy kyau inanan daku ai zakudawo hanya yafad'a yareda shigewa bedroom d'inshi yayinda suko sukaci gaba da firarsu..


Washe gari Friday


Nene ce zaune ta tasa su Abba agaba akan lalle yau d'inna sesun d'aurawa su yazeed aure Abba ne yace


"Nene Taya za,ad'aurawa Wanda basudama budurwa aure?"Koma ta yayane wlh Allah yau se and'aurashi Koda yaran gidan marayune idai nice mahai fiyarku inaso Naga lpr dasuke fad'ar sunada indai dagaskene ba matan banza sukebiba.."ah,ah abun bekai ga hakaba cewar dady insha Allah za,a daura yau d'innan kuwa bara nakira alhaji kabeer muji Ra,ayinshi akai domin kinsan bamuda hurumin aurarda D'an shi batareda yasaniba yak'arasa zancen Yana d'auko wayarsa yadannawa mijin ummy K'ira.."atoo komadai yayane sedai anyi shi kabirun ne zece beyadda da zancenaba aikin kawai..wayar nashiga aka d'auka sallamah dady yayi tareda gaida mijin yayartashi.. abangaren alhaji kabeer kuwa amsawa yayi cikin mutintawa tareda martaba juna bayan sungaisane dady yagayamasa buk'atar Nene tareda tambayar sa ko,akwai yarinyar dayaga yadace sadeeq din ya,aura.."haba alhaji zayyan minene nasawoni cikin Wannan maganar Kuma ai sadeeq D'an kune nimiye nawa aciki kodako ahannuna sadeeq yataso zaku,iya zartarda hukunci akansa ballema ahannuku yake banada zabi wlh duk hukuncin dakuka yanke yayi Dede inkunsamu yaran dazaku aura musu to bakomai semu had'u wurin d'aurin auren yafad'a yareda

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login