Showing 1 words to 3000 words out of 18801 words

Chapter 1 - INGARMAN NAMIJI Book 2 Complete by Autar Alheri .txt

12 Jan 2025

3977

INGARMAN NAMIJI
Book 2 Complete
Writing by
Autar Alheri








21&22


Yana fad'in ke-ke-kece? yafad'a cikin harhad'a maganar domin bakinsa yakasa fad'ar abunda yakesan fad'a yayinda idanuwansa suka kasa gasgata Masa abunda yake gani agabanshi..itako tafiya kawai takeyi takasa tsayawa dudda taji ana magana abayanta tinaninta komasu cutarda itane..shiko yazeed kallan inda Ahmad kenunawa yayi danyaga wacece yakeyiwa magana


Mace yagani dashiga irinta arnan daji gafatar jikinta fara soll kamar aljana..cikin mmki yajiyo Adan razane Yana kallan Ahmad daya kwace hannunsa daga hannun shi tareda binyarinyar dabesan kowaceceba..cikin sauri shima yabi bayanshi tareda kiranshi Amma kowaigowa Ahmad beyiba..itako Jin anbiyota takara sauri domin tayi Bala,in tsorata gafad'uwar gaba takeji sosai kamar zuciyarta tafaso kirjinta tafito..abangare Ahmad ma haka abunyake..ganintana sanshigewa wani surk'umi tab'ace masane yasa yahad'a hadda gudu yazeed ma nabiyedashi abaya Yana kallan ikon Allah.


Cikin sauri Ahmad yasha gabanta gocewa tayi zata wuce yak'ara tarota akarona 4 ganin batada niyyar tsawane yasashi rik'e shoulder dinta tareda kafeta da Ido..ahakanma beyi aikiba domin Tak'i tsayawa wuri d'aya se k'ok'arin k'wacewa takeyi shiko yak'i Bata dama..cikin takaici yazeed yadoka Mata wata razananiyar tsawa tahanyar fad'in "keeeeee da Allah dakata anan anatsaidaki kina kokarin guduwa daganinki bakida gaskiya mikikeyi anan cikin Wannan mummunan jejin? kedawaye anan? Yafad'a cikin daga murya.


Kallansa kawai Ahmad yayi tareda juyowa gareta "babyyyyy yafad'a tareda Jan baby d'in da bakinsa cikin shauk'i datsan,tsan Jin dad'in ganin mafalkinshi nashirin zama gaskiya..shiru tayi Bata amsaba tana sauraronsu domin yanzu tagane bamasu cutarwa bane Amma takasa fahimtar suwaye ne.."bazakimun maganaba babyyy kecefa kike Sona nine ruhinki kobaki ganeniba bane? Yafad'a araunace kamar zeyi kuka..itadai takasa cewa komai komatakasa Tina Aina tasan Wannan muryar Kuma tin wani lokaci tasanta..shiko nakunfa yashak'a iya shak'a zuci tazomai har wuya jiyakeyi kamar yarufesuda duka Amma baze iya dukan maceba Kuma baze iya yiwa biyayyen shi komaiba..cikn mugun Jin haushinsu yafincikota taredayin jifada ita Yana fad'ar Wai bazakiyi magaba anamiki magana kina share mutane yafad'a cikin tsawa.. fad'uwa tayi akan wani dutse tabige kanta cikin zin zafin buguwar tafasheda rauna taccen kuka me tsuma zuciya taname dafe wurin dataji rauni..cikin tashin hankali Ahmad yazaro Ido tareda saurin k'arasawa wurinta yaname tallabota jikinshi yanaso tad'ago kanta yaduba Mata wurin Amma Tak'i yadda tad'ago jajayen idanuwansa yazubawa yazeed dake tsaye gefe Yana huci kwamar kumurci tareda girgiza Masa kansa cikin rauni idanuwansa na zubda wasu zazzafan k'walla wace "biyayye miyasa kayi Mata haka please? Nasan bakasan ko,ita din wacece agareniba dabaza kayiba.."koma wacece ita Ahmad bazata Rena Mana hankaliba Kuma dakake zancen bansan mitake awurinkaba yarinyar damuka gani yanzu Aina kasanta har tazan wani abun agareka? Kuma ubanme take acikin jeji?? Yak'are zancen chikin d'aga murya da hargani yana lumshe kyawawan idanuwansa tareda dafe kansa domin yayi bala,in gajiya Wannan zancen kawai dayayi.


D'agowa tayi itako cikin sauri tareda bude dara,daran idanuwanta Dan Jin anzageta domin in akwai abunda tatsana aduniya bewuci zagiba bud'e idanuwan datayi setayi saurin kallon inda taji anamaganar cikin fad'a hakan yasa Wannan farin abun me bantsoro yayi tsike akan wata katuwar bishiya atake bishiyar tak'ame k'am tareda duk abunda kejikinta fannin dabbobi..Ido suka zaro cikin Al,ajabi datarin mmki Amma bawanda yatsorata acikinsu..itako dagangan takalli wurin domin atunanita yazeed nawurin batasan Yana Gama zancenshi yabar wurin kamar yasan mizefaru..mayarda kanta tayi kasa tareda cigaba da kukanta..shiko Ahmad Yama rasa tinanin dazeyi mi hakan ke nufi? Itad'in aljannah ce ko mutin? Komadai micece ita yanasan abarsa ahakan kodako zatayi sanadin rayuwarshine..yanacikin tinanin yaji anriko hannunshi d'agowa yayi yaga yazeed ne kecansa tashi yayi tsaye tareda ita yashiga bin yazeed..shiko tsayawa yayi Yana kallonsa kamun yace saketa Mana biyayye inazakaje da Wannan aljanar? Marairaice fuska yayi domin in yazeed be yadda suje da,itaba baze iyayin abunda zebata Masa raiba Kuma baze iya barintaba domin yanaji ajikinshi itad'in alkairice agareshi.."please biyayye muje da,ita Mana karmubarta anan Dan Allah.👏"akanme Ahmad bakada hankaline aljanar zamuje da,ita?? "Ni wlh ba aljana bace Dan Allah kadena alakantqni da aljannu tafad'a cikin wani sweet vocie meratsa zuciya tareda fashewa dawani Sabon kuka..Jin muryarta yasa Ahmad kara tabbatar da zabinsace..cikin k'uluwa yazeed yace to inke ba aljana bace micece ke.. "itad'in rayuwatace biyayye kamar yadda nake ruhinta inasanta biyayye inamata k'aunarda banyiwa kaina inajin santa da begenta acikin jinin jikina tinbansan ita d'in waceceba please biyayye help me..yajiyo muryar Ahmad nabashi amsa tareda yimai magiya runtse mayatattun idanuwansa yayi tareda dafe kansa 🤦 domin kominene aduniya Ahmad yafi k'arfinshi awurinshi Amma jiyadda yake Masa magayi.


Jiyowa yayi yakallesu bareda yace komaiba tinani yakeyi aranshi to yanzu in yabari sukaje da,ita tacutarda Ahmad d'infa? Koma inbe Bari yatafida itaba Kuma yabatawa biyayyen shi rai.. muryar Ahmad takatse Masa tinanin Yana fad'ar please biyayye.."okay kawai yace tareda Sakai yawuce..shima Ahmad cikin farin ciki yamaramai baya jayeda hannunta..itako Bata hanasaba domin tasan batada wata mafita bayan Wannan Amma ak'asan zuciyarta falyakeda fargaba.


Ahakan suka tadda yaransu tareda Yan bidigar dasuka kamq suma shiga mutar sukayi tareda barin jejin baki Ahmad mak'ale da Yar jejinsa😜




Azamfara ma hakan abun yakasance domin anyi artabo sosai tsakin Yan ta,adda da sadeeq yayinda suka Sami nasarar kashe wasu suka Kama wasu..suma ahakan suka dauko hanyar dawowa cikin farin cikin samun nasara atafiyar tasu.




Kano




Saurat ce tafe itada k'awayenta cikin shiga iri d'aya gadukkan alamu daga islamiya suka fito tafiya sukeyi cikin gajiya kowacce tak'osa tajegida domin bawadda kiyiwa Y'ar uwarta magana ko Y'ar firannan tak'awaye basayi SAURAT kuwa se yamutsa kyakkyawar fuskarta takeyi domin tafi kowa gajiya acikinsu.




Daga gefe kuwa sumayya ce itada fauza da k'awarta Amina suma tafiya sukeyi ahanyar suna tsokana daneman fitina kamar ance tad'ago kanta Aiko karab suka hada Ido da SAURAT hararata bankamata tareda murguda baki..Ido SAURAT tazaro tareda nuna kanta da yatsa.. d'aga Mata Kai tayi alamar eh d'in tareda sakin tsaki tana ware hanna yenta duka biyu tana zagin saurat..Ido SAURAT takara zarowa tareda nufar wurin SUMAYYA cikin fishi itama sumayya nufota tayi tana cewa su fauza gawatanan zuwa merabon Shan duka *dama ya lafiyar kura balle antsokanota* Aiko suka gyara tsayuwarsu itama SAURAT kawayenta biyota sukayi suga inazataje cikin Wannan gajiyar dasuke ciki domin duk abunda sumayya kemata Basu ganiba.


Tana zuwa gaban sumayya batatsaya komaiba tadaddage tawanka Mata Mari seda taduk'e domin tajishi sosai kamun saurat tasauke tannunta taji itama sumayya tad'auketa dawani wa,wan Marin seda tayi baya Aiko anan dambe yakaure tsakanin sumayya da saurat su fauza da kawayen saurat dambe sukeyi baji bagani sauk'in abun kawai acikin alinsu anty khadi ne bawasu mutanen awurin..sun daku iya dakuwa domin tsakanida Allah saurat tagaji Dan Bata Saba irin wannan ta,addancin ba itako oganniya sumayya kamar yanzu tafara domin wani mugun karfi takeji nashigarta yayinda k'awayen saurat suke neman wurin guduwa Amma fa abun yaci tira domin sunk'i Basu dama.




Wata motace tazo wucewa dagudu awurin harta wucesu tasake dawowa nacikin motarne yabud'e yafito kyakkyawan yausarayine Masha Allah k'arasowa yayi wurinsu cikin sauri tanafad'ar ke lpy kuwa? Ya,Isa hakan kudena haba Dan Allah sekace ba Yan Mataba yafad'a tareda janye fauzi dagajikin d'ayar Aiko Kamar jira sukeyi kowacce tasaki abokiyar yinta yayinda takun ko,a jikinta se caskalewa sukeyi itada saurat..ganin su Basu Dena baneyasa Wannan saurayin Kai hannu ze rabasu aiko kowacce taja baya cikin sauri Kamar suga abun k'yank'yami domin kowacce Bata k'aunar wani yatab'ata..dariya yayi sosai daya kallesu kowacce tayi wujiga2 da,ita dasauri saurat yajuya yad'auki Jakarta data Fad'i taja kawayenta dasukayi laushi soasi suka tafi yayinda sumayya ma tayi tsaki tareda bankama saurayin,nan harara kana tajuya taredasu fauza sukawuce..kiransu yakeyi Sosai Amma ko kallanshi basuyiba sukayi tafiyarsu..shiko mota yakoma cikin sauri yamara musubaya..












Inasan kagin kyakkyawan comment Dan naga yanayin Kar buwarshi gareku👌






Autar alheri ✍️✍️




23 & 24


__yabibayansu..gidan anty khadi sukanufa sunazuwa sukashige ciki kotakan me gadin dake musu magana basubiba..shiko Wannan saurayin bakin Gert yatsaya suka gaisada megadi kamun yace "Dan Allah baba kayimun sallamah da megidan,nan.."to shikenan bara nagayamasa Dan kuwa yanzun,nan yashigo yafad'a tareda wucewa perlon gidan sallamah d'auke abakinsa..anty khadi kuwa da mujinta suna zaune aperlo suna dariyar su sumayya dasuka wuce kamar ankorosu ko kallan inda suke basuyiba se Amina ce kawai tagaidasu..anty khadi ce tace "abban Islam ana sallamah fa.. d'agowa yayi tareda,amsa sallamar Yana fad'ar aibanjibane yafice.


Bala megadi yagani tsaye bakin perlon k'arasawa yayi yanafad'ar ya,akayine Bala?"alhaji wani saurayi ne kesan ganinka shine yace nayimasa sallamah dakai.."ok badamuwa muk'asa yafad'a tareda wucewa gaba Bala na biyedashi abaya..saurayin nan kuwa Yana tsinkayar su yataso cikin girmamawa yagaida abban Islam shima hakan ya,amsa mishi cikimutintawa bayan sun gaisane abban Islam yadube saurayin nan yace "sedai banwayekaba bawan Allah..duk'arda kansa yak'arayi kana yace"ni sunana muhseen yallabai anan bayan layin ku nake Naga Yar gidannan ce inaso shiyasa nace baranazo na nemi izzini kafin nafara yimata magana.."tofa 🤔 Yar gidannan kuma? Bawan Allah ai bawata yarinya babba agidan,nan..da mmki shima muhseen ke kallan abban Islam kamun yace wlh kuwa yallabai yanzunan sukashigo Nan gidan su ukku.."ok habaa bay'an gidannan bane gaskiya k'annen matatane da k'awarsu Amma ba komai indai cikin k'annen natane ai nanma gidane Zan,iya yiwa mahaifinsu magana badamuwa wacce to kake nufi acikinsu? "Wadda kesanyeda fakistan farace sosai.."ok sumayya ce to shikenan bakomai zanyi magana da abbansu insha Allah karkaji komai Allah yasanya alkhairi.."ameen y Allah ngd sosai yallabai Allah yak'ara girma.."ameen yace kana sukayi sallamah abban Islam yakoma cikin farinciki yake sanarwa anty khadi sumayya tayi saurayi itama murna tashigayi sosai sunkusa hutawa da rigimar sumayya domin idan tayi aure doline tanutsu acewarsu...






Acikin gunkiya


Yau suke taron k'arshen wata kamar yadda suka saba akowanne karshe wata cike k'aton hold d'in yake tab da mutane Kuma dukansudai Wannan shigarce ajikinsu yayinda ogansu ma shigarsa irinta ranarce wato Yello daga gefen damanshi kuwa MAYAH ce tsaye itama dashigarta ta black din Kaya da nik'ab.


Magana ogan yafara cikin sauti marar dad'in sauraro yake fad'ar"munrasa damarmu akaro na farko damuke ganincewa zamu cimma burinmu na mulk'ar duniya Kuma hak'ik'a dodo yayi fishi mezafi Amma yak'ara bamu wata damar sabida hakan yadace kusaka Ido sosoi domin samun abun harinmu tayadda zamu samu biyan buk'ata cikin sauk'i doline a Wannan karon kubazu acikin duniya baki d'aya bama iya jihohin Nigeria ba domin yazama wajibi munemo abun ahinmu duk inda yake afad'in duniya kamun lokacin bikin shekara kusan tabbas dodo yafito bamu samoshiba to akwai gagarumar matsala sabida hakan doline mud'au babban mataki ga MAYAH nanzata temaka muku tinda ita macece akwai inda Bazaku iya shigaba idan anzo wurin kwa nemi temakonta yanzu kumotsa Dan mufara samun biyan bukata tukunnah mudawo Kan masu bibiyarmu...


Angama oga gab'us yadda kace hakan za,ayi duk inda abun harinmu yake afadin duniya semun nemoshi suka fad'a atare..jinjina Kai oga gab'us yayi tareda juyawa yajanyo wata k'atuwar tukunya tareda bud'eta yarega tareda jinjina Kai jayewa yayi MAYAH tazo taduba tareda saurin kauda kanta ahakama sauran kowa seda yazo yaduba d'aya bayan d'aya seda suka Gama dubawa kana oga gab'us yace"haryanzu munada sauran dama domin ga tabbaci duk kungani duk ranarda zuciyar dodo tabar abun harinmu toranar dodo doline ya bayyana ko lokacin bayyanarsa beyiba faruwar hakan Kuma tashin hankali ne agaremu sabida hakan kumotsa.."angama oga suka fad'a itako mayah hannu tad'aga Masa 👍 shima yamayar matada martani.




Unguwar Gama B Kano


Saurat nashiga gida ta taradda abbanta yadawo bayan tafiyar dayayi natsawon lokaci bayanan cikin Jin Dadi tazo wurinshi tareda mak'ale shi tana ihun murna Sam tamantada wata gajiya ko wani dambe shima abbanta yayi farincikin ganin autar tashi ahakan yayunta maza sukazo aka had'u aperlon abban anata firar yoshe gamo da mahaifin nasu ahaka suka wuni ranar cikin farin ciki da Jin dad'in...


Sameer ne zaune Yana wayada abokinshi Imran akan zancen Wannan hatsabibiyar kungiyar domin Imran natemaka masu sosai akan binciken Amma fa yanzu dukkansu kansu yad'aure harshi Imran domin duk bin kwakwab d'insu sunkasa samun wani k'wak'waran hujjar dazasu tunkari kungiyar kaitsaye..seda suka Gama tattaunawa kana sukayi sallamah tareda yanke wayar..ajiye wayar Sameer yayi zetashi kenan yaji shigowar sak'o dawowa yayi yad'auka tareda dubawa..Ido yazaro cikin sauri tareda k'arasa bud'e sakon dayagani anturo Masa med'aukeda tambarin kungiyar dubawa yashigayi Sosai duk wani information dasuke nema akan gungiyar shine akaturomai tareda bashi tabbacin zasuyi taron karshen shekara Wanda duk wani members na gungiyar doline zezo hadda uban gayyar..cikin farin ciki yashiga bin nomber da,aka turomai sak'on Amma batashiga akacemai akashe layin yake Dena Kira yayi yatashi yad'auko laptop d'inshi yakwashe Gabaki d'aya sak'on yamayar Nan kana yakwashe kayanshi yabar wurin..




Matafiya


sun sauka lpy a abuja yayinda hukumar sojoji kecikin matsanancin farin ciki nasamun nasara akan wadd'annan miyagun mutanen..ahakan kowa yanufi masaukinshi tareda k'udirin idan gari yawaye sunufi gidajensu kamun sudawo bikin karin girman daza,amusu..abangarensu yazeed kuwa Basu kwantaba suna fitowa sukace su yanzu zasu tafi sulaiman kawai suka bari ahakan sud'auko hanyar gida yayinda suka tsara yadda zasu gayawa su abba akan yarinyar dasukaxoda,ita domin yazeed yace bazeyu sufad'i asalin abunda yahad'asu da,itaba dudda shima yanada tarin tambayonyin dazeyiwa Ahmad Amma baze iyaba yanzu barinshi zeyi sesun koma Dan yasan sadeeq bakyaleshi zeyiba doline yatuhumeshi dubada irin kallan dayakemai yanzu na tuhuma daganan idan yatambeshi shima seyaji tashi amsar dahaka yabar zancen acikin ranshi har suka iso kano.




Bawanda sukagayawa zuwansu shiyasa bawanda yasanda zasudawo dayamma liss suka susho unguwar tasu sunakawowa da motarsu ana bud'ewa abbe Gert suma Danna hancin motarsu ciki sukayi Perkin tareda fitowa sadeeq ke driving Dama yazeed na gefenshi yayinda Ahmad kebaya da Kuma budurwar jeji wurin abbe suka nufa yayinda Ahmad yacire jerked din jikinshi yasaka Mata kana suka fito suma kanta akasa sukanufin wurin abbe..cikin farin ciki abbe ke kallansu kamun yace "too gwarazan Nene saukar yoshe bako sanarwa yafad'a tareda rungume sadeeq dayazo wurinshi.. murmushi kawai sukayi dukkansu tareda gaidashi..amsawa yayi Yana cigabada hogging dinsu d'aya bayan d'aya..tareda kallan budurwar dake gefensu Amma bece komaiba..ahakan suka rank'aya zuwa cikin gidan pert d'in big mom anan duk suka Sami sauran Yan uwannsu zama sukayi akad'an gaisa kana suka tashi zuwa pert d'insu bin bayansu tayi kanta ak'asa takasa d'agowa balle takallikowa awurin big mom ce talurada,ita cikin sauri tace"Wannan wacece abayanku sadeeq? Se asannan sukatinada,ita shiko Ahmad bamantawa yayiba kunyar yin magana yakeji Kuma yayi tinanin Yan uwan nasa zasuyi yayinda gogan yayi tafiyarshi ko waigowa beyiba..


"Am wlh mantawa mukayi big mom acan muka karb'ota hannun Y'an bindigar cewar sadeeq.."ayya sannu baiwar Allah zomuje kiyi wanka kicanza Kaya kinjiko Kuma koje inkun huta kuzo kuci abunci tafad'a tareda jan hannunta suka wuce..suma fitar sukayi tareda nufar pert d'insu..


Bayan Isha,I


Kowa yadawo gidan an had'u duka apert din hajiya mama bayan sunci abunci akadawo perlo aka zazzauna Abba ne yakalli Salman yace"jekacewa zarah tazo dabak'uwar yarinyarda su yazeed sukazo da,ita.."ok Abba yafad'a tareda barin perlon yanufi gun big mom..suko dukansu addu,a suke aransu Allah yasa shirinsu yakarbu agun su Abba musamman ma Ahmad suna nan zaune big mom tayi sallamah tareda yarinyar Salman nabiye abayansu zama big mom tayi kusan hajiya mama tareda zaunarda yarinyar kusan Abba.




Gyaran murya Abba yayi tareda bud'e taro da addu,a dakuma yiwa yaran nasu sannudazuwa bayan yatayasu murnar samun nasarar aikinsu kana yasake tambayar inda suka samo Wannan budurwar..yadda suka gayawa big mom hakan suka sake fad'a..jinjina Kai Abba yayi tareda dubanta yace y'ata k'arabonan kinjiko..matsowa takarayi kusan Abba Amma batace komaiba.. kallanta Abba yasakeyi kamun yace"yasunanki?


"SAFNAH tafad'a ciki dadd'an vocie d'inta kanta Duk'e batareda tad'agoba. Seda Ahmad yalunshe kyawawan idanuwansa yasabida yadda sunan yashigeshi sosai.."Masha Allah SAFNAH inane garinku? Abba yak'ara jifo Mata tambayar..shiru tayi batace komaiba.."kinaji ana magana kinwani share mutane sekace badake akeyiba yazeed yafad'a cikin Jin haushinta domin ganiyake duk tabata musu lokaci gaya tasakasu yin k'arya.."Inna K'arajin bakinka ana yazeed Sena sab'ama kaike tambayarta Koni Allah Kar wanda yak'ara d'aga Mata murya kunji nagaya muku muryar Abba tadaki kunnu,wansu wani sanyi Ahmad yaji aranshi domin har yafara B'ata Rai.


"Inajinki safnah gayamun inane garinku zansaka amaida hargida kinji..kasa magana tayi se shash,shekar kukanda takeyi hajiya mama tazo kusanta tafara lallab'ata tareda Bata hak'uri kana tasake memeta Mata tambayar da Abba yayi mata...cikin matsanancin kuka me tsuma zuciya tace"ni Yar nigar ce Kuma banada kowa aduniya duka sunkashesu sunkashemun iyayena da Y'an,uwana duka banada kowa ayanzu tak'arasa zancen chikin wani sabun kukan.."karya takeyi abbah Wannan aljanar muzaki renawa han..hadiye sauran Maganar yazeed yayi sabida bigemai bakida abbe yayi..itako cikin kukan tacigaba da fad'ar "wlh Allah dagaske nake niba aljanah bace mutin ce Kamar kowa sedai inada tawaya arayuwata domin idanuwana nada matsala sabida komiye nakallah sunanshi gawa mutin ko dabba ko wani abun daban indai nakalleshi to ze mutune..kallanta kawai su Abba keyi cikin mmkin furuncinta kamun abbe yace bamu gane mikike fad'a ba gayamuna yadda zamu gane.


"Nima wlh Allah bansan komiyeba Amma abunda nake fad'a gaskiya ne..shiru wurin yad'auka bawanda yasamu damar yin magana tsawon lokaci kamun dady dase yanzu yayi maganq yace"to ahakan aka haifekine?"ah,ah befi shekara 1 ba da abun yasameni alokacin mutuwar iyayena Kuma Wanda suka kashesu haryanzu farautar rayuwata sukeyi..."nashiga aljannah da izzinin ubangiji wakuma ake farautar ranshi tofa 🤔 Wannan tambad'ewar har Ina ah,ah wlh nikam Banga meshan jinin jikina ba yawwa ayi zamani kowa yazama gantalalle..cewai hajiya Nene dake shigowa yanzu.."bakowa Nene abunda kefaruwane agari muke tattaunawa cewar dady.."ato yanzu naji zance suwad'an,nan jibga,jibgan yoshe sukadawo bako gaisuwa? yanzu har nayi lalacewar da zaku bargari kudawo kuk'i nema na kosabida nayi maku zancen aure to Dani kuke zancen Dan wlh Allah indai nicenan nahaifesu gasunan tanuna su abba to bawanda mako ze juyo bashida Mata sedai idan bana duniya yawwa. Tak'arasa zancen tana cinnu Dan kwali gaban kanta.


Ido suka zaro 😳 atare cikin razana dafurucinta tareda cewa mikikace Nene?"abunda kukaji shina fad'a lusarai kawai Kuma kamunnan duk Sena kaiku gidan boka yadubamin lafiyarku.."boka Kuma Nene ? Dady yafad'a tareda San K'arin bayani.."eh Mana boka to minene shi inba bokaba rikita kukecemishi ko minene Ohoo dai Amma Sena kaisu hassibiti yawwa.. murmushi duka sukayi Jin abunda Nene kenufi kana Abba yace dus sutashi suje seya nemesu..itako big mom hannun safnah rakama suka mik'e zasu fice se,asannan Nene takula da safnah"ke Zara,u wacece Wannan kyakkyawar yayinyar Y'ar makauniya? "Wlh barayin Mutane suka saceta Nene shine mazajenki suka cetota yanzu magani za,amata anan garin sabida sun kashe iyayenta.."ayya Allah sarki baiwar Allah sannu ko Y'ar Nan allah yasaka Miki kinji Zaki zauna damuko? "Eh safnah tace kanta akasa.."to shikenan ma tazo gidan sauk'i gwarazan nawa nasamowa d'aya Mata a
Cikinsu

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login