Showing 45001 words to 47553 words out of 47553 words
“ Na gaza Bama Yaron ka tarbiyya a matsayina ta uwa , ka yafe mun Bukar ”.
Muryar Alhaji Bukar ne ya dauki rawa“ Hajiya Maryam kina nufin Yaro na Haidar yana nan a raye ? Yana ina ina Ɗa na yake???? . Kallon sa tayi a tsayen da take ba tare da ta zauna ba , cikin dannewa ta furta “ Wannan matashin da aka yanke masa hukuncin shekaru Ashirin da biyar a gidan yari wato ALEXANDER the young billionaire ba kowa bane fache yaron ka ɗan ka na cikin ka Aliyu Haidar.................!
Jiri ne ya fara ɗiban Alhaji Bukar wanda cikin ganin duhuwa ya lalibi kujeran dake gyefen sa yana zama ba tare da ɗago ba , Wani irin juwa yake ji na ɗibar sa ,a hankali ya fara tunano haɗuwar sa da Alex na da furucin sa garesa “ idan kai matsafi ne Ni babban ka ne! Ina yawan ganin ka a mafarki na tun ba yau ba ,to ka sani ALEXANDER ya fi ƙarfin ka.......Huhhhhmmmmmm Wani irin Dogon numfashi ya sauke ,kana ya furta “ Innalillahi wai'innah ilaihir raj'iun......!
Kuyi haƙuri Please page din bai yi tsawo ba🙏🏻
*🕊️ZAKI🕊️*
Na
*Aunty Ayshatou Mamanteddy*
Book 3
65-66
_________________________
The Writer of :
1)Ƙwarton manya
2)the Sexy Boss
3)Gidan ƙwarata
4) Walijaam
5)ƙwarton manya
6)siyasata
7)my Lady boss
8)Ƴar tsakar gida
9)fyade
10)Ƴar aikina
11)ƴar waye
12)dijama yar Fulani
13)Bintoto
14) zuma da maɗaci
15)the virgin maid
16)Rainon soja
17)Duniyar shahara
18)Sadaka yallah
19)Gidan zaurawa
20)Ƙwayar sama
21) Bafullatanan Ruga
22)Taɓarah
23)x world duniyar shahara.
*And now ZAKI......🔥*
_________________________
Littafin na kuɗi ne Regular payment ₦500 Vip payment ₦1000 SPC payment ₦1500 via 6037312299 Mohammed A'isha keystone bank ko katin MTN ta Wannan number 08081202932
Ganin yanda Alhaji Bukar Macciɗo ya zauna hankalin sa tashe yasa Mom juliana itama zama a kujeran dake fuskantar wanda yake zaune . A hankali ta fara kora masa bayanin Alex da kuma yanda Mom Silvaline wato yayar ta ta raine sa , Daga karshe ta gangaro masa har Haɗuwar sa da A'iee da Aurenta da yaje Church aka daura masa , Wanda a yanzu juna biyu ne da ita ”. Hummmmnnnn Jan Numfashi Daddy yayi mai karfi yana saukewa kana yace “ Aisha kiyi Haƙuri da duk abin da ya faru ki yafe mawa yaro na bisa ga cutarwar da yayi Miki ,tabbas ko wani Ɗan adam yana tafiya ne a bisa zanen ƙaddarar sa ,Wannan ƙaddara ce ta Alex wanda ga makomarta duka ba zai mana dadi ba. A yau zan mai daki ma iyayen ki muje domin ayi masu bayani mu kuma basu haƙiuri ”.
Kallon Alhaji Bukar Macciɗo A'iee tayi kana tace “ eh na san da Wannan amma kuma ban ji kayi maganar fito da Aliyu ba, Shima burin sa kenan har muka shigo nan garin ,duka a tunanin sa zai je ga iyaye na ya basu Haƙuri sai wannan Abin ya faru , zan fi jin dadin ace dashi a Wannan tafiyar zuwa gidan mu kaman yanda shima yaso hakan .
Shiru su duka sukayi suna jin bayanin A'ieeee , Kana Alhaji Bukar ya girgiza kai tare da cewa “ Hajiya Maryam zaki iya biyoni don muje ga Hajiyata sannan inaso na tara duka family na don nayi masu bayani....ina mai baki haƙuri Maryam domin kuwa Ahlaan ƙanwar Aliyu itace wacce ta fallasa duk wani Ayyukan sa ma ƙasa har aka kai ga Wannan matakin ”. Saurin ɗagowa Mom juliana tayi tana kallon Alhaji Bukar kana tace “ ALLAH mai iko , ba komai bane ai , Sanadin Wani abu zaka ga Allah yayi sanadiyar Haɗuwar babban Abu . Gashi zata ji labarin ɗan uwan ta ne , sannan kuma nima zan ga Ƴa ta wacce na barta tun bata fi shekara ɗaya ba a duniya .
Girgiza kai Daddy yayi yana jajanta wa yayin da A'ieeee sam bata ma jin su , don data rufe idanun ta a yanzu fuskar Alex kawai take gani yana sakar mata Wannan murmushin nasa Wanda ita kaɗai take ganin irin sa daga gare sa. Ina Sonki matata! Wannan furucin nasa ta tuna wanda yasa ta zuba wasu irin zafafan ƙwallah”.
*
4:00pm.
Shiru duka falon aka ɗauka tsawon mintuna goma daga masu kuka sai masu haɗawa dogon tunani. A'ieeee ce na hango zaune kusa da Wata ƴar tsohuwa wato mahaifiyar Alhaji Bukar Macciɗo Hajiya Turai.
Allahu Akbar! Allahu Akbar!!! Tabbas ƙwarai Maryamu kinga Rayuwa , Kin kuma cika ƴar halak da kika kasa sakin addinin Musulunci. Don haka inshallah wannan kin dawo cikin zuri'ar nan tamu kenan dawowa ta har abada. Juyawa tayi ga Alhaji Bukar Macciɗo tana share hawaye kana cike da girma tace “ Tabbas kayi kuskure daka raba ƴa da uwar ta , Ita Hajiya Rahima ba zata iya karɓar ƙaddara ba , data haifi yaro ya mutu sai Maryamu zaka rarrasa ka amshi ƴar ta Ahlaaan da suka haifa a rana ɗaya ka bata? Shima Wannan kuskure ne babba . Ƙwarai Ahlaan ki yafe mana duk da ban san Ni lokacin da aka yi wannan aiki ba ,amma Tabbas Mahaifiyar ki kin yi sa'ar uwa ta gari mai sadaukar da farin cikin ta don wasun ta .
Ɗago da ido Ahlaan tayi tana Sharɓan Hawaye , cikin dasushshiyar murya ta furta “ Yanzu kenan babu yanda za'a yi a fito da Ɗan Uwa na daga kurkuku ?, Tabbas nayi nadama na kuma danasanin kasancewata ta ƴar jarida . Kiyi haƙuri Ahlaan ƙaddara ce , tabbas Wannan haka Allah ya rubuta , Fahad ya furta idanun sa sunyi jajir shima dagani kasan yana cikin ƙunar rai da rashin jin daɗin Al'amuranta su .
Tabbas daga yau na ajiye Aikina ta ƴar jarida, na bar jarida bari na har Abada!
Kallon duka suka yi , har da Hajiya Rahima wacce sam bata yi la'asar ba , don dawowar Mom juliana rayuwar ta tabbas ta kudurci yin Abubuwa da yawa na daukar fansa na kuma ganin ta bar da ita Rayuwar ta dana mijin ta ,ga kuma uwa uba sabon labarin da taji a yanzu wai Ahlaaan ba yar ta bace yar Hajiya Maryam ce wato Mom juliana .
Haba Ahlaan ki kwantar da hankalin ki please, Aliyu zai dawo ,duk yanda zamuyi a yanzu babu yanda za'a yi mu fito dashi daga wannan halin , har sai nan da Wasu watanni a lokacin da Mahaifin ku ya zama president , sannan ba daga zaman sa ba ne zamu fito dashi dole sai ya dau wani lokaci tukuna ”.
Kamin Ahlaan ta ba ma A
Hajiya Rahima amsa ne suka ga A'ieeee ta mike tsaye idanun ta a kumbure murya a ɗashe tace “ Yayi ina maku fatan ALLAH yanada sa'ar siyasa Ni zan wuce garin mu yanzu , saboda banga amfanin zama daku ba sam ”. Ba zaki tafi ba Ai'eesha! Ba zan taba barin Matar yayana ta koma Kauye tayi rayuwa ba , A taƙaice tayi nesa damu , Bamu san halin da kike ciki ba da kuma yaron cikin ki , don haka Nima nagama yanke hukuncin barin kowa nawa....zan bar Nigeria Mom Maryam kuyi mun afuwa ba zan taba dawowa ba har sai ranar da Dan uwana ya zama ƴantacce , Don haka zan tafi da A'ieeesha don cika ma Ya Aliyu mafarkin sa .......!
Hummmm muje zuwa💃🏻
*🕊️ZAKI🕊️*
*69-70*
_________________________
Jikin su ko ina Rawa yake yi banda A'ieeee wacce ta tsaya kurum tana zubawa sarautar Allah ido . Tsohuwar kin san wannan menene? Ɗaya daga cikin su ya furta yana ɗaura ma Mama Abu Bindiga a ka , wanda jiki na kyarma mama Abu tace“ Kuma girmansa Allah kar ku cutar damu....mene muka yi maku?”. Wannan itace tambaya ta masu hankali ,wani ya furta yana takowa zuwa inda A'iee take tsaye itama sun daddaura mata Bindogogi aka ,tamkar wacce tayi kisan kai ”. Ke yarinya! Ki taimaki tsohuwar ki da kuma jaririn cikin ki , Ki bamu dukkan wani abu da Sir Alexander ya baki , idan kuma kin ƙi zamu tafi daku muyi maku kisan wulaƙanci ”. Hmmmm Shine Abin da ya kawo ku? Koda ban sani ba kuna daga cikin Yaran sa ,wanda ashe dama ba zamar ALLAH kuke yi dashi ba , don ya garere ku ne da ba don haka ba da tuni shima Kun nemi tasa Rayuwar , To Ni kam a yanzu sai da kuyi mun duk abin da zakuyi ba zan bada komai ba ,don ba zaku sami komai daga gareni ba ”. A'iee ta furta Muryar ta a dake babu alamar tsoro,don ita gaba daya taji zuciyar ta ta ƙeƙeƙashi tun daga Ranar da ta rabu da Alex , Sau da dama tana mamakin kan ta itama , don cewa take me yasa take jin sa a ko wani rufe ido da zata yi ta bude ,mai yasa a kullum take ganin sa a barcin ta ,tabbas tafi alaƙanta wannan da Tausayin sa ne ya ɗarsu a zuciyar ta .
Muryar Wani inyamiri ne ya katse ta yana cewa “ Tabbas da ba don kar muyi abin da bashi ba ,mu karya umarnin malam Silvaline to da a yanzu mun kar ki , mun raba ranki da jikin ki ”. Ku tasa su mu wuce dasu duka! . Haka Aka tasa su Mama Abu suka fice dasu daga gidan ,suna tura su a motocin su tare da kai su inda basu sani ba ”.
*
Alhaji Bukar yau dai Allah yayi ka gani Allah ya baiyana mana Abin da muka dade muna jiran dawowan sa ,wato Hajiya Maryam . Don haka Yazama dole a cikin satin nan mu nemi malamai muji ya Auren ku yake , za'a sake mayarwa ne ko kuwa Auren yana nan? , Hajiya Turai ke maganar tana kallon Alhaji Bukar da yayi zama a gaban ta cike da ladabi ta uwa da Ɗa . Hmmm Gaskiya ne Hajiya ,Nima kai na a kwanakin nan da Wannan tunanin nake kwana da tashi . Sam hankalina baya natsuwa in gan ta a can wani gida da ban ba gidana ba . Ƙaran shigowar saƙon wayar sa ce yasa shi kai idanun sa saman screen ɗin ,inda yaga an turo masa saƙo kamar haka “ Barka da warhaka ranka yadaɗe . Yanzu na sami labarin sakin Yaron mu Aliyu daga gidan kaso, akan wasu Ƙwaratan hujjoji, sannan ina ta kokarin kiran wayoyin sa duka basa shiga ”.....zumbur Alhaji Bukar yayi yana miƙewa tsaye tare da ƙara gyara zaman medicated glass din idon sa . Lapiya wani Abu ne ya faru? . ALLAH yasa muji alheri ....Hajiya Turai ta furta tana kallon Alhaji Bukar tare da jiran jin amsar me zai ce daga bakin sa .
Hajiya Yanzu Hajiya maryam ce ta turo mun da saƙon Aliyu baya gidan yari gomnati ta sake shi saboda wasu hujjoji yanzu haka bata san inda kuma ya nufa ba. Alhamdulillah 🙏🏻 ALLAH mun gode maka , yanzu meye na shiga tashi hankali kuma?. Hajiya Aliyu bai san Ni mahaifin sa bane , kar ki manta mun so gomnati ta bar Ni nayi magana dashi amma suka ce a'a sai yayi sati biyu a gidan kaso sannan kowa ke da daman ganin sa . Kar ki manta Ahlaan ce tayi sanadin Faruwar komai , Aliyu Haidar Ni nasan waye shi ZAKI ne ,wanda baya taɓa barin akai sa ƙasa bai rama ba . Ahlaan ce abin harin sa a yanzu ,kar ya cutar da ƙanwar sa uwa ɗaya uba ɗaya bai sani ba ,yayi ba dagangan ba .
Tabbas maganar gaskiya ce , kayi kiran Ahlaan ka turketa a cikin gida kar ta fita har sai an ga Aliyu Haidar sannan . Juyawa Alhaji Bukar yayi saurin yi yana faɗin tot,to to....Hajiya badamuwa bari naje....yana maganar tare da Kiran layin Hajiya Rahima don yaji Ahlaan na cikin gidan ne!
*🕊️ZAKI🕊️*
*71-72*
_________________________
Tun a mota yake kiran Numbern Hajiya Rahima amma kuma kashhh bata shiga hankalin Daddy idan yayi dubu yayi kololuwar tashi . A haka yake cewa da drivovin su kara gudu .
*
Kin sanni?
Ta furta tana sauke mata faskeken Gilashin idonta, ga wasu zaƙozaƙon eye lashes da suka sauko . Bin ta da kallo A'ieeee tayi kana tace “ Ban sanki sai dai yanzu idan kin mun bayani”.
Juyawa Mom Silvaline tayi tana kallon su David kana tace“ hmmmm Ashe yarinyar cararrace bata da kunya ”. To ba sai na ƙara magana da ita ba , Domin ada nayi niyyar barin ta a raye , amma kuma a yanzu ku kashe su duka da ƴar da uwar , shi kuma sauran duk abin da muke buƙata daga hannun su ,David ka tura Wasu daga cikin Mutanen mu su nufi gidan suyi sanka sanka da komai a fiddo da su .
Ƙasa magana Mama Abu tayi , wanda A'iee itama da ido take kallon matar da a kallo Daya zaka fahimci Bata da imani ko tsoron Allah. Ɗago da A'isha suka yi suna inguzata tare da tasa ƙyayarta suna kokarin fitar da ita daga Wurin don su cika umarnin Ma'am Silvaline . Joshua dake gaba ne suka ga ya yo baya a tsorace yana fiddo da idanun sa , gumi na karyo masa a lokaci ɗaya ..... Cikin daka tsawa Mom Silvaline ke tambayar sa lapiya? Amma sai Muryar sa ya harɗe ya hau Rawa yana furta “ Boss ”.
Boss” , ta furta cike da rashin fahimtar ina ma ya dosa , ya kuma nufa . Kai dalla kayi mana magana , David ya furta a zafafe yana yin gaba tare da jan labulen,inda shima da sauri yayo baya ji yayi kamar yayi fitsari a wandon sa don tsoro . Muryar sa na Kyarma da Rawa ya kalli Ma'am Silvaline yana cewa “ Ya Dawo! Shikenan mun shiga uku!
Cike da Shan jinin jiki ta furta wa kake so kace mun? Alex? .
Yes king is back......, Saurin Ɗagowa A'iee tayi tana kallon su jin an ambaci sunan Alex tasan waye suke nufi , kamin suyi wani matso tuni jami'ai sun banko ciki , Alex na basu umarnin su kama su duka ”.
Bai tsaya bi takan kowa ba , cikin izzan sa ya taka yana isa zuwa inda Ma'am Silvaline take , kana yace “ Kar kiyi mamaki Yaron ki ya wuce yanda kike zato , Na gode Da kulawar ki da kika bani na rabani da Mahaifiyarta da ɓoye asalina na taso a Arne wanda rayuwar sa babu daɗi sam....tabbas shigowar ta Rayuwata haske ne ta kasance mun fitila ,ya furta yana nuna inda A'ieeee ke tsaye ,kana ya cigaba da cewa “ ita din wata babbar gudumuwace Allah ya turo ta rayuwata ,don na banbace baƙi da fari .... shiyasa nake Son ta sosai . Ina Sonki A'ieesha . Matsawa yayi zuwa inda A'iee take yana kai hannun sa tare da shafa gyefen kuncinta , a hankali ta ɗago idanun ta Da suke zubar da ƙwallah da ta rasa na mene ne? Ganin haka bai tsaya duba ga jami'ai ba ko mama Abu da bai san wacce ita ba , kawai sai haɗa bakin sa yayi da nata yana kissing yana Rungume ta tare da manna ta jikin sa .
Dpo ne ya furta “ Sir zamu wuce dasu yanzu . Don shi kam shi abin na Alex ya ƙayatar dashi ,tabbas yana zafin son matar shi ko ba'a faɗa ba , a aikace zaka fahimci hakan. Ba tare da ya zare bakin sa daga nata ba , da hannu ya ɗaga ma D.p.o alamun yayi aikin sa . Haka aka tattara su Mom Silvaline dai dai su Daddy na shigowa........💃🏻