Showing 42001 words to 45000 words out of 47553 words
“ Ba haka ake sallah ba , kana so kayi ne? . Lumshe idanun sa yayi yana buɗewa kana yace “ Eh , koya mun”. A'a ba zai yiwu na koya maka ba , Har sai ka amshi Addinin Musulunci sannan zaka fara sallah Allah kuma ya karba ”. Shiru yayi kana yace “ Yanzu ba zaiyiwu nayi ba kenan , Kema amsar addinin kika yi , sannan ki fara Sallah ? .
Girgiza kan ta A'iee tayi tana cewa “ A'a Ni a cikin addinin Musulunci aka haife Ni ,kaine da aka haife ka a wata addinin sai ka amsa sannan . Takawa yayi yana isowa gaban ta kana yace “ Yau kin yi mun magana ,wanda baki taɓa ba ,ko meyasa? . Nima ban san me yasa ba , Amma dai kawai dariya ka bani ”. Thank God yau na sakaki kin yi dariya ko a yanzu na rasa rayuwata naji daɗi . A'a baka huta ba , saboda babu kafirin da zai mutu a kifirci yaji daɗin lahira , har sai idan ya amshi musulunci kuma ya musulunta saboda ALLAH da Manzon sa . Gani tayi Alex yayi baya kaɗan yana cewa “ Gobe zamu sauka a Egypt zan amshi Addinin Musulunci,daga nan zamu koma Nigeria, Kiyi farin ciki zaki rabu da Alex amma zaki ga Iyayen ki”.
Cike da rashin fahimtar sa ta saki murmushi har hakoranta suna bayyana kana tace “ Da gaske , ka taimake Ni don Allah , Mama kawai nake son gani . Hannun sa yasa yana Rungume ta tare da shafa bayan ta a hankali kana cikin sanyin murya ya furta “ Zaki ga Mama, amma please A'ieesha kiyi mun alƙawarin zaki So abin da zaki haifa nawa,sannan Zaki kula mun da kan ki da Babyna sosai ”. Cikin sauri A'ieeee ta gyada kan ta tana cewa “ Nayi maka alkawari,indai zaka bar Ni nayi rayuwata Ni ɗaya ”. Ɗan raba jikin ta yayi da nasa kana ya nufi inda ya tashi yana ɗauko wata jaka yana cewa “ Wannan Ki riƙe shi da kyau duka naki ne kar ki ba kowa ,kar kuma ki bari kowa yasan meye a cikin sa . Ki kula sosai . Sannan Mom juliana ma na san ko bayan Rai a Zata kula mun dake ”. Turusss tayi tana kallon jakar,kamin tayi wata magana taga ya juya yana cewa “ Zan je gidan Mom juliana a wannan daren gobe da safe Flight din mu zuwa Egypt daga nan zamu wuce gida.
*🕊️ZAKI🕊️*
Na
*Aunty Ayshatou Mamanteddy*
Book 3
59-60
_________________________
The Writer of :
1)Ƙwarton manya
2)the Sexy Boss
3)Gidan ƙwarata
4) Walijaam
5)ƙwarton manya
6)siyasata
7)my Lady boss
8)Ƴar tsakar gida
9)fyade
10)Ƴar aikina
11)ƴar waye
12)dijama yar Fulani
13)Bintoto
14) zuma da maɗaci
15)the virgin maid
16)Rainon soja
17)Duniyar shahara
18)Sadaka yallah
19)Gidan zaurawa
20)Ƙwayar sama
21) Bafullatanan Ruga
22)Taɓarah
23)x world duniyar shahara.
*And now ZAKI......🔥*
_________________________
Littafin na kuɗi ne Regular payment ₦500 Vip payment ₦1000 SPC payment ₦1500 via 6037312299 Mohammed A'isha keystone bank ko katin MTN ta Wannan number 08081202932.
Wani irin sanyi taji yana ratsa zuciyar ta cike da jin daɗi ta sakin masa murmushi jin ya ambata kalmar Gida . Hannun sa yasa yana warewa tare da rungumeta kaɗan , tamkar wanda baya son raba jikin sa da nata yake zame jikin sa ,kana ya Ɗaga mata hannu tare da furta kalmar ki kula sosai ,zanje na dawo . Gyaɗa masa kai tayi ba kuma tare da tace komai ba , har ya fice ”.
Ranka yadaɗe a yanzu me yayi saura jiran dawowan sa kawai muke daga nan Zamu yi raaam dashi ,kai tsaye kotun ƙoli za'a wuce dake garin Abuja, a yanke hukuncin sa a kuma aika sa gidan kaso,idan na kisa ne duka ya cancanta ”. Chief of judge ɗin ne ya gyaɗa kai kana yace ” Idan Muna so shari'ar ta tafi wurin yanke hukuncin gaggawa ,shine kar a aika masa da Wani saƙo na ko yasan halin da ake ciki , mu bari yana isowa ayi rammm dashi .
Jan dogon numfashi Ahlaan tayi bisa Tuno da bayan da suka yi da Alƙali , murmushi ta saki sam ta manta a dinning table suke suna Yin break fast ”. Ahlaan lapiya kuwa? Kina ta murmushi ke ɗaya? .Fahad ya furta yana sake duban Ahlaaan wacce ta farga da abin da take yi . Alh Bukar Macciɗo ne ya furta “ Nima dai tun ɗazu shi nake ta gani .
Hummmm Daddy dole ku ganni haka, Dalili kuwa Ana gab da kama mai laifin da Aka daɗe ba'a kama ba, wanda ƙasa ma ke shakkar sa Wato King Alex , Idan zaku iya tunawa shine yazo gidan nan yaci mana mutuncin mahaifi a gaban idanun mu ,babu wanda ya iya tankawa, Alhmdlh a yanzu dukka wasu hujjojin laifin sa suna hannun gomnati wanda Shari'a kuma ta hau kan sa , A kiyasce ƙila hukunci ne Ɗaya zuwa biyu dole a yanke masa , Na ɗaya Kisa bisa abubuwan daya aikata,na biyu Ko zaman gidan kaso na har abada ”.
Ajiye fork ɗin hannun sa Fahad yayi cikin sauri yana furta “ Ahlaan nikam sai naji banji daɗin hukunci da za'a yanke masa ba tun a duniya, Cox Arne ne , ace yazo duniya ya mace a haka ,kuma a lahira ga makomar sa . Why not a rabu dashi , Allah ya shiryar dashi sai naji ba daɗi sam duk da abin da yayi mana bai ƙyauta ba .....Kai yi ma mutane shiru Fahad! Mutumin da yake lalata yara har yake safarar su kake magana a ƙyale ,ai kuwa da duk wasu masu faɗa aji na Nigeria zasu koma gurɓatattu wannan shine dai dai ....“Cewan Hajiya Rahima cike da Tsawa , shi kam Alh Bukar Macciɗo tun da suka fara wannan tanka tankan sam bai tanka ba , ganin haka yasa Mufidah kashe Maganar da cewa “ Ohh wannan fa bamu san shi bamu da wata jiɓi ko alaƙa dashi ,to meye na damuwa dashi har muke nemar musu da rabuwar kai a tsakanin mu . Wallahi Ni kam koda rataye shi za'a yi ba zanji komai ba ,saboda kafuri ne , mara kuma imani”. Uhmmm Kema dai kyama dai kya faɗa ”. Cewan Hajiya Rahima ,wanda jin hakan yasa Fahad yin shiru bai kuma ce masu ta tafasa ba ”.
Tun da ya fara magar hawaye ke bin kuncin Mom juliana, Tsawon lokaci tana riƙe da hannun Yaron nata ,wanda take jin ƙaunar sa da Tausayin sa a zuciya . Mom zan tafi ina so ki kula mun da matata da abin da zata haifa, Ina Son matarsa ina son Aysha . Miƙewa taga yayi yana nufin tafiya sannan yasa Mom juliana sa hannu tana sharce Hawayen fuskar ta ,kana tace “ Aliyu! Damnnnnnnnn.......!!!” yaji ƙirjin sa ya buga da ƙarfi , amma sai bai dakata da tafiyar ba ,a tunanin sa ba dashi take ba ,don bai taɓa jin wani ya kiransa da makamancin Wannan suna ba ”. Da kai nake yi.....Ta furta tana Saurin takawa zuwa inda ALEXANDER yake . Mom Wani suna naji kin kirani dashi na daban wanda nikam ban taɓa jin sa ba , sunana Alexander tun taso wata da wannan suna nake . Girgiza kai tayi tana sharɓan wasu zafafan hawaye , a hankali ta furta “ Ba SUNAN ka bane Wannan suna ce da ta biyo bayan sunan da mahaifin ka ya sanya maka . Sunan ka Aliyu Haidar,kuma Ni a musulunci na haife ka ....ina mamakin baka taba tambaya na mahaifin ka ba Haidar . I'm sorry mom Ban taɓa wannan maganar ba ko tambayar ba saboda nasan ke mahaifiya ce ta ƙwarai ba zaki taɓa kawo Ni duniya da wata tabo ba . Ta hanya me kyau kika haife Ni , yo koda ta gurɓatacciyar hanya ce to Mom sai dai ƙaddara,amma ba'a son ranki ba , Maganar mahaifina a yanzu lokaci ya ƙure, Na bar ki lapiya ”. Rungume Mom Juliana na yan sakanni yana jin wannan shine rabuwar tasu ta ƙarshe wanda ba zai sake ganin ba , Bare har suyi magana haka. Janye jikin sa yayi yana Ɗaga mata hannu alamun banƙwana kana ya fice ,Wani irin kuka ne yazo mata nan take ta zube a ƙasa tana Wani irin kuka mai gurnani tamkar zata haɗiye ran ta ta mutu ..... ALLAH ga Ɗana nan ,Allah kai taimake mun Aliyu ,Allah ka tsallakar mun da ZAKI na daga dukkan Wani sharri da duk wani abu da zai cutar dashi da Rayuwar sa .
*
Egypt
Filin saukar jirgin ne duk da ya rage tawagarsa amma kuma kai daga Ni kasan babba ne ya shigo matashin mai firgita manya , ALEXANDER sarki kuma zaki . Kallon sa A'ieeee keyi wacce take Gyefen sa yana riƙe da hannun ta raaam suna mai nufar jirgin da zai iso dasu gida Nigeria . Kallon sa A'ieeee tayi tare da cewa “ Yanzu Kana nufin ka amsa musulunci kamar yanda na gani kuma naji da kunnni na? . Gyaɗa mata kai yayi yana dan matsa yatsun ta a hankali . Amma banji sunan da ka sauya ba , don bana iya faɗan sunan ka ban iya ba sam . Kallon ta yayi yana ɗan murmushi kana yace “ Aliyu Haidar . Yayi Miki dadi, idan kika haifa mun ɗan cikin ki , ki sanar masa da Sunan baban sa Aliyu ”. Shiru tayi don har yanzu Hausar nasa a gwarance take jin shi ,wannan yasa ta cewa “ Yanxu gida zaka mai dani? . Inshallah! Saurin kallon sa tayi jin furucin inshallah da yayi , murmushi ya kuma yi mata yana cewa “ Hau step din a hankali ”. A hankali ta saka ƙafarsa tana shigewa cikin jirgin yana biyo bayan ta . Wanda ko mintuna biyar basu dauka ba jirgin su ta ɗaga zuwa gida Nigeria .
*
Tun da jirgin ya fara alamar sauka , ya tsaya yana kallon A'ieeee tare da kafe ta da wani irin mayataccen kallo . Ina zamu rayu tare , da kin fahimci wani irin so nake Miki , ina jin ki a zuciya ta , ki kula sosai bana son duk abin da zai cutar dake . Wannan kudi ne a ciki , duk abin da kika ga ya faru dani kar ki tsaya ki gudu, kar kibi mutane na , ki nufi hanyar da zata sada ki da garin ku . Ki ba iyayen ki Haƙuri bisa abin dana aikata Miki . Amma ki masu albishir da kin haɗu da mijin da ke mutuwar sonki,akan ki ya sadaukar da komai nasa harta rayuwar sa ”.
Mu tafi . Taji Muryar sa ya katse ta kamin tayi masa wata magana a hankali suka fara sauka daga jirgin , ganin baƙar fata da tayi ta ko ina yasa Ai'eee tabbatar ba yaudara Alex yayi mata ba , Murmushi ta saki tana furta “ Babu wanda ya taɓa mun alƙawari ya cika a rayuwata kamar ka , Kana da halarci tabbas musulunci.......... Ɗauke Wuta tayi sakamakon ɗagowa da tayi tana ganin jami'ai Da sojoji sun zagaye Alex sunyi attack din sa da Bindigogi suna daura bisa kansa . Ki gudu! Ya furta yana saurin matsawa daga gareta Tare Da yin tamkar ba'a tare suke ba . Kasa motsawa tayi tana kallon sa , Idanun ta duka sunyo waje , mene yayi maku? Ta tambaya kan ta tsaye ba tare da tsoro ko fargaba ba . Tare kuke! Wani soja ya daka mata tsawa , Kamin A'ieeee ta basa amsa ne Alex yayi saurin cewa “ Ba tare muke ba , mene zai haɗa Ni da Wannan wacce ba addini na ɗaya da itaba ,A taƙaice bahaushiya ce ban san ta ba .
Baka sanni ba ? Ta furta cike da mamaki ,wanda kamin ta kara wata magana Ahlaan ta iso da tawagar ta ,tana tafiya cike da izzah . A gaban Alex ta tsaya tana Sauke Baƙar Gilashin ta ,kana tace “ Wlcm to Nigeria King Alexander, Fatan ka gane Ni da ƙyau? . Yesssss! Ya furta yana kafe ta da manyan idanun sa wanda suke dauke da kwarjini . Kotu muka nufa kai tsaye yanzu kuma . Alright Ina Miki fatan nasara! Ya furta yana fara takawa tare da shige moton jami'an . Baiwar Allah mene yayi maku? A'ieeee ta furta jikin ta na Rawa .
Kallon ta Ahlaaan tayi tana kai hannun ta tare da dafa Ai'eee kana tace “ Kema kina ɗaya daga cikin wanda yake safarar ku ,don haka zamu je kotu dake ki bada hujja don a yau za'a yanke masa hukumcin kisa shi nake tunani . Fizge jikin ta A'iee tayi, tana mai cewa “ Baki da hankali! Ni yar kauye ce ,bani da ilimi ammma kuma kin san matsayina a wurin sa...................???
Tooohhhhh makaranta muje zuwa💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻
*🕊️ZAKI🕊️*
Na
*Aunty Ayshatou Mamanteddy*
Book 3
61-62
_________________________
The Writer of :
1)Ƙwarton manya
2)the Sexy Boss
3)Gidan ƙwarata
4) Walijaam
5)ƙwarton manya
6)siyasata
7)my Lady boss
8)Ƴar tsakar gida
9)fyade
10)Ƴar aikina
11)ƴar waye
12)dijama yar Fulani
13)Bintoto
14) zuma da maɗaci
15)the virgin maid
16)Rainon soja
17)Duniyar shahara
18)Sadaka yallah
19)Gidan zaurawa
20)Ƙwayar sama
21) Bafullatanan Ruga
22)Taɓarah
23)x world duniyar shahara.
*And now ZAKI......🔥*
_________________________
Littafin na kuɗi ne Regular payment ₦500 Vip payment ₦1000 SPC payment ₦1500 via 6037312299 Mohammed A'isha keystone bank ko katin MTN ta Wannan number 08081202932
Dakatawa Ahlaan tayi tana yin turusssss tare da kallon A'ieeee wanda take maganar ita kanta bata san mai yasa Taji Tausayin Alex ya kamata a lokaci ɗaya ba . To wacece ke? A iya sanina bai hada jiɓi da Musulmai ba ,bare kuma a musulman ma wai yarinya kamar ki bagidajiya . Jan numfashi A'ieeee tayi tana Furta “ Haka ne ,amma a wannan karon zakiyi mamaki idan nace Miki Ni matar sa ce ”. What??? Ahlaan ta furta zancen tana fiddo da idanun ta waje,kana ta sheƙe da Dariya tana cewa “ kai Lallai Alex shaiɗani ne ,mu zai saka ma fatsa da Ƴar ƙauye? Faɗa mana menene shirin ku?”. Sanin Shirin sa baya da amfani a gare ki a halin yanzu , mafi amfanin shi ne ALEXANDER kuma sannan kun kama shi , Don haka indai kin san abin da kike yi babu buƙatar duka wannan zancen a ganina kenan suka jiyo murya daga bayan su wanda cikin sauri a tare suka juya don ganin mai faɗin wannan maganar ”.
Mom juliana ce tsaye wanda sam A'iee bata san lokacin da itama ta sauka anan ba . Wasu irin zafafan ƙwallah ne ya fara biyo kuncin A'ieeee ba tare da tasan mene zata faɗi ba tace “ sun Tafi dashi Hajiya, kuma bai aikata masu komai ba ”. Takowa Mom juliana tayi cike da dakewa kana tace “ Ki ƙwantar da hankalin ki A'ieeesha , Mu saka ALLAH a gaba a bisa al'amuran mu , gyaɗa kai Tayi tana cigaba da kuka Mom juliana ta kamata suna barin wurin tare da barin Ahlaaan anan tsaye ”.
*
Saukowa yayi cike da rawar jiki kamar bashi ba magana yake jikin sa har Rawa yake yi baya ko kallon gaban sa ya furta “ Kina ina ne yanzu , kina ina ??? Gannn....gani nan zuwa . Ya furta yana ƙoƙarin ficewa daga falon Hajiya Rahima wanda sam bai lura da yaran ta da suke zaune ba suna sauraren tashar labarai inda ake gabatar da shari'ar da aka yanke mawa Sarkin matasan Nigeria wato king Alexander . Alhaji dakata mana kaji wannan shari'ar ɗan .....ya isa da ALLAH ya furta yana saurin ficewa ko waiwaye babu .
Turus duka suka yi , kamin Mufidah ta furta “ Mom kaman Daddy baya farin ciki fa? Ko dai da wata matsala ce .? Shiru duka suka yi don babu mai amsar tambayar ta . Nan take suka Cigaba da sauraren irin hukuncin da aka yanke masa ,amma abin mamaki da Tashar take fadi al'umma da dama na mamakin Yanda bai ja da Shari'a ba , kuma Duk da yana da ƙarfin dukiyar da zai iya dakatar da duk wata Shari'a da za'a yanke a kansa amma kuma baiyi hakan ba ”. Wannan shike ɗaure ma al'umma da dama kai ,da kuma mamaki.
*
Zumbur Ai'eee tayi tana miƙa tare da ɗaura hannu aka tana fashewa da ihu tare da cewa “ Wayyo Hajiya Hukuncin ɗaurin shekaru Ashirin da biyar a gidan kaso???????
*🕊️ZAKI🕊️*
Na
*Aunty Ayshatou Mamanteddy*
Book 3
63-64
_________________________
The Writer of :
1)Ƙwarton manya
2)the Sexy Boss
3)Gidan ƙwarata
4) Walijaam
5)ƙwarton manya
6)siyasata
7)my Lady boss
8)Ƴar tsakar gida
9)fyade
10)Ƴar aikina
11)ƴar waye
12)dijama yar Fulani
13)Bintoto
14) zuma da maɗaci
15)the virgin maid
16)Rainon soja
17)Duniyar shahara
18)Sadaka yallah
19)Gidan zaurawa
20)Ƙwayar sama
21) Bafullatanan Ruga
22)Taɓarah
23)x world duniyar shahara.
*And now ZAKI......🔥*
_________________________
Littafin na kuɗi ne Regular payment ₦500 Vip payment ₦1000 SPC payment ₦1500 via 6037312299 Mohammed A'isha keystone bank ko katin MTN ta Wannan number 08081202932
Hawaye ne suka ciko idanun Mom juliana, wanda kamin tayi mawa A'ieeee wata magana , Sallamar sa ya katse su . Tamkar wanda aka dinke bakunan su aka rufe duka suka tsaya suna kallon junan su ,su ukun Wato Alhaji Abubakar Macciɗo, Mom juliana da kuma A'ieeee da Wannan shine karo na farko data fara ganin baƙuwar fuskar Alhaji Bukar Macciɗo . Hajiya maryam! Maryamu baiwar Allah kece nake gani yau da idanuna, kece dai Maryamu matata wanda na dauki tsawon shekaru ashirin da biyar ban saka a ido ba ”.
Ƙwallah ne suka ciko idanun Mom juliana tana kai hannun ta tare da gogewa tana sakin murmushi a saman laɓɓanta ”.
Juyawa tayi ba tare da ta baima Alhaji Bukar Macciɗo amsoshin sa ba ta kalli A'ieeee tana cewa “ Wannan shine mahaifin ALEXANDER wato Aliyu Haidar ”. Daaamnnn ƙirjin A'ieeee ya buga cikin sauri ta juya tana kallon Alhaji Bukar Macciɗo mutum mai cike da kamala , Wannan shine mahaifin ALEXANDER? Mene ya faru ya tsinci kansa a wannan rayuwar dana same shi? Tambayar da A'ieeee keyi ma kan ta kenan , kana daga bisa Ni ta tsinci Muryar Mom juliana tana cewa “ Nice maryam wacce ka sani, Ka mance da komai na Rabuwar mu , Sannan mu dauki hakan a matsayin ƙaddara ”.
Magana ta gaba bana kira ka ne don komai ba Sai don na roƙi taimako guda , ba wai dan wanda zaka taimaka ya gaza ba ,a'a bana so ya ida rayuwar sa bai zauna tare da kai ba.
Hummmm jan numfashi tayi tana furta