Showing 24001 words to 24810 words out of 24810 words
Chapter 9 - GIRMA YA FADI Book 2 Complete By SUMAYYA ABDULKADIR TAKORI.txt
zata ce dasu ba a game da Nuratu, da bata san in da take ba. Amma a duk ranar da ta ganta, to a ranar ne zata dawo garesu.
"GIRMAN su Hajiya Sa'a yana hannunta." Wanda ke nufin, a duk ranar data fadawa duniya Sa'idun nada shegiyar diya, GIRMAN SU ZAI FADI!
"Ita Hajiya Sa'ar ce kece dani SADAKA YALLAH? Bata fadin babban? Wato (Bata fadin ni shegiya ce?)”
Wannan na nufin Hajiya Sa'a, tasan tsakanin Abba Baba Sa'idu da mahaifiyata, Nuratu, ta kuma san rayuwar su ta baya. To amma abinda ban sani ba shine shin Hajiyar ta san cewa sun haifeni? Kai babu kama, sai dai ya zamanto cewa ta san soyayyar tasu, amma bata sanda suka kai ga yin cikina, har suka haife ni ba. Tabbas da bata dinga aibatani akan su Hassan ba. Da bata dinga yin fariyar "su da gidan Uban su ba". In haka ne akwai sauran kallo a gaba. Domin kuwa ko ba-dade, ko ba-jima, sai na je na tsaya a gaban Hajiya Sa'a, na gaya mata ko ni WACE CE? In tabbatar mata da cewa BARAROJI kuma SADAKA YALLAH 'yace ga V.C Professor Sa'idu Bindawa.
Na kai hannu na shafe hawayena. Idanuna ya kai ga shafin karshe, wanda ya warware min rudanin da zuciyata ke ciki, na kokonto da tunanin ina zan dosa? Wa nake da shi a halin yanzu da ya wuce Baba Sa'idu?
Wani farin ciki ya ziyarci zuciyata, ban san sanda fatar bakina ta suBule da murmushi ba, naji kamar an dauke min wani nauyayyan dutse ne aka. To amma ina da tabbacin in sun san ta hanyar da 'yar tasu ta haifeni, zasu yarda su karBeni a matsayin JININ SU har su bari in zauna a cikin su? Inada tabbacin in sun san cewa ita kanta 'yar tasu, gudu tayi ta barni, tun ranar data haifeni don tsira da mutuncinta, zasu yarda su karBeni?
Wata zuciyar tace " na Allah basa karewa Zaynab, a ko'ina ba'a rasa na Allah, irinsu Ya Faruq da Yaya Halima, wadanda tunanin su ya sha banban dana sauran mutane, ra'ayin su ya banbanta dana sauran al'umma. Su irin wadannan mutanen kamar wasu mala'ikun Rahma ne da Allah ke saukarwa bayinsa masu matsala irin nawa. ‘They are just like angels in the midst of people' wadanda suke a shirye da sadaukar da kansu domin farin cikin wani.
Wannan ne ya kara sani dubar rubutun da nayi shekara daya da wata daya da ya wuce, daga bakin Inna ta;
"Kyauta mu ba baroroji bane, sune 'yan kasarmu dake daji, mu 'yan kasar Nijar ne, 'yan usulin wani gari Damagaram, amma iyayen mu da 'yan uwan mu a babban birni Yamai (Niamey) suke zaune, har yanzu suna can”.
“In kika shiga Niamey, kika ce kina neman wani daya shafi iyalin MAINASARA KANGIWA, ko yaro kankani ya san wannan sunan.."
Don haka na cusa littafin cikin jakata, na kishingida ina jiran garin Allah ya waye in kama hanyar kasar Nijar neman dangin Innata, in gaya masu rasuwar ta, in rokesu alfarmar su barni in zauna tare dasu, ta hanyar cewa ni ‘yar ta ce. Kamin a hankali in nemo Imran, inyi masa aure da Adda Mami, daga nan nasan ina da Uban da zai rikeni ya kuma cigaba da yi min addu'a ko bayan raina. Wato in zauna tare da shi da iyalinsa muddin rayuwata.
Na dauko wasikar da na rubutawa Ya Faruq, na sake binta a nutse, ko akwai wani gyara a ciki? Na tabbatar, babu. Ga abinda na rubutawa dan uwana rabin jiki UMAR FARUQ;
"Ya Faruq .
Zuciyata ta kasa amincewa da wai in cigaba da zama da Yaya Halima, bayan sanin ko ni wace ce?
Gangar jikina ta kasa amincewa da kai wai a matsayin miji, domin tana ganin baka cancanci hada jiki da kazamtacciya kamata ba;
You are pure as a clean glass, and I'm a green, but rotten leaf. Har ila yau, zuciyar ta takasa yafewa Nuratu da V.C Sa'idu, don ni ba zan taBa kuma kiran sa ‘Baba’ ba, ba zan taBa iya kiranta ‘Inna’ ba. Don haka na tafi, inda a hankali nake tunanin zan samu labarinta.
In tambayeta dalilin shegantani da tayi, ta kuma nemo min dan uwana a duk inda yake cikin duniya a dalilin bakin cikinta. ‘I know it will hurt, but you donno how deeply it hurts the victim’. Faruq ka yafe mani, ka yi mun godiya ga Innarmu, ina nufin (Inna Dubu).
Ina fatan watarana Allah ya hadamu cikin alherinsa".