Showing 9001 words to 12000 words out of 24810 words
Chapter 4 - GIRMA YA FADI Book 2 Complete By SUMAYYA ABDULKADIR TAKORI.txt
in fada mishi ciwon marata, sai in ga kamar abin da yake nuna mini a zahiri ba haka yake a zuciyarshi ba. Akwai dalilin shi na yin hakan. Amma in na tuna kalaman shi “jarababbiya, duk wanda ya aure ki ya shiga uku!” Sai in tabbatarwa kaina Imran wulakanta ni kawai yake.
Washegarin tafiyar Ya Faruq a cikin ajinmu kuka kawai nake su Iftahal na rarrashi na, sun dauka kukan tafiyar Ya Faruq nake basu san abin ya fi gaban nan ba. Gaba daya rayuwar Sokoto ya fice min a rai, ina ganin nisan kwanakin da suka rage tafiyana gida gaban Innana mai sona. Na yi dakacen zuwana gidan baba Sa’idu, don na san da a ce ina gida gaban Innana da duk haka ba ta faru dani ba, da ban dora idanuna a kan Imranan nan da ke wahalar da rayuwata a yau ba.
Lokacin fita cin abinci ya yi, Anti Rose malamar da ke koyar damu (compuer-studies) ta ce kowa ya taho (computer-room) za ayi (practical) bayan cin abinci. Kowa ya tafi sai ni kadai aka bari a ajin, na kifa kai cikin benci ina ta rafzar kuka.
Kasancewar na fi kowa iya (computer) a ajinmu yasa Anti Rose ta sanni, ta ke kuma nan-nan dani. Sai dai ko ita ta yi kuka dani a jiya kan makina na test dinta da ta ce ba ta ji dadinsa ba. Ba yadda Azizah ba ta yi ba in tashi mu tafi na ce ban zuwa, dole suka kyale ni suka bi sauran ‘yan ajin suka tafi suna ta kakabin sai ka ce a kaina aka fara tafiyar dan’uwa.
Can sai ga Anti Rose da kanta ta zo ta zauna a kan tebirina. Anti Rose tana da aure da ‘ya’ya biyu, za ta yi shekaru talatin a duniya, ‘yar kabilar Igala ce. ta daura hannunta a kaina tana lallashi na ta ce in biyo ta muje bayan ajinmu.
Muka zauna a kan kujeru masu fuskantar juna, cikin dabaru irin na manya take tambaya ta abin da ke damuna nake neman gurgunta karatu na a shekarar da ya dace in kara azama, wato (semi-final).
Da fari kuka nasa mata, ta kwantar dani a kafadunta na yi kukana mai isata, ba ta katse ni ba har sai da na yi shiru don kaina.
Zuciya ta nutsu da Anti Rose, don sai na jita kamar Mamana saboda yadda ta nuna matukar damuwa da halin da nake ciki, yadda ko iyayen rikona basu damu da su tirkeni haka don jin abin da ke damuna na hakika ba.
Na warware mata tun zuwana gidan Abba, da farkon haduwata da Imran shekaru uku a baya, amma al’amarin bai zafafa a gareni ba sai a wannan shekarar. Na warware mata irin abin da nake ji cikin jikina da zuciyata baki daya game da Imran, wanda na kasa boyewa har ya gane, da kuma abin da ya ce dani, da sabuwar halayyar da ya tsiri yi mana daga baya, wanda na san don ni kadai yake yi tunda su Ifty ina ruwan su? Sai kuma tafiyar da ya yi ba zato na ba tsammani, wadda ta janyo min azabar zucin da nake ciki yanzu.
Anti Rose ta dade tana dubana kamin ta jefo mun tambayar da ban tsammana ba, “Zaynab kina karatun soyayya, ko kuwa kina kallon fina-finai irin na batsa?”
Na zaro ido cikin tsoro, firgici da tashin hankali, na shiga rantse mata bana yin ko daya, ni ban ma san su ba, ban san a inda ake samun su ba. Ta sake kallo na sosai ta ce, “Shekarun ki nawa?” Na gaya mata goma sha biyar. Ta ce, “To kin san abin da ke damun ki a kan Imran?’ Na girgiza mata kai da karfi, idanuna kuru-kuru cike da tsoron amsar da za ta bani, kirjina na harbawa kamar ana luguden sakwara, haka gaba dayan kafafuna sun sage, makoshina a bushe rayas!
Ta ce, “Lust! Ko kin san wannan kalmar? Kin fada a soyayyar sa, wadda matsananciyar sha’awa ce jigon soyayyar taki. Kin shi sha’awar shi fiye da kaunar shi (lascivious passion), wanda hakan ba karamin hatsari ne ga rayuwarki ba, kasancewarki yarinya karama cikin shekarun (adolcense) wannan bai dace da ke ba.
Ki godewa Imran domin shi mai hankali ne, mai kaunar ki ne, ba don ya kasance mai kaunar ki ba, tunani da hangen nesa, da tuni ya biye miki kun aikata ba dai-dai ba. Abin da na fahimta a labarinki shine, da fari Imran yana son ki, ko-ko in ce ya fara kaunarki. Amma da ya fahimci irin taki soyayyar, ke jigonki sha’awa ce ba kauna ba. Shi yasa yake hora ki, yana so ki kiyo kaunar sa ba sha’awarsa ba, ta hanyar nuna miki kuskuren ki a fili.
Amma don son zuciya irin naki kin sa kafa kin take ke dai kawai ya yi miki abin da kike so. Ina kara gaya miki Imran mai kaunar ki ne domin da baya kaunar ki da tuni ya yi amfani da damar da ya fahimta daga gare ki ya gurbata miki rayuwa, yadda rayuwar ki za ta gurgunce, abin nufi, bayan kawar miki da wannan sha’awar ya barki, a lokacin da ke kuma ba za ki iya rabuwa da shi ba, hakan zai zamo nakasu ga rayuwarki kuma har abada ba zai kaunace ki ba, ba zai aure ki ba in ba wani babban rabo ba, tunda ya riga ya keta miki mutunci a banza.
Na yi mamakin inda kika samo wannan halayen, gaki dai a fuska yarinya saliha (innocent) mai addini, wadda kuma ga dukkan alamu kin fito gidan tarbiyya za ki tsinci kanki cikin sha’awar aikata ZINA tun baki gama sanin kanki ba……”
Tunda ta fara magana hawaye nake yi, amma da ta zo nan sai na dago ido cikin matsananciyar razana na dube ta. Wannan dama shine ZINA, da Innana ke tsorona da aikatawa, da Innana ta gaza samun kwanciyar hankali a gaba dayan rayuwarta don tsoron kar in aikata, da Ya Faruq ya wanzar da muhimmin lokacinshi wajen gaya mun illar ta, da abin da take haifarwa.
Amma rana daya na so in rushe tarbiyyar shekara da shekaru, in rushe ginin shekara da shekaru, in rugurguza zuciyar Innana dake cike taf da bakin cikin rayuwar da har abada ba za ta daina ba, wanda na tabbata ZINA ne tushen bakin cikinta ko ba a fada min ba, idan na yi la’akari da irin kalamun da ke fita bakinta.
Anti Rose ta lura da irin razanar da na yi, ta girgiza kai domin kara tabbatar min da gaskiyar kalamanta, ba kuma tare da ta bukaci jin komi daga gareni ba ta ci gaba da cewa.
“Na yi mamaki na biyu kasancewar kin ce bakya karance-karancen banza ko kallace-kallace, don haka duk yadda akai wannan abun a cikin jininki ne, ina nufin a halittarki ne, wanda ba sai da Imran ba, da kowa ma da zuciyarki ta kyasa, in har zai amince miki za ki iya aikatawa Zaynab….”
Na rushe da kuka, na ce, “Don Allah Anti Rose ki daina gaya mun haka, ki daina yi mun mugun fata, Allah ya tsareni. Kalamanki kamar digar dalma suke a zuciyata, Allah ya hana, Innana da Ya Faruq sun dade suna min gargadi a kan hakan, Allah ya dauki raina kamin ranar da hakan za ta sameni…… Innana ta ce da in aikata zina gara mata mutuwana da rayuwata, nima mutuwar na fi so da in aikatata….”
Ta ce, “Ki yi shiru Zaynab in gama maganata sannan mu samo solution ga problem dinki, kuka da maganganun fatar bakinki ba shine ba, ba za su amfane ki da komai ba saboda ba ke ce kike sarrafa zuciyarki ba….”
Na tsagaita da kukan, amma ban bar hadiyar zuciya ba, kallon ta kawai nake da sauraron sabuwar bakar maganar da za ta yabo mani, domin cikin kalamunta kakaf babu na tausayawa, sai masu bakanta zuciya, wanda in na nutsu na yi amfani da hankalina zan fahimci gaskiya kawai take gaya mini.
“Zaynab idan kina son Imran, kina kaunar da ya zamo abokin rayuwar ki, zuciyar ki ba za ta fi ba da karfi ga son ku aikata abin da kike so din nan ba, illa kokari za ki kiga kin mallake shi gaba daya, wato ya zamo (life-partner) dinki na har abada ta halastacciyar hanya!
Amma ina tabbatar miki Imran ba zai taba yarda ya aure ki a haka ba, tunda ya san ciwon kansa. Ko ya aure ki hankalinsa ba zai kwanta da ke ba, zai dinga tunanin ranar da baya nan, ko ranar da ya baki wannan abin da kike son shi kenan za ki daina son sa ko komawa wani, tunda hakan kawai kika sawa zuciyarki.
Soyayya ta kwarai kuma ta gaskiya ba ta nufin physical relationship kadai, wato (gamayyar jiki). A’a, matual intimacy, understanding one another (kusanci da fahimtar juna) sune tubali na kwarai wajen gina soyayya. A duk inda soyayya ta rasa wadannan to jigonta sha’awa ne, kuma sunanta rusasshiya.
To ke Zaynab a sayayyarki babu wannan, kuma ina kara gaya miki Imran yana kaunarki! Amma ba zai nuna miki ba sai kin koyi kaunar shi, domin ke sha’awarshi kike yi ba son shi kike ba.
Kinga ke musulma ce, a addininku zina ba ta kamace ki ba, ko mu da muke addinin kirista a wurinmu zina haramun ce. Sai dai da sani muke takewa. Ki yi kokari ki fi karfin zuciyarki ki koya mata son Imran da kaunar sa, ki daina sha’awar sa kwata-kwata, ki dauki komi nashi a ba komi ba, a matsayin wani wanda bai isheki kallo ba, wani wanda ba shi da abin da zai burgeki da shi. Ki daina kawata komi nashi a ranki, ki dauke shi da da babu duk daya. Ki zama mai kame kanki da bakinki da idanunki a gaban sa.
Ba shi kadai ba, duk wasu maza ma domin da ba don kin yi katari da mai tsoron Allah ba da tuni farin cikin rayuwarki ya zama tarihi! Ki samu wani abu wanda zai dauke miki hankali daga tunanin Imran, ki daina zama ke kadai. Ki mai da hankali a kan karatun ki za ki sha mamakin Imran. Sai ya tsugunna da gwiwoyinsa yana rokonki ki aure shi Zaynab, ni na gaya miki.
To a sannan ne kika ci ribar soyayyar ki sai ayi muku aure. A sannan kina da ‘yancin baiwa gangar jikinki abin da take so, za kuma ki mallaki Imran din da kike mafarkin samu tare da komi nashi, daga kanshi har yatsun kafa cikin kwanciyar hankali, amma ba yanzu ba da ko sakandire baki gama ba”.
Hankalina ya kwanta da shawarwarin Anti Rose, a raina ina godewa Allah da ya matsi bakina na gaya mata matsalata, da tuni na san na kai kaina na baro, don tuni na fara tunanin in fara kula samarin da ke zarya a kaina, wanda na san dukkansu abin da yake kawo su kenan ba na Allah da Annabi bane.
A wani bangaren godiya nake kwararawa Ya Im, Imranan da bai biyewa son zuciyata ba, gaskiyarsa ne da ya ce kuruciya ke dawainiya dani. Na kara jin GIRMAN sa da kimarsa gami da mutuncinsa sun karu a idanuna. Sannan wani nutsattsen abu mai dadin da baya misaltuwa ya tsarga a zuciyata (so na hakika), wanda babu sha’awa ko son zuciya a cikinsa.
Na dago sannu a hankali ina murmushi na dubi Anti Rose na ce, “Ko na gama sakandire Anti Rose ba za a barni in yi aure ba, amma zan iya rike kaina. Babana da Abban Imran sun sha cewa sai na yi shekaru ashirin da biyu, wato a lokacin na san kaina, na san ko ni WACE CE”.
Anti Rose ta ce, “A kan me? Sam, idan kin kare makaranta Imran ma ya nuna a shirye yake da ya aure ki, ki fito gar da gar ki nuna amincewar ki. In ta kai ta kawo ko uwar dakinki ne ki samu ki rufe ido ki gaya mata matsalar ki, na san za ta fahimce ki ta kuma fahimtar dasu. Ciwon ‘ya mace na ‘ya mace ne, ba ke kadai ce hakan yake faruwa dake ba, sannan you are not the last! Akwai da yawa, halitta ce”. Na ce cikin tsananin girmamawa, “Anti Rose na gode”.
Ta ce, “Kada ki damu Zaynab, ai ke ‘yata ce. duk wasu yara da aka kawo mana nan amana ce aka kawo mana, yadda ba zan so ‘yar cikina Nkiru ta shiga halin da kika shiga ban ganar da ita illa da kuskuren dake ciki ba, haka ba zan kyale ki ba. Ki daure ki bi shawarwarina Zaynab, am sure you’ll laugh some day! Na tabbata miki za ki ga yakini a ciki. Duk wani ci gaba da aka samu, ki neme ni ki sanar dani in san a matakin da muke, da kuma (next-step) da ya dace mu dauka”.
Muka mike dukkanmu ni na nufi aji, ita kuma ta nufi hanyar (staff-room), ina tafiya kamar a kan kwai, ina godewa Allah a zuciyata da kuma Anti Rose. A wani bangare kuma jin kunyar kaina nake da kunyar Ya Im.
Wai kirista ma kenan ta san illar zina (abin da iyayenmu mata da yawa basa ba da hankali a kai su fadakar da ‘ya’yansu mata a wannan zamanin). Wallahi sai na ji ni sakayau, kamar an dauke mun wani nannauyan dutse a ka. Na alkawartawa raina jajircewa da jurewa bin shawarar Anti Rose, insha Allahu! Sai Ya Im ya yi mamakina, ya kuma yi nadamar jefa ni a halin da ya jefa ni ya tsallake ya barni, maimakon ya zauna ya ganar dani a matsayinshi na mai hankali fiye dani.
Tun daga ranar na soma azumin tadauwa’i wanda in na yi yau gobe ba zan yi ba (wannan Mazon Allah (S.A.W) ya yi ikirarin sa maganin gusar da sha’awa ne) kuma alhamdulillahi na ga nasibi a ciki, domin jina na yi kamar ba ni ba na koma ZAYNABU-ABU na kamar yadda nake a gaban Malam da Innana, ban san wani wai shi Imran ba.
Ga nafilifilin dare ina yi, haka nan bana rabo da karatun Alqur’ani dare da rana, ko ina zamu akwai dan karamin Alqur’ani na bugun Misra cikin jiki, ko cikin aji in ba abin da nake zan fiddo ina karantawa madadin hira ko zama shiru. Su Iftihal da Mama sun ji dadi kwarai da sauyin rayuwata ta kunci da kuntatawa kai, da suke tunanin saukin ciwon kan da nake fama da shi cikin dare na samu.
Muka zana jarrabawar mu cikin kwanciyar hankali muka samu hutun karshen shekara, inda in mun dawo zamu shiga aji shida. Murna wurinmu kamar me zamu zamo seniors wanda hakan shine babban burin Azizah a ce ta gama makaranta ta shiga jami’a. A kullum ta kan ce tana son zama Adda Mami ne budurwar Ya Im, sbaoda haduwar ta.
Azizah tun muna kanana muguwar ‘yar iyayi ce, komi nata sai designer, don haka duk ta fimu daukar ido. Ni da Ifty rayuwarmu ba yabo ba fallasa, domin bamu da karya kuma bamu da karanta, in ka dube mu za ka san ba abin da muka nema muka rasa.
An shirya tafiya Bindawa dubu dangin Abba, daga nan kuma za a dubo Malam Ali a kuma barni in yi hutun kirsimeti na a can. Su Azizah sun ce Porthearcourt za su gidan Antin su in sun dawo, don haka tun ana sauran sati daya muka soma shirye-shirye.
Ni dai farin ciki har guda biyu ya tarar mani, ga murnar ganin iyayena don rabona da Gwarzo watanni shida kenan cif, don a wancan hutun ban je ba mun tafi yawon bude ido na yankin Senigal gaba daya gidan. Murna ta biyui kuwa zan kara samun nutsuwa da hutun zuciya ta hanyar yin nisa da duk wani abu da zai tuna min Imran. Na san yanzu su Hafsisi ma duk sun zo hutun zamu TUNA BAYA…. su debe min kewar su da na kan samu kaina da yi a yawancin lokuta, domin dai kowa ya bar gida….. Hausawa suka ce wai gida….. ya barshi.
Abba ya raba mana kudi kamar ko yaushe zamu Gwarzo ko Bindawa don yin tsaraba, bayan nashi da baya fasawa. Duk da Inna Rabi ba ta taba yin amfani da tsarabar da nake kai mata ba, a kan idona take rabarwa kishiyoyinta ko almajiran Malam, hakan bai sa dai-dai da rana daya da zan je na fasa ba.
Wannan kuma nasihar Abba ne, ya kan ce, “Ba ta yi amfani da shi ne abin nema ba Zainabu, albarkar ta muke nema”. Don haka muka shiga kanti muka soma ragargazar sayayya. Na kan saya mata dirkeken vasiline ne (Bebe and Maman) da manya-manyan gwangwanin NIDO da MILO da sauran kayan shayi, sai sinkin sabulun wanka, omo, da na wani da turamen atamfofi biyar manya da kanana.
Mun dauko hanyar Katsina cikin babbar (peageout 506) din Abba mai cin mutane goma, hudu a layin farko, hudu a kujerar baya, biyu a gidan gaba. To Abba ne shi kadai a gaba, mu da su Hajiya Mama da sauran yara muna baya. Abba yana ta yiwa Shehu direba fadan ya ja mota danja ba ta ba shi hannu ba shi dai baya daddara da shiga kurkuku.
Azizah tana ta dariya domin ta tsani Shehu. Ta ce, “Anti Abu za ki iya tuna ranar da su Ya Im suka dauko mu daga makaranta ranar da aka saki wankin kashi? Ya Im yana ta balbalemu wai ashe Shehu ne ya ba shi haushi, ya taho daukarmu ya wuce danja ba ta sallame shi ba, ashe akwai ‘yan sanda a kusa suka cafkeshi shi da motar, aka aikowa Abba shi kuma ya tura Ya Im ya fiddo shi. To ashe haushin Shehu ne mu ma ya shafe mu, ya kusan cinye mu, amma kin ganshi bai daddara ba, da Abba ma a mota bai fasa ba”. Mama ta buge bakinta ta ce, “Sa’anki ne? Bana son rashin kunya”. Hajiya ta ce, “Ai ita in ba ta yi labarin an sa Zaynab wankin kashi ba bata jin dadi”.
Abba ya juyo kadan da waya a kunnensa cikin mamaki ya ce, “Wankin kashi? To ke me kika yi suka saki wankin kashin?” Na dukar da kai ina murmushi ina tuno fuskar GG a ranar da maganganunshi, ban san sanda na yi dariya ba.
Su Azizah dama kiris suke jira suka shiga taya