Showing 6001 words to 9000 words out of 24810 words

Chapter 3 - GIRMA YA FADI Book 2 Complete By SUMAYYA ABDULKADIR TAKORI.txt

watau mafi girmanku a wurin Ubangiji shine wanda ya fi jin tsoron sa, hakannan ban taBa daukar Ubanka a matsayin mai kudi ba, da shi da abinda ya mallaka da mukaminsa a gwamnati, ban san su ba, bana kuma son in san su, balle in ga girmansu.
Har yau almajiri na nake kallonsa, wanda ya duka nan a gabana ina koya masa (Alhamdu), har kuma na saukar da shi Alqur'ani mai girma da sauran littafan addini. Don haka inda a ce Zaynabu 'YA TA CE, ba yadda za’a yi in hana maka aurenta, koda kuwa kai din dan shugaban kasa ne ba dan Sa'idu ba. To amma Imran ita Zaynab 'YAR SA CE, da ya haifa da jikinsa. Ina la'akari ne da ayar nan ta Ubangiji (S.W.A) dake cewa "hurrimat alaikum ummuhatikum wa banatikum wa khalatikum wa akhwatikum wa ummahati nisa'akum……. har zuwa karshen ayar.
To ita ZAYNAB-ABU, 'yar sa ce, ina nufin kanwarka ce, ta jinni, tunda itama Sa'idu ne ya haifeta, kenan ta zama (muharramarka). Don haka maganar aure ta kau. Sai zumunci, wanda shi dama dole ne kuma ana yin sa.
Yanayin rayuwa gami da take da fadar Allah da akai, shine yayi sanadiyyar hakan, ya kuma rubuto cewa Zaynabu bazata tashi a gaban iyayenta biyu ba, amma ta zauna na lokaci mai tsawo tareda mahaifinta wanda ita kanta bata san hakan ba.
Imran, a matsayinka na DA NAMIJI mai cikakken hankali, ina fatan zaka fahimce ni, ka yarda da kaddarar da Allah ya daura maku, kada ka butulcewa mahaifinka domin ya yi tsarkakken tuba, tubanda Ubangiji (S.W.T) ya yi alkawarin karBar shi, wato tuban da akayi shi da tabbacin ba za’a sake komawa izuwa zunubin ba. (Kamar yadda Malam mai akhdhari (ahalari) ya fada).
Wannan kuma tsakaninsa da Ubangijinsa ne, idan har ya yafe masa, mu nan bamu da abinyi banda daukar darasi daga gareshi, kada kace hakan zai sa ka daina girmamashi ko ka daina ganin GIRMANSA Allah ba zai barka ba, tunda ba kai yayiwa laifi ba, wannan tsakanin bawa da Ubangijinsa ne. Ka yi aiki da hankalinka na da namiji, wanda yafi na 'ya'ya mata. Ka ji tausayin mahaifinka, ka janye niyyarka na auren Zaynab ina kake so ya sanya kansa? Idan ka dage cewa sai ka aureta, abin dake Boye shekaru goma sha takwas a tsakaninmu dinnan dake zaune a dakinnan, sai Rabi da dan uwanka, zai fito duniya ta sani, wanda hakan zai zubar da GIRMAN mahaifinka, ya sanya rayuwar Zaynab cikin kuncin da bazata taba rabuwa da shi har abada ba, ya lalata mata rayuwa, ya sanya ta tsani kowa harda kanta kuwa. Kayi juriya ka karfafa imanin ka, ka yarda hakan Allah ya ga dama daku gabadaya".
Sai ya soma janye jikinsa sannu a hankali daga kusa da Abban, tamkar yaga wani abin tsoro da kyama. Rokon Allah yake cikin zuciyarsa, idan mafarki yake ya farkar da shi.
Ya koma kallon su a tsorace, kafin ya mike tsaye idanunsa a rufe, yaki budesu ya kalle su, don gani yake idan ya bude ya kalle su, to GIRMANsu da kimar su da ke cikin idanunsa ZAI FAdi. Ya soma magana yana ja da baya a hankali.
“Baba Malam ina ganin GIRMANKA, ina darjanta furfurarka da farin gemunka, ina ganin kimarka da mutuncinka, kada kayi sanadin da zasu FADI a idanuna.
Idan ba zaku bani auren Zaynab bane, na hakura, ba sai kun SHEGANTATA ba, ba sai kun lalata mata suna ba. Zan juri rashin aurenta amma ba zan juri ganin tagayyararta, a rayuwa ba.
Ba zan bari wani cikin ku yayi mata wannan tozarcin ba, koda zan rasa raina ne Zaynab bazata rasa ‘identity’ dinta na Zaynab Aliyu Gwarzo ba. Zanyi shari'a da ku har kotun koli akan hakan, koda duk abinda na mallaka zai kare sai na karewa Abu martaba, da mutuncinta.
……. Me wannan baiwar Allah tayi muku da zafi, data cancanci irin wannan tozarci? Abba daure kace nine shegen, ba Zaynab ba. Wa zai aure ta? Wa zai ije mata bukatun gangar jikinta na shekara da shekaru ta hanyar aure, alhalin kun ce ita shegiya ce? In gaya maku gaskiya idan ma ba’a aure tsakanin Wa da kanwa, to daga kan mu za’a fara. Tunda kace ‘yar ka ce, to ina sonta, ina neman aurenta a hannunka V.C Sa'idu, don ni yanzu ka tashi daga nawa Baban na hakura na barwa Zaynab, ni na zama shegen na ji na yarda, na amince, ko zaku baiwa SHGE auren diyarku?"
Ya bude idanuwan da ya rufe gabadaya, yana sauraro amsar su, bil haqqi, shi da zuciya daya yake Magana. Kallo daya zakai masa ka tabbatar ba’a hayyacinsa yake duk maganganun da yake yi ba, suna dai fita ne kawai daga fatar bakinsa.
Ganin duk sunyi shiru sun dukar da kan su kasa, basu da niyyar amsa masa, ya sake jefosu da wata tambayar da ta addabi kwakwalwarsa;
"Tukunnama in tambayeka Abba, ko kuwa Malaminka zan tambaya? Ta yaya akai ka zamo Uban nata?
Kai ka fara auren Inna Rabin, ka saki, Malam din naka ya aura, koko yana aurenta, don ya baka daki a soron gidansa, kana kwana, ka nemeta har kuka yi cikin da kuka haifi Zaynab, saboda ka ganta ‘yar fara kyakkyawa……..?” Inna Dubu ta dauki warin takalmin shi dake dai-dai inda take zaune, ta saita bakinsa ta maka masa iya karfinta, jini ta hanci ta baki, ya soma bilbila, amma bai fasa magana ba
"Kaima kenan da zamaninku baku san menene so ba, ka kasa kauda idonka akan Innar sai ni da na zo a wannan karnin, nasan menene abinda zuciyata ke so? Na san su waye mata irin Zaynab diyar Inna Rabi, shine kuke yi min bakin cikin, kar in dandani irin abinda ka dandana a jikin Innar, shine za’a ce wai Allah yace kar na aure ta, Allah bai ce kar ayi zina ba, sai ni mai neman aure ta tsaftatacciyar hanya.
To ai Allah shi ya ce ayi aure, ba ayi zina ba, don haka zan auri Zaynab no matter what don ina sonta…, ba ruwana da wata rayuwarka ta can baya….., ba ruwana da wani 'yar ka ce tunda babu wanda ya shaidi aurenka da mahaifiyarta……” cikin kuka Inna Rakiya ta ce
"Kai dannan, mahaifinnaka kake gayawa haka?"
Ya maida kallonsa a kanta, idanunsa kuru-kuru kamar ya cinyeta "Inna shi bai yi tunanin watarana, zai janyo mana irin wannan mutuwar zuciyar ba, a sanda yake shan shagalinsa da Innar Abu? Bakya tunanin mu yanzu gabadayan zuri'armu ya lalata mana suna? A bar ta baiwar Allah Zaynab, da bata ji ba, bata gani ba, idan ta samu wannan almara ina zata tsoma zuciyar ta?
Soyayya mai sauki ce, kuma ba dole bace, amma zuciyarta zata mutu. Duk wani buri da take da shi a rayuwarta zai zama TARIHI! kaunar da nake yiwa Zaynab, tafi gaban ta soyayya kadai, kaunarta nake kamar yadda nake kaunarsu Iftihal, ban taBa kawowa raina sha'awarta ba. Kawai inada burin ta zamo uwar 'ya'yana ne, saboda hakuri, tarbiyyah da juriyarta. Mace ce mai matukar juriya da fin karfin zuciya. Amma duk juriyar ta wannan al'amarin ba zata jure shi ba………”.
Sai anan ne ya samu hawaye suka fito, amma tun sanda ya fara maganar idanunsa a bushe suke. Idan ka kalli Maigirma V.C Professor Sa'idu Salisu Bindawa, a wannan lokacin sai ya matukar baka tausayi. Lokaci guda shekarunsa guda hamsin da biyar, sun fito baro-baro akan kyakkyawar fuskarsa, wadanda ada jin dadi ke boye su, suna sake mayar da shi matashi dan shekaru arba'in a duniya.
Babu shakka yayi nadama irin wadda bai taBa yinta ba a rayuwarsa. Ya dade yana tunanin zuwan wannan rana, wadda ko ba-dade-ko-ba-jima ya tabbatar babu makawa sai ta zo, amma bai taBa zaton zata zo mai irin haka ba, bai taBa tsammanin soyayya tsakanin dan lalenshi da 'yar lelenshi ce zata zamo sanadiyyar zuwanta ba. Allah ka yafe mana!

A hankali Imran yabi bango ya durkushe akan kafafunsa, ya dunkule hannuwansa a kirjinsa hawaye masu zafi suka soma bi ta kasan idanunsa yana rokon Allah ya dauki ranshi kamin wannan abu da yake ji yazam tabbatacce, yasa mummunan mafarki ne yake yi ya farka.
Baya tausayin kansa sai Zaynab, bai san sanda ya ce da karfi "Allah ya isa tsakanin mu daku… Abba!"
Malam Ali ya mike ya dauki allon da yake yin rubutu kamin shigowar Abban ya kantara masa a tsakiyar ka, amma ba kakkarfan duka da zai mai lahani ba cikin kwakwalwaba, da karfi ya ce
"Ina jiye maka fushin Mahaliccinka Imran! Na dauke ka yaro mai hankali, tunani, da rangwame cikin al'amarinka, shine zaka nuna min halin yahudawa na rashin girmama iyayen su? Wallahi idan kayi wasa sai Sa'idu ya rigaka shiga Aljanna, fushinsa ya kaika Sa'ira. Domin dai shi lafiya ya rabu da iyayensa suna masu sanya mai Albarka. Ni dake tare da shi shekaru arba'in da doriya, bai taBa batamin ba, kullum albarka nake sa masa na kuma tabbata albarkarce ke bibiyarsa har yau. Kai din nan baka isa ka shiga tsakanin bawa da mahaliccinsa ba. Idan Ubangijinsa ya yafe masa, kai keda kaicon fushin iyaye a rayuwa……” Abban ne ya yi tari yayi gyaran murya, muryar sa bata fita sosai, in banda tsit din da dakin yayi, da maiyuwa ba za'a ji abinda yake cewa ba.
"Kyaleshi ya zageni son ransa Malam, ina girman yake? Ai ya riga ….YA FAdI! Saidai ka gaya masa ba rarrashin sa muke ba gaskiya ce kawai muke gaya mishi domin hakkin hakan da Allah ya dora mana, amma ba tsoronshi nake ji ba, illa son tserar da shi damu kanmu daga fushin Ubangiji mai tsanani da zai same mu in muka bari ya auri shakikiyarsa.
Na fada na kara Zaynabu 'YA TA CE, ke nan KANWARKA ce, don haka BA ZAKA AURE TA BA! Ba kotun koli ba, ai an gaya maka in banda mu da muke zaune a dakinnan da Faruq da Innar Zaynabu, babu wanda yasan al'amarin nan. Don haka dauko filo ka turmushe kowannenmu, har sai ya daina numfashi, ita ma Innar ka je kayi mata hakan sai ka dauki Zaynab ka tafi da ita in da ake sonta, inda ba za'a tazortata ba, tunda mu ka ce BAMA SONTA! Sharri ne zamu yi mata don mu hanaku aure. Sai ku tafi can inda ake sonku, inda ba’a sanku ba ayi muku auren don kuwa mu nan musulmi ne 'ya'yan musulmi rainon musulunci, babu mai aura maka Zaynab a matsayinta na kanwarka ko a lahira bamu da hakkinka tunda mun gaya maka abinda baka sani ba.
[7/11, 3:58 PM] +234 706 160 2791: Abban kuwa da suka kai wa karar korarsu ya yi, ya ce Imran ya kyauta mishi, ya yi mishi dai-dai har mota zai sake masa don gode mishi a kan hakan, yanzu haka samarin banza muka fara kulawa. Suka shiga yi mai rantsuwar Allah ba abin da muke yi. Ya jawo wayar cajinshi ya soma tsula musu suka kwasa da gudu wurin Mama suna neman mafaka. Ni kadai na san dalilin Ya Em na yin hakan, sai ko Allah da ya halicce shi.
Idan na zauna ina tunanin al’amarin sai in gicciye in yi ta kuka, in ji na tsani kaina amma shi Imran din nayi-nayi in tane shi na kasa, sai kaina da a kullum nake kara tsana. Duk kuma wannan barazanar tashi ta daure fuska, sababi gami da zare ido basa kara min komi sai abin nan dake kara kamari game da shi a tare dani.
Idan abin ya ciwo ni sai in sanya takalmi in dauki hanyar dakin su. Faram-faram sai na kusa kaiwa sai in yi tunanin Ya Faruq suna tare ko yaushe, kuma dai kwata-kwata babu wata ‘ya mace a gidan da na taba gani ta shiga baskwata.
Shi kuma kamar ya sani ko kuwa mai karantar abin da ke cikin zuciya, sai ya rage shigowa gidan in ba lokacin cin abinci ba, shima din fuska a daure. Yana ci yana hade girar sama da ta kasa, yana harare-harare da sexy-eyes dinsa masu kara dimauta ni, inda mu kuma duk zamu bi mu kasa sukuni ko kwakkwaran motsi har sai ya tashi ya bar wajen, in da zai barbade ni da kamshin daddadan turaren sa ‘eternity moment.’ Idan ya bar wurin, ji nake kamar zuciyata zata fashe, domin ganin shi ma kadai, sauki ne ga ciwo na.
Muna zaune a falo da daddare ana hira da Mama, ya shigo yana goge gilashinsa da hankici, ya dubi Mama ya yi murmushi ya ce, “Maman ‘yammata mu fa gobe zamu daga kodago, zamu fara shiga ofis in Allah ya yarda”. Ta ce, “To Imran Allah ya ba da sa’a ya kade sharrin makiya da na abin hawa, yasa a fara a sa’a, ya fidda haram daga cikin halal…”
Ya ce (cikin jin dadin addu’ar ta) “Amin-amin Mama, na gode da addu’ar ki”. Ya cira kai ya dube mu a gicciye. Ni dai zuciyata kadai ke fat-fat kamar in daura hannu aka in saka ihu, jin cewa Imran zai tafi Abuja bakin akinsa da babu ranar zuwa, aikin da an fi watanni uku da samuwarshi suna ta yi mai jeka-ka-dawo, sai yanzu Allah yaiwa takardun daukar fitowa kamar yanda Iftihal ta gaya mani.
Ban yi aune ba sai ga hawaye sun shararo mani, na yi saurin sar da kai, na yi azamar dauke su da yatsuna biyu ban kuma yarda na dago ba balle wani ya ga halin da na shiga. Yana murmushi kamar ba shi ba ya ce, “To ‘yammatan gaya, ‘yan gatan Mama, shalalen Abba me zan samu ne?”
Gaba dayanmu mun yi mamakin yadda yau ya kula mu har yana janmu da wasa, to ko don ya ga tafiya zai yi ne? Sai muka ji banbarakwai aka rasa mai amsawa. Mama ta ce, “Ba abin da za ka samu daga wadannan ‘yammatan nawa, tunda ka hana masu zukar iska da rawar gaban hantsi, ni na san yau ransu kal kamar takarda”. Ya yi dariya ya ce, “Wai haka Zaynab?” Ko dagowa ban yi ba, sai ya mai da akalar tambayar shi kan Azizah kada Mama ta gane akwai wata ‘yar tsama a tsakaninmu. Cikin lallashi yake cewa,
“Yanzu don Allah don Yaya na son ‘yan kannen shi su zama zarra a karatu sai su ji haushin shi? Su ce ya takura masu? A zatona wanda kake kauna shi kake so da ALHERI (sunan littafin Takori mai zuwa), amma ba za ku san gata nake muku ba, sai a nan gaba idan kun fito da A3, B3, C3 a NECO da WAEC”.
Duk suka yi murmushi, nan ma ban dani. Karewa ma sai na mike kamar mai son shiga toilet, ya bini da kallo kamar zai ce wani abu, ya ga babu alamun wargi don haka ya sa kai ya fita yana cewa “Mu kwana lafiya Mama”.
Mun yi shirin kwanciya Iftihal ke cewa, “Tabdijam! Kwanan nan mugun mutumin nan zai soma kama millions, wulakanci kuma zai karu”. Azizah ta ce, “Gaskiya kam, aiki a AGIS din Abuja (Abuja Geographical Information System) ai sai mai sa’a, ni dama Faruq ne ya samu ba shi ba, ‘yammatansa ma na san yanzu duk watsar dasu zai yi a samo (new catch) na Abuja”.
Iftihal ta ce, “Duk abin shi ai bai isa ya watsar da Adda Mami ba….” Na yi lamo cikin bargona ina sauraron hirarsu mai ban haushi tana kona zuciyata, wani makoko ya zo ya tokare ni a kahon zuci. Na shiga zubar da hawayen da ban san dalilinsu ba, na tafiyar Imran ne? Na jin zancen ita wannan Mami ne? Ko-ko na wulakancin shi ne wallahi ban sani ba. A ranar na rantse yadda na ga rana haka na ga dare, saboda KISHIN ita wannan Mami da suka ambata dake kokarin hanani numfashi.
Tun bayan tafiyar Ya Im duk sai na zamo wata sukuku babu kuzari, ramata ta soma fitowa fili, haka su Azizah suka fara damuwa da rashin walwalata, da rashin cin abinci na. Bayan suna ganin yanzu ne ya dace in saki jiki, mu ci duniyarmu da tsinke tunda dodon namu baya nan.
Basu sani ba, sau dubu gara sanda yake nan din, ko ban ganshi ba zan iya leken shi ta window, zan jiyo muryarshi in yana dariya da mutane, zai mana fada, zai hantare mu in ji muryar sa wanda duk wannan sauki ne a gare ni. Amma yanzu ko turaren shi babu a gidan, ya bishi can inda yake, sai ni da aka bari da radadin zuci.
‘Performance’ dina a school kullum yana karki babu bana iya barci sai murkususu a kan gado, sai na shiga karewa a tsaye kamar kudin guzuri, kasusuwa suka yi min sarka a wuya, idanuna suka burma loko kai ka ce farfadowa na yi daga doguwar jinya.
Hajiya Azumi ramata ta fara damun ta, rashin walwalata ya soma addabar ta, ta yi tambayar duniyar nan na ce mata babu komi sai ciwon kai da nake fama da shi da daddare, ta rubuta magani ta ba Shehu ya sayo min kullum ina ta sha, amma sauki sai wajen Allah. Rannan ta ce, ko dai tunanin Rabi da Malam ne? Na bita da eh. Ta ce, in kwantar da hankalina, ba sati biyu ya rage mu samu hutu ba sai in tafi.
Shima Faruq bayan sati biyu da tafiyar Imran gurbin da ya nema na karatun kwamfuta a (Informatics-Singapore) ya fito ya fara shirye-shiryen tafiya. Hankalina ya kara tashi, domin Faruq ne kadai nake iya gayamawa damuwana, amma shima wannan ba zan iya fada mishi ba, ban san yadda shima zai dauke ni ba, tunda wanda Allah ya doran lalurar a kansa, a lalatacciya kawai ya dauke ni.
Ya fadi ya kara fadi, duk da bai fito fili ya ware ni ba na san dani yake. Wani lokacin in na zauna ina tunanin maganganun shi na baya, kamin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login