Showing 3001 words to 6000 words out of 24810 words

Chapter 2 - GIRMA YA FADI Book 2 Complete By SUMAYYA ABDULKADIR TAKORI.txt

ji zuciyata ne neman faso allon kirjina, saboda wani mugun kishin matar nan da Allah ya dora mini, wani makoko ya zo ya tokare ni, da gudu-gudu na karasa cikin gida na shige dakin mu na fada toilet na yi ta kuka har Allah ya gajisshe ni. Ina jin wayar da ke cikin filona na ta burari har ta tsinke don kanta.
Bani na fito ba sai da alwalar sallar magariba, na dasa sallah babu sassautawa, domin tursasawa zuciyata fidda Imran a cikin ta. Na tabbata na fada a matsananciyar soyayyar Imran da harshen da ba zan iya bayyanawa ba. Kishinsa nake kamar in sa bindiga in harbe Mami, duk da ya fadi ba sonta yake ba. Sai dai ni kaina na san ba karamin yaudarar kaina nake ba, haka shi din, ba karamin raina mun hankali ya yi ba, da yake gaya mun wasu maganganu na yaudara, masu nuna min mai mata kamar su Mami Abdulhadi zai taba dubar karamar alhaki kamana dake tutiya da bazar Uban su da sunan so a duniya.
Waya kam ya yi ta har ya gaji, kamin ya turo sako misalin karfe goma na dare.


“Ki dauki waya ki ji abin da zan ce miki, rashin daukar wayar ki ba shi zai sa ba….”


Sannan ya sake kira, wannan karon bayan kashe wayar da na yi, har bude ta na yi na zare (sim) din na sanya a dirowa.
Muna kalaci da safe duk mun yi shirin tafiya, zuwan Shehu kawai muke jira. Ya turo kofar dakinmu ya shigo ko kayan barcin (pyjamas) dake jikinshi bai cire ba, babu alamun wasa ko kankani a tare da shi, idanun shi sun dan tasa alamun rashin wadataccen barci a daren baki dayansa.
Suka duka suka fara gayas da shi, ya amsa ba tare da ya dube su ba idanunshi a kaina, ya ce, “Ya yi kyau, kuma abin da ki kai kin cancanci a a baki lambar yabo. Sai dai kar ki manta kina wahalar da kanki ne kawai a banza Zaynab wannan ba za ta fisshe ki ba. Gara ma ki fito fili ki nuna musu abin da kike boyewa, amma ni babu gudu babu ja da baya Zaynab, I said it infront of all those you are kidding (na fada a gaban wadanda kike rainawa hankali cewa) I LUV U very-very much!”
[7/11, 3:58 PM] +234 706 160 2791: Naki tashi, na kara matsawa jikin Malam sosai nace “Inna ya zaki ce in ta shi? Baki fara tambayar dalilin suman Malam ba, baki nemi dalilin tashin ciwon Baba Sa'idu ba?" Ta karfi tasa hannu ta finciko ni, ina tirjewa tana kara jana da karfin da na kasa amincewa na Inna na ne, ta jefe ni a daki tasa kuba ta datse mu. Imran ya bita da kallo, a ransa yana cewa ashe dai da gaske ne, da Iftihal ke cewa Innar Zaynab, mahaukaciya ce?
Malam Ali yayi ajiyar zuciya, ya karanto karshen ayoyin suratul Hashri, yayi salati ga Annabi, ya yi istigfari, yayi hamdala ga Allah yayi tasbihi ya tsarkake shi, yace "hakika Ubangiji ba karamin hakuri yake da mu ba. Idan da zamanin sauran Annabawa ne, da tuni an kifar da mu. Idan da Ubangiji bai yiwa Annabinmu alkawarin ko me zamuyi, bazai kifar da mu ba, har zuwa tashin kiyama, da mai yiwa hukuncin mu sai ya fi na al'ummar Annabi Nuhu, yafi na al'ummar Annabi Ludu, yafi na Yunus yafi na Yusufa, ya kuma fi na al'ummar Fir'auna.
Amma yana hakuri da mu, har zuwa sanda zai kamamu a hannu, ya tambaye mu yadda muka gudanar da rayuwar mu, abisa tsarin da yai mana ne ko a’ah?
Ba karamin cuta Yahudu da Nasara sukai mana ba, ba kuma don komai sukai hakan ba sai don sani da suka yi cewa su dama taBaBBune, wuta ta tabbata a gare su. Don haka suka jamu a jikinsu suka dulmiyar damu da akidunsu da sunan cigaban, ilimi, wayewa, da 'yancin kai (independence).
Su ZINA ce ta haifesu, a cikinta suka tashi, kuma a cikinta suke rayuwa. Don haka suke bakinciki da mu da muke da tsarkakakken asali, suka nuna mana ita din ba komai ba ce (Zinar), alhalin bakin-cikin da take haifarwa, ya fi jin dadin dake cikinta yawa. Banda tsayawa gaban Sarki Allah, ranar gobe kiyama”.
Ya yi shiru yana share hawaye, Imran jikinsa yai sanyi, don ya fara shan jinin jikinsa, cewa Malam da Baba Sa'idu sun dauka ‘zina’ suke aikatawa shida Zaynab, shine dalilin shigarsa cikin halin da suka same su.
Ya ci gaba da cewa “tsakaninmu da nasara sai Allah ya isa, don cuta kam ya gama yi mana, ya lalata tarbiyyar da iyaye, kakanninmu, sarakunan mu na gargajiya da malamanmu na addini suka wanzar da rayuwarsu a dora mu akai, kadan ne, kuma masu rabo, zasu gane hakan. Da in haifi 'ya'yan da zasu rinka aikata zina, gara da ban haifa ba, gara da nake haifarsu suna mutuwa wallahi….".
Gabadaya falon sukace "Wa’iyazu billahi Malam, dukka 'ya'yan Musulmi 'ya'yan kowa ne, kada bacin rai ya kaika ga son kai, sai dai ace Allah ya shirya 'ya'yan musulmi bakidaya, ya ganar da su illar aikata zina, ya kuma basu iko da karfin imanin nisantar ta". Ya share hawayen da suka kara yanko masa, ya dubi Baba Sa'idu, wanda har yanzu numfashinsa bai koma da-dai ba, amma duk abinda Malam din ke cewa yana shiga kunnuwansa, yana gasgata kowacce kalma dake fita bakinsa.
Kana ya maida dubansa ga IMRAN, ya dade yana kallon shi, da idanunsa da suka kada suka yi jajur kamar gauta, yace "Imrana!” Cikin kakkausar murya.
Bai amsa ba, illa ya dago lumsassun idanunsa ya dubeshi, yana sauraron abinda zai ce da shi, tuni zuciyarsa ta gama sanin me Malam din zai ce? Kasancewarsa mai karantar mutum tamkar yadda yake karanta inji, ya kuma gane inda yasa gaba tun kamin bakinsa ya furta. Ya manta cewa ko zaka iya karantar mutum, bazaka iya karantar abinda ke karkashin zuciyarsa ba, domin ita zuciya wata abin sirri ce da Allah (S.W.T) ya bamu, domin Boye abubuwan da baki, ido da kwakwlwa ba zasu iya karantarsa ba.
Eh, tabbas ya sunsani abinda Malam din zai ce, amma bai zaci zai yi GIRMA da bunkasar haka ba, bai zaci zai yi muhimmancin wannan ba, bai zaci kwakwalwarsa, tunaninshi, zuciyarsa da gangar jikinsa zasu kasa daukar nauyin abinda ke fita daga karshe daga bakin Malam din ba.
Ya fi sakan uku bayan kiran sunan nasa da yayi, kafin ya ce masa komai, haka shima ko ta-tafas bai ce masa ba, balle ya nuna zakuwarsa ga son jin abinda Malam din zai ce da shi, wanda yake da yakinin ba mai dadin ji ba ne, ba kuma na tausasawa ba ne kamar yadda ya saba yi masa.
"Meke tsakaninka da Zaynabu, ina nufin, me muka gani kuna aikatawa dazunnan kai da ita? Dubi mahaifinka, ko kana da masaniyar irin abinda kuke yi kai da Zaynabu, shine sanadiyyar shigarsa cikin wannan wahalar, tun shekaru goma sha takwas da suka wuce? Ya taBa gaya maka "ciwon zuciya” yake ba ciwon hawan jini ba? Ya taBa gayama da koda daya yake rayuwa?"
Baiyi magana ba, amma fuskarsa ta nuna tsantsar tashin hankali da firgicin da kalaman Malam din suka jefe shi a ciki, yayi hamzarin duban Baban daya runtse idon sa a hankali, cike da nadamar wannan rana, cike da tunanin kodai kada ya bari Malam Ali ya fasa kwan ne? Shin idan Imran ya ji meke akwai tsakaninsa da Zaynab, da matsayin ta gareshi, zai ci gaba da yi masa wannan rungumar mai cike da kauna jin kai na iyaye da yayi masa? Babu shakka GIRMA ZAI FADI!, To amma kafin ya hana Malam Ali furtawar kamar yadda ya umarceshi, akwai bukatar sanin hakikanin meke tsakanin Imran din da Zaynab? Zargi kawai suke basu tabbatar ba, kuma abin da ya gani bai yi kama da babban abin ba, yafi kama da matsananciyar soyayya (romance), sai wata aba wai ita maganar aure, in haka ne fadin gaskiya ya zama tilas, in ba haka ba, wace hujja garesu ta hanasu yin auren?
Lallai wanda ya rigaka kwana, dole ya riga ka tashi, kuma wanda yaki daukar shawarar na gaba da shi, yana tare da aikin dana sani. Da yabi maganar Rabi tun farko, na barin Zaynab a Gwarzo ta yi karatunta cikin mutunci tare da su Hafsisi, da duk haka bata faru ba. Da ina zata ga Imran din har su kulla soyayya? Da yayi mata aurenta a kauye, cikin rufin asiri ba tare da faduwar girma ba, tunda har yau in ka dauke Inna Dubu, Faruq da Inna Rakiya, babu wanda yasan Zaynabu-Abu wacece a gareshi? Gaskiyar Rabi ne zaman Abu tare da ita, shi ne babbar martaba da mutuncin yarinyar. Kuma kan-kan din da take da ita, tayi da-dai, bashi Sa'idu bane bata so ya raBeta, tattalin mutuncinta take. Baya tausayin kansa da Imran, kamar yadda yake tausayin, Zaynab, Allah Sarki!
Shin ya zata ji a zuciyarta, idan ta ji cewa ba Inna Rabi ce mahaifiyarta ba? Ya zata ji a zuciyarta, Idan aka ce shine mahaifinta na hakika? Ya zata ji a zuciyarta, idan ya bayyana gareta cewa ya sanar da itane ta dattin zina? Duk kaunar nan da take masa, tabbas kiyayya zata koma mai tsanani, ninkin-ba-ninkin wadda Inna Rani ke masa.
Wasu siraren hawaye suka fito daga idanuwansa zuwa cikin kunnuwan sa, musamman da yake a kife yake kwance flat, bisa cinyoyin Imran, yayin da Imran din ke shafa kirjinsa a hankali saboda bugun da zuciyar Abban ke yi, ji yake tamkar ya fiddo zuciyar Abban ya maida jikinsa, shi yayi fama da mai ciwon. Abba Baba Sa'idu, Uba ne na kwarai, abin alfaharin 'ya'ya da daliban UDUS bakidaya, dama al'ummar Nijeriya gabadaya. Kamuwar irinsu da ciwon zuciya ba karamin lahani bane ga rayuwarsu, ba karamin nakasu bane ga gudummawar da suke baiwa al'umma, musamman ta fuskar cigaban ilimi.
A daular Usmaniyya gabadaya, a wani nazari da aka yi cikin shekaru ashirin da suka gabata, Jami'ar Sokoto na daga cikin koma bayan jami'o’in Nijeriya, amma tun daga zuwan jagorancinta hannun Sa'idu, cikin shekaru kalilan, za’a iya sanyata cikin sahu na hudu na jami'o’in Arewa dake kan gaba wajen bada shaidar karatu mai inganci da cusa kyawawan dabi'u ga dalibanta duk da cewa dama (Islamic University) ce.
Saboda nisa da yayi a tunani, bai ji tambayar da Malam din yayi masa ba, ya sake kiran sunansa a karo na biyu tare da maimaita masa tambayar da yayi masa, yayi firgigit ya dube shi cikin nutsuwa yace "Ka kwantar da hankalinka Malam, wallahi-wallahi kaji rantsuwa na dan musulmi kenan, babu wani abu makamancin wanda kuke tunani da ya faru tsakanina da Zaynab, ni musulmi ne kuma nima ina tsoron Allah, ina kuma tuna ranar gamuwata da shi, ko bayan wannan Zaynab tafi karfin haka a gareni, tafi karfin in nemeta da haramun, sai dai in nemeta da AURE.
In maisheta uwargida na uwar 'ya'yana saboda addini da tarbiyar ta, da kowanne namiji zai kwadaitu da zamantowar ta matar aure agareshi. Abinda kuka gani ba shi kenan ba, illa kun kawo wa ranku hakan kawai, saboda hakan da kuka riga kuka sa a ranku. Rungumarta kawai nayi ina rarrashinta ta amince in gabatar da zancen neman aurenta gareka, tana ki, don a cewarta matsayin mu ba daya ba, wanda ni ban taBa kawowa raina hakan ba. Amma a yanzu mun sulhunta a junanmu, albarkarku da amincewaku kawai muke nema, domin muna matukar kaunar junanmu".
Ya dukar da kai yana wasa da kan wayar sa, saboda wata kunyar Malam din da tazo ta lulluBeshi irin wadda bai taBa ji ba. Baba Sa'idu cikinsa ne ya murda, sai far-far kawai tabbacin gudawa na haduwa, ya mike ya zauna sosai ya soma tari kuful-kuful, Imran yai hanzarin mika masa ruwan da ya bashi magani a kwano yana ta faman "sannu Abba”, Malam Ali zamewa yayi ya dau buta ya zaga bayan gida, fiye da minti goma sha biyar kamin ya fito yana takawa da kyar, domin ba duka ya samu yayi ba wata ta makale taki fitowa saboda tashin hankali. Yana shigowa shima Baban ya tashi yana dafa bango, ya dauki butar da Malam din ya aje shima ya zaga. Shiru-shiru bai fito ba, ba kuma wanda yayi magana a falon, daga baya Malam ya sake tashi ya koma bakin kofar ‘toilet’ din yana jiran fitowar Sa'idun, domin zuwa lokacin wadda ta makale masa ta dai-daita, itama ta yi shirin fitowa har ta soma mintsininsa ta fara zuba kadan-kadan, don haka Sa'idun na fitowa ya afka ya dinga shararata.
Imran dai zaune yake tamkar an kafe shi, yana kallon su cikin nutsuwa daya bayan daya, a ransa yana cewa "ku gama gudawar, fargaba da tsoron na lalata muku 'ya, kuzo ku aura min ita in lalatata sosai da hujja, sai kace a kanku aka fara haihuwar 'ya mace, in bata ta din zanyi, me ya hana tun a can gidan mu inyi hakan, inda babu mai sa mana ido, sai anan? Kuma a dakin soro kusa da dakinka, wannan na shiga wannan na fita kuma kofa a bude? Don ni bani da wayo ko don kun maisheni mai karancin tunani? Yarinyar nan shekaru shidda muna tare da ita, duka a shekarun banyi hakan ba sai yau a gidan Ubanta? A gaban Uwarta a dakin Yayanta Haba! Ai keta haddin sai yai yawa. Inda sun san ita tuntuni ta shiryawa lalatar, har ta nemi ta lalatashi, kafin ta yi hankali tafi karfin zuciyarta, ashe da ranar dukkansu sai Darussalamu “kun san ba kwa son mu aikata zinar, maiyasa tun muna kanana ba kuyi mana aure ba, kamar yadda (S.A.W) ya umarce ku? Ni yanzu talatin nake neman rufawa, nayi karatu na dade ina aiki, cikinku wa ya taBa tarata ya ce Imran ya dace ka yi aure? Ita kuwa Zaynab shekarunta goma sha takwas, amma kuna cewa ba zatayi aure ba sai ta yi shekaru ashirin da biyu, ta san WACE CE ITA? Shin wane sani ne ga diya mace da ya wuce na tayi al'adarta ta farko a gidan mijinta?
Allah ya halicceta da son kusantar da namiji, addini ya ce kuyi mata aure, tun bata kawo hakan ba (Shekara tara), amma baku yi ba, wai ku tayi ta karatu meye amfanin karatun diya mace, musamman na boko? In ma yana da amfani to yafi kyautatuwa tayi shi a dakin mijinta, amma ba’a gaban iyayenta ba. Sannan yanzu ku zo ku ishe mu Allah yace Annabi ya ce, bayan ku kun baro fadarsu tun ran gini, sai ranar zane zaku fada mana???? (To iyaye, maza da mata kuna ji fa).
Bai san sanda yayi tsaki ba amma kasa-kasa, dai-dai sanda Malam da Baba Sa'idu, suka nabba’a a mazauninsu, amma wannan karon da bango ya jingina, bada jikin Imran ba. Imran din yayi saurin jawo tuntu dake gefensa, ya sanya masa har zuwa lokacin Abban bai kara yarda sun hada ido da shi ba. Malam Ali ya dube shi cikin karfin hali da karayar zuciya, yace "wato ita rungumar, a wajenka ba komai ba ce Imran, har kana kiranta ‘kawai’, ko kasan daka kama hannun matar da ba taka ba, gara ka kama sandar wutar jahannama?”
Ya kara dukar da kai cikin girgigizawa "Na tuba Malam, kayi hakuri, ba zan sake ba, kuskure ne. Na tuba nabi Allah na bika, kada ka yi amfani da wannan a matsayin abinda zai hanaka aura min Zaynab, ban san yadda rayuwata zata kasance ba……".
Duk dariyar da Malam din ke yi, bai san sanda hawaye suka zubo masa ba, shikansa Abban hawaye ya soma, Malam ya sa haBar taguwarsa ya share zufa da fuska duka, yace (yana mai kawas da fuska daga gareshi).
"Aurenka da Zaynabu-Abu bazai taBa yiyuwa ba Imran, ka zamo musulmi na kwarai, mai yarda da karbar kaddarar yadda duk Ubangiji ya shirya masa rayuwa, hakan ne zai sa ka ci riba, kaga mai kyau a rayuwarka".
Ya dago ya dube shi, ba tare da alamun damuwa ba ko mamaki ko kankani a tare da shi, ya ce "Hujja? Komi yana da dalili, to meye dalilinku na hana mani auren Zaynab, alhalin duk muna son juna? Inada wani mugun hali ne ka gayamin nayi maka alkawarin dainawa. Idan kuma kaima kana la'akari da hujjar Zaynab ne, na amince in dawo nan, in baro iyayena da 'yan uwana, in baro aikina da gidanmu dake saku tunanin ni wani ne, in dawo nan in zauna tare da ku, in ya so sai in dinga kula da gonar Abba dake nan…".
Inna Dubu ta tashi zata fita, tana kuka kashirBan da hawayenta, bata iya jure ganin wannan abin bakin-cikin da ban takaici, ta wani bangaren abin tausayi. Har ta kai bakin kofa Malam yace da ita "dawo ki zauna, don kema wat shaida ce da zan gabatarwa Imran da Zaynab su yarda da hujjata".
Ya maida hankalinsa ga Imran, da a yanzu ya koma bashi tausayi, duk kawaici, kunya da ladabi irinnasa, a yau idanuwansa a bude yake masa magana tabbacin suna neman kure ladabinsa, don shi baiga dalilinsu na son yi mai yawo da hankali ba, don kawai yana son auren diyar su, yana sonta yana kaunarta itama hakan, sai dai in abin akwai zalinci da son zuciya a ciki.
Malam yace "ko daya bana la'akari da uzurin Abu, domin (inna Akaramakum indallahi ataqakum),

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login