Showing 132001 words to 133143 words out of 133143 words

Chapter 45 - GABA DA GABANTA By Ayshercool.txt

28 Dec 2024

5866

je tsakiyar falon gidan, sannan ya kalleta ya ce "Ki shiga wancan ɗakin, kiyi sallolinki, za a kawo miki Abinci ki huta da la'asar Zakiru zai zo ya kai ki gida"


Jiki a sanyaye ta ce to, dan ita duk ba haka ta so ba.


Ta ware mayafinta ta yafa sosai, tayi sallar azahar, tayi adduointa, ta kira Inno ta sanar mata sun sauka, yanzu zasu ƙarasa gida, sun ɗan jima suna waya sannan Amina ta kashe wayar.


Ajiye mayafinta tayi a kan gadon dake ɗakin, ta tafi gaban mudubi tana duba fuskarta, ta kwance ɗan kwalin kanta tana sake gyara shi, kawai aka turo ƙofa, tsayawa yayi a bakin ƙofar yana ƙare mata kallo, gaba ɗaya sai ta ɗan rikice, gashi tayi nesa da mayafinta da ke kan gado.
Lumshe idanunsa yayi ya buɗe, kamar wanda aka yiwa dole ya ce "Zo ki karɓa" yayi maganar yana miƙo mata leda.
Kasa motsi tayi daga in da take tsaye, saboda kunya da ta gama mamayeta.


"Meenal, am talking fa"


Sunkuyar da kanta tayi ƙasa, ta fara tafiya a hankali, tana jin yadda idanunsa ke yawo a jikinta, ta ƙarasa in da yake tsaye ba tare da kalleshi ba.


"Menene? Ya naga kina sunkuyar da kai meyafaru" Yayi maganar tamkar bai san meya sanyata cikin ɗari-ɗari ba.


"Babu komai" ta faɗa ba tare da ta kalleshi ba.


"Ga Abinci nan, da kin yi sallar la'asar kije haraba Zakiru na jiranki, ni zan tafi yanzu, zanje wani wuri"


Ta karɓi ledar hannunsa ta ce "Na gode"


Kamar yadda ya gaya mata, bayan sallar la'asar ta tarar da Zakiru a harabar gidan yazo ɗaukarta, ita har mamaki ma take yi, Daddy baya tsoron ko Zakirun ya gayawa Hajiya Zainab cewar suna yawo tare, har gidansa ya kai ta.


Zakiru bai nuna mata komai ba, sai tambayarta ya ta baro mutan gida, a haka har suka isa gida.


Baba na ganinsu ya taso da murnarsa zuwa wurin motar, Amina ta fito tana masa murmushi tare da gaishe shi.


Ya amsa mata cikin sakin fuska ya ce "Ya hanya, ya babar taki?"


Amina ta ce "Lafiya lau Baba, kamar kar in dawo gida da daɗi"


Baba yayi murmushi ya ce "To ko zaki koma ne?"


"Ai Baba ba dan wannan tafiyar ta makarantar mu ba, da ba zan dawo yanzu ba"


"To shikenan, maza shiga ciki ki samu ki huta"


Amina ta juya ta ɗau Akwatinta da Zakiru ya fito mata da ita, Baba sai sannu yake masa, Amina ta ja Akwatinta zuwa cikin gidan.


A falo ta tarar da Hajiya Zainab da ƙawayenta su Turai, sun ci Abinci duk sun bar kwanukan.


Amina ta ce "Ina wuninku?"


A yamutse suka amsa mata, dan Hajiya Zainab bata amsa ba, sai ma kallonta da tayi ta ce "Zo ki kwashe kwanukan nan"


Mamakine ya kama Amina, Hajiya Zainab dai ba makauniya ba ce ba, taga Akwati a hannunta yanzu ta dawo, amma saboda tsabar son ta wulaƙantata wai ta zo ta kwashe kwanuka.


"Ko ba zaki zo bane, kika cake a wurin kina kallona?" Amina ta jingine Akwatin, ta zo tsakiyar falon, ta kwashe kwanukan ta kai Kitchen, ta zo kuma kwashe sauran, Mummy ta kuma kallonta ta ce "Idan kin gama, na fito da labulaye na barsu a kan gado, zaca cire na part ɗina gaba ɗaya a sanya wannan, Carfet ɗin bedroom ɗina ma, zaa a canza wani, wannan fita da shi za ai, Zakiru ya kai shi Car wash.
Amina kawai ta jinjina kai ta tashi, ta kai kwanukan ta dawo ta ja Akwatinta.
Hajara ce ta fito daga ɗakinta, sanye da hijjabi alama salla tayi, ta washe baki tana faɗin "Amina ashe kin dawo ya hanya?"


"Lafiya lau Hajara, ya aikin?"


Hajara ta kwaɓe fuska ta ce "Aiki gashi nan, kin tafi kin barni, matar gidan nan da alama akwai abin da yake damunta, kullum cikin sauke mini kwandon bala'i take, da na motsa sai hantara, haka ita ma 'yar ta ta, kai wanan masifa ni Hajara wanan mutane kamar gadonta suka yi"


Amina ta ɗan taɓa baki ta ce "To Allah ya kyauta".




Hajiya Turai ce ta kalli Hajiya Zainab ta ce "Ita kuma wannan 'yar aikin taki daga ina na ganta da uwar akwati?"


"Wai nan ƙauye ta je"


Turai ta ce "Ni fa gani nayi tana wani ƙara kyau"


"Ke ni bar ni da zancen banza, Hajiya Salma, ya batun yarinyar nan da kika ce in haɗata da Khalil, da wuri zan duk abin da ya dace, kan ya lallaɓa ya koma wurin waccan shahshashar ban sani ba"


Hajiya Salma ta ce "Karki damu duk ranar da kika shirya, ki zo muje kiga yarinyar"


"Allah ya kaimu jibi, zan zo muje"




Amina ta shiga aikin canza labulaye, kamar yadda Hajiya Zainab ta umarce ta, Amina ba ta gama aikin nan ba sai bayan sallar isha'i, gaba ɗaya ta gaji.


Kasancewar tafiyarsu ta ƙarato, ya sanya Amina ta duƙufa cigaba da bitar karatun da tayi, ana sallar isha'i, ta shige ɗakinta, hatta Abinci a ɗakinta ta ci.


Wajen sha ɗayan dare ta ga kiran Daddy, ta ɗaga ta saka wayar a handsfree taƙi magana.


A hankali ya ce "Meenalin Daddy"


"Na'am"


"Au na zaki kulani ba, ki ka ɗaga wayata ki ka yi shiru?"


"Ai kaima watarn haka kake mini"


"To naji, zan samu tea?"


Amina ta ɗan tura baki ta ce "Ni gaskiya a gajiye nake, daga dawowata aka sani canza labulaye da Carfet, da nayi niyyar ko girki na yi maka, amma ko akwatina ban ajiye ba aka sani aiki"


"Waye ya saki aikin?"


"Ai kai ma ka sani"


"To shikenan naji, da safe idan Allah ya kaimu, ki mini girki kin ji Meenalina, am missing your delicious food, kuma kinga kin fi kowa sanin Abincin da ya dace da ni"


Ta yi wani murmushi kamar tana gabansa ta ce "I Will in sha Allah"


"Ranar Wednesday zaku tafi, so ki cigaba da shiri, idan da wani abu da kike buƙata ki sanar da ni"


"Eh, abu ɗaya nake so"


Cikin zaƙuwa ya ce "What it is?"


"Your presence their" tayi maganar a shagwaɓe.


"Rigimar ce ko, sai da safe" ya kashe wayar. Ajiye wayar tayi tana cigaba da mita, ta mayar da hankali ga karatunta.






Cikin rashin samun mafita, da rashin karsashi Khalil ya kira Mummy a waya, sai da ta kusa katsewa sannan ya samu ga ɗaga.


"Yau ka ga dama ka neme ni kenan?" Yaji muryarta maimakon ko gaisawa ta bari suyi.


A saɓule ya ce "A'a ba haka bane, bani da lafiya ne"


"Eh, ko ba baka da lafiya ba? Kana fama da ciwon so ko, gubar Asirin da suka zuba suka baka a Abinci bata sake ka ba, to ka sani in kai sun shanye ka ni basu shanye ni ba".


"Mummy dan Allah duk a bar wannan maganar, ni kiranki nayi na gaisheki"


"Ka riƙe gaisuwarka bana so, jibi in Allah ya kaimu zanje naga iyayen yarinyar da na zaɓa maka, next za a kai kuɗin Aurenka da ita"


"Innalillahi wa innalillahi raji'un, dan Allah Mummy kar ki mini haka"


"Ai tuni ma an riga an yi, idan ka ga dama kayi mini biyayya, idan ba ka ga dama ba kabi 'yar matsiyata mai awara a hanya!!




AYSHERCOOL
08081012143

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login