Showing 30001 words to 33000 words out of 133143 words

Chapter 11 - GABA DA GABANTA By Ayshercool.txt

28 Dec 2024

5906

na gaishe ki ɗazu da ki ka fito karyawa".


"To kin fi ƙarfin ki sake gaishe ni ko kice mini sai na dawo ne?"


Amina ta ce "A'a ki yi haƙuri, A dawo lafiya Allah ya tsare".


Ba ta amsa ba ta ce "Ki shiga ɗakina ki tattara kayana suna nan ki ninke ki shirya mini su, amma sai kin musu kabbasa tukuna".


"To zan yi insha Allah" Hajiya Zainab ta juya ta fice.


Amina a ranta ta ce "Dan jaraba, dole sai an ƙaƙalo abin da za a ƙasƙantar da kai'


Ta ɗago ta ce "Yaya Hajaru, wanda zai dawo ɗin nan, shi ne wanda zai kai ni makarantar?".


Hajara ta ce "Eh shi ne".


"Allahu Akbar, to shi ya yake? Yana da kirki ko shima dai duk haka suke?".


Hajara ta ce "Eh to, ba na ce ba, shi dai gashi nan miskili ne dai sosai, kuma bai fiye shiga abin da ba ruwansa ba, kuma ba ya wani shiga sabgar 'yan aiki, shi yasa idan nace miki ba shi da kirki na yi ƙarya, dan bai taɓa yi mini ba"


Amina ta washe baki ta ce "Allah ya sa dai kar yayi mini nima, koma ba shi da kirkin lallaɓa shi zan yi, in bishi a sannu in ta masa biyayya dan ya kai ni Makaranta, ni ɗauko mukullin sashin nasa, muje a gyara".


Hajara ta riƙe haɓa ta ce "Ohh ni Hajara, yadda ki ke ƙaunar karatu Amina, Allah ya cika miki burinki ya sa al'umma su amfana"


"Ameen Yayata".


Ko da su Amina suka shiga sashin Khalil, mamaki Amina ta dinga yi, ɗakinsa har ya fi na Fadila tsaruwa, komai akwai sashinsa har da kitchen da kwanukansa da komai, hatta fridge da cooking gas duk akwai.


Amina ta zage suka ƙara tsaftace ko ina, sannan suka baro sashin. Amina na ta fatan Allah ya sa yana dawowa babu ɓata lokaci ya kai ta Makaranta.










Alhamdilillah, Hafsa ciniki ya nata haɓɓaka, sai ai babban abin da yake ci mata tuwo a ƙwarya bai wuce yadda maza ke zuwa su taru a wurin ba wanda sam hakan ba ya yi mata daɗi, gashi wasu 'yan iska wasu na kirki, da yake gata ga wurin mai shayi, wasu ma haka zasu zo su zauna suna shan sigari a wurin. A haka wasu suke nuna suna sonta, da zarar ta musu halin nata na miskilanci, sai zagi da cin mutunci, ita dai bata taɓa ɗaga kai ta kula kowa ba balle ta bar abin faɗa.
Abin na damunta, amma ba ta gaya wa Mama ba, dan da zarar ta ji abin da yake faruwa, zata iya dakatar da cigaba da sayar da awarar, kuma idan ta dakatar sana'ar me za suyi?. Dan haka ta ja bakinta ta yi shiru, take ta Addu'a Allah ya kawo musu mafita.




Tun bayan fitowar su daga test, Fadeela sai murna take yi, ko bakomai ta samu abin da ta rubuta, amma sam ba ta ji ta damu da abin da ya faru da Yazeed ba, dan a ganinta ai ba ita tace ya taimaka mata ba.
Tana tsaye tana waige-waige, ta hango Yusra tana ƙarasowa in da take, ta kalli Fadila ta ce "Girl ya na ganki duk wani iri ne?"


"Bari kawai unexpected test aka yi mana".


Yusra ta yi murmushi ta ce "Baki shirya ba kenan?".


Fadila ta ɗan yamutsa fuska ta ce "Ina na wani shirya, ni gaba ɗaya ma bana gane course ɗin, gashi dama muna takun saƙa da lecturer, kinga wata applied question da ya yi mana, abin ba a magana".


"Amma dai kin rubuta wani abu ko?".


"Me kuwa na rubuta? Wani ne ya gaya mini na rubuta, shi kuma aka yi masa minusing marks".


Yusra ta ce "Subhanallah garin yaya?".


Nan Fadila ta bata labarin Yazeed.
"Girl gaskiya ba kya kyautawa, ban ji daɗin abin da kike masa ba".


"Ni na sashi ya dinga mini shishshigi? Kinga ni muje in samu wani abun in ci yunwa nake ji".


Yusra ta kalli agogon hannunta ta ce "No, kinga yau Friday, zo muje masallacin cikin school mu saurari huɗuba, idan aka yi sallar juma'a, sai mu je muci Abincin daga nan mu tafi gida".


Fadila ta ce "Masallacin Juma'a sai ka ce wasu maza?".


"Kin ji ki, ai mata ma na zuwa sallar juma'a, ma samu muji huɗuba"


Haka Yusra ta takurawa Fadila, suka tafi masallaci, a hanya Fadila take sanar wa da Yusra da batun dawowar Khalil. Suka dinga planing ɗin yadda zasu shawo kan Khalil a kan ya so Yusra.
Suka ƙarasa masallacin mata, suka shiga suka zauna. Sai dai shiru liman bai zo ba, balle a fara huɗuba, can aka fara gyaran murya aka fara da buɗewa da addu'a, can kuma ya fara gabatar da huɗuba cikin harshen larabci.
Subhanallah, kai ba ka ce mai yin huɗubar ya taɓa jin yaren hausa ba, duk da Fadila ba ta jin larabci, amma ta nutsu tana sauraren yadda huɗubar ke ratsata, bugu da ƙari yaren larabci na matuƙar burgeta, aka jima ya fara huɗubar da Hausa, wanda yayi huɗubar akan tsoron Allah da riƙon gaskiya yayi, ya yi amfani da hikima sosai a wurin gabatar da huɗubar.
Bayan ya kammala kuma, aka tada salla. Subhanallah sai da ya fara karatun Alkur'ani, a lokacin wata nutsuwa ta sake saukarwa Fadila, muryarsa mai daɗin amo da saurare, ga wurin yayi tsit kamar ruwa ya cinye su. Fadila ji ta yi tamkar kar a idar da sallar nan, saboda tsananin daɗin karatun, tabbas makarancin gwani ne wurin iya sarrafa harsashe, dan hatta a cikin huɗubarsa akwai salo na narka zuciyar mai sauraro, karatunsa akwai amo mai sanyawa zukata nutsuwa.
Haka aka idar da sallar nan suka nufi wurin cin abinci, amma still Fadila na cigaba da jiyo karatun nan a cikin kunnuwanta, tamkar ta magantu sai kuma ta yi shiru, suka tafi cin Abinci.




Bayan sun kammala cin abincin, Yusra ta tafi don ta kammala lectures ɗinta na ranar, Fadila kuwa suna da lectures 2-5.
Ko da ta shiga ajinsu, ta tarar da duk matasan samarin nan na ajin su, sun kewaye Yazeed, shi kuma ya ɗan ɓata fuska duk da da wuya ka ga fushi a fuskarsa, dan mutum ne mai yawan murmushi, da alama dai sun takura masa, sai sunkuyar da kansa yake yi.
Captain ya cire hular kan Yazeed, ya duƙa a gaban Yazeed yana cewa ya Sheikh, a shafa mana karama.
Wani siririn kyau ne ya bayyana a fuskar Yazeed, bayan Captain ya cire masa hula, yana da wani kwantaccen baƙin gashi, da ya haɗe da sajensa ya kwanta a fuskarsa, zuwa ɗan madaidaicin gemunsa.
Ya miƙa hannu ya karɓi hularsa tare da mayarwa kansa. Yamutsa fuska Fadila ta yi ta ce "Dan Allah ku tashi ku bani wuri, kawai kun kafa daba kun cikawa mutane kunne da hayaniya".
Captain y kalli Fadila ya ce "Ke kul, mun kafa dabar kwasar tabarraki ne, ashe muna zaune da babban malami amma babu labari, ai tun da nake zuwa sallar juma'a ban taɓa jin huɗubar da ta ratsani kamar wadda Sheikh, Malam Yazeed ya yi ba" Saroro Fadil ta kalli Captain ta ce "Kamar yaya?".


"Ai duk wanda ya je sallar juma'a yau a masallacin school ɗin nan, ya ji yadda ya dinga zuba larabci, sai ma da ya fara karatun Alqur'ani, kamar mutum ya suma dan daɗi"
She can't believe that Yazeed ne ya yi wannan karatu, guntun tsaki ta ja, ƙila ma ƙaryar Captain ce kawai.
Zama ta yi a wurin zamanta ta yi shiru, tana tunanin muryar da aka yi huɗuba, tabbas muryar Yazeed ce, ko da be fiye surutu ba, amma muryarsa a nutse take cike da nutsuwa da kuma iyayi, kamar yadda take faɗa.
Shi kuwa Yazeed tuni ya bar ajin, dan baya son abin da suke masa sam.
Nan taji ana hirar, limamin masallacin ne ba lafiya, ya shirya zai taho, ya yanke jiki ya faɗi, kuma ba a samu information da wuri ba, an tsaya mujadalar wanda zai ja Sallar, shi ya karɓa ya yi.


Har aka shigo lectures, Fadila na satar kallon Yazeed, da son tabattar yanzu daga bakin wannan ɗan tahalikin wannan karatun ya dinga fitowa ɗazu? Sam babu kama.
Karaf Yazeed ya ɗago ido, suka haɗa ido da Fadila, wata uwar harar ta watsa masa, kamar ba ita take kallonsa ba.
Ɗauke idonsa yayi, yana fatan Allah ya sa ba wata tsiyar Fadila take shirya yi masa ba.


Amina wuni tayi tana sintiri tsakanin falo da harabar gidan, dan ganin me kaita makaran ya dawo, amma babu shi babu alamar sa. Gaba ɗaya har ranta ya fara ɓaci ta fara tunanin ko dai ba yau ɗin zai dawo ba.
Shi kuwa Khalil tuni ya dawo, dan tun bayan azahar ya dawo, ya shiga sashinsa, ya yi wanka ya yi kwanciyarsa dan a gajiye yake sosai.
Ya makara sallar la'asar, dan haka a ɗakinsa ya yi ta, sannan ya shirya ya fita.


Amina kuwa tana zaune a falo, ta zubawa TV ido, tana kallo, tana fuskantar wani abu daga larabcin da ake fassara yaren jaruman.


Ba tsammani ta ga mutum ya faɗo falon, dogo da shi kawai ya sa kai ya nufi sashin Hajiya Zainab, ba tare da ko sallama ya yi ba.


"Kai bawan Allah daga ina? Zaka faɗowa mutane haka ba sallama kawai ka miƙa wuya kamar raƙumin jeji zaka wuce".
Cak ya tsaya, ya waiwayo ya kalli bakin mai wannan maganar, gabanta ne ya faɗi da suka yi ido huɗu da shi, sai yanzu ta tuna da uwar ba'ar da tayi masa, ga kammaninsa sak da Alhaji Ahmad sun bayyana, ba in da ya bar mahaifinsa a kamanni, sai dai yafi Alhaji Ahmad ƙuruciya ko ba a gaya mata ba ta san wannan shi ne wanda aka ce zai dawi.


Amina ta hau kame-kame "Yi haƙuri dan Allah, na manta Hajiya ta ce zaka dawo, kuma kaga kaine ma da ka shigo ba ka yi ko sallama ba, amma dai Hajiyar bata nan ta fita, ina wuni".


Ƙare mata kallo ya yi a ransa ya ce "Ko wacece wannan, a ina aka samota kuma oho?" Bai kula ta ba ya cigaba da tafiyarsa. Yana wucewa Amina ta ce "Subhanallaahi, na yi shirme wannan shegen bakin nawa, Allah ya sa kar ya gayawa babarsa na masa rashin kunya. Amma ai ba rashin kunya ba ce gaskiya ce ka shigo zalau-zalau babu sallama".


Amina na nan zaune ta taradaddin abin da ta aikata, Hajara ta fito falon, sai dai Amina ba ta gaya mata me tayi ba.
"Amina ya na ganki wani iri ne haka?"


Amina ta girgiza kai ta ce "Ba komai".


"To shikenan, mai yakamata a dafa ne yau da daddare?"


Amina ta ce "Nima ban sani ba, a dafa abin da ya sawwaƙa"


"Wai naga gaba ɗaya yanayinki ya canza".


"Ba komai fa, kawai ina tunanin Baba ne".


"Ke Amina, baban da ɗazu ya tafi kuma zai dawo".


"Ai ba yau zai dawo ba, wataƙila sai gobe ko in Allah ya kaimu jibi" suna tsaka da hirar sai ga Khalil ya fito, nan da nan Amina ta yi shiru.


Hajara ta risuna ta ce "Ina wuni Yallaɓai, ashe ka dawo?".


"Eh na dawo, Fadila ba ta dawo daga school bane?".


"Eh har yanzu ba ta dawo ba".


Khalil ya ce "Well Shikenan".


Hajara ta sake risunawa ta ce "A kawo maka Abinci ne?"


"Eh ajiye mini a kan dining, zan shigo in ci".


Amina dai ba tace komai ba, sai zazzare ido da take yi.


Bayan fitarsa Hajara ta ce "Shi ne fa wanda zai kai ki makaranta, da ki ke ta jira ya dawo, ya dawo amma ba ki iya gaishe shi ba".


"Na gaishe shi mana, ai ina zaune a nan falon ya zo ya wuce".


Hajara ta ce "Au to, ai na zaci baki kula shi bane, shi gaskiya ba shi da matsala sosai, be fiye wulaƙanci kamar ƙanwarsa ba".


Ita dai Amina fatan ta, Allah ya sa kar abin da tayi masa ya sanya ya ce ba ze kaita makaranta ba.


Fitarsa babu daɗewa ya dawo, ya zaune a kan dininga ya zuba Abinci ya fara ci.
Amina sai satar kallonsa take, ko zai yi magana amma bece komai ba. Tana cikin wannan zullumin Fadila ta faɗo falon babu ko sallama, ranta a haɗe da alama ta gaji matuƙa.


Sai dai tana ƙarasa shigowa falon, tayi tozali da Khalil ta saki murmushi.


Ya kalli Fadila shima ya yi mata murmushin ya ce "'yan Jami'a" dire jakarta ta yi ta nufi dining ɗin tana cigaba da murmusawa cike da gajiya, ta janyo kujerar kusa da Khalil ta zauna tare da furta "Welcome home dear".


"Ai ke zan yiwa welcome, ya school ɗin?".
Ta taɓe baki ta ce "School gamu, muna ta shan wahala".


Ya tsiyayo lemo mai sanyi ya kai bakinta, ta buɗe bakin tana sha tana lumshe ido, Amina zuba musu ido ta yi a ganinta wannan ai fitsara ce, su a ƙauye ai ko kusa da yayyanka namiji baka zama, balle a kai ga bada abu a baki.


Khalil kuwa hirarsu suka cigaba da yi cike da kewar juna. Allah ya rufawa Amina Asiri ganin Khalil ya sanya Fadila ta laifin da Amina tayi mata da safe.
Fadilan ta shiga bawa Khalil labarin abin mamakin da taji game da Yazeed cewa take "Brother bai fa iya turanci ba, ka ji kwaɓar da yake yi idan zai turanci, amma baka ji larabci ba, ni fa har yanzu mamaki nake, anya kuwa shi yake yi?".


"Dama waye ya gaya miki sai ka iya turanci shi ne ka ke da ilimi?".


"Ai ni na gama raina gayen ne gaba ɗaya, kai ka ganshi, kaga dressing ɗin da yake idan zai zo school? Wannan aka bashi taimako karɓa zai yi"


Khalil ya ce "Ke kika ga haka, irin wannan basu da duniya ba balle abin da yake cikinta".
Ta ɗan taɓe baki, tare da janyo plate ɗin gaban Khalil, ta sanya cokali ta fara ci.












Labarin batun Amina tana wurin Baba a birni, za ta yi karatun boko kuwa ya cika gari, wasu suka dinga Allah wadai da tirr da abin da Baban ya aikata shi da Amina a ganinsu wannan tsantsar rashin hankali ne, da rashin sanin ya kamata.
Ko da labari ya iske Jarmai, a ƙulu iya ƙuluwa, yayin da iyalansa suka dinga Allah ya ƙara.
Gidansu Amina ya tafi, zuciyarsa cunkushe da takaici, na yadda ya ga samu sannan ya ga rashi.
Ya sa aka yi masa sallama da Baba Hassan. Babu wani jinkiri kuma Baba Hassan ya fita, ya ƙarasa in da Jarmai ke tsaye tare da yi masa sallama ya miƙa masa hannu su gaisa, Amma Jarmai ya ce "ka ga ni ba wannan ne ya kawo ni wurinka ba, illa in zo in tabattar maka da na samu labarin abin a ya faru, ka haɗa kai da 'yar ka ta gudu, bayan nan an karɓe ni kuɗin Aurena, to tun wuri kaje ka samu 'yan uwanka, ku haɗu ku dawo mini da kuɗina, kafin in ɗauki matakin da ya dace a kan ku".


Baba ya girgiza kai ya ce "To ai kaga ni ba ni na karɓi kuɗin Auren nan ba, bani da masaniya akan komai sai yanzu, dan haka bani zaka tambaya ba".


"Oho dai, ni dai a biyani kuɗina kawai, aikin kawai mutanen banza"


Baba dai bin Rabe kawai ya yi da ido, yana mamakin ƙarfin hali da rashin ta ido irin na Jarmai.




Da Hajiya Zainab ta dawo, kusan raba dare suka yi da 'ya'yanta a falo suna hira, kowa yana kawo hirar abin da ya dame shi, suka ci Abincin dare tare, suka yi ta hira sai bayan sha biyun dare, sannan suka watse.
Har washegari shiru, Amina ba ta ji Khalil ya yi Magana ba, hakan ya sa ta fara sarewa, wata zuciyar ta ce 'kije ki masa magana' wata kuma ta ce "Ki ƙara ba shi lokaci, kar ki yi garaje' gaba ɗaya ta bi ta ƙosa, gashi idan suka haɗu ko gaishe shi ta yi, sai dai ya kalleta ya ɗauke kansa, amma ba zai amsa ba. Ko aiki ne sai dai ya kira Hajara ya sata, amma ba zai kula Amina ba. Amina ba ta da zaɓin da ya wuce ta cigaba da Addu'a, dan haka ta duƙufa da sallar dare tana fatan Allah kar ya kawo abin da zai mata katanga da samun ilimin ta.


Idan taga Fadila ta shirya zuwa Makaranta, abin ba ƙaramin burge Amina yake ba, tana da burin zuwa Jami'a amma ba ta da tabbacin Baba zai iya ɗaukar nauyinta zuwa Jami'a, shiyasa take taƙaita burinta a iya Sakandire kawai.


Yadin jikinsa kawai ta hango ta san shi ne, saboda zuwa yanzu zata iya ƙirga adadin kayan da yake sawa idan zai zo, dama takalmansa guda biyu ne kacal yake zuwa da su. Sai da taje daidai in da yake, sannan ta tada wata irin ƙura, ta bule shi da ƙura ta yi gaba abinta. Duk wanda suka ga abin da ya faru ba su ji daɗi ba, su kai ta bashi haƙuri, ya nuna musu bakomai ya cigaba da tafiya zuwa ajinsu.
Yau a bencin bayan Fadila ya zauna, yayin da ita kuma take jikin window.
A nata gudanar da lectures kamar kullum. Tari ne ya sarƙe Yazeed, ya saka hankici ya toshe bakinsa, ya kifa kansa yana ta fama, yana tarin ƙasa ƙasa, ya ɗago idanunsa sun yi jawur. A lokacin lecturer ya fita amsa waya, dan haka Yazeed ya fara kira sunan Fadila a hankali, ta waiwayo tana yamutsa fuska ta ce "Meye?".


"Dan Allah ki taimaka mini, jikin window nake so ki bani, ki dawo wurina dan Allah ba dan ni ba, bana son zafi, bana iya numfashi sosai".


Wata uwar harara ta yi masa ta ce "Au Allah, Sannu ajebo ai ni banga alamar hakan a tare da kai ba, ai da sai ka dinga dakon A.C ko fanka daga gida kana dasawa a wurin zamanka, ba in da zan tashi in je" ta juya ta cigaba da rubuce rubucen ta, shi kuma lecturer ya ɗora da bayani.


"Dan Allah Fadila" ya faɗa yana jan numfashi.


"Excuse me sir, kaga Wannan mutumin ya takura mini, sai kiran sunana yake ya hanani jin abin da ake yi".


Lecturer ya ce "Malam meye haka? Kalleka da gemu a haka kamar na Allah, tashi daga wurin nan ka koma baya, seat ɗin ƙarshe na last row" Jimm Yazeed ya yi, sannan ya tashi tsaye a hankali ya nufi in da malamin ya yi masa umarni.


Babson da ke kusa da Captain ya ce 'Shima gayen nan kamar wani maye, duk in da yarinyar nan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login