Showing 126001 words to 129000 words out of 133143 words

Chapter 43 - GABA DA GABANTA By Ayshercool.txt

28 Dec 2024

5886

haɗe ransa babu annuri sam, hakan baya rasa nasaba da canza lamba da yayi ya kira Fadila, tayi masa wankin babban bargo ta ci mutuncinsa.
Ya shigo yana ta muzurai, da hura hanci, da fari bai lura da Yazid da ke zaune a ajin ba, sai daga baya bayan ya yi rubutu a kan board ya juyo.


Ya sauke idonsa a kan Yazid, sake haɗe rai yayi ya kalli ce "Me kake yi a class ɗina?"


Yazid yayi shiru bai ce komai ba.


"Zo ka fita ka bar mini aji, dan baka da mutunci shi ne zaka zo ka zauna mini a aji, zo ka bar mini aji, kuma ka sa a ranka ba zaka zana jarrabawata ba, come and leave my class usless"


Kalmar usless ɗin nan ba ƙaramin ƙonawa Fadila rai tayi ba, ji tayi kamar ta zagi Kankiya.


Captain ya ce "Sir kayi haƙuri ba shi da lafiya ne, yau ya dawo"


"Shut up! Nace ka sa mini baki ne? Ai ya riga ya san na hana shi zama a ajina, tashi ka bar mini ajina"


Yazid ya ja jikinsa a hankali, ya tashi tsaye, sai da ya tashi Fadila ta lura da Cannula a hannunsa, a hankali yake jan ƙafarsa, tare da dafe gefen cikinsa ya fice daga ajin.
Kankiya yayi tsaki ya ce "Nonsense"
Miƙewa Fadila ma tayi, ta ɗau jakarta ta nufi hanyar fita, tana jin Kankiya na kiranta amma tayi masa banza ta bar ajin da sauri.


Hajiya Zainab ce ta shigo ɗakin Daddy tana masifa "Wai ni ina wannan sakaran direban naka ya tafi? Tun ɗazu nake nemansa, yazo ya karɓo mini saƙo a wurin Hajiya Salma.


Cikin ko in kula Daddy ya ce "Na aike shi ne"


"Zuwa ina? Jiransa nake yi ni akwai in da zani"


"To ke ki ɗauki mota kije ki karɓo da kanki mana, ko ta yi miki aike"


"Haba Baban Khalil, ina gaya maka uzurina kana gaya mini wani abu daban, dan Allah ka kirashi ya zo ya je mini aiken nan"


Alhaji Ahmad ya tashi zaune ya ce "Na aiki Zakiru Shanono, zai kai Amina gidansu"


"I don't get you, and what does that mean? Meyasa zaka aike shi ya kaita ƙauye, a matsayinta na wa?"


"Mahaifinta ya nemi hakan, dan ba zai yiwu ya bar yarinya ita kaɗai ta tafi ba"


Rai a ɓace ya ce "I don't care, me yasa zaka yanke wannan hukuncin ba tare da na sani ba, 'yar aiki tafi aikin gidana muhimmanci kenan? Ubanta ya kaita mana, yanzu waye zai je mini aiken nawa?"


Miƙewa tsaye Daddy yayi ya ce "Zainab, ba Khalil bane da Ahmad kike Magana, duk wanda yake aiki a ƙarƙashina yana da damar ya nemi alfarma a wurina nayi masa" ya fice ya bar mata ɗakin.


AYSHERCOOL
08081012143


GABA DA GABANTA


AISHA ADAM AYSHERCOOL




44


Ganin Alhaji Ahmad ma ya ɗau zafi sosai, ya sanyata saurin saukowa daga nata fushin, dan da wuya yayi fushi amma idan yayi fushi wahalar sha'ani ne da shi fiye da tunani.
Dan haka ta ce "Naji shikenan ya wuce, na haƙura da saƙon na san yadda zan yi"
Bedroom ɗinsa ya wuce ya barta, tabi bayansa tana cigaba da lallaɓa shi, amma ya shareta ya ƙi saurarta.


Ba ƙaramin yarfa Kankiya Fadila tayi ba, ganin yadda yake muzurai ake tsoronsa amma Fadila ta yarfa shi a gaban ɗalibai, hakan ba ƙaramin ɓata masa rai yayi ba, kuma hakan ya jefa zargi a zukatan ɗaliban, mai zai sa Fadila ta tsinka malamin haka duk da yadda ake tsoronsa.


"Yazid, Yazid" tsayawa yayi ya waiwaya da jin muryarta a cikin dodon kunnuwansa.


Ta ƙarasa in da yake da sauri, bai ƙosa ba ya jira har ta cin masa.


Cikin damuwa ta ce "Sannu, ya jikin naka? Ashe baka da lafiya?"


"Eh, amma da sauƙi sosai Alhamdilillah"


"Wai meya sameka ne?"


"Rashin lafiya ne" ya bata amsa.


"Wane irin rashin lafiya?" Ta kuma tambayarsa cikin kulawa.


"An mini aikin appendix ne, sai kuma asma da ta dameni shikenan amma da sauƙi sosai"


"To yanzu ina zaka daga nan?"


"Gida zan tafi"


"Ok, to muje in sauke ka"


Da sauri ya girgiza mata kai ya ce "A'a ki bari na gode zan tafi"


"Ba ka ganin a yadda kake tafiya, kazo muje in sauke ka"


"Na gode, amma ba zan hau motarki ba, ban kai in hau mota irin wannan ba, ba ta dace da hawan talaka kamata ba" daga haka ya juya yana tafiya a hankali.


Tsayawa tayi tana cigaba da kallon yadda yake tafiya a hankali, har ya ɓacewa ganinta.


Tafe suke suna hira jefi jefi ita da Zakiru, yana bata labarin yanayin zamantakewar gidan kafin zuwanta.


"Ai nake gaya miki, ko 'yan uwan maigidan nan duk zumuncinsu sun haƙura sun daina zuwa, sun zuba masa ido, shi kansa sai lokaci lokaci yake zuwa, dama bata yadda yaranta suje ba, kuma fa 'yan gari ɗaya ne, saboda azabar baƙin halinta, duk son sa da yayi taimako sai dai yayi bata sani ba. Ai matar nan bana zaton tana son taga Annabi"


Amina ta ce "A'a karka ce haka, amma ina mamakin ita ko nata 'yan uwan basa zuwa sai ƙawaye"


"To ina taga wasu 'yan uwa ma, sukan zo wasu lokutan suna ba wani kallon arziki take musu ba, amma a hakan tana jidar kaya ta bani in kaiwa wasu daga 'yan uwanta, ai ita idan kika ga tana rawar kai tana nan nan da kai, to mai kuɗi ne kai, duk ta kanainaye maigidan baya jin maganar kowa sai tata, ai har gara yanzu a kan da, sanyinsa yayi yawa, sai ya fito cikin mutane ya fito yana taƙama baki Ga yadda ake girmama shi a waje ba, amma a gidansa ba shi da kataɓus ga shegen son 'ya'ya kamar masifa, waccan tsigalaliyar 'yar ta sa idan ta zauna tana taɓara abin takaici, gata halinta ɗaya da uwarta na rashin mutunci, ba kunya idan nayi kuskure take ƙare mini zagi, ai Alhaji Ahmad yayi ta kowane fanni amma a gidansa dai damisar kwali ne"


"Zakiru ya isheka haka, wasa yayi wasa banda tsikarin uwar miji da taɓarya" tayi maganar ranta a haɗe.


Zakiru ya ce "Kamar yaya kenan?"


"Ina ruwanka da abin da ke faruwa a gidansa kake ce masa damisar kwali, kai waya san yadda taka matar ke juyaka, ya isheka bana son wannan hirar"


Zakiru ya yi murmushi ya ce "Allah ya baki haƙuri, tuba nake"


Amina ta basar da shi ta haɗe rai.


Message ɗin Daddy ne ya shigo wayarta.
"Yaya hanya, kun isa kuwa?"


Tayi masa reply "A'a muna hanya"


"Ina fatan ba kya jin yunwa, idan kina jin yunwa ya tsaya ki ci Abinci"


"Ka manta na karya kafin mu tafi, mun shiga Shanono, mun kusa gida in sha Allah"


"Ok, to Alhamdilillah, ki gaishe su"


"Thank you, za su ji" ta ɗan yi murmushi ta ajiye wayar.


Hajiya Zainab ce zaune a ɗakinta tana waya da Hajiya Salma "Dan Allah Salma ki ƙara haƙuri, kwanan nan duk na kasa gane kan babansu Khalil, ya ce zai bani kuɗin amma sai wasa yake mini da hankali, da abu ya ɗan haɗamu sai ya hau fushi, a yadda yake ɗin nan idan na matsa, zai iya hana kuɗin nan, kuma ni kinga na tattare kuɗin hannuna na yi order kaya, kuma ba zai yiwu in kwashe sauran kuɗin hannuna in baki ba, saboda suma juyasu nake".


Hajiya Salma ta ce "Ni yanzu ya zan yi? Turai ta bani aron million biyu, dama na wajenki nake jira da million bakwai coustom suka ce zan bayar a sakar mini kayana, da ƙyar suka bari a 5million, kuma kinga Alhaji kwanan nan ya ƙara mini jari ya ce ba zan samu ba"


"Kiyi haƙuri, zan cigaba da lallaɓa shi saina karɓa zan baki in Allah ya yarda, kuma ina ga zan je Abuja a satin nan in Allah ya yarda"


"Too, Zainab me zaki yi a Abuja kuma?"


Hajiya Zainab ta ce "Wurin yaron nan Khalil mana, gaba ɗaya ya ɗauki gaba da ni, ubansa kawai yake tuntuɓa, ba ruwansa dani"


"Kaii yaran zamanin nan, anya ba asiri suka yi masa ba, duk yadda Khalil yake miki biyayya, amma yanzu a kan wannan yarinyar ya daina shiga harkarki"


"Bari kawai Hajiya Salma, bana son babansa ya gano actual abin da nayi masa, kin san halinsa a kan 'ya'yansa, gaba ɗaya ina cikin damuwa dole in je Abuja"


"Ke Zainab, ai ba a yiwa yaran zamanin nan haka, ba ke yakamata kije ba, ki kai yarinyar wurin malamai, idan ma wani abun suka masa a karya shi, sannan ki nemo masa wata matar, akwai 'yar ƙanwata Hajiya Badi'a ai kin santa Kursum ki haɗa shi da ita kawai"


"Kin kawo shawara haka za ayi, zai ga tsiya"


"Ai kawai ba sai kinje ba, sai bayan an kai kuɗi da komai, ki ce masa ya zo ga mata shine zaki hukunta shi ki nuna masa ke uwace"


Hajiya Zainab ta ce "Hakan ma yayi, na gode sosai Salma, zan zo gidanma da kaina mu ƙarasa tattaunawa"


"To shikenan, sai Allah ya kawoki" suka yi Sallama Hajiya Zainab na jin ta gamsu da shawarar da Hajiya Salma ta bata.


Amina tayi ta kwatantawa Zakiru hanya har ƙofar gidansu, suna parking ta buɗe motar ta tafi da gudu cikin gida, wasu daga yaran su Kawu Bala suna ƙofar gida suka bi motar da aka kawo Amina da kallo, dan ɗaya ce daga irin jibga jibgan motocin da Alhaji Ahmad yake hawa ne aka kawota.
"Inno! Inno!" Amina ta dinga ƙwalawa Innon kira.


Inno ta saki ƙwaryar hannunta, ta buɗe hannayenta Amina ta zo ta rungumeta, Inno ta ƙanƙame Amina kamar zata mayar da ita ciki, Amina kuwa kuka ta fara yi tana jin tsananin kewar Inno.


"Amina, Amina na rasa mema zance"


"Inno, yaushe rabon da in ganki?"


Inno ta ce "Yau ai gashi kin ganni"


Tuni wasu daga cikin yara har da 'yan matasa na maƙotansu, suka cika tsakar gidan suna kallon Amina.


Suka shiga ɗakin Inno, Amina sai sake ƙanƙame Inno take yi.


"Amina ya gida ya karatun bokon?"


"Karatu lafiya lau Inno"


Inno ta riƙe haɓa ta ce "Ohh, Amina buri ya cika ana can ana boko"


"Inno kenan, ai zaki ga ribar boko in Allah ya yarda, bari in yiwa Zakiru magana ya shigo ku gaisa"


Inno ta ce "Waye shi kuma?"


"Direban gidan da nake aiki ne"


"Au ai na zata siriki ne"


Dariya Amina tayi ta ce "Ba wani siriki"


Amina taje ta kira Zakiru, ya shigo gidansu Amina, suka gaisa da Inno, daga nan suka ɓige da hira kasancewar Inno ta san garinsu Zakiru yayarta tana aure a can.


Mutane sai shigowa suke suna sun zo yiwa Amina sannu da zuwa, nan kuwa gulma suke zuwa yi, suna ta maganganun Amina ta zama ƙatuwa, gashi ta yi fresh ta zama 'yar gayu, ga uwar waya a hannunta.


Zakiru ya kalli Amina ya ce "Amina ko zaki haɗani da wanda zasu tayani kwaso kayan da ke motar"


Amina ta miƙe tana faɗin "Ai ko nima sai in ɗauka"


Ya kalleta ya ce "Ki ɗauki me? Zo muje ki gani fa" Amina tabi bayan zakiru zuwa mota.


Ya saka hannu ya buɗe mata boot, waro ido tayi ta buɗe baki da tayi tozali da abin da ke cikin Boot ɗin.


Kayan Abinci ne kamar za a buɗe kanti, ta kalli Zakiru ta ce "Zakiru, wannan fa?"


"Aike Amina kin ciri tuta a gidan nan, shekaranjiya ya saka na ɗau motar nan muke je da shi muka sayo, jiya da daddare ya ce mini a wannan motar zamu tafi, kar in bari ki san da kayan"


"Na shigesu ni Amina, Zakiru kalli uban kayan fa"


"Ke ki gode Allah, Allah ne ya baki, da waccan matar ta sani ba zata bari a baki ba"


Amina ta ce "Zakiru kaima ka ɗiba"


"A'a nima ya sallameni, bari in kira wasu su tayani"


Haka aka dinga kwasar kaya ana shiga da su gidan su Amina, nan da nan sai ga matan su Baffa Lawan da yaransu sun cika gidan suma.


Sai da Zakiru ya tabattar da an gama kwashe kayan an shiga da su, yayi musu sallama ya ajiye musu bandir kuɗi ya ce in ji Alhaji Ahmad.


Gaba ɗaya Mamaki ya gama kashe Amina, amma ta basar kamar bata wani damu ba.


"Ohh Amina, kalli yadda kika koma, lallai yanzu kin wuce ajin Jarmai, birni ya karɓeki" Cewar Amaryar Kawu Bala.


Suka yi ta yaba Amina, suna son jin ƙwaƙwaf, ance musu gidan da Baba yake aiki a nan Amina ma take yi, amma shi tun da yake bai taɓa zuwa da wanan kayan ba, kuma ba a taɓa kawoshi a irin wannan mota ba sai Amina. Suna ta son su tanbaya suyi tsegumi, amma Amina ta haɗe rai ta haye Gadon Inno tana latsa wayarta, dan ba zata manta wulaƙanci da rashin mutuncin da suka dinga mata ba a baya.




Gaba ɗaya Fadila ji daɗin reaction ɗin da Yazid yayi ba, ji tayi gaba ɗaya bata son zaman makarantar, dan haka ta ɗauki motarta ta wuce gida.




Zuwa azahar sai ga su Baffa Lawan, an je har Gona an sanar da su, ga Amina can an kawota a wata ƙatuwar mota daga birni.
Basu ƙara tsinkewa da lamarin ba, sai da suka ɓangaren su Amina, suka tarar da uban kayan Abinci fal tsakar gida, cikin ɗaki kuma kayan sawa ne da kayan ciye-ciyen da Daddy ya saiwa Amina.


"Ke ina Aminar take, wanann kayan kuma na menene?" Cewar Baffa lawan yana shafa buhun shinkafa.


Inno ta ce "Bismillah Baffa ku shigo"


"Ba zamu shigo ɗin ba, ina Hassan ɗin ma tukuna?"
Inno ta fito tare da faɗin "Ai ita kaɗai ta dawo ban da shi, shi ya zazzo a 'yan kwanakin nan"


Bala ya ce "Ina Aminar ne?"


"Tana ɗaki"


"Eh lallai, rashin tarbiyyar ta ta har ta kai ta kasa fitowa ta gaishe mu?"


Inno ta ce "A'a ba haka bane ba, ke Amina fito mana" banda Inno ta saka baki babu abin da zai sanya Amina ta fito.


Gaba ɗaya suka bi ƙofar ɗakin Inno da kallo, Amina ta yi ƙiba, fatarta ta ƙara haske.


"Ina wuninku"


Kawu Bala ya riƙe baki ya ce "Ba shakka, yanzu dama irin wannan rayuwar Hassan ya zaɓi kiyi, shi ya sanya ya tattaraki ya kai ki birni? Ko in ce kuka haɗa baki kika gudu, yawon ta zubar ai shikenan gaki ga duniyar nan, kin ƙi sunnar ma'aiki kin shiga duniya bin yaran yahudawa"


"Kawu Bala, Tazubar kuma?"


"Eh yawon ta zubar mana, idan ba haka ba wani irin aiki ne kike yi haka da kika samo wannan kayan, tun da uban naki yake aikin a birni ya taɓa zuwa da makamancin haka ne?"


Ran Amina yayi bala'in ɓaci, kawai ta tashi ta bar musu tsakar gidan, dan idan ta cigaba da zama zata iya rama cin zarafin da suke mata.


"Ka gani ko Yaya Bala, wai mu muke mata magana ta tashi ta tafi, idan ba bariki ba mai zai kawo haka?" Ita dai Inno tayi mus shiru, suka gama cin mutuncinsu suka tafi.


Inno ta koma ta samu Amina a ɗaki ta ce "Amina kiyi haƙuri, wallahi tun da kika tafi suke surutai da ƙanann maganganu"


Amina ta ce "Aikuwa sai sai suyi, dan bani da lokacinsu, na gaba ya riga yayi gaba, kuma Inno a ɗibar musu wani daga kayan Abincin nan a basu, aniyarsu ta bisu"


Da yamma Amina ta shirya, ta tafi sada zumunci wurin sauran 'yan uwa, kowa sai son ya ganta yake yi, masu ƙananan maganganu kuma suka cigaba da yi.
Su Bala kuwa da aka ɗebi kayan Abinci aka basu, lumi suka karɓe duk da suna iƙrarin kayan haram ne.


Da daddare Amina da Inno suna tare, Amina tayi musu girkin dare, suna ta hira Inno na bata labarin abubuwan da suka faru bayan tafiyarta, haka ita ma Amina ta dinga bawa Inno labarin birni makaranta da yanayin rayuwar mutanen birni.


"Gaskiya Inno an mana nisa, cigaba yana birni, in Allah ya yarda a dalilin karatun nan nawa sai garin nan ya samu cigaba na gaske"


"To Allah ya sa, amma da fari nima naso kiyi aurenki duk da ba Jarmai na ke so ki aura ba, amma yadda na ganki ɗin nan naji daɗi sosai, kin san bayan tafiyarki Jarmai mata biyu ya aura ya saka"


Amina ta ce "Allah ya rufa mini asiri, da tuni nima ina ciki"


Wayar Amina ce ta fara vibrating tana kawo haske, ganin sunan Daddy ya sanya ta kalli Inno ta ce "Ina zuwa"


Ta miƙe ta bar ɗakin ta koma wani, ta zauna sannan ta amsa wayar tare da yin sallama.


Sai da yayi ajiyar zuciya sannan ya amsa ya ɗora da cewa "Da ba zaki ɗaga bane?"


"Wace ni in ƙi ɗaga wayarka, ina tare da Inno ne ina cin abinci"


"Ok, nayi zaton kin yi bacci ai"


"Ai dare bai yi ba sosai"


Daddy ya gyara kwanciyarsa Sannan ya ɗora da cewar "Ina fatan kin ci kin ƙoshi"


"Na ƙoshi sosai ma, gani ga Inno muka ci fa, nayi kewarta sosai"


Yayi murmushi ya ce "That's good, ni kuma na kasa cin Abincin"


Ɗan waro idonta tayi ta ce "Me yasa?"


"Ba a bani wanda nake so ba, fruit kawai naci na kwanta"


Cikin damuwa da tausayawa Amina ta ce "Meyasa baka sa an dafa maka wanda kake so ba? Kar ka kwana da yunwa fa"


Ya shafi cikinsa ya ce "Abincin ne bana jin daɗinsa idan bana ki ba, na san da kina nan zaki dafa mini abin da nake so"


"Kar ka kwana da yunwa kaji Daddy, dan Allah ka ci wani abu"


"To me zanci, kar ki damu zan kwana haka ba wata damuwa"


Noƙe kafaɗa tayi ta ce "Ni ban yarda ba"


Dariya yayi ya ce "Rigima ko?"


"Allah da ina gida da komai dare saina dafa maka Abinci, me zai sa a bar mai nemowa ya kwana da yunwa, rashin kyautawar yayi yawa"


Har cikin ransa yaji daɗin abin da ta faɗa, na nuna damuwa da shi sosai.


"Ai nace karki damu, na ƙoshi na sha fruit sosai da cock"


"Cock kuma?" Ta faɗa da ɗan ƙarfi.


"Eh Cock" ya bata amsa.


"Daddy ba a hanaka sha ba?"


"To ya zan yi idan ban sha ba?"


"Daddy baka kiyaye lafiyarka sai wani abu ya sameka, daga tafiyata ka cigaba da ciye-ciye ko"


Sosai ta bashi dariya ya ce "Da wasa nake yi, ban sha ba"


"Har naji daɗi na zata ka sha"


"Mhmm ban sha ba Meenali"


Amina ta ɗan numfasa ta ce "Daddy"


"Mmm"


Ta ɗan tura baki ta ce "Ka amsa mana"


"Na amsa ai" yayi maganar yana murmushi.


Ta ce "Kace Na'am Meenali"


Dariya yayi ya ce "Kina son sunan kenan?"


"Eh mana, idan ka faɗa sai in jini kamar wata irin babbar 'yar gayun nan, nan kuwa 'yar ƙauye ce"


Ba ƙaramin dariya ta bawa Daddyn ba, "Allah ya shirya mini ke"


Ta sake nutsuwa ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login