Showing 54001 words to 57000 words out of 133143 words
kar kayi amfani da damar ka taimakeni ka turasasa mini yin abin da bani da ra'ayi a kansa, dan Allah ka ƙyaleni".
"Hafsa ba kya tausayina ko? Kin san so kuwa? Saboda ke fa na baro aikina na taho, kawai dan na ganki, meyasa ba zaki dubeni ba. Ko ina da wani aibu ne ban sani ba?".
"A'a, baka da wani aibu ni dai kawai ka rabu da ni".
"Shikenan tunda haka kike so, jibi in Allah ya kaimu zan koma, zan zo muyi sallama, ina sonki sosai Hafsat.
Kalmar ina sonki, ta daki Hafsa sosai, dan har cikin kwayarta taji tasirin kalmar, amma ba ta jin zata iya yadda da soyayya balle tayi aure, gara su cigaba da lallaɓa rayuwa ita da Mama.
Khalil bai taɓa zaton akwai ranar da zata zo, ya dinga 'yar talakawa kamar Hafsa yana neman soyayyarta tana gara shi ba.
Aminatun Baba Hassan kuwa, ta ƙara kilewa sosai da sosai, tayi sababbin ƙawaye, gashi nan da nan ta zama sananniya a makarantar saboda ƙoƙarinta da kuma surutunta, suna ta shirye shiryen fara jarrabawar zango na farko.
Amina ta mayar da hankali wurin tattalin haddar Alqur'aninta bata zube ba, dan tana yawan tilawa kuma ta cigaba da rubutun alƙur'ani tana sake gyara kura kuranta,ta ɗora haddarta tana samun masu duba mata a makarantar.
Hajara ce a sashen Mummy, tana ta aikace aikace, Hajiya Zainab ta fito ta tarar da ita a falonta, ta kalli Hajara ta ce "kira mini 'yar mai gadin nan" Hajara ta ce to, ta tafi kitchen ta kirawo Amina. Suka dawo tare. Hajiya Zainab ta kalli Amina ta ce "Muje sashen maigidan na nake so a gyara a yiwa kwalema, gobe in Allah ya kaimu zai dawo".
Amina ta ce "To, amma na ɗora girkin rana".
"Bar shi ita ta ƙarsa, muje in buɗe miki wurin" Amina tabi bayan Hajiya Zainab, zuwa sashen da take kyautata zaton shi ne na Alhaji Ahmad.
Masha Allah, yafi ko ina kyau da tsaruwa a gidan, duk ya yi ƙura amma hakan bai hana sashin yin kyau ba, duba da kayan alatun da aka ƙawata wurin da shi.
"Gashi nan, ki gyara duk abin da yakamata, karki mink rawar kai ko kiyi abin da ban saki ba, ki gama aikin da na saki ki fito".
Amina ta ce "To insha Allah".
Bedroom kawai guda biyu ne a sashen, kowanne ya sha furnitures na alfarma. Falon kawai gari ne guda, dan set ɗin kujeru biyu ne a falon.
Amina mamaki ta dinga yi, duk wannan aljannar duniya, amma ace mutum sai ya bar gida har wurin watanni uku ba nan, yana wata uwa duniya ta daban.
Amina haka ta dinga tular uban aiki, da tana ganin kamar aikin babu yawa, amma da ta fara taga aikin nayi ne, haka ta zage, wanke wannan goge wancan, karkaɗe can haka ta kusa wuni tana fama, sai dai idan za tayi salla ta ajiye aikin taje tayi.
Sai da ko ina ya zama tsaf ta gyara, sannan ta koma da baya, tana ƙarewa ko ina kallo, ta tabbatar komai ya gyaru tsaf, hankalinta ya sauka a kan katafariyar plsma tv wadda ta kusa cin rabin bango, tunani ta fara yi a ranta, ko a cikin wannan tv mutane sunfi girma a kan sauran ƙanan tv. Take zuciyarta ta raya mata ta kunna taga ya zata ga mutanen cikin.
Aikuwa Amina ta ƙarasa, ta kunna Tv da fari sai da ta rage yadda ta ware idanunta, saboda hasake da kuma yadda taga mutane sun bayyana a tv, kamar ta zura hannu ta ɗauko su.
A hankali ta buɗe idon, ta cigaba da kallon mutanen tv, shaf ta manta da a ina take, ta samu wuri ta zauna a kan kujera, tana cigaba da kallon Tv.
Sai ga Amina ta bararraje ta shantake, ta cigaba da kallo abinta hankali kwance.
"Ke ubawa ya baki izinin zama a kan kujerar nan? Lallai ne gidan ubanki ne nan ɗin?" A tsorace Amina ta waiwaya ta kalli in da Hajiya Zainab ke tsaye tana nunata da yatsa. Da sauri Amina ta tashi tsaye, tana rarraba ido.
"Waye ya ce ki zauna a falon mijina, har ki harɗe ƙafa kina kallo, nawa ne a ciki kuɗin babanki da aka haɗa aka gina ɗakin aka zuba furnitures ɗin?" Babu babban abin da ke ƙular da Amina irin da tayi laifi, sai a fara ambaton Baba ana ci masa zarafi.
Amina tayi shiru tare da sunkunyar da kai, tana jin yadda sautin maganganun Hajiya Zainab ke amsa kuwwa a cikin kunnuwanta, suna sukar zuciyarta.
Maganganun Baba ta tuna, da yake nanata mata ba yau ba gobe a kan tayi haƙuri, dan ta samu ta kammala karatun ta lafiya, hakan ya saka nutsuwa da haƙuri ya shigeta, a sanyaye ta ce "Dan Allah kiyi haƙuri, insha Allah ba zan sake ba".
"Ki ma sake, munafuka sai kin yi rashin mutunci ki koma kina wani kwantar da kai, ni zan fita Yanzu, ki zo ki wuce ki bar sashen nan, idan na fita daga ke sai halinki a gidan, idan kin ga dama, ki kuma aikata wani rashin mutuncin, sai kin koma in da ki ka fito" Amina dai ba tace uffan ba, sumi-sumi ta bar falon, ƙasan zuciyarta kamar ta ƙundumawa Hajiya Zainab ashariya, dan ɓacin rai.
Ɗakinta ta koma kawai ta fashe da kuka, dan ta samu sassauci daga zafin da maganganun Hajiya Zainab ke mata a zuciyarta, gaba ɗaya zaman gidan ya sire mata, sai da tayi ta gaji, sannan ta wanke fuskarta ta fito, tana fitowa babban falon gidan ta ci karo da wasu manyan mata, kai da ka gansu kaga gogaggun 'yan duniya, sun sha ado sai baza ƙamshi suke.
Ɗaya ta kalli Amina ta ce "Ashe da mutane a gidan, muke ta kwaɗa sallama amma shiru".
Amina ta ce "Eh da mutane, amma masu gidan basa nan".
"Tayi nisa ne?" Suka tambayeta.
Amina ta ce "Ai da yake ni ɗin ba 'yar ta bace, balle in san in da ta tafi, bata gaya mini ba sai dai ku kirata a waya"
"Ikon Allah, ke baki iya magana bane?"
Amina tai shiru ba tace komai ba, suka sami wuri a kan kujera suka zauna, Amina ta kalli ƙafar ɗaya daga cikin su, fuskarta fara tas ta sha mai, amma ƙafarta kamar ta ƙone ga ƙafar ta ta kamar ta maza, ga taƙi ɗaukar bleaching ɗin.
A zuciyarta ta ce "Ikon Allah, wata ƙatuwar ƙafa kamar ta Jarmai".
"Ke ɗan bamu ruwa, ƙishirwa ta dameni".
Amina ta koma ciki ta ɗoro pure water biyu a plate ta kawo ta ajiye musu.
"Hajiya Sarah, yau nake ganin ikon Allah, wace irin 'yar aiki Zainab ta samo haka bagidajiya, ke mun miki kama da wanda zasu sha wannan ruwan? Babu na roba?".
"Ai gidan nan baƙi ba su da hurumin shan ruwan roba, na leda kawai aka ce in bayar guda ɗaya" tayi maganar tana ɗan hura hanci, alama matan sun fara takurata.
Nan suka cigaba da hirarsu da 'yan zage-zagensu, Amina kuwa ta bar musu falon. Kusan Mintuna talatin Amina ta kuma fitowa da niyyar idan sun tafi, ta gyara falon amma ta tarar da su basu da niyyar tafiya, sai ma ƙure tv da suka yi suna kallo.
Ba tunanin komai ta wuce ta kashe socket ɗin tv gaba ɗaya.
"Ke lafiya, meye haka?" Cewar Hajiya Turai.
"Ai ba wuta solar ce, kuma ta fara ƙara a kowane lokaci zata iya ɗaukewa, mai siyo fetur kuma baya nan, dan haka idan ta ɗauke ni za a saka zuwa sayen fetur ni ba namiji ba, kinga ai gara in kashe ai reserving solar".
"Ke wai ke meye matsayinki a gidan nan ne?".
" 'yar aiki" ta faɗa kanta tsaye.
"Kin san mu suwaye da kike mana wannan iskancin?".
"A'a Anty, ba laifina bane dokar matar gidance a haka".
Hajiya Sarah ta ce "To bari Zainab ɗin ta dawo muji daga bakinta"
Komawa kitchen Amina tayi, a ranta tana ƙunƙuni.
Sai daf da magariba sannan Hajiya Zainab ta dawo gidan, ko da ta shigo falo ta tarar da su Hajiya Turai, suka sanya wata uwar shewa.
"Hajiya Turai yaushe ki ka shigo ƙasar nan?"
Hajiya Zainab tayi maganar tana ƙoƙarin zama, cike da mamakin da ya mamaye fuskarta.
Turai ta ce "Sati na ɗaya, nace bari nayi miki zuwan bazata".
"Amma Sarah meyasa baku gaya mini zaku zo ba? Ai da ban fita ba. Hajiya Turai mutanen Saudiyya" Nan suka ɓarke da hirar yaushe gamo.
"Kun ci abinci kuwa?".
"Wane Abinci, ke dai a garin yayime yayimenki sai kin yayi mo mai zane ki, wata tsigalalliyar yarinya muka tarar marar mutunci, ko ruwa hanamu tayi sai pure water ta bamu".
Hajiya Zainab ta ce "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, wannan Yarinyar ta zame mini jaraba, tun da tazo gidan nan nake fama da ita".
"To ki sallameta mana" Hajiya Sarah ta faɗa tana yatsuna fuska.
"Yarinyar ce tunda nake masu aiki, ban taɓa samun 'yar aiki mara son jiki kamarta ba, ba ta jin jikinta wurin aiki, ba ta da ƙyuya ba munafunci, sai iya shege da rashin mutunci a cikinta. Sai naji kamar in koreta amma sai in tuna irin aikin da take mini in ƙyaleta".
"Ai irin haka warning zaki kasa mata, koma ki bata suspension, Yarinyar bata da kunya sam".
Rai a ɓace Hajiya Zainab ta dinga ƙwalawa Amina kira, ita sam Amina ma bata san ta dawo ba, ƙasa-ƙasa take jiyo kiran, ta fito falon tana sussunkuyar da kai kamar mara gaskiya.
"Ke shine nayi baƙi kika wulaƙanta su, ki ka basu ruwan leda dan baki da mutunci?"
"Hajiya kefa kika ce kar in sake bawa duk wani baƙo ruwan roba balle Abinci sai pure water, shiyasa na basu".
"Kuma dan baki da hankali wannan sun miki kam da waɗancan ne? Ƙawayena ne wannan tun na ƙuruciya saboda baki da mutunci sai ki wulaƙanta su? Ke nifa na gaji da wannan iskancin naki, bari shi me gidan ya dawo, ki koma ƙauye ki cigaba da shan baƙar kuka. Kin zo birni kin sha miya zaki miƙe ƙafa kina mini iskanci" ta sunkuyar da kai tayi shiru ba ta ce uffan ba, suka haɗu su uku suka mata wankin babban bargo.
Tun abin na damun Amina, ta fara daina jin komai, ta fuskanci kamar ɗabi'a ce ta masu kuɗi, wulaƙanta wanda suke ƙarƙashin su, suka ƙare mata zagi da cin mutunci tsaf, sannan suka sallameta. Harabar gidan ta koma, tayi zamanta ya yin da Baba yake bakin gate yana aikinsa.
Abdul da Khalil ne zaune a ɗakin Abdul, Khalil ya zuba uban tagumi.
Abdul ya ce "Wai kai Khalil meye haka ne? Sai ka sanya damuwa a ranka ka kasa sukuni?".
"Abdul ba zaka gane bane, ni kaina ban taɓa zaton abubuwa zasu cakuɗe mini haka ba. Baka san yadda nake jin yarinyar nan a raina ba, amma naga tana da taurin kai, babu alamar zan sameta na karaya Abdul".
"Haba Khalil, kar ka karaya, ka san meye matsalarka? Garaje da gaggawa idan kabi komai a sannu zai zo maka a sauƙaƙe, yanzu kana jin abin da nake ji game da ƙanwarka ko? Hmm haka al'amarin so yake, na san babban yaro kamarka da mata ke rushing a kansa, abin mamaki ne ace ya maƙalewa 'yar talakawa kamar wannan, amma haka sha'anin so yake. A yanayin Hafsa kamar akwai wani ɓoyayyen abu da yake damunta a zuciyarta, dan haka domin shawo kanta, sai ka rage shishige mata, da cigaba da nuna mata soyayya, ka danne son kawai ka nemi ku saba da ita. Ka dinga kyautata mata da kulawa ka fara gano meye matsalarta kan ka cigaba da nuna mata soyayya".
Khalil ya ɗan yi shiru sannn ya ce "Kana ganin hakan mafita ne?.
"Ita ce babbar mafita, tunda soyayyar ce ba ta so, to ka bar shi a friendship ka gama fuskantar ta tukuna".
"Shikenan, zan jarraba hakan, insha Allah gobe in Allah ya kaimu zan koma wurin aiki, zan jarraba shawarar taka".
"Wai da gaske ba zaka gida ba?"
"Abdul idan naje Mummy tuhumata za tayi a kan dalilin dawowata, ba sai naje ba, sai nan da kamar 3weeks zan kuma dawowa insha Allah"
"To shikenan, Allah ya kaimu sannan ya daidaita ku".
Yau sai shida na yamma suka kammala jarrabawar yau, kanta har wani juyawa yake yi saboda ta gaji yau sosai da sosai, da ƙyar take iya ɗaga ƙafafuwanta, saboda zaman ajin. Jarrabawowin yau Alhamdilillah tayi abin Arziƙi da kanta, dan tayi karatu sosai da sosai.
"Hmmm Madam, glucose yayi ƙasa ne naga kina tafiya da ƙyar?" Cak ta tsaya tana ɗan sauke numfashi, ta waiwayo ta sauke masa gajiyayyun idanuwanta da suka ɗan yi ja saboda gajiya.
"Yau ko nemana ba ayi, tun shekaranjiya ko kallon in da nake ba balle a harareni. Amma ina fatan kin gama komai dai ko?".
"Ban gama ba, jira nake kazo ka ƙarasa mini"
Sauke facemask ɗinsa ya yi ya ce "Me kika ce?".
"Ban sani ba" ta faɗa ba tare da ta kalleshi ba.
"Kalleni ki faɗa mana idan ba tsoro ba" ɗagowa tayi ta kalli Yazeed, sai dai tayi saurin janye idonta daga nasa.
"Dan Allah ka rabu dani".
"Muje in rakaki wurin motar".
"Ina da ƙafa ai" ta faɗa tana cigaba da tafiya sannu a hankali.
"Ai ƙafar taki ce kamar ta gaji, da ƙyar kike tafiya, ko in ɗauke ki in kai ki motar ne?" Ɗagowa tayi ta kalleshi ta mayar da hankali a kan tafiyarta.
Yusra ce ta tunkaro in da suke tana murmushi, ta kalli Yazeed ta ce "Patient ɗinmu, kai ne ka warware haka?"
Yazeed ya yi murmushi ya ce "Alhamdilillah, jiki ya ware".
"Haka ake fata dama, madam zuwa nayi mu tafi gida tare, yau ba mota a hannuna".
Fadila ta ce "Gaskiya a gajiye nake gida zan tafi sai dai in ajiye ki a hanya".
"Aikuwa baki isa ba, nima a gajiyen nake, ka sa baki ta kaini gida mana" Yusra tayi maganar tana kallon Yazeed.
Yazeed ya ce "Wane ni, ku gaida gida".
"A'a ka tsaya, saita ɗaukemu wallahi, muje ko rage maka hanya muyi".
"A'a ba zan hau ba, Allah ya kai ku lafiya".
Yusra ta ce "Dan Allah ka zo muje, ko a hanya mu ajiye ka".
"A'a ni ba zan hau ba, wa zai hau motarta, ko tuƙinma bata iya ba, ta watsar da mu a hanya, ku sauka lafiya" kallon Yazeed tayi, tama rasa me za ta ce masa.
Fadila na ƙoƙarin kunna mota ne, Yusra ta ce "Wallahi Fadila kun dace da gayen nan, anya ba sonki yake ba?"
"Amma baki da hankali ko? Ke na miki kalar sa, karki ɓata mini rai".
"Wallahi Fadila ni tausayi yake bani gaba ɗayansa, Wallahi kamar sonki yake"
Fadila ta haɗe rai ta ce "Yusra bana so, karki sake haɗani da shi"
"Ai shikenan, bari mu zuba ido mu sha kallo".
Wani irin horn Fadila take yi a ƙofar gidan tamkar zata daki gini idan ba a buɗe ba, Baba kuma ya shiga banɗaki a lokacin, ba tare da ya kammala abin da yake ba, ya fito bagatatan ya buɗe mata gate ɗin, ai ko kashe motar ba tayi ba, ta fito ta hau Baba da bala'i ta in da ta shiga bata nan take fita ba, ya risuna ya dinga bata haƙuri.
Haka ta nufi cikin gida fuuu kamar guguwa, ba ta tsaya ta saurari Mummy tana da baƙi ba ta hau bala'i a falon "Gaskiya Mummy ku sallami wannan tsohon, haba ai ko aikin gwamnati ne ha kai yayi retire mutum sai bai san aikinsa ba, ya bar mutane a waje ina ta faman horn sai kace wani kurma, gaskiya na gaji a sallame shi. Ga securites nan na kamfani Daddy ya ɗauko amma ya dage a kan wannan baƙauyen, mara kuzari, saura kaɗan in zage shi yau". Jikin Amina ne ya ɗau rawa, ta kalli Fadila ta ce "Baban nawa zaki zaga?".
DOMIN GYARA SHARHI KO SHAWARA
08081012143
READ THE CHAPTER 16 OF GABA DA GABANTA AT AREWABOOKS
https://arewabooks.com/chapter?id=638b441e942c7e82ce7bfb71
GABA DA GABANTA
AISHA ADAM (AYSHERCOOL)
To get the latest update of the story
Follow me on Watpad
Ayshercool 7724
Arewabooks
Ayshercool 7724
What's app 08081012143
P16
"Eh, shi zan zaga ko akwai abin da zaki iya yi a kai?" Fadila tayi maganar cikin isa da iko.
Maganganun Baba ne suka dawowa Amina a cikin kunnuwanta, tabbas idan ta ɗau mataki, ta san dole ta koma ƙauye, kuma babu abin da zai hana aurenta da Jarmai, jikinta na rawa hawaye na zuba daga idanunta, ta juya ta koma jikinta a sanyaye, Allah kar nuna mini ranar da za'a zagi Baba a gabana, ba zan iya jurewa ba.
Fadila ba ta kalli baƙin Mummy ba, ta wuce ɗakinta tana cigaba da huci kamar wata mesa.
Hajiya Turai ta ce "Wai dama 'yar mai gadinku ce?"
Mummy ta ce "Eh, 'yar sa ce".
"Lallai ne, ai gara da Fadila tayi mata hakan, yaran nan idan ana saurara musu miƙe ƙafa suke yi su yi ta iskanci kamar a gidan ubansu"
Hajiya Zainab ta ce "Wallahi kuwa, ai Fadilan ce dai-dai da su".
Fadila kuwa a gajiye ta ƙarasa ɗakinta, ta jefar da mayafinta, ta tuɓe doguwar rigar jikinta, ta shiga cikin banɗaki, ta haɗa ruwa mai ɗumi tayi wanka, ta yo alwala ta fito, sallar magariba ta gabatar ta idar, sannan ta shirya kanta cikin riga da skirt, na English wears ta fito.
Sai a wannan karon sannan ta gaida baƙin Mummy, ta wuce kitchen.
Amina ta gani a tsaye idanunta sun yi jawur, kamar ta kwana ta wuni tana kuka.
"What do you cook for dinner?" Fadila ta tambaya cikin ko in kula.
Zuciyar Amina na tafasa, tamkar ta ce mata ubanki na dafa, amma ta dann ta ce "Tuwon semovita".
"Ban ci Abincin rana ba, dan haka ba zan ci tuwo ba, ki dafa mini cous cous vagetable cou cous da irish, ki hanzarta kuma" tana gama maganar ta jiya ta fice.
Muciya Amina ta rarumo, ta ɗaga sama kamar ta bi bayan Fadila, ta sauke mata wannan dogayen kafaɗun nata, masu kama da dirakun firamaren garinsu.
Amina tana kuka tana yiwa Hajiya Zainab Allah ya isa, ta yiwa Fadila girkin nan ta kai mata, ta koma ɗakinta.
"Hafsa ni dai ina tsoron sake komawarki wurin sana'ar nan, bana son wannan yaron ya zo ya kuma ɗaga mana hankali".
"Mama idan ba wannan sana'ar ba wacce za muyi? Idan a gida nace zan cigaba da saida awarar nan, ya zama mu uku muke awara a layin nan fa, kusan duk wata sana'a da zamu yi, a na yinta a cikin unguwar nan, zama haka ba zai yiwu ba Mama".
"Haka ne, amma dama can sana'ar nan ba sonta nake ba, bana ƙaunar zaman titin nan da kike yi, ni ban san ma yadda aka yi yaron nan ya san inda