Showing 54001 words to 57000 words out of 135734 words

Chapter 19 - GARGADAN SO Book Complete Document by M. Shakur .txt

M Shakur   

23 Nov 2024

17441

hoping yana shiga yana kallon asibitin da tunda yazo duniya baitaba ganin asibiti mai kyau irinsa ba yana kara tsorata yana addu’a Allah yarufa musu asiri, Khaleel na tsaye a reception din yana waya Baba yashiga kiciniyar turo Glassdoor dakeda karfi da aka rubuta push ajiki, tsabagen yanda baida karfi kuma yarude baisan sanda karfenshi ya turgude yafita daga hannunshi ba Baba yafadi tim karafunan ma na zubewa dan takalminshi na kafa daya dayake sawa shima yafita yayi tsalle zuwa wani waje, dasauri Khaleel dake waya yadago jin kara ganin tsoho mai kafa daya yafadi hakama crutches nasa yasa dasauri yacire wayan daga kunnenshi yayi wajen kafin others suzo yarigasu yabude kofan yafita da sauri, one thing about him tun yana yaro yanada tausayin masu nakasu any disabled person have a special place a zuciyan Khaleel.
Ahankali yaduka agaban Baba yakai hannayenshi yakama kafadan Baba da jikinshi ke rawa yana ambaton Allah har lokacin sama, cikeda tausayi yace “sorry” tsayuwa yayi da kyau yana jingina da bango yana kallon fuskan Khaleel dahar ya duka yana kwasanmai crutches din yataso yabashi da sauri, ahankali yace “sorry, are you hurt anywhere”? Yashiga duba Baba yana kakkabemai gaban riganshi yasake komawa yadaukomai slippers nashi wari daya ya duka gabanshi ya ijiyemai Baba yasaka, Khaleel yasake tasowa for the first time yayi hausa ganin kaman mutumin bai gane turenci ba yace “kaji ciwo? Akwai inda kema zafi?” Girgizamai kai Baba yayi yace “thank you Allah maka albarka babu inda kemin ciwo y’ata ne dai ke ciwo” Kaman zaiyi kuka yace “kirana akai y’ata Hawwa tayi hatsari tana asibitin nan ko kasan inda ake tambaya? Ni wama yakawota nan? Bamuda kudin biyan irin wannan asibitin, Innalillahi wa Innailaihi raji’un Allah karufamini asiri” Baba yana maganan yana kalle kalle he’s just distabilize, ahankali yasa hannu yamai pushing door din, Baba yasake kallonshi yace “nagode kaji” yashiga ciki Khaleel yabishi, sannan yamai pointing dakin da Hawwa take ciki yace “kaduba wanchan dakin” dasauri Baba ya kalli Khaleel saikuma ahankali yace “nagode ko yaro ya sunanka”? Dan kyafkyafta idanu Khaleel tayi sau biyu yakai hannunshi ya shafa kanshi kaman mara gaskiya ahankali yace “Ibrahim Khaleel” ahankali Baba yace “nagode Allah maka albarka Ibrahima bari naje” gyadamai kai Khaleel yayi ahankali Baba yawuce Khaleel yabishi da kallo saikuma yawuce yafita dasauri.


Baba na kaiwa wajen dakin ya hango Hawwa kwance ga bandage a goshinta da hannunta shima ansa bandage ga ciwo a lips dinta sosai an samata drip kala uku all at once bude dakin yayi yashiga yana salati da sallallami yarike hannun Hawwa kawai saiya fashe da kuka yama kasa magana, shigowa dakin akayi wata nurse ce tace “sannu Sir kaine mahaifinta”? Dagowa Baba yayi yana share hawaye yace “eh” tace “Baba muna bukatan information nata dakuma signature” ijiyan zuciya Baba yasauke yana karban takardan gabanshi na faduwa yace “toh Allah karufamana asibiti nawane duka abubuwan nan? Nawa zamu biya?” Dan murmushi nurse din tayi tace “karka damu Baba bawan Allah daya kawota yabiya kudin komi tatas” Dasauri Baba yace “ohh Allah waye shi? Yana ina nagode mai”? Murmushi nurse din tayi tace “ai naganku tare just now kuna magana awajen kofa” baki Baba yarike yace “Ibrahima? Yanzu shine daman amman shine bai sanar dani ba kuma harda nunamin dakin, to Allah yamai albarka, Allah yarabashi da iyayenshi lpy, bari nayimai godiya sainazo na cike” yamika mata paper zai tashi dasauri tace “yatafi ai” yadai ijiye wayanta da jakanta dani, ijiyan zuciya Baba yasauke saikuma ya shiga rubutu, tass Baba yayi komi yabata tafita chan takawomai wayan Hawwa da jakanta Baba ya karba yana tofamata addu’a, Ammi tashiga kiranshi dagawa yayi Ammi na kuka sosai tace “Malam kakai wajen Hawwan yaya take”? kaman ba Baba ba yace “ya isa ya isa dena kuka gatanan dai Alhamdulillah banga likitan tukunna ba amman ance convulsion tayi a mota harta jawo hatsari wani bawan Allah yakawota asibiti yabita kudin komi” cikeda damuwa Ammi tace “Alhamdulillah Alhamdulilah nima ina hanya” Baba yace “Allah yakawoku lpy” wayanshi Baba yadauka yashiga kiran Ni’ima ya sanar da Ita kawarta tai hatsari amman baya shiga hakan yasa ya nemi number Baban Yaseer yakira ringing daya yadaga anatse yace “Baba barka da warhaka” cikeda damuwa Baba yace “Aliyu Hawwa tayi accident gatanan a asibiti rai a hannun Allah” yanda zuciyan Baban Yaseer yabuga yakusan fitowa yace “wat?! Baba Hawwa tayi hatsari!”?


[9/21, 5:34 PM] M Shakur: 💫GARGADAN SO💫




✍🏻M SHAKUR




EPISODE 3️⃣2️⃣




KUNSAN ME AKE NUFI DA INTIMACY CLASS?
CLASS NE DAYA KUNSHI KOYARDA ABUBUWAN YAKAMATA KOWACE MATAN AURE DA AMARE YAKAMATA SU SANI, TUNDAGA KAN MENENE SHI SADUWA DA IYALI, YA AKE SARRAFA MIJI A GADO, YA AKE KULA DA MIJI, YAZAKI ZAMA GWANA KIYI FINCINKAU CIKIN MATAN SA🥰
A INTIMACY CLASS BABU KALAN ABINDA BAZAKI KOYABA DAN HAKA JOIN US TODAY WITH JUST 5K SHEKARA DAYA NE CLASS DIN.
MAKESURE KINADA TELEGRAM KAFIN KIBIYA
CHAT ME UP IDAN KINASON SHIGA WANNAN CLASS MAI TARIN FA’IDA


wa.me/+2347012181461




Ni’ima na kwance adakinta dan tun rannan maganan kirki baya shiga tsakaninsu, shima Baban Yaseer ya tattarata ya ijiye a gefe dan baison wahala da hayaniya, idan yashigo dakin yazo daukan kayane, yanda ya tattarata ya watsar abin bakaramin cimata rai yakeba, duktai wani iri kaman ba itaba, batada aiki sai shan kayan matan da Mama ta aiko mata dashi sabida duk randa zasu shirya yadawo yaga chanji, tana kwance awajen taji muryan Baban Yaseer ya ambato sunnan Hawwa, mummunan faduwa gabanta yayi dasauri ta zabura tamike tsaye tasauka daga gadon tai wajen kofa tasa hannu tabude tafito tahaderai tai folding hannu a kirji tana kallonshi, daidai lokacin Baban Yaseer yana sauke wayan daga kunnenshi da bala’in damuwa yakalleta yama manta basa wani maganan kirki fada suke yace “Hawwa had an accident Wife, Innalillahi! Suna asibitin Leadway, je dauko mayafi lets quickly go, ya Allah please keep Hawwa safe for me, please please please, yi sauri wife dauko mayafi” yayi maganan duk yadamu baimasan meyake fita daga bakinshi ba, tunda Ni’ima ta ayrı Baban Yaseer bata tabajin bakin ciki kansa kaman na yanzu ba, yanda yakeyi wlh koda tana labour room zata haihu bataga kalan rudewan nan atattare dashi ba, kirjinta kaman ana sassake kitsen wajen sabida suyan dayake mata na azaba, azuciye tashigo cikin falon yana kallonta danya dauka akwai wani abu dazata dauka awajen, batai wata wata ba tasa hannu tadauki car key shi dake kan table tarike gam a hannunta, Baban Yaseer yakalleta dasauri, Ni’ima tace “we are not going” da mahaukacin damuwa akan muryan Baban Yaseer yace “me kikace?” Kallonshi tayi afadace ta matso dab dashi tana hucin kishin fitina ganin yanda baya hayyacinsa sabida kawarta tace “Hawwa ta mutu ma idan zata mutu is not my business tunda ba yar uwanmu bace ko munhada jini da ita ba, kuma bazaka ba wat is your business with her? Nagadai kawata ce ba taka ba? Kataba ganin ina shigema abokananka maza? Baruwanka da Hawwa” baki Baban Yaseer yabude zaiyi magana Ni’ima taci numfashinsa tace “Aliyu stay away from my friend! Hawwa kawata ce she has no business with you! Baruwanka da ita! Wayataba cewa dole sai miji yadauki responsibility kawar matansa? Get a hold of yourself kadaina bin kawata kuma ba zakaba!” Tun bayan abinda yafaru ranan yadan bata space cus yasan she’s not okay, amman yaudai no, damuwan daya ciki ma jin Hawwa tayi hatsari bazai taba iya tsayawa gardama da ita ba he just want to see kanshi gaban Hawwa, hannu yamika mata strictly yace “give me my car keys” faduwa gabanta yayi yanda yahade rai yana tabashi key bama ta maganganun datamai yakeba ta masoyiyarshi dake asibiti yake baidama lokacin biyemata suyi fada hakan yakara tunxurata cikeda karfin hali tace “bazan bayarba, nace bazaka je ba, uban me kahada da Hawwa? I’m tired of yanda every little thing you will be running to her rescue, rannan haka kafita tsakar dare without thinking twice Aliyu kabar ni da yaranka biyu cikin gidan nan katafi wajen wata, wat if mu wani abu yasame mu? Wat if barayi sun shigo? I’m your wife you know nikeda hakki akanka ba Hawwa ba, bakada wani business or what so ever da abokiyata, wlh bazan bada key nan ba” cikin kakkausan murya Baban Yaseer yace “this is the last time zan miki magana, hand over my car key! I don’t have time for argument ko bala’i dake, ruhina, zuciyata da kuruwata basa nan suna wajen Hawwa da gangan jikina kawai kike magana, give me the damn car key Ni’ima” yanda kalaman Aliyu ke samata bakinciki kaman ta hadiye zuciya ta mutu awajen, ita Aliyu ke gayama magana haka, jitayi koma mexai faru yafaru kaman zata haukace da bakin ciki tace “wlh saidai kome zakayi kayi bazakaje asibitin nan ba, bazakaje wajen Hawwa ba, ina matarka kana gayamin kuruwanka na wajenta da gangan jikinka nake magana” kawai tafashe da kuka mai ciwo tace “macuci, maciyi amana kawai, mayaudari, kawata zaka so har kana haukacewa akanta haka dame Hawwa tafini? Baban Yaseer kaci amanata wlh kaci amanta, Allah ya kashe Hawwa! Allah ka dauki ranta afito da gawanta daga asibitin na……n” hannu dayaga ya kaimata mari a fuska sai kuma ya tsaya chak hannun na gab da landing a fuskanta tareda sauke hannun kasa yana huci sosai jin addu’an datama Hawwa, hannunshi tabi da kallo daya dunkule da yanda yake huci tace “ni zaka mara sabida Hawwa eh Baban Yaseer? Ni matar ka? Ni Ni’ima zaka kusan daurama mari sabida kawata? Baban Yaseer ni”?.






Bai tankataba cus baiso fushi yadebeshi yayi wani abun dazaiyi nadama nan gaba, baiyi believing in hurting women ba, but harga Allah Ni’ima is pissing him off, baima fahimci this whole anger da fushi da wani tantrums nata ba akan zancen nan shi baice zai auri Hawwa ba out of goodwill bawai dan bazai iyaba no sabida kawai bayason yabata beautiful years of friendship nasu, and again bai sanar da Hawwan ba, Hawwa have no idea yana sonta so what is all this haukan da Ni’ima keyi? Hannunshi yasa yakamo nata azuciye zai karbi key din Ni’ima tashiga kokawa dashi tana kaimai duka da hannu daya tana haki. “Wlh bazan bayarba saidai ka kasheni ka amsa” murde hannunta Baban Yaseer yayi Ni’ima tai kara tace “Aliyu you’re hurting me sabida Hawwa, wannan rawan jikin da haukacewan sabida best friend dina kakeyi, Aliyu I hate you, how could you? Why will you fall in love with Hawwa? Meta fini dashi? Yarinyar datai kwnatai sabida bakin jini? Yarinyar da Babanta ke rokon mutane suzo su aureta, rawan jikin menene kakeyi dame Hawwa tafini”? Hannunta ya murde da karfi ya karbi key sannan yanunata da hannu amasifance yace “Hawwa tafikida komi! Tafiki hankali! Tafiki natsuwa! Tafiki ilimi! Tafiki kyau da iya murmushi! Tafiki kunya! Tafiki iya girki! Tafiki kwazo! Tafiki kwarjini da haiba! Daga ranan bikinmu rannan dana fara haduwa da Hawwa naji inama ita na aura bakeba! Haryau har gobe I wish inama Hawwa na fara sani not you! I wish itane matana! Hawwa will never act like this! Hawwa carry kanta with dignity! She respects kanta! She knows what she’s doing unlike ke, look at the way kike behaving kaman dakikiya! I explained something for you but brain dinki yakasa comprehending ko ascertaining duka abinda nace, bayan you forced me to speak cus kece kikaje kikamin bincike who sent you to check my phone? Kina bincikamin waya who do you think you’re? Kece ke aure na? Kinama Hawwa wishing mutuwa kawarki that did everything in her power for you! Kin dauka inda inaso na aureta bazan iyabane? Kira daya zanma Baba angama magana, I explained everything for you but still jibi yanda kikeyi? What is all this classless attitude? For wat exactly? I hate razz woman idan kika zama one I will terminate aurenmu cus ban iya ihu ko fada ba, bakina baida kyau, don’t push me, if you push me wlh wlh saina auri Hawwa kuma agidan nan zata zauna! Don’t push me to the wall Ni’imatullah!” Kadakai yayi yawuce yafita abinshi Ni’ima tafashe da kuka sosai awajen kaman ta kashe kanta yau tayi dana sanin sanin Hawwa, ita Baban Yaseer zai kira dakikiya Innalillahi, batun yau yafara son Hawwa ba?.




EPISODE 32


WOWW WOWW BABAN YASEER YAKIRA NI’IMA DAKIKIYA😫


YA KYAUTA???


WLH DA CIWO MIJINKA IS THIS CRAZY INLOVE WITH YOUR BESTY💔
[9/21, 5:34 PM] M Shakur: 💫GARGADAN SO💫




✍🏻M SHAKUR




EPISODE 3️⃣3️⃣




KUNSAN ME AKE NUFI DA INTIMACY CLASS?
CLASS NE DAYA KUNSHI KOYARDA ABUBUWAN YAKAMATA KOWACE MATAN AURE DA AMARE YAKAMATA SU SANI, TUNDAGA KAN MENENE SHI SADUWA DA IYALI, YA AKE SARRAFA MIJI A GADO, YA AKE KULA DA MIJI, YAZAKI ZAMA GWANA KIYI FINCINKAU CIKIN MATAN SA🥰
A INTIMACY CLASS BABU KALAN ABINDA BAZAKI KOYABA DAN HAKA JOIN US TODAY WITH JUST 5K SHEKARA DAYA NE CLASS DIN.
MAKESURE KINADA TELEGRAM KAFIN KIBIYA
CHAT ME UP IDAN KINASON SHIGA WANNAN CLASS MAI TARIN FA’IDA


wa.me/+2347012181461




Khaleel na zaune a premises na asibitin kan wani hadadden kujera dake under wani shade na flowers yana jiran suzo su daukeshi dan sunce sun kusa akwai traffic a hanyan school na Noor sabida accident din nan, kuma hakanan baiso yakoma ciki sabida Baba tunda yagane Baban Hawwa ne yakejin nauyinsa hakanan, motan Baban Yaseer daya danno kai cikin hospital din Khaleel yabi da kallo, wanda kallo daya yama motan yagane motan sabida plate number shi kanshi baisan how come ba but yatuna rannan yakalli plate number motan kuma yazauna akanshi baimasan me dalilin da plate number wani random mutum zai zauna akansa without permission ba, haderai yayi tamau yabi motan da kallo, parking Baban Yaseer yayi nesada inda Khaleel yake zaune yakashe motan yafito yana sanye da riga da wando na shadda mai ruwan goro dayamai kyau, yakafa hula akanshi, haskenshi yafito bau ga bakin glass akan idanunshi, zagawa yayi zuwa bayan motan yabude yafito da manya manyan ledojin for you supermarket yayi shopping yarufe motan yawuce yana tafiya anatse, abu Khaleel yaji ya tsayamai a wuya sai kawai yatashi da hannu yakira security asibitin yazo da gudu yace “Yallabai gani” cikeda isa yanuna Baban Yaseer yace “seize ledojin da mutumin chan yazo dasu” dasauri security yakalli Baban Yaseer saikuma yakalli Khaleel daya haderai sosai yadan rage murya yace “Oga mezan gayamai? I can’t seize abinshi” ihu Khaleel yamai ranshi abace yace “tell him we give our patients food, we don’t accept akawo musu anything daga waje it’s a law daga yanzu go!” Khaleel yafadi aharzuke security yajuya yatafi da sauri shikuma ya tsaya awajen yana kallonsu dudda baiji meyake fadiba but dan bacin rai daya gani akan fuskan Baban Yaseer yamai dadi dan murmushi yayi yana tsaye awajen saiga Baban Yaseer yajuyo, dauke kai Khaleel yayi abinshi haushin sa yakeji kawai yaciro waya ma abinshi, haka Baban Yaseer yabude mota yadawo da komi ya ijiye sannan yawuce Khaleel yajuyo ya watsamai kallo mara kyau daidai motanshi na shigowa wucewa kawai yayi yashiga ya zauna sukabar hospital din sai alokacin hannunshi yafaramai zafi ya kalli hannun, dan tsaki yayi ya yarfe hannun yadan kishingida da kujera bacci yakeji sosai, yau kwata kwata bai sami baccin da ranshi keso ba.


Gida suka wuce ana parking yafito yayi flat dinsu yabude kofa Momy yagani zaune tareda Momy Sam matar kanin Excellency wacce take baturiyan bahaushiya, mahaifiyar ta yar Nigeria ce yar kano bature ta aura ta haifesu saisa duk sukai kaman da baturen but hausa rass abakinsu, suna magana yashigo wajen Mommy yawuce ashagwabe yazauna kusada ita babu batun gaidasu yamika mata hannunshi kaman dan yaro yace “Moma zafi” duk randa shagwaban shi yatashi Moma yake kiran Mommy, dasauri Momy tace “Subhanallahi, Khaleely tayaya kaji ciwo haka? Menene amfanin guards dinka dazasu barka kaji ciwo haka? Why are they getting paid”? Afusace Mommy Sam dan duk jirgi daya ya kwasosu tace “fire them they don’t know their job, Khaleely ne zai kulada da kanshi? They’re very useless, Sorry Son” tai maganan tana kallon Khaleel dake abu kaman yaro yana kallon ciwon dakemai zafi, duk Mommy tarude ta tashi da sauri ta dauko first aid kit tazauna kusadashi spirit tadauka da sauri tana gutsuran auduga tasa aciki takai zatasa a hannun wlh kaman dan yaro, kaman Noor karama ya fizge hannun yace “Momy ni banson spirit zafi yakeyi” kaman Mom zata fashe da kuka dukta susuce tace “yakuri ka daure nasa maka kaji Khaleely, wai yama akayi kaji ciwo eh? All this workers namu sunsan babu abinda na tsana irin naga mistakenly kaji ciwo? Ya akayi kaji ciwo haka”? Turo baki yayi batare dayayi magana ba, Mom Sam ta taso itama tazo wajen tadafa kadanshi tace “muga hannun” nunamata hannun yayi ahankali cikeda dabara tace “toka daure give your Mom to treat it kaga yanda ta damu” kallon Mom yayi datai kaman zatai kuka kaman wani babban abine ya sameshi tsabagen yanda take sonshi, ahankali yace “small zakisa Mom” dasauri tace “eh naji, kadan zan sama” bata hannun yayi tasa kadan Khaleel yayi ihuu zokaga yanda suke lallashin sa ohh ikon Allah kaman kwai, sannan tashafa healing balm yamike ahankali, Mom tace “zokai breakfast” ahankali yace “I want to sleep I’m sleepy Mom” bangarenshi yayi Mom ta kwalama PA kira, dasauri PA tazo tana sanye da suit baki, Mom tace “cikin 3 girls din nan dasuka rage akaimai daya” Gyadamata kai tayi PA tayi tace “yes Ma” tajuya itakuma Mom suka cigaba da hira, fitowa PA tayi da Zainab dasai murna take cus bata dauka zai kara nemanta nabiyu ba aka kaita side nashi har zuwa sama, knocking PA tayi gaban dakinshi shiru hakan yasa tabude kofa takalli zainab tace “shiga” shiga ciki Zainab tayi itakuma PA tawuce.


Fitowa Khaleel yayi daga wanka daure da towel a waist ruwa na bin chest nashi yakalli Zainab dake tsakiyan dakin tsaye, suna hada ido ta sauke kanta kasa dasauri jikinta har bari yake sabida dadi, awulakance yadauke kai wucewa closet yayi dan yaji sanda ake knocking bai wani jimaba yafito sanye da boxer yana kamshi yagaji bacci kawai yakeso fadawa gado yayi yana sauke ijiyan zuciya yana kallon sama hakanan kawai deep down he’s wishing ta farka

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login