Showing 51001 words to 54000 words out of 135734 words
Chapter 18 - GARGADAN SO Book Complete Document by M. Shakur .txt
kalli Hawwa tace “sabida Ni’ima kikazo ko?” Gyadamata kai Hawwa tayi, Mama tasauke ijiyan zuciya tace “Hawwa dagake har Ni’ima ba yara bane, tariga ta sanar dani komi dake faruwa, she’s just trying to protect her home so I think is best idan kinyi respecting decision nata and give her space datake so, idan tanaso kudawo da kawancen zata nemeki, don’t blame her rayuwa yazama abin tsoro, sai ana sara ana duban bakin gatari fa, kibarta and move on ba dole Hawwa, tunda abu yakai ga haka kifita daga rayuwanta kinji” sosai Hawwa ke kallon Mama dake maganan irin ko ajikinta dinnan, wani iri Hawwa taji hawaye na taruwaa idanunta, Mama tace “kidena nacin nan dan Allah antaba kawance dole? Yo amintan dole ne? Idan kuma kin nace sai kinyi to kema Hawwa ki yarda da mijin da Baba yamiki mana Malam Kabiru kiyi auren kowama yahuta kinayi nasan Ni’ima zata dawo gareki, kinji kiyi tunani akan abinda na fadamiki” Hawwa takarayin shiru zaune awajen akasan simenti, Mama tace “tashi to kitafi” ko motsi Hawwa takasa yi, Mama ta tabe baki tace “Allah kyauta, tashi kije dan Allah nima kada ki sake zuwan gida, wacce ta hadamu tace batayi, kowa nasa yasani aduniyan nan ba’a kuma dole, just don’t take it personal, Ni’ima is protecting her space ibada take, a musulunce miji yafi kawa sau dubu ko nine mijina zan zaba bawata kawaba ana zaune lafiya, yanda kikeda wayau da ilimin nan ko kece a situation din Ni’ima haka zakiyi wlh put yourself in her shoe, y’ata ta samu gidan hutu yo idan kawa zata mata summun bukumun basai aja mata layi ba kowa yayi takansa? Kingani saida safe bari nahadama Malam abincin dare” tawuce kitchen abinta, Hawwa kawai tafashe da kuka da kyar ta dafa bango ta mike bayanta har yanzu ciwo yakemata fita tayi ta shiga motanta, taja ahankali tabar unguwan takoma gida.
Baba bayanan but tana shiga dakinta taga ya ijiye mata kula zama tayi ahankali tabude kulan kaza ce ta soyu ansaka kulikuli da yaji gasu cabbage, tana ganin girkin tasan Baba yadafa mata dama yace dayana saurayi yayi sana’an balangu da su gasassun kaji, hannu takai ahankali tadauki daya takai bakinta daidai nan Baba yayi sallama ya shigo yana rikeda leda ganinta zaune gaban kulan yasa yayi murmushi yace “yauwa Hawwa gashinan naje bakin hanya na sayomiki chivita na grape mai sanyi, ranan nan na dandanashi yamin dadi zakiso shi”
Yazo yazauna kusada ita yana ijiye karafunan a gefe lumshe idanu Hawwa tayi jin Baba ya zauna kusada ita tabude su tana ganin yanda duk yadamu yana bude mata juice din, this is the first time takejinta so vulnerable she’s tired of being a strong girl, komima na duniya yamata ahankali tadaura kanta jikin hannun Baba gently tasaka hannunta takama hannunshi ta kankame sosai a kirjinta tafashe da kuka mai tsuma zuciya, bala’in tashi hankalin Baba yayi dasauri yajuyo yace “Hawwa, ke, Hawwana? Me akamiki mesa kike kuka haka? Hawwa” sheshekan kuka take jikinta har rawa yake tarike Baba sosai takasa magana dasauri Baba yadago kanta saikuma yajuyo da kyau idanunshi sunyi jaa yace “zonan Hawwa zo” yajawota yasata a kirjinshi tai hugging Baba so tight this is abinda bata tabayiba hugging Baba saidai maybe datana yarinya, bayanta Baba yashiga bubbugawa yace “ya isa Hawwa ya isa, zakisa hankalina yatashi, koma menene ke damunki baifi karfin Allah ba, ya isa Jiddalo na, ya isa, yi shiru yi hakuri kinji, kinada matsala awajen aikinki ne?” Girgixamai kai tayi alamun a’a tana tsagaita kukan tana sauke ijiyan zuciya ba kakkautawa a kirjin Baba, ahankali yace “to menene ke damunki”? Murya chan kasa tace “Baba aure nakeso nayi nagaji da yanda kowa keyi dani sabida banyi aureba” ahankali Baba na buga bayanta yace “karki damu zaki aure, anmini kwatancen wani Malami na Islamic chemist ranan asabar tunda ba aiki zan kaiki muje muji ko aljanu gareki dake hanaki aure, kokice baki sonsu kosu sugudu zamuji dalili kidena damun kanki namiki alkawari bazan kara takura miki ba, lafiyanki yafi komi mahimmanci agareni Hawwa na, kiyakuri kinji yarinyana yar albarka kiyakuri da rayuwa, komi tsari ne na ubangiji kizama mai juriya da hakuri akwai Allah Hauwa’u kinji” gyadamai kai Hawwa tayi, Baba yayi shiru chan yadago ta daga jikinshi yace “zafin jikinki ya baci kinsha magani kuwa?” Gyadamai kai tayi ahankali Baba yace “to zai sauka, sha lemon kici naman bari naje masallaci, kada kuma kisake kuka kinajina” gyadamai kai tayi yadafa gadonta yana mikewa daukan crutches din tayi tabashi ya karba yafice tabishi da kallo saikuma ta kalli abincin bata iyaci, wayanta ne yahau ringing da mugun sauri takai hannunta ta dauki wayan Ammi tagani a screen sanyi jikinta yayi tadauki wayan Ammi ma sake kwantar mata da hankali tayi sun sade suna waya ahaka bacci yayi gaba da ita koda Baba yadawo ganin tayi bacci yawuce yana jawo mata kofa duk ya damu ganin bataci abinci ba.
I KNOW SOME PEOPLE MIGHT BLAME HAWWA ACE KE BAKIDA ZUCIYA NE MENEMENE
LİSTEN I THINK IDAN KANAMA MUTUM SON GASKIYA YOU DO EVERYTHING IN YOUR POWER TO HAVE THEM BACK IDAN KUN RABU.💔
IDAN SO DA KAUNAN NA GASKIYA NE AT FIRST BAZAKA YARDA LALLAI LALLAI KUN RABU BAFA SAI REALITY HIT YOU💔
DONT BLAME HAWWA, SHE VALUE NI’IMA, BUT KUNA GANIN ABINDA MAMAN NI’IMA TAMATA SHINE DAIDAI????
[9/19, 11:55 PM] M Shakur: 💫GARGADAN SO💫
✍🏻M SHAKUR
EPISODE 3️⃣0️⃣
KUNSAN ME AKE NUFI DA INTIMACY CLASS?
CLASS NE DAYA KUNSHI KOYARDA ABUBUWAN YAKAMATA KOWACE MATAN AURE DA AMARE YAKAMATA SU SANI, TUNDAGA KAN MENENE SHI SADUWA DA IYALI, YA AKE SARRAFA MIJI A GADO, YA AKE KULA DA MIJI, YAZAKI ZAMA GWANA KIYI FINCINKAU CIKIN MATAN SA🥰
A INTIMACY CLASS BABU KALAN ABINDA BAZAKI KOYABA DAN HAKA JOIN US TODAY WITH JUST 5K SHEKARA DAYA NE CLASS DIN.
MAKESURE KINADA TELEGRAM KAFIN KIBIYA
CHAT ME UP IDAN KINASON SHIGA WANNAN CLASS MAI TARIN FA’IDA
wa.me/+2347012181461
Washegari around 5 ta farka da ciwon kai har bata iya bude idanu da kyau, gashi tai staining kayanta da wajen abinda bata tabayiba, ta tashi tacire kaya da zanin gadon batada karfin wanki a basket na laundry tasa, tasake kwanciya ko daga kafa tayi saitaji akanta, tana ahaka Baba yayi knocking da sallama da katuwan muryan nan nasa yace “zan shigo” kofan yabude ya shigo dakin yaganta kan gado hankalinshi yakara tashi ganin sosai Hawwa fa batada lpy, batama iya bude idanu, cikeda damuwa yace “Hawwa na” yazo wajen gadon yana dagota jikinta kaman fire Baba yace “subhanallahi, Hawwa zoki lallaba kiyi wanka muje asibiti, kokuma bari kiga nakira Ni’ima” wayansa yaciro daga aljihu yashiga kokarin kiran Ni’ima Hawwa na kallonshi da kyar harya katse bata dagaba yace “bata dagaba bari kinsan asuba ne hala bata tashi ba, bari nasake kira” yasake dialing number saiya cema Baba busy kusan sau 4 yana trying yace “busy busy yake gayamin” dan murmushi kadan Hawwa tayi ganin shima Baba tai blocking nashi, cikeda karfin hali muryanta baya fita da kyau tace “Baba karka damu bari naci abinci zan lallaba naje asibitin nasu adubani” gyadamata kai Baba yayi yajuya yace “shirya wankan bari nahada miki ruwa” sosonta yaduka yadauka yafita yana dungura sanda yashiga kitchen Umma na kitchen din ta banka uban tsaki ko kallonta baiyiba, ruwan da aka ijiyemai nashi na wanka yajuye mata yadauka yafito yatara na sanyi ruwan yayi dalam dalam dan jikinta akwai zafi sosai yakaimata bayi sannan yadawo dakin yabuga mata yace “fito Hawwa” fitowa tayi da hula akanta ahankali take tafiya tana dafe kanta da hannu daya hannu daya tana dafe bango, Baba yakama hannunta gwanin ban tausayi ya jinginata a bangon wajen yaci bari nakawo miki kujera, kujera ya dauko yasamata abayin sannan ya shigar da ita yarufo mata kofa, bata taba sani ana irin ciwon kan nan aduniya ba, kowani motsi tayi sai kan ya amsa, tadan jima tabude kofan Baba na jiranta, brush yabata daya koma daki yadauko mata tayi yariketa yakai daki ya zaunar kan gado, Allah sarki da kanshi yabude sip yazaro mata yar doguwan rigan da yagani na atampa green, ya ijiye mata kusada ita, tabishi da kallo yanda yake dingisawa yadauko mata mayyukanta yakawo gadon ya ijiye duka kusada ita murya chan kasa yace “sa kaya ganinan zuwa” yawuce yafita, da kyar ta tashi tadauko su pad, pant bra tashiga shiryawa ahankali tasaka green atampan da Baba yadauko, dogon riga very simple yet stylish dinki dan har collar gareshi rigan, ta zauna ahankali kome zatayi kaman kanta zai fadi, dan karamin gyalenta green ta dauka ta yafa tasake kwanciya agadon Baba yashigo da shayi a hannu yazo gadon yazauna kusada ita yace “zoki sha muje” hannu tadagamai alamun bazata iyasha ba, tana lumshe idanu saikuma dan gajeren bacci yayi gaba da ita wuraren 7 ta farka, jikinta har kyarma yake sabida zazzabi kaman ana tsinka hanjin cikin jikinta, idanunta sunyi jajir, gyalen tasake dauka tayafa dan bazata iya daurin dankwali ba ta lallaba ta mike tana daukan wayanta da handbag da car key a hannu tasaka flat shoe black tafito, Baba na compound tafito yamike dasauri yataho da sauri yana kallonta yace “kin tashi” dan murmushin karfin hali tamai tace “bari naje asibitin su adubani” Baba yace “zaki iya tuki kuwa da ciwon kan nan”? Murya cha kasa tace “zan iya Baba karka damu” har mota yarakata ganin hankalinshi bai kwanta ba da fitan ita kadai yasa ahankali tace “Baba ko Ni’ima zata iya dawo dani kazauna kaji” gyadamata kai yayi ya maida mata kofan yarufe ta tada motan taja Baba yabi motan da kallo.
Ahankali take tukin, da kyar take iya bude idanu har jiri jiri take gani amman sabida karfin hali haka tashiga hanya jikinta kaman wuta, ko kadan bata gudu sosai cus jiri take gani, har layi take, hospital nasu na yan sanda takeso taje tunda Ni’ima tace tadaina zuwa hospital nasu wanda shine hospital datake using idan batada lpy, sunkai wajen traffic light na zone 3 ta tsaya tana jiran yakai turn nasu tawuce, dan tsayawan kawai yasa taga idanunta sun fara ganin duhu, kawai idanunta suka fara kukkullewa suna firfir, internally taji kaman an kunna wani engine na vibration a jikinta, kawai jikinta yafara rawan da bata iya controlling tana fisfisgewa tafara convulsing.
Bakin rigiman Noor yasa yau yatashi da wuri cus tace shizai kaita school, tunda suka shiga motan nan surutu takemai, ganin an kirashi yafara waya yasa ta barshi tawuce window tamike tsaye tana kallon hanya ganin sun tsaya chak, motan dake next to them a layi yar corolla data tsufa ba irin tasu ba ta kalla, ihu tayi tace “Dady loook someone is sick, Dady someone is shaking, I think is Fairy Angel Anty, Daddy!” Yarinyar tai ihu dayasa Khaleel yadan dakatar da wayan dayake yazo wajen yace “Princess menene”? Leko da kanshi yayi shima idununshi suka sauka kan Hawwa dake convulsing acikin mota ita kadai kanta na karkacewa yawu nabin gefen bakinta, daidai tawani mike ta sandare ta danna tootle motanta yayi gaba yana arnen gudu jikake karakakakakap!!!! Motanta yana dukan motocin dake gabanta with full speed…
Dawani irin sauri Khaleel yabude bayan motan yafito yanabin motanta da gudun bala’i kaman bashiba acikin traffic din nan some people ma nafitowa dan some people anga Hawwa na convulsing, every gudu da Khaleel yake he’s telling her in his mind don’t die! Don’t die! Saida motanta yahada 5good cars suna gudu saida sukakai jikin wani trailer ne akai gwarap!!! Dole motocin suka tsaya hakama nata ya tsaya but still pushing nata keyi sabida kafanta, glass na gaban motanta ya tarwatse kwasha kwasha kanta na jini hannayenta na jini, lafiyayyen accident Hawwa ta hada, Khaleel yafara reaching wajen motanta yana zuwa wajen motan nata dake hayaki sosai yashiga budewa jama’a nataruwa ana tayashi budewa ana zuwa wajen sauran motocin yana kallonta yana kokarin bude motan yanda har airbag na motan yafito yatareta tagaba, bude motan yayi nasaran yi yashigo jini nabin hannuwanta da goshinta ga some kwalabe ajikinta, ya zare sitbelt dinta, Hawwa tafado jikinshi tana convulsing kumfa nafitowa ta gefen bakinta da yawu, jini nabin gefen goshinta, dasauri Khaleel yasa hannunshi yariketa, yakai hannunshi ya zare kafafunta daga tootle flat slippers nata nafita daga kafafun, lips nata na jini sabida yanda take biting nasu zata cigaba dasauri Khaleel yakai hannunshi yasa abakinta ta shiga tattaunewa tana datse hakoran akansu, daidai Salman da bodyguards nashi da mopol dinshi rikeda bindigoginsu sunzo akahau kallonsu jama’a while ana ciro sauran mutanen da Alhamdulillah babu wanda ya mutu saidai ciwo, rike Hawwa yayi gam ajikinshi yace “Salman pay for all damages she caused, I’m taking her to the hospital!”.
[9/19, 11:55 PM] M Shakur: 💫GARGADAN SO💫
✍🏻M SHAKUR
EPISODE 3️⃣1️⃣
KUNSAN ME AKE NUFI DA INTIMACY CLASS?
CLASS NE DAYA KUNSHI KOYARDA ABUBUWAN YAKAMATA KOWACE MATAN AURE DA AMARE YAKAMATA SU SANI, TUNDAGA KAN MENENE SHI SADUWA DA IYALI, YA AKE SARRAFA MIJI A GADO, YA AKE KULA DA MIJI, YAZAKI ZAMA GWANA KIYI FINCINKAU CIKIN MATAN SA🥰
A INTIMACY CLASS BABU KALAN ABINDA BAZAKI KOYABA DAN HAKA JOIN US TODAY WITH JUST 5K SHEKARA DAYA NE CLASS DIN.
MAKESURE KINADA TELEGRAM KAFIN KIBIYA
CHAT ME UP IDAN KINASON SHIGA WANNAN CLASS MAI TARIN FA’IDA
wa.me/+2347012181461
EPISODE 3️⃣1️⃣
Wucewa yayi two bodyguards na binshi abaya daya rike da jaka da wayan Hawwa da Salman yabasu su biyoshi, dayan babu komi a hannunshi, suna zuwa wajen rolls Royce dinshi suka budemai baya shiga ciki yayi yana rike Hawwa ajikinshi Noor tafashe da kuka tana kallon yanda jikin Hawwa ke fizgewa, Khaleel yace “sauke glass na motan kasa she need breeze” saukewa yayi, driver yayi kwana kawai suka fara gudu a lane din kafin su sami uturn su dauki wani hanya, hannun dogon long sleeve dinshi Khaleel yakai bakinta gently ya goge yawun dake fitowa daga bakinta yana kallonta damuwa sosai akan fuskanshi kaman zai kirata da idanu yace ta farka ta farka tsabagen yanda yake kallonta, Noor na kallonsu tace “she’s biting your hand Dady” murya chan kasa yana kallon Hawwan dake jikinshi yace “she’s sick that’s why” dasauri Noor tace “Dady I love her alot can I take her pain away?” Shiru yayi yana kallon fuskan Hawwan yace “pray for her” yanda Oga yace aje hospital yasa driver yakaisu hospital din Excellency daya gina, hamshakin hospital ne, kallon Hawwa Khaleel yake bayako kyafta idanu, suna parking ana zuwa, karbanta akai daga jikinshi sukai ciki da ita.
Sauka yayi daga motan yabama bodyguard nashi hannu alamun yabashi wayan da handbag din Hawwa ya karba yace “drop Noor a school” yakalli Noor saikuma ya matso ya manna mata kiss a goshi ahankali tace “Dady will my FAA be fine?” Gyadamata kai yayi yace “she can fight! She will fight the sickness trust me” washe baki Noor tayi tace “My FAA is very strong right Dady” gyadamata kai yayi, ahankali tace “Dady please stay with her don’t fight like that day at super market” shiru yayi saikuma yace “you talk too much go to school” yarufe mata kofan yawuce yashiga cikin hospital din zuwa dakin emergency da aka kwantar da Hawwa, wayanta dake hannunshi ne yashiga ringing dasauri yadaga yaga suna Baba, jimmm yayi he remembered Salman yagayamai mutumin baida kafa he’s crippled that means he’s a sick old man idan yatadamai hankali fa? No! Yafadi ahankali.
Yana tsaye awajen rike da wayan harya katse, daidai Nurse tazo wajen da form a hannu ta mikamai tace “Sir can you fill the form or you have to call her family” sabida yagaya musu hatsari tayi yakawota, paper yakalla da nurse din kaman wanda baiso yayi magana yace “I will call the family”, sannan yadanna screen na wayanta ganin babu key yasa yashiga call log nata number daya gani da Ammi yayi dialing ringing daya Ammi tadaga tace “Hawwa na kin dena damuwan ko” shiru Khaleel yayi baisan yanda ake communication da normal mutane ba sai masu kudi yan league nashi muryan matan is so calm, “Hello Hawwa” Ammi tasake magana, dan gyaran murya Khaleel yayi kaman wanda aka bama big task adan hankali yace “she just had an accident Ma’am she’s in the hospital they’re call for her family” “Innalillahi wa innailaihi raji’un, Hawwa tai accident, tana ina kace? Wai Hawwa na? Jidda ake magana?”
Dan sosakai Khaleel yayi yajuya kozaiga security nashi yabasu wayan suyi yatuna yasasu sukai Noor school, murya yar kadan kaman wani bawan Allah yace “yes Ma’am” sai kawai yaji Ammi tafashe da kuka sosai dasauri yacire wayan daga kunnenshi yana dan yatsine fuska irin mehaka takeyi saikuma yaji muryan namiji Babba na Hello Hello maida wayan yayi kunnenshi yace “yes” Baffa yace “bawan Allah awani hospital take? Ya condition nata yake, idanunta biyu ne kahada mu da ita muyi magana” kai tsaye Khaleel yace “she’s very sick, she’s unconscio…..” ai kafin yakarasa maganan yaji kukan mutane dayawa, Baffa yace “ya sunan asibitin”? Ahankali Khaleel yace “Leadway” “to mungode gamunan zuwa, mu muna zaria zankira Babanta yanzu zai taho”
Baba na zaune a kofar gida yaga number Ammi na kiranshi kin dauka yayi chan saiga number mijinta Baffa hakan yasa yadauka yana kokarin mai sallama Baffa yace “Malam yanzun nan aka kiramu da number Hawwa” faduwa gaban Baba yayi sosai bana wasaba yace “Hawwa, Hawwa? Batajin dadi ai taje asibitin su Ni’ima” Baffa yace “wanda yakiramu yace tayi hatsari amman ka kwantar da hankalinka tana asibitin Leadway nan aka kaita katashi kaje ana neman yan uwanta na jini badai musan me ake ciki ba” salati Baba yafara yana sallallami baima tsaya yakarajin wani bayani da Baffa keyiba da sauri yamike yakoma ciki yana salati kaman wanda ya haukace duka kudadensa dabaya kashewa ya tattaro yafito yana salati kawai. “Innalillahi wa Innailaihi Raji’un, Ya Allah Hawwa na, Ya Allah y’ata, marainiyata Ya Allah, Innalillahi Wa Innailaihi raji’un, Allahuma ajirni fi musibati, Lahaula walaquwata illabillahil aliyul azeem” salati kawai Baba yake ko kallon Umma dake tambayanshi lafiya baiyiba yafito luckily saiga keken daya sauke mutane zai juya taresa Baba yayi yashiga yafadamai sunan asibitin yashiga still salati yake.
A gate na asibitin aka sauke Baba ya shigo baya hayyacinsa dauriya kawai yake irin na maza da crutches nashi yake dungurawa yana