Showing 21001 words to 24000 words out of 24725 words

Chapter 8 - KARSHEN ZALUNCI Complete Document by Sarkin Marubutan Yaki .txt

23 Nov 2024

3221

ne mu ajiye kasuwar buƙata mu fuskanci abun hari, ma'ana mu tabbatar mun mallaki zakanya juraima da takobi, kuma mu hallaka waɗanda zasu hana mu cimma burin mu jaruma Sulairat da tawagarta".
Koda jin wannan jawabi daga bakin sarauniya abidat sai sarakunan suka yi shiru suna dogon nazari, daga can bokanya Zulaima ta bushe da yar ƙaramar dariya mai kama da kukan jaki sannan daga bisani ta turmuke fuska, cikin kakkausar murya kai kama da haushin kare ta bude baki ta ce "haƙiƙa wannan shawara ce mai kyau, amma wani hanzari ba gudu ba, shin yanzu idan mun kawar da su Sulairat mun mallaki zakanya da takobin Saiful-imfal shin a cikin mu wane ne zai iya haƙura ya ƙyalewa ɗan uwanshi ya mallaki Saiful-imfal? To amma dai masu iya magana na cewa sai an gwada akan san na kwarai, ga fili ga mai doki"
Sa'adda bokanya Zulaima tazo dai-dai nan azancen ta sai kawai tayi murmushi mai tattare da mugun tanadi da baƙin tuggu.
Shi kuwa sarki Nadiyar abin da ya faɗo mashi a rai shine taya ya zai samu nasarar mallakar zakanya juraima da takobin cikin sirri ba tare da kowa ya farga ba.
Wani ɓangaren a zuciyarshi ya ce da shi ya zama wajibi ka canja tunanin ka a game da wannan yarjejeniya, tunda sanin kanka ne cewa gaba ɗayanku yaudara ce a tattare da kowanensu, burin kowanne ya ci amanar ɗan uwanshi, saboda haka shawara a gare ka ita ce a lokacin da sauran abokan gabar suka yunƙura wajen hallaka su Sulairat kai kuma kayi ƙoƙari wajen ceton rayuwarsu tare da basu goyon baya.
Hakan zai sanya su aminta da kai har su baka goyon baya su taimaka maka wajen cimma buƙatar ka ta samun ruwan ƙaramar shajarul-shifa domin samun haihuwa.
Sa'adda sarki Nadiyar yazo dai-dai nan a tunanin shi sai ya yi murmushin farin ciki.
Daga wannan furuci ne sarakunan suka sake rikiɗa izuwa tsuntsayen suka kaɗa fuka-fukansu, kowannensu ya nufi sansanin shi.
A can dajin baitul-shazwas kuwa, al'amarin su sulairat tun sa'adda suka kammala fafatawa artabu da su sarauniya Abidat, sai suka kasance cikin shirin ko ta kwana, lokacin da dare ya tsala sai suka hallara a cikin kogon dutse.
Bawa Hilwas ya katse shirun da ya wanzu a tsakanin su ta hanyar buɗar baki ya yi gyaran murya, ya kawo gwauron numfashi ya ajiye ya ce "ya 'yan uwa abokan share hawaye ku yi sani cewa haƙiƙa abun da ya faru a yau a filin yaƙi ya tabbatar mana da cewa sai mun sake tanadi, domin masu iya magana na cewa na zaune bai ga gari ba, kuma komai sammakon ka wani a hanya ya kwana. Idan a yau mun yi artabu da sarauniya Abidat kaɗai to ku sani cewa a gobe zamu yi fito-na-fito ne da tawagar sarakuna biyar.
Kar mu manta cewa sarkin yawa ya fi sarkin ƙarfi, kuma alamar ƙarfi tana ga mai ƙiba.
Dole a yauzu mu canja tunanin mu da nazari akan tunkarar gumurzun gobe".
Sa'adda bawa Hilwas ya zo nan a zancen shi sai kowa ya shiga damuwa ainun aka yi shiru tsawon daƙiƙa talatin babu wanda ya ce ƙala.
Sai daga bisani ne Sulairat ta yi gyaran murya ta ce "haƙiƙa zancen ka dutse ya kai Hilwas, wani abu da baka sani ba shine dukkan sabbin tawagar sarakunan da suka bayyana ba komai ne ya kawo su ba face, buƙatar mallakar takobin saiful-imfal da zakanya,
Sai dai abin da suka manta shine masu iya magana na cewa "kifi na ganin ka mai jar koma" babu wani a cikin su da isa ya sarrafa takobin saiful-imfal koda ya mallake ta face yana tare da sarƙar tsafi, domin matuƙar ya ce zai sarrafa ta take takobin za ta hallaka shi.
Bisa dogon nazari da nayi akwai yiwuwar a gobe sarakunan za su haɗa ƙarfi da ƙarfe domin su kawar damu, daga baya a tsakanin su sai su san abin yi"
Lokacin da Sulairat tazo nan a azancen ta sai kowa ya jinjina kai yana mai yuya al'amarin a ran shi.
Suhaimt tayi gyaran murya a karo na farko ta ce "tabbas dukkan maganganun ku suna kan tsari, kuma a halin yanzu hankalin duniya yana kan takobin saiful-imfal da zakanya juraima, duk da cewa matuƙar yawan abokan gaba bamu da tabbacin zamu samu nasara akan su, amma kar mu manta cewa yaƙi ɗan zanba ne, Dole a gobe mu yi amfani da tuggun yaƙi ba iya na takobi ba,
Shawarar da zan bamu ita ce me zai hana a gobe mu tura iya zakanya juraima da takobi a gaɓar shiga daji, mu sai mu ɓuya a cikin duhuwa mu hangi yadda yaƙi zai ɓarke tsakanin sarakunan, zasu yi ta kashe junan su inda daga ƙarshe dole wani ya yi nasara a cikin su ya mallaki takobi da zakanya.
Shi kuma koda ya mallaka sun tashi a banza domin dole ne takobin ta dawo hannun Sulairat.
Wannan wata mafita a gare mu bayan baƙin artabu, kun san masu iya magana na cewa "gida biyu maganin gobara".
Sa'adda Suhaimat mahaifiyar Sulairat tazo nan a zancen ta sai kowa ya cika da farin ciki bisa jin wannan kyakkyawar shawara, daga wannan kowa ya koma can gefe inda shimfiɗar shi ta ke ya kwanta domin huce gajiyar dake tattare da shi.
Amma koda su Sulairat ta zo hucewa ta gaban Himlas sai da ta jefe shi da wani ƙayataccen murmushi mai tattare da tsantsar so da ƙauna, shima ya mayar mata da martanin murmushin.
Wannan shi ne abin da ya wakana a
dajin baitul-shazwas.




BABI NA SHA TAKWAS

Kashe gari tun da duku-dukun safiya, su bokanya Zulaima da sauran tawagar sarakunan suka yi sahu-sahu a gaɓar shiga dajin baitul-shazwas, domin tsumayen fitowar tawagar su jaruma Sulairat,
Sai dai wani abu da ya ɗaurewa tawagar kai shine babu su ga sarki nadiyar da dakarunshi.
Shin ina sarki nadiyar da ya shiga? Shin ya koma izuwa birnin shi ne ko kuwa ya canja wani tunanin domin cin amanar su.
Amsar da tawagar da suka kasa bawa kan su kenan.
Duk da cewa a daren jiya sun samu ƙari a cikin tawagarsu wato gimbiya Hasinat 'yar uwa ga gimbiya Husnat
ma'abociyar addinin musulunci.
Tsawon daƙiƙa arba'in ana cikin wannan hali ba tare da anji motsin komai ba,
Daga can sai aka ji ganyayyakin bishiyun dajin suna motsawa alamun dake nuni da cewa wani abu mai rai yana shirin bayyana a wajen.
Zuwa can sai aka hango Jaruma Sulairat, bawa Himlas, Suhaimat, baiwa Sunaila tare da wasu baƙin jarumai biyu da suka rufe fuskokinsu da baƙin yanki, idanuwansu kaɗai ake gani. Baki ɗayansu suna shirye cikin gagarumar shigar yaƙi mai matuƙar kwarjini daban tsoro kana gani kasan fitowar yau cike take da mugun tanadi, kuma fitowa ce ta ko a mutu ko ayi rai.
Ba wasu ba ne baƙin jaruman da suka bayyana ba face.
Jaruma Husnat yar uwa ga gimbiya Hasinat tare da sarki nadiyar, nan fa aka fara kallon-kallo tsakanin duka ɓangarorin ashe abin da su su sarauniya Abidat ba su sani ba shine a daren jiya Jaruma Husnat ta samu shiga dajin baitul-shazwas kuma ta bayyanawa su Sulairat abin da ke tafe da ita. Kuma a halin yanzu baki ɗayansu sun ƙarɓi addinin Musulunci.
Wannan dalili ya sanya aka ajiye zakanya juraima da takobi a cikin daji kasancewar abubuwa ne na shiri.
Daga can sai ɓangarorin suka tunkari juna, yayin da ya rage saura taku goma tsakani sai kowannen su yaja ya tsaya, aka sake sabon kallon-kallo na tsawon daƙiƙa arba'in, daga can sai Husnat ta dubi 'yar uwarta Hasinat tayi gyaran murya ta ce "yake yar uwata kuma gudan jinina kiyi sani cewa ban zo nan domin na yaƙe ki ba sai domin na yi miki nasiha ki tuba zuwa ga Ubangiji ki dawo zuwa addinin Musulunci".
Koda jin wannan batu daga bakin Husnat sai 'yar uwarta Hasinat ta taƙarƙare ta bushe da dariyar mugunta, daga can ta turɓune fuska tamkar an aiko mata da saƙon mutuwa ta ce "wannan nasihar ta ki abbanmu ya yi dubunta amma bai sanya koda kwarzane na imani ya ɗarsu a raina ba. Ina mai tabbatar miki da cewa sai na cimma burina na mallakar takobin saiful-imfal domin ɗaukar fansa akan abbanmu saboda haka ki shirya ga maza nan bisa kan ki".
Koda gama faɗin hakan sai ta miƙa hannunta a gadon bayanta ta zare wata sharɓeɓiyar takobi a cikin kubenta, sannan ta ruga da gudu izuwa kan 'yar uwarta tana ihu da kururuwa mai firgitarwa.
Koda ganin hakan sai Husnat ta zare takobin dake damtsenta ta tare ta gami da ƙwala kabbara da ƙarfi.
Sa'adda tawagar sarakunan duniya suka ga abin da ya ke faruwa sai suka yi ɗauki kan su Sulairat.
Sarauniya Abidat ta tari Sulairat, bawa Himlas ya tari sarki Damzaru, Baiwa Sunaila ta tari bokanya Zulaima, Suhaimat, sarki Nadiyar da dakarunshi suka tari tawagar sarkin matasan ifritai na duniya, da dakarun sarki Damzaru.
Lokacin da ɓangarorin biyu suka haɗu da juna sai aka ruguntsume da azababban yaƙi mai matuƙar muni, ban tsoro da ban al'ajabi gami da tashin hankali.
Wohoho! Haƙiƙa yaƙi KARON MAZA sai GWARAZAN JIYA da suka sha gwagwarmaya a GUMURZUN SHEKARA DUBU.
Haƙiƙa ranar bikin farar kaza balbela ba abar gayya ba ce, idan manyan giwaye suka fito fagen artabu dole ne yaƙi ya zamto tashin hankali kuma ban tsoro.
Nan fa ƙarar karafniyar ƙarafa, gami da ihu da kururuwar mazaje ta cika dodon kunne, ƙura ta turnuƙe sararin samaniya tamkar hadari ya gangamo, za'a kece da matsanancin ruwan sama.
Husnat da Hasinat suka wanzu suna kaiwa juna sara da suka cikin matuƙar zafin nama JURIYA DA BAJINTA ta gaban kwatance, duk sa'adda makamansu suka haɗu da juna sai kaga tartsatsin wuta ya tashi. Wani abu da zai ɗaurewa mutum kai kuma ya bashi mamaki shine yadda salo da dubarun yaƙin 'yan uwan yakasance iri ɗaya sak.
Amma a ɓangaren manyan giwaye kuwa wato Jaruma Sulairat 'yar baiwa da sarauniya Abidat, tuni labari ya sha banbam, domin gaba ɗaya sun zamto taurari ababan haskakawa a filin yaƙin, domin komai hassadar mutum idan ya ga yadda suke artabun dole ne ya jinjina masu ya tabbatar da cewa sun cika mata masu kamar maza, masu ƙarfi na Allah ya isa.
A ɓangaren Bawa Himlas da sarki Damzaru an yi kunnen doki babu rinjaye ga kowanne abokin gwami. Ma'ana anyi kare jini biri jini,
Sai dai ana samun asarar rayuka tsakanin dakarun sarki Nadiyar da tawagar muridai haɗi da na sarki Damzaru,
Yazamana cewa duk inda mutum ya kai dubanshi sai dai ya ga Suhaimat da Sunaila na bazar da dakaru a ƙasa tamkar suna sassabe a gonar auduga.
Nan fa waje ya cika da mutuwar mazaje, ƙarar karafniyar makaman yaƙi haɗe da hargowa da kururuwar mazaje ta cika dodon kunne, duwatsu suna dinga karo da juna suna yin bindiga suna tarwatsewa, dawakai suka dinga dudufniya suna haniniya kofatunsu na kartar ƙasa suna tayar da ƙura, wasu na zubar da mahayansu suna nausawa cikin daji saboda matuƙar firgici.
Wohoho! Haƙiƙa duk wanda ya iya ya huta, komai hassadar mutum idan yaga yadda Zaratan matan biyu ke ragargazar yaran ifritu da sauran abokan gaba dole ya jinjina masu ya tabbatar cewa sun cika GWARAZAN JIYA masu ƙarfi na Allah ya isa.
Nanfa sarkin matasan ifritai ya ɗinauce bisa ganin yadda Suhaimat da Sunaila suka zame masu gagarabadau kuma ƙadangaren bakin tulu.
Kaico! Haƙiƙa yaƙi shine mabuɗin dukkan wata musiba a doron ƙasa, domin yaƙi shine ke haddasa asarar rayuka, dukiya, fari da JUYIN SARAUTA.
Haƙiƙa wanda bai san shi shine yake fatan zuwan shi shine yake fatan zuwan shi.
Abin da sarakunan kafuran ba su sani ba shine bakomai ne ya sanya su Sulairat ke samun galaba akansu ba sai domin addu'o'i da suke karantawa.
A wannan rana sai da aka shafe tsawon sa'a biyu da daƙiƙa arba'in ana wannan ɗauki ba daɗi.
Haƙiƙa Ubangiji ya nuna ikon shi a wannan rana domin ya kunyata maƙiya Addinin Allah,
Baiwa Sunaila ta samu nasarar hallaka bokanya Zulaima ta hanyar karya mata wuya ta jefar da gawarta a ƙas.
Shi kuwa sarki Damzaru ya miƙa wuya ga bawa Himlas bisa ganin cewa zai iya rasa rayuwar shi, zai tashi a tutar babu.
Kamar yadda ya wakana tsakanin Damzaru da bawa Himlas haka al'amarin ya kasance tsakanin sarauniya Abidat da Jaruma Sulairat domin sai da Sulairat ta samu nasarar kai ta ƙasa sau babu adadi amma bata hallaka ta ba.
Lokacin da Abidat ta fahimci cewa kowanne lokaci zata iya rasa rayuwarta, nan take ta miƙa wuya. Domin dai ina amfanin baɗi ba rai,
A ɓangaren gimbiya Hasinat da 'yar uwarta Hasinat kuwa sun yiwa juna ƙananun raunika, kuma Hasinat ta miƙa wuya tayi nadamar abin da tayi.
Sai dai sarkin yaƙinta ya rasa rayuwarshi.
Wohoho! Haƙiƙa a wannan rana Ubangiji ya nuna ikon shi akan bayinshi ya kunya kafurai maƙiya addinin shi.
Cikin matuƙar farin ciki Jaruma Husnat ta karanta kalmar shahada baki ɗayansu suka amsa, faruwar hakan ke da wuya nan take sarki Damzaru yaji yanayin jikinshi ya canja, koda ya duba sai ya ga cewa halittar mata maza dake tare da shi ta bar shi, yanzu yana ɗauke da cikakkiyar halitta ta kowanne ɗa namiji lafiyayye.
Nan fa ya cika da matuƙar farin ciki maral musaltuwa, ya ji ya ƙara imani da Ubangijin gaskiya.
Kafin ya bar filin yaƙin sai da Jaruma Husnat ta fito da takobin saiful-imfal ta lalata shirin dake jikinta ta hanyar karanta ayatul-kursiyyu ta tofa, ita kuwa zakanya juraima koda aka tofa mata ayatul-kursiyyun nan take wani baƙin aljani ya fito daga jikinta ya kama da wuta ta ƙone ƙurmus, ashe duk abin da take gudanarwa wannan aljani ke sarrafa ta hanyar amfani da sarƙar tsafi.
Haƙiƙa a wannan rana babu wanda ya kai Sulairat da mahaifiyarta matuƙar farin ciki bisa ganin cewa suna kawo ƘARSHEN ZALUNCI a doron ƙasa baki ɗaya.
Da yake akwai sauran sa'o'i kafin faɗuwar rana sai aka ɗunguma izuwa birnin Sin, aka kafa tutar musulunci dukkan al'umma suka yi mubaya'a bisa jin abin da ya faru da sarauniya Abidat.
Sai da Jaruma Husnat ta shafe tsawon mako guda tana koyar da dukkan al'umma yadda ake gudanar da ibadar Ubangiji, sai da aka aika da wasikar gayyata izuwa ga sarki Shaibat domin ya zamto waliyyi a ɗaurin auren 'ya'yanshi, ya yi matuƙar farin ciki bisa jin labarin nasarar da Husnat tayi.
Sai da ya iso tare da tawagarshi sannan aka shiga shagalin bikin sarauniya Abidat, Jaruma Sulairat ma'abociyar zakanya, Jaruma Husnat da bawa Himlas. Sarki Damzaru da Gimbiya Hasinat.
A wannan rana anyi shagalin da ba'a taɓa yin tamkar shi ba iya tsawon wanzuwar birnin Sin.
Ango Hilmas ya tare da amaren shi Abidat, Sulairat da jaruma Husnat,
Kuma ya zamo sabon sarkin birnin Sin mai cikekken iko, sarauniya Abidat ta zamto shugabar sarauniyoyin birnin Sin.
Farin ciki maral-musaltuwa ya mamaye zuciyar Suhaimat matar marigayi sarki Urwat da baiwa Sunaila mahaifiyar sarki Hilmas.
Al'amarin sarki nadiyar kuwa lokacin da ya koma izuwa ƙasar shi nan take ya tarar da dukkan matayenshi sun samu juna biyu, ashe duk sihirin tsafin da aka yi masa ne ya kwantar da juna biyun. Yanzu kuma tun da ya karɓi addinin musulunci, sihirin dake tare da shi da matayenshi ya lalace.
Nan fa ya cika da matuƙar farin ciki maral-musaltuwa kuma ya sanya aka rushe dukkan ɗakunan bauta aka jaddada addinin Musulunci.
Faruwar hakan ya sanya dukkan al'ummar ƙasar shi suka kasance cikin aminci da soyayyar juna.
Daga wannan rana farin ciki ya mamaye dukkanin sassan duniya, aka kawo ƘARSHEN ZALUNCI, uwar azzalumai sarauniya Abidat ta dawo sarauniyar adalci saboda hasken musulunci.




Alhamdlillah.


Anan na kawo ƙarshen wannan littafi mai taken ƘARSHEN ZALUNCI daga littafi na 1&2 zuwa na 3 ina fatan Ubangiji ya yi min afuwa bisa kusakuren da nayi. Abun da nayi na alheri kuma Allah ya bamu ladan baki ɗaya.
Godiya ga dukkan masoya littattafai na a ko ina suke maza da mata.


Sai mun haɗu a sabon littafi na ɗaya tamkar da dubu.


KUNDIN AL'AJABI


Daga mai ɗebe maku kewa a kullum da koyaushe.


Mansur Usman Sufi
Sarkin Marubutan Yaƙi
Wthapp Number
08137237071




ƊANƊANO
Daga Littafin




KUNDIN AL'AJABI


Ƙasaitaccen keken doki ne da aka ƙawata shi da nau'ikan kayan ado na sarauta.
Kuma dokin dake janye da keken yakasance ingarmar doki fari sol!.
Dokin na janye da keken ne cikin matsanancin gudu na keta sa'a a cikin wani ƙasaitaccen daji ma'abocin kwarjini daban tsoro, haɗe da sarƙaƙiyar duhuwar bishiyoyi, duwatsu da ƙoramu.
Abin da zai bawa mutum mamaki kuma ya ɗaure masa kai shi ne,
Duk da irin ƙawatuwa da kayan alatun da keken dokin ke tare da shi amma babu bil'adama a kanshi face wata akwatu ta baƙin karfe guda daya jal ajiye a cikin shi.
Sai da ingarmar dokin ya shafe tsawon sa'a ɗaya yana falfala azababban gudu a dajin ya wanzu yana ratsa ƙoramu, duwatsu, sarƙaƙiyar duhuwar bishiyu, gami da ƙwazazzabai babu alamun gajiya a tattare dashi,
Babu abin da zai burge mutum face yadda dokin yake gudu cikin gwanin ta da ƙwarewa,
Duk da irin duhun daren da ya mamaye dajin tamkar akwai wani bil'adama dake sarrafa shi,
Sa'adda yazamana dokin ya shafe tsawon zango biyu yana tafiya sai karfin gudun sa yafara raguwa.
Ana Cikin wannan hali ne bisa kuskure wasu saiwar bishiya ya harɗe ƙafafuwan dokin na gaba,
Take ya hantsila yayi adungure wannan akwatu dake cikin keken ta faɗi can gefe guda.
Kaico! Haƙiƙa rashin sani yafi dare duhu ashe inda dokin ya faɗi gangare ne wanda a ƙarshen shi wani rami ne mai zurfin gaske,
Ai kuwa sai keken dokin ya dunga gangarawa har ya faɗa izuwa ƙarshen ramin.
A dai-dai wannan lokaci ne wani mafaraucin ya rugo izuwa wajen sakamakon haniniya gami da kukan dokin ya cika cika dajin baki ɗaya,
Ko da isowar shi sai ya kai duban shi inda ramin da keken dokin ya faɗa,
Nan take takaici ya turnuƙe shi bisa ganin cewa bai samu nasarar ceto rayuwar keken dokin da mutanen dake kanshi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login