Showing 15001 words to 18000 words out of 24725 words
Chapter 6 - KARSHEN ZALUNCI Complete Document by Sarkin Marubutan Yaki .txt
hawa tare tawagar rakiya dakaru dubu biyar suka ɗauki hanyar da zata kai su izuwa birnin Sin.
Wannan shi ne abin da ya wakana ga sarki Nadiyar na kasar Madinatul-haiwan.
BABI NA SHA UKU
Al'amarin sarauniya Abidat kuwa lokacin da ta Kaɗaita a cikin turakarta cikin matuƙar takaicin yadda abokan gabarta suka suɓuce mata, sai ta wanzu tana kai komo a cikin turakar ta kasa zaune ta kasa tsaye tana juya al'amarin a cikin ran ta.
Tana cikin wannan hali ta iso madubi yake koda ta kalli fuskarta taga yankan da SULAIRAT ta yi mata bata san sa'adda ta dunƙule hannunta ɗaya ba ta naushi madubin ya tarwatse sannan ta taƙarƙare ta kurama wawan ihu, tsawon daƙiƙa goma tana cikin wannan hali sannan daga bisani ta murtuke fuska tamkar an aiko mata da SAƘON MUTUWA.
Kwatsam! Sai taji an tura ƙofar shigowa turakar, wani garjejen ƙato mai ƙirar samudawan farko ne sanye cikin sulken yaƙi ya bayyana gare ta. Sannu a hankali yana takawa da ƙafafuwanshi har yazamana tazarar dake tsakanin su bata huce taku uku sannan ya zube ƙasa bisa gwiwoyinshi ya kwashi gaisuwa kanshi a sunkuiye.
A sannan sarauniya Abidat ta juya cikin ƙasaita da baƙar izza ta dube shi da kyawawan idanuwanta masu haske da kwarjini, sannan ta buɗi baki cikin murya mai tattare da fushi ta ce " ya kai dirkar birnin Sin kayi sani cewa bakomai ne ya sanya na kira ka nan ba sai domin kafi kowa sanin abin da ya faru da ni a fada na suɓucewar abokan gabata.
Ba'a taɓa keta mutumcina da ƙasƙanta darajata tamkar yau ba.
Saboda haka ina so ka shirya tawagar mayaƙa da baka taɓa tsara tamkar ta ba, gami da abin guzuri da masu hidima domin ba zan dawo gida ba face na kawar da abokan gabata kuma na mallaki takobin Saiful-imfal, ina so asubar fari ta yi mana a gaɓar shiga dajin Baitul-Shazwas."
Koda jin wannan batu daga bakin Abidat sai sarkin yaƙi ya buɗe bakin ladabi ya ce "an gama ya sarauniyar kyawawa hadari malafar duniya. Kece guguwar ajali mai share TAWAGAR MAYAƘA, GAWURTACCIYA kike uwar hatsabiban duniya. KAIFIN TAKOBI kike mai raba tsakanin masoya, ANNOBA ƊARI kike duk wanda ya tono ki zai baƙunci barzahu. Kasaitaccen daji kike babu mai yi miki ƙyaure sai mahaukacin kafinta. MURUCIN KAN DUTSE kike baki fito ba sai da kika shirya. DAMISA ƘI SABO kike ki fyaɗe na gida ki fyaɗe na daji".
Lokacin da sarkin yaƙi ya zo nan a kirarin da yake yiwa sarauniya Abidat nan take taji wata irin BAƘAR IZZA da ƙasaita ta cika kwanyarta. Ta dube shi ta ce "ya kai Hunaifu maza ɗago da kan ka ka dube ni haƙiƙa ka cancanta ka kalli sura a matsayin tukwicin wannan kirari naka".
Koda jin wannan batu sai sarkin yaƙi Hunaifu ya buɗi baki cikin ladabi ya ce ya shugabata ba zan iya duban kyakkyawar surarki a matsayina na bawanki ba. Sai dai ina tsoron saɓa umarninki."
Koda ya zo nan a zancen shi sai ya ɗaga kan shi ya ƙurawa Abidat idanu yana kallon surarta ko ƙiftawa ba ya yi tamkar wanda ruhinshi ya fita daga gangar jikinshi.
A wannan lokaci sarauniya Abidat tana sanye ne da wata ƙasaitacciyar alkyabba mai shara-shara gaba ɗaya surar jikinta ta bayyana, tun daga wuyanta har ƙirjinta a bayyane suke, har kana iya ganin tsinin kan ƙirjin tamkar idan aka tsoka ne su da yatsa koda harshe zasu fito waje, cinyoyinta har zuwa kwankwason ta sai sheƙi suke suna ɗaukar hankali.
Tun da sarkin yaƙi yazo duniya bai taɓa ganin wata 'ya mace mai kyawun sura tamkar sarauniya Abidat ba.
Koda Abidat ta fahimci cewa idan har ba ta suturta jikinta ba sarkin yaƙi ba zai dawo da hankalin shi sai kawai ta juya mashi baya, a sannanne ya dawo hayyacin shi yana mai sauke numfashi.
Cikin matuƙar shauƙi sarkin yaƙi ya buɗi baki muryar shi na rawa ya ce cikin ladabi "ya shugabata na rantse da wannan kyawun sura da zati naki farautar su jaruma Sulairat zai zamo tamkar kawar da yunwar cikina."
Da jin wannan batu sai Abidat ta yi murmushi da ya ƙarawa tona asirin kyawunta har fararen haƙoranta suka bayyana cikin zazzaƙar murya mai ɗimauta zuciyar duk wani ɗa namiji ta ce
"je ka abin ka ya kai garkuwar birnin Sin."
Koda jin hakan sai sarkin yaƙi ya juya ya fice daga turakar.
***
Bokanya Zulaima ta ƙurawa tukunyar tsafin dake gabanta idanu ko ƙiftawa bata yi, kwatsam sai taswirar wata runduna guda biyu mabanbanta ta bayyana, runduna ta farko bisa jagorancin wata kyakkyawar budurwa ce ma'abociyar sarauta, runduna ta biyu kuwa bisa jagorancin wani namijin sadauki ne ma'abocin tarin shekaru.
Baki ɗaya tawagar biyu suna tafiya ne cikin hanzari a cikin ƙasaitattun dazuka.
Koda taswirar tazo nan sai bokanya Zulaima ta nuna tukunyar da hannu taswirar ta ɓace ɓat! Sannan ta dawo da duban ta izuwa ga ifritu Shammar da ƙwala-ƙwalan idanuwanta da suka ƙarawa fuskarta muni cikin kakkausar murya mai kama da kukan jaki ta ce "ya kai sarkin matasan ifritai na duniya kayi sani cewa haƙiƙa abun nan da masu iya magana ke faɗa ya faru gare mu wato, "kowa ya daɗe zai ga daɗau, kuma a bari ya huce shine kawo rabon wani"
Amma dai ai masu iya maganar sun ce sa'a tafi sammako. Kuma duk mai nema yana tare da samu.
Takobin Saiful-imfal da na shafe tsawon shekaru ɗari huɗu ina jiran bayyanar ta yanzu lokaci ya yi. A halin yanzu takobin tana tare da wata jaruma yar baiwa mai suna Sulairat, raba Sulairat da takobin abu ne mai matuƙar wahalar gaske domin wata zakanya dake gadin takobin ba za ta taɓa bari wani mahaluki ya kasance ta ba.
Babban abin damuwar shine babu wani mahaluki da zai iya sarrafa takobin Saiful-imfal face ya mallaki wata sarƙar sihiri dake rataye a wuyan jaruma Sulairat.
Bincike ya tabbatar min da cewa manyan sarakunan duniya biyu sun fito domin farautar zakanya Juraima da takobin Saiful-imfal.
Wannan ita ce damar mu ta ƙarshe da zamu ɗauke takobin ta kowacce fuska.
Haƙiƙa burina ya kusa cika na mulkar duniya baki ɗaya domin cigaba da shimfiɗa baƙin mulkina.
A halin ruhikan sarakunan duniya guda dubu shida dake aijye a cikin akwatin siddibaru sun kammala tsumuwa da sihirin tsafina, a ranar da zan mallaki takobin Saiful-imfal dukkan ruhukan za su shiga jikina, wannan shine zai bani damar shafe miliyoyin shekaru a duniya, domin sai na rayu adadin shekarun da kowanne ruhi zai yi a duniya.
Ya kai sarkin matasan ifritan duniya kayi sani cewa sai na sanya duniya a cikin musiba da annobar da bata taɓa gani ba. Zan shafe duk wani addini dake doron ƙasa.
Lokacin da bokanya Zulaima yazo dai-dai nan a zancenta sai sarkin matasan ifritai ya dube ta cikin ladabi ya ce "tsafi ya taimake ki ya uwar bokayen duniya uwa ma bada mama, yanzu batare da ɓata lokaci ba gaba ɗaya rundunar afritai za su bayyana a gare mu wacce ba ki taɓa ganin tamkar ta ba.
Da yardar tsafi abin dogaro sai kin cimma nasara."
Koda jin wannan batu daga bakin ifritu Shammar sai bokanya Zulaima ta taƙarƙare ta bushe da dariyar mugunta mai kama da haniniyar doki, al'amarin da ya sanya baki ɗaya kogon dutsen ya kama girgiza tamkar zai tsaye.
Take ifritu Shammar ya ɓace ɓat! Daga kogon tamkar bai taɓa bayyana ba.
Ita dai bokanya Zulaima ta kasance gawurtacciyar matsafi da tayi shura a cikin bokaye har masu bincike da hasashe na duniya ke yi mata laƙabi da uwar matsafa,
Babban burin Zulaima shine ta mulki duniya baki ɗaya, bisa binciken da ta yi ne ta gano cewa dole sai ta mallaki ruhikan sarakunan duniya guda dubu shida ta tsafe su sun shiga jikinta, bisa wannan dalili ya sanya ta dinga farautar sarakunan tana hallaka su ta ƙarfin sihiri.
Wannan shi ne abin da ya wakana tsakanin uwar bokayen duniya bokanya Zulaima tare da sarkin matasan ifritai na duniya.
BABI NA SHA HUƊU
A can dajin Baitul-Shazwas kuwa kamar yadda bawa Himlas ya tsara haka al'amarin ya kasance wato a daren wannan rana suka kammala sanya dukkan tarkuna a dajin cikin kyakkyawa shiri, ta yadda komai kallon ƙurillar mutum ba zai iya gane an sanya abubuwa masu cutarwa a dajin ba.
Kashe gari tun da duku-dukun safiya aka hango ƙura ta turnuƙe sararin samaniya tamkar hadari zai gangamo a kece da ruwa. Koda ganin hakan sai kowa ya miƙe ya kimtsa jikin shi, Sulairat shigar kayan fata tayi tun daga ƙasa har sama a gadon bayanta tana rataye da wata rantsattsiyar kwari da baka, a gwiɓin cinyarta kuwa tana ɗauke da takobin Saiful-imfal wacce a daren jiya zakanya Juraima ta yi mata jagora izuwa inda takobin take ta ɗauko, a wuyanta kuwa tana rataye da sarƙar tsafinta kuma ta raba gashin kanta gida biyu ya zuba akan kafaɗunta.
Shigar ta yi matuƙar yi mata kyawu da kwarjini, bawa Himlas da Sunaila tare da Suhaimat shigar tufafi iri ɗaya suka yi sak gaba ɗaya sun rufe fuskokinsu da baƙin yanki idanuwansu kaɗai ake gani.
Cikin hanzari kowanne ya tsaya a matsayar shi kamar yadda aka tsara.
Sulairat ta tsaya a ɓangaren gabas tana zaune bisa kan zakanya Juraima, Suhaimat a yamma, Himlas kudu sai Sunaila a yamma.
Tsawon daƙiƙa ɗari aka shafe a cikin wannan hali sai daga bisani ne duhun dake sararin samaniya ya ye sai aka jiyo ƙarar takun sawaye haɗe da haniniyar dawakai ta cika dajin baki ɗaya.
A can bakin gaɓar shigowa dajin Baitul-Shazwas kuwa sarauniya Abidat tare da tawagar ta na ƙara kusantar dajin, lokacin da ya rage saura taku arba'in tsakanin su da dajin sai Abidat ta ɗaga hannunta sama aka tsaya can! A wannan lokaci Abidat tana sanye cikin baƙin sulken yaƙi tun daga ƙasa har sama kanta sanye da hular ƙarfe a gadon bayanta tana rataye da wata rantsattsiyar takobi a cikin kubenta, sanye a jikinta akwai makaman yaƙi fiye da guda ashirin, kaico! Haƙiƙa babu wani gwarzo da zai yi arba da Abidat a cikin wannan hali face ya razana domin shigar da tayi, shiga ce ta tawagar mutuwa.
A gefen hannunta na dama sarkin yaƙi ne cikin shigar yaƙi mai matuƙar kwarjini da ban tsoro.
Abidat ta ƙarewa dajin kallo tana nazarin shi zuwa can sai ta dubi sarkin yaƙi ta ce "ya dirkar birnin Sin kana ganin cewa su Sulairat ba su san da zuwan mu ba, ko kuwa wani tanadi suka yi mana domin su yi mana mamayar bazato?
Koda jin wannan tambaya sai sarkin yaƙi ya dube ta cikin ladabi ya ce "ya shugabata haƙiƙa abokan gabarmu sun shirya wani tuggu domin su mamaye mu, na tabbata cewa suna cikin wannan daji domin babu wani waje da zamu ɓuya da huce nan, sannan koda a ce ba su san da zuwan mu ba ai bayyanar mu ta zo masu domin hakan dole mu fara kai farmaki na somin taɓi."
Koda jin wannan batu sai sarauniya Abidat ta ce "zancen ka dutse ya kai dirkar birnin Sin dole ayi hakan, sannan kasancewar ba ni da ikon shiga dajin Baitul-Shazwas dole ne mu tura dakarun mu su kai hari da yadda dole su Sulairat za su fito mu yi GABA DA GABA da su."
Ya yin da sarauniya tazo nan a zancen ta sai sarkin yaƙi Hunaifu ya risina kawai sai ya yiwa waɗansu dakaru mutum dubu inkiya ta wutsiyar idanu, tamkar dakarun sun fahimci abin da yake nufi sai kawai suka sanya hannayensu suka ciro kibbau daga cikin kwarinsu suka tsoma su a cikin wani kuttu mai ɗauke da guba, kana suka sanya a cikin bakansu suka ja suka ɗame sannan suka harba. A lokaci guda kibban suka tafi cikin matsanancin gudu suka durfafi dajin, duk inda suka sauka sai wuta ta kama koda korran tsirrai ne sai wutar ya ƙonamu. Nan fa hayaƙi ya turnuƙe dajin wuta ta kama ci ganga-ganga.
Tsawon daƙiƙa ɗari ana cikin wannan hali al'amarin da ya fusata sarkin yaƙi Hunaifu kenan ya fara wasi-wasi ya fara tunanin shin ko su Sulairat sun yi nisa a cikin dajin.
Kawai sai ya dakawa dakaru dubu uku tsawa da ke nuna ba su umarni suka afka cikin dajin.
Cikin hanzari dakarun suka zaburi dawakansu suka durfafi dajin.
Kaico! Haƙiƙa rashin sani ya fi dare duhu kuma tsuntsun da ya ja ruwa shi ruwa kan doka inda ace waɗannan dakaru sun san abin da zai faru da ba su gangancin kutsa kai ba.
Lokacin da suka isa ciki nan take suka fara faɗawa tarkuna suna hallaka tare da dawakansu. Nan fa ihu da kururuwar mazaje ta cika dajin baki ɗaya
Sa'adda sarauniya Abidat taga yadda dakarunta ke yin mutuwar wulaƙanci sai takaici da baƙin ciki suka turnuƙe ta ta ji tamkar ta kunna kai izuwa cikin dajin amma da ta nuna babu halin hakan sai ta haƙura,
Kafin shuɗewar daƙiƙa hamsin fiye da mutum dubu na dakarun sun baƙunci barzahu, cikin hanzari sarkin yaƙi Hunaifu ya yi umarni a ja da baya, kamar taku goma sannan aka tsaya cak aka yi cirko-cirko.
Sai da ƙura ta lafa sannan aka jiyo ihu da gurnanin zakanya Juraima daga can sai ga su sun ratso ta duhuwar bishiyun sun bayyana a fili.
Nan fa aka fara kallon-kallo tsakanin ɓangarorin biyu cikin matuƙar ƙiyayyar juna da mugun tanadi.
Daga can dukkan ɓangarorin biyu suka yunƙura izuwa kan juna gami da falfalwa da azababban gudu, suna ihu da kururuwa mai firgita DANDAZON MAYAƘA, lokacin da ya rage saura kamar taku shida tsakani sai sarauniya abidat ta dako wawan tsalle daga kan dokinta tun a sama ta zare takobinta ta kaiwa Sunaila wawan sara.
Cikin baƙin zafin nama irin na GAWURTACCIYA ta zare takobin Saiful-imfal ta kare harin, koda takubban suka haɗu da juna nan take aka kwantsama wata tsawa gami da walƙiya marar daɗin sauraro wacce ta sanya bishiyu karairayewa suna haɗu izuwa kan mayaƙa da dama suka faɗi ƙasa matattu.
Sannan Abidat ta sauka ƙasa cikin gwaninta bisa diga-diganta.
A dai-dai lokacin ne bawa Himlas ya tari sarkin yaƙi Hunaifu, baiwa Sunaila da Suhaimat kuwa suka kutsa izuwa cikin abokan gaba.
A lokaci guda duka ɓangarorin suka haɗu da juna aka ruguntsume da azababban yaƙi mai matuƙar kwarjini muni daban tsoro,
Kaico! Haƙiƙa duk wanda bai ziyarci filin yaƙi ba to bai ga maƙurar tashin hankali ba. Domin yaƙi shine ke sanyawa a rasa rai, dukiya, da mutunci baki ɗaya.
Wohoho! Idan gwani ya haɗu da gani a filin fama dole yaƙi ya zamo gwanin sha'awa da tashin hankali.
A ɓangaren manyan giwaye biyu Sarauniya Abidat da jaruma Sulairat kuwa gaba ɗaya sun ɗauki hankalin duk wata halitta dake filin yaƙin, domin kuwa suna artabun ne cikin gwaninta da ƙwarewa tamkar na'ura ce ke sarrafa su, jikkunansu ba su kasance na jini da tsoka ba, ita kuwa zakanya Juraima aiki biyu yake tana kaiwa sarauniya abidat hari tare da farmakar dakaru tana yi masu ɓarna.
A ɓangaren Bawa Himlas da sarkin yaƙi Hunaifu kuwa sun wanzu suna kaiwa juna hare-haren cikin JURIYA DA BAJINTA irin ta 'yan MAZAN JIYA, duk sa'adda takubbansu suka haɗu da juna sai kaga tartsatsin wuta ya tashi gami da ƙara marar daɗin saurare.
Suhaimat da Sunaila kuwa duk inda suka sanya a gaba sai dai kaga dakaru na zubewa ƙasa magashiyan waɗansu matattu.
Wohoho! Haƙiƙa komai hassadar mutum idan ya ga yadda Waɗannan zaratan mataye ke ragargazar 'yan maza suna maishe su mataye, dole ne ya jinjina masu ya tabbatar cewa tabbas sun cika mataye masu kamar maza kuma zaratan mayaƙa.
Sai da aka shafe tsawon sa'a ɗaya da rabi ana wannan ɗauki ba daɗi.
Nan fa ƙura ta turnuƙe sararin samaniya tamkar hadari ya gangamo, ƙarar karafniyar ƙarafa, ihu da kururuwar mazaje haɗe da haniniyar dawakai suka cika dodon kunne.
Haƙiƙa a wannan rana dakarun sarauniya Abidat suna ganin tashin hankalin da ba su taɓa ganin tamkar ta ba.
Ana cikin wannan karon batta ne sarauniya Abidat ta kaiwa Sulairat wani wawan sara da takobinta a kafaɗa da nufin tsinke mata wuya.
Cikin wani irin baƙin zafin nama Sulairat ta wurƙila da zillewa harin gami da mayar da martani, koda Abidat ta sanya takobin da nufin karewa take ta karya gida biyu ta faɗi ƙas.
Kafin ta yi wani yunƙuri Sulairat ta dunƙule hannunta ɗaya ta kirɓa mata wawan naushi a fuska, saboda ƙarfin naushin sai da Abidat ta yi sama ta sauka daga kan dokin ta tayi katantanwa sau biyu sannan ta faɗi ƙasa amma sai ta miƙe tsaye zumbur!
Tana mai gyara tsayuwarta, koda ta sanya hannunta ta shafa kumatunta nan take taga jini a inda Sulairat ta naushe ta ɗin.
Koda ganin hakan sai sarauniya Abidat ta cika matuƙar baƙin ciki, kawai sai ta taƙarƙare ta kwarara wawan ihu ta zare sabbin makamai biyu a jikinta ta sake afkawa Sulairat a karo na biyu, suka ruguntsume da sabon artabu.
Abu kamar wasa sai gashi dukkanin makaman yaƙin Abidat sun karairaye sun faɗi ƙasa.
Abin da bata sani ba shine har abada babu wani makami da zai iya yin tasiri akan takobin Saiful-imfal, bisa wannan dalili ya sanya makamanta suka lalace.
Nan fa taurarin biyu suka ja da baya suna haki da zufa, suna hararar juna tamkar waɗansu zakaru saboda yadda suka bawa hammata iska.
Ita zakanya Juraima sai ta dinga buga ƙafarta ɗaya a ƙasa tana gurnani domin shirin kar-ta-kwana.
Ana cikin wannan hali ne kwatsam! Bazato babu tsammani sai aka ga sararin samaniya ta yi duhu dunɗum! Tamkar dare biyu ne ya haɗu waje guda, sannu a hankali sai aka hango waɗansu irin halittu marasa adadi na ketowa daga cikin gajimare suna sauka a bisa turba, duk sa'adda ɗayansu ya saukan sai ƙasa ta amsa, ya yin da halittun suka kammala sauka sai suka yiwa dajin ƙawanya.
Nan fa dawakai suka firgice suka kama haniniyar suna zubar da mahayansu suna nausa cikin daji bisa arba da suka yi da