Showing 3001 words to 6000 words out of 24725 words

Chapter 2 - KARSHEN ZALUNCI Complete Document by Sarkin Marubutan Yaki .txt

23 Nov 2024

3225

baiwata kuma likitoci sun tabbatar mini da hakan."
Koda jin hakan farin ciki ya turnuƙe Sarki Urwat har hawaye suka zubo daga idanuwanshi ya rungume Suhaimat suna masu fashewa da kukan farin ciki, sai da ƙyar da siɗin goshi sarki ya janye jikinshi daga na Suhaimat suka yi bankwana, suna masu karanto waƙoƙin baitoci. Dake nuna alamun tsantsar so da ƙauna.
Inda a ce mutum yana tsaye a wannan waje a lokacin da waɗannan masoya biyu ke zubar da hawayen begen rabuwa da juna dole ne ya kamu da tausayin su ainun, ya tabbatar da cewa babu abin da yafi rabuwa da masoyi ciwo.
Kai tsaye Sarki Urwat ya fice daga gidan sarautar ya nufi inda ayarin su suke yana isa aka kawo mashi doki ya kama ya haye sannan ya sakar mashi linzami ya ɗauki sauran ayarin suka mara mashi baya, sai da jama'a suka yi masu rakiya har izuwa bakin gari sannan su Sarki Urwat suka ɗauki hanya aka fara tafiya aka nausa izuwa cikin daji.
Da aka fara wannan tafiya sai Sarki Urwat ya yi umarni aka sanya raƙuman dake ɗauke da dukiya da guzuri a tsakiyar, jama'a suka suka yi mata ƙawanya.
Sannan dakarun rakiya suka rabu gida biyu, kaso ɗaya kewaye jama'a kaso na biyu suka sake rabuwa gida huɗu, suka tsaya a gabas, yamma, kudu da arewa, domin tabbatar da tsaro.
Daga birnin Nurul-Kusuf izuwa birnin Sin tafiyar kwana biyar ce ba tare da yada zango ba, amma da yake su Sarki Urwat suna so ne su isa a cikin ƙanƙanin lokaci sai ya zamana ko yada zango ba a yi ba, kuma suna tafiya ne ba dare ba rana. A ranar kwana na biyu ne da La'asar sakaliya su Sarki Urwat suka iso ƙofar birnin sin,
kai tsaye dakaru masu gadi suka wangame masu Ƙofar suka kunna kai zuwa ciki.
Yayin da suka isa fada sai suka tarar fadar ta cika maƙil da jama'a duk inda mutum ya kai duban shi a wannan lokaci fadar ta cika maƙil da bil'adama rututu, tamkar dandazon kiyasai.
Fadar ta kasance tanƙamemiya da aka ƙawata ta da nau'ikan kayan ƙawa da alatun more rayuwa iri daban-daban, wani abin ma mutum bai taɓa gani ko jin sunan shi ba, girman fadar ya kai na wani ɗan ƙaramin gari, kai tsayawa misalta tsaruwa da ƙawatuwar fadar ya huce tunanin mutum sai dai abin da idanuwa suka gani kawai.
Bisa kan wata ƙasaitacciyar karagar mulki da aka sana'anta ta jauhari aka yi matattakala biyar da dutsen zubardaju.


BABI NA UKU


Wata tsaleliyar kyakkyawar budurwa ce ta gaban kwatance.
Tana da matsakaicin kaurin jiki ita ba doguwa ba ce ba gajera ba, fatar jikinta fara ce mai ratsin baƙi, tana dara-daran idanuwa farare ƙwal masu haske tamkar tacecciyar madarar shanu, ɗigon cikin su yakasance baƙi siɗik, tana da dogon hanci mai ɗaukar hankali, a ƙasan shi an tsaga wani madaidaicin baki da laɓɓanshi suka kasance jajur. wuyanta dogo ne mai kyawu tamkar na barewa, ƙirjinta a cike yake kuma tsaye ƙyam! Bai ranƙwafa ba tamkar nunanniyar gwanda, saboda rigar dake sanye a jikinta har kana iya hangen sheƙin fatar su. Cikinta a shafe yake tamkar bata taɓa cin komai ba, ƙugunta a tsuke yake ta gaba daga baya kuma ya yi tudu ainun ta yadda koda kofin lemu aka ɗora zai zauna daram akai. Tana da sharɓa-sharɓan cinyoyi masu ɗaukar hankali, yatsun hannuwanta da ƙafafuwa zara-zara ne, gashin kanta baƙi ne mai ƙyalli ya zuwa izuwa gadon bayan ta har zuwa kan kwankwasonta. sanye take cikin koriyar alkyabba mai ratsin fatsi-fatsi. sanye a kanta akwai kambun Sarauta da aka yi shi da zunzurutun zinare yana sheƙi da ɗaukar idanu.
Wohoho! Haƙiƙa komai nisan gari da wani a gaban shi. Kuma komai sammakon ka wani a hanya ya kwana.
Komai hassadar mutum idan ya yi arba da wannan budurwa dole ne ya tabbatarwa da kanshi cewa ta kai maƙura a kyan diri da sura.
Babban abin da ya ƙara tona asirin kyawunta shine duk sa'adda ta yi murmushi sai kyawawan fararen haƙoranta sun bayyana, fuskarta na fitar da sheƙin kyawu tamkar hasken farin wata.
Babu wani ɗa namiji mai hankali da zai yi tozali da wannan kyakkyawar sura face ya kamu da matukar kaunarta.
Ba wata bace wannan budurwa ba face Sarauniya Abidat.
Sarauniya Abidat Bintu Hatyal ta kasance gawurtacciyar Basadaukiya mai dakawa maza gumba a hannu, ta shahara ainun a sanin ilimin tsafi gami da tarin dukiya, daɗin daɗawa kuma ta tara zakwakuran MAYAƘA masu juriya a filin daga.
Bisa wannan dalili ya sanya take kai farmaki izuwa ƙasashe da biranen da ke maƙwabtaka da ita domin ta faɗaɗa girman masarautarta.
Tsananin zaluncin Sarauniya Abidat ya zarce tunanin mutum, domin babu wanda ta ragawa tsakanin talakawanta, attajirai har ma da fadawanta.
Akwai wata rana da Sarauniya Abidat ke zagayawa cikin kasuwa domin ganin yadda al'amuran cinikayya ke gudana.
Tafe take a bisa ingarman doki cikin ƙayatattun tufafi ta rufe fuskarta da rawani idanuwanta kaɗai ake gani, waɗansu irin gabza-gabza samudawan dakaru ne ke take mata baya, hannayen su ɗauke da miyagun makamai sai muzurai suke yi tamkar za su ci babu, kallo ɗaya za ka yi masu ka fahimci cewa murmushi bai taɓa wanzuwa a kan fuskokinsu ba.
Duk wajen da Sarauniya Abidat da dakarun suka durfafa a kasuwar sai dai ka ga yara da manya na zubewa ƙasa suna kwasar gaisuwa cikin ladabi, kuma suna darewa suna buɗa masu hanya tamkar sun hango mutuwarsu, ko ciniki ake yi da zarar su Abidat sun durfafo wajen sai ka ga masu siye da sayarwa sun zubar da kayayyakin dake hannayensu, sun faɗi ƙasa sun kwashi gaisuwa.
Haka dai Sarauniya Abidat da tawagarta suka ci gaba da tafiya suna ratsa layuka da unguwannin kasuwa.
Ana cikin wannan tafiya ne Sarauniya Abidat ta hango wani dattijo yana gyara waɗansu kayan marmari a cikin kwandon kaba, har ya zaman tazarar dake tsakaninsu bata huce taku shida ba amma dattijon bai daina aikin da yake ba ya zo ya kwashi gaisuwa.
Koda ganin hakan sai Abidat ta fusata ainun zuciyarta ta kama tafarfasa tamkar za ta kone bisa ganin yadda dattijon ya nuna rashin ladabi a gareta.
Cikin matukar fushi Abidat ta kama linzamin dokinta ta sauko ta yiwa dakarun ta inkiya da wutsiyar ido.
Tamkar dakarun sun san abin da take nufi sai kawai suka je suka cakumo wannan dattijo suka gurfanar da shi a gaban ta
Kawai sai Abidat ta zaro wata 'yar siririyar wuka a damtse ta yanke kunnen dattijon na dama, saboda tsananin raɗadi da zogin da dattijon ya ji bai san sa'adda ya kurma wawan ihu ba a lokacin da jini kezuba daga wajen, cikin alamun rashin imani Sarauniya Abidat ta sake yanke masa dayan kunnen na ɓarin hagu jini ya yi tsartuwa gami da feshi.
Haka ta ci gaba da yankewa dattijon ƙananan gaɓoɓin da ke jikinshi. Haƙiƙa Sarauniya Abidat ta cika AZZALUMA ta gaban kwatance, domin komai rashin imanin mutum idan ya ga yadda dattijon ke ihu da koke-koken neman agaji dole ne ya tausaya masa ainun.
Da yawa daga ckin jama'ar da abin ke wakana a kan idanuwansu ba su san sa'adda ƙwalla ta cika muasu idanu ba suka fara zubar da hawayen tausayi.
Koda Sarauniya Abidat ta ga cewar ta yanke duk wata gaɓa da ke jikin dattijon sai kawai ta takarkare ta bushe da dariyar mugunta.
A dai-dai wannan lokaci ne numfashin dattijon ya sarƙe jikinshi ya sandare ya faɗi ƙasa, alamar dake nuna rai ya yi halinshi.
Kawai sai aka jiyo ihu da kururuwa a tsakiyar jama'a, koda Sarauniya ta duba sai ta ga ashe matar wannan dattijon ce ta rugo izuwa wajen, tana mai rusa kuka, hannayenta riƙe da jariri ɗan shekaru biyu da haihuwa.
Kafin matar dattijo Safwan ta iso wajen, Sarauniya Abidat ta zaro wani dogon mashi a jikin badakaren ta jefawa matar, mashin ya tafi cikin matsanancin gudu a cikin iska ya soke a ƙirji, ya fasa ta gadon bayanta jini ya kwaranya gami da tsartuwa, take ta sulale ƙasa tana shure-shuren mutuwa, kafin wani lokaci idanuwanta sun ƙafe, komai na jikinta ya daina motsi, alamar ta baƙunci barzahu, amma wani abu da ya ɗaurewa Sarauniya Abidat da sauran jama'a kai shi ne, duk da kasancewar matar dattijo Safwan ta sheƙa barzahu babu rai a tare da ita, amma hannunta riƙe yake da jaririnta gam! Kuma fuskarta cike da annuri.
Cikin matuƙar mamaki Sarauniya Abidat ta nuna jaririn da ɗan yatsan ta na hagu, take jaririn ya baro hannun mahaifiyarshi ya sauka a hannayenta biyu yana mai tsala kuka, koda ta ƙura wa jaririn idanu sai ta ji zuciyarta ta buga da ƙarfi, al'amarin da ya yi matukar ba ta mamaki, kenan ta ce a cikin ranta, "Me ya sanya da na haɗa idanu da wannan jariri zuciyata ta buga da ƙarfi alhalin hakan bai taɓa faruwa a gare ni ba?"
Amsar tambayar da ta kasa bawa kanta kenan kawai sai ta miƙawa wani badakare jaririn, sannan ta kama linzamin dokinta ta hau, ta zabure shi ta shige gaba dakarun ta suka mara mata baya, yayin da aka isa gidan Sarauta sai Saruaniya Abidat ta bayar da renon jaririn ga wata baiwarta mai suna Sunaifa, daga wannan rana Sarauniya Abidat ta kasance dare da rana face bincike bisa halarar tsafinta domin ta gano sirrin da ke tattare da jaririn dattijo Safwan.
Sa'adda ya rage saura kamar taku huɗu tsakanin su Sarki Urwat da karagar mulki sai suka zube ƙasa bisa gwiwoyinsu suka kwashi gaisuwa ga Sarauniya Abidat, cikin matuƙar taƙama da BAKAR IZZA Abidat ta karɓi gaisuwar.
Shiru ne ya mamaye fadar na ɗan wani lokaci sai daga bisani ne Sarki Urwat ya dago da kanshi sama ya buɗi baki cikin ladabi ya ce "Ya shugabata gani na amsa kiran ki kuma tare da abin da ki ka buƙata domin FANSAR RAYUKAN jama'ata."
Koda jin wannan batu daga bakin Sarki Urwat sai Sarauniya Abidat ta miƙe tsaye tsam! Daga kan karagarta ta tako
matattakalar fadar ta sauko ƙasa, sannan ta taka da kafafuwanta har izuwa inda Sarki Urwat da jama'arshi ke duƙe ta shiga kewaya su tana mai bushewa da dariyar mugunta a lokaci guda kuma sai ta turɓune fuska tamkar an aiko mata da SAKON MUTUWA ta dubi sarki Urwat ta ce "ya kai Urwat ka bi dukkanin wani umarni da muka baka sai dai a halin yanzu ina so ka umarci mutanen ka su fice daga birnin Nurul-Kusuf su nemi wajen da za su zauna."
Koda jin wannan batu daga bakin sarauniya Abidat sai idanun sarki Urwat suka zazzaro, cikin alamun matuƙar kaɗuwa da firgici ya dubi sarauniya Abidat cikin biyayya ya ce.
"Haba ya sarauniyar duniya ta ya ya zan cewa al'ummata su fice daga birnin Nurul-Kusuf bayan cewa tun iyaye da kakanni suke zaune sannan fiye da rabin harajin da na kawo miki sune suka haɗa rabinshi ina neman alfarma a wajen ki da ki janye wannan ƙudiri na ki."
Da jin wannan batu sai sarauniya Abidat ta bushe da dariyar mugunta a karo na biyu daga bisani ta haɗe rai ta ce, "Tabbas duk tsuntsun da ya ja ruwa shi ruwa kan doka, kuma rashin sani ya fi dare duhu" ya kai Urwat ka yi sani cewa, tun da nake a rayuwata kai ne mutum na farko da na taɓa faɗar magana ya ce ba haka ba, yanzu zan gindaya maka sharuɗɗa guda biyu dole ne ka zaɓi ɗaya daga ciki. Na farko shi ne ko dai kai da jama'arka ku fice daga birnin Nurul-Kusuf ko kuma ku bayar da ZARATAN MAYAKAN KU mutum hamsin."
Sa'adda Sarki Urwat ya ji waɗannan sharudɗa daga bakin Abidat sai ya sake marairaicewa, yana mai yiwa yi mata magiya a kan ta janye waɗannan sharudɗa na ta.
Al'amarin da ya jefa tausayi a zukatan jama'ar kenan kuma zukatansu suka kama tafarfasa tamkar za su kone, bisa ganin yadda Urwat ke ƙasƙantar da kanshi a gaban wacce bata huce 'yar cikin shi ba.
Su kansu sauran jama'ar fadar sai da suka kamu da matukar tausayin shi.
Ya yin da Abidat ta fahimci cewa Sarki Urwat ba shi da niyyar amincewa da ɗaya daga cikin sharuɗɗan da ta gindaya mashi sai kawai ta yi wuf ta zare wata sharɓeɓiyar takobi a gadon bayanta ta datse masa wuya, take kanshi ya yi fitar burgu gangar jikin ya faɗi ƙasa rikica! JINI ya yi tsartuwa haɗe da feshi tamkar an buɗe kan famfo.
Kafin ɗaya daga cikin jama'ar marigayi sarki Urwat ya yi wani yunƙuri sarauniya Abidat ta afka masu da azababben yaƙi cikin abin da bai gaza daƙiƙa talatin ba gaba ɗaya ta sare kawunansu ta zubar da gawarwakinsu a ƙasa ɗayan su bai tsira da rayuwarshi ba, nan fa jini ya dinga malala tamkar an ɓalle ƙorama. Sannan aka ga Abidat ta runtse idanunwanta ta karanto waɗansu ɗalasiman tsafi, tana gama rufe bakinta sai aka ga wani baƙin hayaƙi ya ratso daga cikin karkashin ƙasa ya tashi izuwa saman fadar ya ɓace ɓat! Kawai sai ta sake bushewa da dariyar mugunta tamkar ba za ta daina ba.




BABI NA HUƊU


A can birnin Nurul-Kusuf kuwa, shugaba Hushaib na zaune a fada bisa karagar mulki a matsayin halifan Sarki Urwat ana gudanar da sha'anin mulki cikin walwala. Ana cikin wannan hali ne kwatsam! Sai aka ga sararin samaniya ta yi duhu dunɗum! tamkar hadari ya gangamo, nan take gari ya kaure da guje-guje haɗe da iface-ifacen jama'a.
Har shugaba Hushaib ya buɗi baki da nufin ya ce wani abu sai aka hango sarkin yaƙi ya shigo fadar hankalinshi a matuƙar tashe, tun kafin ya iso inda karagar mulki take shugaba Hushaib ya je ya tare shi ya dube shi cikin alamun tsananin damuwa ya ce, "Ya dirkar birnin Nurul-Kusuf shin mene ne ke faruwa?"
Koda jin wannan tambaya sai sarkin yaƙi Ikram ya dube shi cikin tashin hankali ya ce, "ya shugabana ka yi sani cewa tabbas yau ce rana ta farko da zamu fita yaƙi iya tsawon kafuwar wannan birni namu domin kuwa waɗansu irin halittu ne suka sauka a wannan birni namu, ni kaina tunda nake ban taɓa ganin irinsu ba ko a labari.
Koda jin wannan batu daga bakin sarkin yaƙi Ikram sai shugaba Hushab ya dube shi cikin kaɗuwa ya ce, "Haƙiƙa na ji a jikina cewa shugaba Urwat da tawagarshi na cikin halin tsaka mai wuya kuma waɗannan halittu da suka bayyana a garemu ba sa rasa nasaba da abin da ya faru da su a can birnin Sin ɗin saboda haka sai ka yi umarni a yi maza a je a buga kugen yaƙi domin a tari abokan gaba..."
Kafin shugaba Hushaib ya gama rufe bakinshi sarkin yaƙi ya juya, ya fice daga fadar da sauri.


***
A can fadar sarauniya Abidat kuwa sai da tayi dariya ta ishe ta sannan ta yi umarnin a kwashe gawarwakin sarki Urwat da jama'arshi kuma aka goge jinin da ya zuba a fadar, sannan ta koma kan karagarta ta mulki ta hakimce.
Kawai sai ta zura hannunta a cikin aljihunta na hagu ta ɗauko madubin tsafinta wanda duka tsawonshi bai wuce girman faɗin tafin hannunta ba ta shafeshi da hannun hagu tana mai karanto waɗansu ɗalasiman tsafi, tana gama rufe bakinta sai ga taswirar abin da ke gudana a birnin Nurul-Kusuf ya bayyana a kan madubin.
Sa'adda sarauniya Abidat ta ga yadda waɗannan miyagun halittu da ta tura ke hallaka jama'ar marigayi Urwat ba ji ba gani tamkar suna kashe kiyasai, hatta dabbobin garin ba sa
ƙyalewa ballanatana ƙananan yara.
Koda ganin wannan al'amari sai farin ciki ya cika zuciyarta haka dai ta ci gaba da kallon yadda artabun ke gudana har kawo izuwa lokacin da halittun suka kammala kashe duk wata halitta da ke birnin kasancewar su ma su shugaba Hushaib ba karamar ɓarna suka yi masu ba.
Jim kaɗan sai taswirar birnin ya ci gaba da canja launi har ya nuno taswirar wata mata tana gudu a bisa doki, a cikin daji waɗannan halittu na biye da ita a baya suna so su cimmata amma sun gaza.
Ba wata ba ce wannan mata ba face Suhaimat matar marigayi sarki Urwat, Suhaimat na cikin gudun ne ta iso wani waje mai tattare da kwazazzabai al'amarin da ya sanya gudun dokinta, ya ragu kenan, kuma ya bawa ɗaya daga cikin halittun dama ya samu nasarar mako ta daga kan dokinta.
Kash! Hakika rashin sani ya fi dare duhu, ashe inda dokin Suhaimat ya durfafa wani ƙaton rami ne wanda a ƙarƙashin shi akwai ruwa, koda wannan halitta ta make Suhaimat daga kan dokin sai ta ci gaba da mirginawa a ƙasa ya yin da ta isa daf da ramin ta ga inda za ta afka sai kawai ta taƙarƙare ta kwarara wawan ihu take numfashinta ya ɗauke.
Sa'adda taswirar ta zo dai-dai nan akan madubin tsafin sarauniya Abidat sai ta bushe da dariyar farin ciki, ta mayar da madubin izuwa cikin aljihunta sannan ta sake miƙewa tsaye tsam! Daga kan karagar mulkin ta ta durfafi wata ƙofa da za ta sada ta da gidan sarautar dakaru na take mata baya.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login