Showing 9001 words to 12000 words out of 24725 words

Chapter 4 - KARSHEN ZALUNCI Complete Document by Sarkin Marubutan Yaki .txt

23 Nov 2024

3222

a zancen shi sai Sunaila ta sake fashewa da kukan farin ciki tana mai sake rungume shi tana cewa, "Ina alfahari da kai ya ɗana kai ne cikar burin rayuwata na tabbata cewa kai ne za ka kawo KARSHEN ZALUNCIn sarauniya Abidat daga doron kasa."
Wannan shi ne abinda ya faru tsakanin baiwa Sunaila da Bawa Himlas dan dattijo Safwan, wanda Sarauniya Abidat ta bayar da renonsa a hannun Baiwa Sunaila bayan ka yiwa mahaifinsa kisan gilla.




BABI NA TAKWAS


A can dajin Baitul-Shazwas kuwa, Suhaimat da jaririyarta na cikin ƙoshin lafiya walwala da jin daɗi.
Sannu-sannu ba ta hana zuwa sai dai a daɗe ba a je ba sai kwanci tashi sai ga shi jaririyar Suhaimat ta cika shekara sha biyar da haihuwa, da ranar haihuwar ta zagayo ne aka raɗawa jaririya suna Sulairat bintu Urwat.
Kyan ɗa ya gaji ubanshi, kamar yadda marigayi sarki Urwat ya kasance GWARZON MAYAƘI ma'abocin hikima, haka Sulairat ta kasance.
Wasu lokutan idan Sulairat da zakanya Juraima na bawa junansu horon yaƙi sai ka ga Sulairat ɗin ta samu nasara akan Juraima. kasancewa Sulairat ba ta da abokan ɗebe kewa sai zakanya Juraima sai suka shaƙu ainun kwanciyar barci ce kaɗai ke raba su ko farauta Sulairat za ta je bisa gadon bayan Juraima take hawa su tafi tare.
Idan a kazo batun kyawu kuwa Sulairat ta gaji mahaifiyarta Suhaimat har ta ɗarata ne sa ba kusa ba, kasancewar a koda yaushe ba su da wani abin kalaci da ya wuce naman tsuntsaye da nau'ikan kayan marmari sai ya zamana cewa fatar jikinta ta yi lub-lub ta yi kyau da sheki tamkar a tsaga ta jini ya fito.
Wata rana da hantsi bayan Sulairat da mahaifiyar ta sun yi kalaci suna zaune a cikin wannan kogon dutse sai Sulairat ta dubi mahaifiyarta ta yi gyaran murya sannan ta ce.
"Ya Ummina shin ina Abbana yake, ya tafi ya bar mu a cikin wannan daji, ko kuwa mu kaɗai ne bil'adama a wannan duniya?"
Koda jin wannan tambayoyi sai Suhaimat ta yi murmushi mai taushi a gare ta, sannan ta dubeta ta ce, "Ke kuwa me ya sa ki ka yi mini waɗannan tambayoyi, bayan cewa kina tare da ni ina yi miki duk wani abu da ki ke buƙata na rayuwa."
Sulairat ta ce "ya ummina ke kuwa mene ne ya sa duk sa'adda na yi maki waɗannan tambayoyi ba kya amsa su, tabbas akwai wani al'amari da kike ɓoye mini wanda ba kya so na sani."
Koda ji wannan batu sai zuciyar Suhaimat ta buga da ƙarfi kuma hankalinta ya dugunzuma ainun ta ce a cikin ranta, tabbas rashin bayyana wa Sulairat gaskiyar lamari na iya sanyawa mutuncina ya ragu a idanunta, sannan kuma idan har na sanar da ita dole ne ta ce za ta je ta ɗauki fansa.
Wani ɓangaren a zuciyarta kuma na cewa da ita ai babu wata mafita face ki sanar da Sulairat gaskiyar lamari, domin ai duk daren daɗewa dole ne ta sani.
Koda Suhaimat ta zo daidai nan a tunaninta sai ta dubi Sulairat ta ce "Ya 'yata ki yi sani cewa a yau ne zan ba ki amsar tambayoyin da ki ka daɗe kina yi mani, na cewa ina abbanki yake."
Nan take Suhaimat ta shiga bawa Sulairat labarin mahaifinta sarki Urwat da irin kisan gillar da Abidat ta yi mashi tare da jama'ar birnin su, har kawo izuwa lokacin da zakanya Juraima ta ceci rayuwar su daga sharrin dakarun Abidat daga farko har ƙarshe ta zayyanewa Sulairat.
Sa'adda Suhaimat ta zo dai-dai nan a labarin ta sai ta fashe da kukan baƙin ciki tana mai rungume 'yarta su duka biyun suna zubar da hawaye tamkar ba za su daina ba.
Sai daga bisani ne Suhaimat ta janye jikinta daga na Sulairat har ta buɗe baki da nufin ta ce wani abu sai suka ji alamun motsi a bayansu, koda suka waiga sai suka ga ashe zakanya Juraima ce a tsaye idanunta sharkaf da hawaye.
Al'amarin da ya yi matuƙar bawa Sulairat da mahaifiyar ta mamaki kenan, abinda ba su sani ba shi ne dukkanin hirar da ta gudana tsakaninsu zakanya Juraima ta ji, saboda haka tsananin tausayinsu ne itama ya sanya ta zubar da wannan hawaye.
Suhaimat ta ci gaba da cewa, "Ba komai ne ya sanya na ɓoye miki wannan sirri ba, sai domin sanin cewa za ki iya yunƙurin ɗaukar fansa a kan sarauniya Abidat a halin yanzu.
"Ina so ki kwantar da hankalinki ki sani cewa lokaci zai zo da za ki shiga har cikin birnin Sin ki ɗauki fansa a kan Sarauniya Abidat ki kawo KARSHEN ZALUNCIn da take shimfiɗawa al'umma."
Da jin wannan ƙarin wajabi sai Sulairat ta ji ta daɗa ƙaunar mahaifiyarta fiye da ko yaushe.
Sannan ta sake duban mahaifiyarta ta ce "Ya Ummina idan ba za ki damu ba ina neman wata alfarma a wajenki."
Cike da matuƙar mamaki Suhaimat ta dube ta ta ce "faɗi alfarmar da kike nema a waje na ni kuwa zan yi miki ita."
Sulairat ta numfasa sannan ta gyaɗa kai ta ce, "alfarmar da nake nema a wajen ki ita ce ki amince na shiga birnin Sin domin kawai na ga yadda sauran bil'adama irinmu ke rayuwa."
Koda jin wannan alfarma sai Suhaimat ta dubi 'yarta cikin alamun tsananin damuwa ta ce, "Haba ya 'yata yanzu ta ya zan bar ki ki ziyarci birnin Sin bayan cewa a koda yaushe Sarauniya Abidat na farautar rayuwarki."
Ya yin da Sulairat ta zo nan a zancen ta, sai ta hango zakanya Juraima na yiwa Sulairat nuni da ta zo inda take.
Ba tare da gardamar komai ba Sulairat ta miƙe tsaye ta taka da kafafuwanta har zuwa inda zakanya Juraima ke tsaye, da zuwanta sai Juraima ta yi mata nuni da ta tona wani waje a kogon da ke saitin kafarta.
Cikin hanzari Sulairat ta tsugunna ƙasa ta sanya hannayenta biyu tana ƙwakule kasar wajen ta yi rami da girmanshi bai huce kamu ɗaya ba, sai ta ji ta taɓo wani abu tamkar ƙarfe ya yin da ta ciro shi, sai ta ga ashe wata sarƙa ce fara sol da aka yi ta da ƙarfe jauhari, sai sheƙi take yi tana ɗaukar idanu.
Kawai sai zakanya Juraima ta yi mata nuni da ta sanya sarƙar a wuyanta.
Sannan Juraima ta yi wa Suhaimat ishara da ta ƙyale Sulairat ta ziyarci birnin Sin tana yi mata nuni da cewa wannan sarƙa da Sulairat ta sanya a wuyanta za ta bata kariya har ta je ta dawo lafiya.
Koda fahimtar hakan sai Suhaimat ta dubi 'yarta ta ce "Na amince ki ziyarci birnin Sin kuma ina yi maki fatan samun nasara."
Da jin hakan sai murna ta kama Sulairat ta yi godiya ga mahaifiyrta sai ta juya ta fice
daga kogon dutsen, sai da zakanya Juraima ta yi mata rakiya har izuwa gaɓar dajin Baitul-Shazwas sannan ta dawo bayan ta dora ta a kan hanya.
Kai tsaye Sulairat ta tasamma hanyar da za ta sadata da birnin Sin tun a kan hanya ta fara cika da matuƙar mamaki har ta isa birnin Sin domin sau tari za ta haɗu da miyagun namun daji amma sai ta ga sun ratse sun ba ta hanya, tamkar ba su ganta ba, ƙiri-ƙiri gashi masu gadin ƙofa na ganinta amma haka ta kunna kai zuwa ciki ba tare da sun yi yunƙurin afka mata da yaƙi ba, da shigarta zuwa birnin sai ta kama kalle- kalle da dube-dube tamkar dan ƙauye ya shigo birni.
Abin da Sulairat ba ta sani ba shi ne matsawar tana sanye da wannan sarka da zakanya Juraima ta ba ta, babu wani mai cutarwa da ya isa ya ganta, ya kusanci inda take ballantana har ya cutar da ita.
Haka dai Sulairat ta wanzu tana tafiya a cikin birnin Sin ta wanzu tana ratsa layuka da unguwanni, ba tare da ta haɗu da wani abu mai cutarwa ba.
Tana cikin tafiya a kasuwa ne sai kawai ta hango jama'a suna guje-guje da iface- iface, maza da mata yara da manya. Nan fa aka dinga barin kayan abinci, masu ƙarfi suka dinga bangaje masu rauni suna zubewa a kasa ana tattaka su.
Al'amarin da ya yi matuƙar bawa Sulairat mamaki kenan, kawai sai ta koma gefe guda ta ja ta tsaya, tana mai zuba idanu, domin ta ga abinda ya sanya jama'a suke GUDUN CETON RAYUKA.
Tana nan tsaye kwatsam sai ta hango dakaru masu tarin yawa shirye cikin matsananciyar shigar yaki sun shigo kasuwar su bisa tsakiyar dakarun wani
ƙasaitaccen keken doki ne da aka yi mata ado kayan kyale-kyale na sarauta.
Bisa cikin keken dokin wata budurwa ce a kishingiɗe sanye da tufafi na alfarma.
Budurwar ta kasance kyakkyawa ta gaban kwatance, ma'abociyar dara-daran idanuwa farare kal a cikin su akwai ɗigon baƙi, hancinta siriri ne gwanin ban sha'awa, tana da madaidaicin baki wanda leɓɓanshi suka kasance jajur, ƙirjinta a cike kuma ya tsaya kyam! Tamkar nunanniyar gwanda fatarsu tana sheƙi da ɗaukar hankalin duk mai kallo. Sun cika tsaleliyar rigar jikinta tamkar za su fito waje, Gashin kanta baƙi sidik mai ƙyalli da sheƙi ya zuba har izuwa kan kafaɗunta.
Haƙiƙa duk inda kyawu yake wannan budurwa ta kai maƙura domin duk irin tsantsar kyawu na Sulairat da ta yi arba da wannan kyakkyawar halitta sai da ta raina kanta ta tabbatar da cewa gaba da gabanta aljani ya taka wuta."
Ba wata ba ce wannan kyakkyawar budurwa da ke kishingiɗe a cikin keken dokin ba face Sarauniya Abidat.
Sulairat ta ƙurawa budurwar idanu ta sa kare mata kallo, a sannan ne ta fahimci cewa wannan budurwa ba wata ba ce face Sarauniya Abidat wacce take neman ta ruwa a jallo.
Nan fa zuciyarta ta kama tafarfasa tamkar za ta ƙone kuma ta ji ƙiyayyar Abidat ta daɗu ainun a zuciyarta.
Ya yin da ya zamana cewa sarauniya Abidat da dakarunta sun matso daf da inda Sulairat take tsaye, sai Sulairat ta hango wani zabgegen kyakkyawan saurayi jikinshi ko riga babu face bante da ya rufe cibiyarshi zuwa cinyarshi, gashin kanshi ya zubo izuwa kan fuskarshi, hannayenshi da kafafuwanshi sanye suke cikin da sasari na baƙin ƙarfe yana jan keken dokin da Sarauniya Abidat ke ciki a maimakon ace dawakai ne ke janye da keken.
Nan fa Sulairat taji ta kamu da matuƙar tausayin saurayin, kuma ta tabbatarwa da kanta cewa, tabbas duk inda mutum ke tsammanin zaluncin Sarauniya Abidat ya wuce nan.
Ana cikin wannan hali ne wannan kyakkyawan sarauyi da ke janye da keken dokin ya dago da kanshi sama, ya kalli inda Sulairat ke tsaye sadda suka yi arba da fuskokin juna sai nan take a karo na farko a rayuwarsu suka ji sun kamu da matuƙar ƙaunar junansu, Sulairat ba ta san sa'adda ta sakarwa sarauyin wani tattausan murmushi ba mai tattare da tsantsar so da ƙauna.
Bisa mamaki sai Sulairat ta ga saurayin ya mayar mata da martanin murmushin, kuma ya tsaya cak daga jan keken dokin yana ci gaba da sakar mata lallausan murmushi.
Al'amarin da ya yi matuƙar ɗaurewa Abidat kai kenan, kuma ya fusata ainun ta dakawa badakaren dake kula da keken dokin tsawa.
Abin da ya ɗaure mata kai kuma ya bata mamakin shi ne ita dai ta duba ba ta ga komai ba amma mene ne ya sanya bawa Himlas kw kallon wajen
yana murmushi, abin da ya fusatat a kuwa shi ne ta ya Himlas zai daina tuka keken dokin.
Kafin sarauniya Abidat ta gama rufe bakinta badakaren dake kula da keken dokin ya daga bulalarshi sama ya zabgawa bawa Himlas, take inda ya dake shin ya dare jini ya yi tsartuwa ya zuba a ƙasa, amma har sai da badakaren nan ya yi mashi bulalar fiye da talatin amma Himlas bai daina kallon wajen da Sulairat take ba yana yi mata murmushin.
A ɓangaren Himlas kuwa, babban abin da ya ɗaure mashi kai kuma ya ba shi mamaki shi ne gashi dai kuru-kuru dakarun sarauniya Abidat na kallon na Sulairat amma ba su yi yunƙurin cutar da ita ba.
Koda Sulairat ta fahimci cewa matsawar wannan saurayi bai daina kallonta ba to wannan badakare ba zai daina dukanshi da bulala ba.
Sai kawai ta juya ta nufi hanyar da za ta fitar da ita daga birnin tana mai waigen saurayin suna jifan junansu da ƙayataccen murmushi mai tattare da tsantsar soyayya.
Sai da Sulairat ta ɓace ɓat! Sannan bawa Himlas ya yunƙura cikin juriya da jarumtaka ya ci gaba da jan keken dokin, a lokacin da raunukan da badakaren ya yi mashi suka shiga yi mashi zugi da raɗaɗi, ga zafin rana na ƙona tafin kafarshi.
Komai rashin imanin mutum babu yadda za a yi ya ga bawa Himlas a cikin wannan hali face ya kamu da matukar tausayinsa.




BABI NA TARA


A can dajin Baitul-Shazwas al'amarin Sulairat kuwa tun sa'adda ta fice daga birnin Sin zuciyarta cike da matuƙar ƙaunar bawa Himlas, sai ta ci gaba da saƙe-saƙe a zuciyarta har ta isa dajin Baitul Shazwas, da zuwanta sai suhaimata da zakanya Juraima suka tare ta cikin tsananin farin ciki suna yi mata sannu da dawowa.
Da yake a wannan lokaci duhun magariba ya kawo kai Suhaimat ta shiga haɗa masu abin kalaci, bayan da ta kammala ne sai ta zauna tare da 'yarta Sulairat domin su fara cin abincin.
Suna fara cin abincin ne Suhaimata ta lura cewa Sulairat na cikin damuwa, domin har sai ta yi loma biyar ba ta yi guda ɗaya ba, don haka sai kawai ta dube ta ta ce "Ya 'yata abar alfaharina shin ina dalilin wannan damuwa ta ki?"
Koda jin wannan tambaya sai Sulairat ta yi murmushi ga mahaifiyarta sannan ta ce "Babu wani abu da yake damuna ya immi kawai sai ina tuna irin zaluncin Sarauniya Abidat ne."
Suhaimat ta yi murmushi da yake nuna fahimtar wani abu game da furucin 'yarta ta dube ta a karo na biyu ta ce.
"Ya 'yata bai kamata ace kin ɓoye mani gaskiyar abin da yake damunki ba, domin kar ki manta cewa baki da kowa a duniya face ni kaɗai, bisa ga yadda fuskarki ta nuna alamu ba komai ne ya haddasa miki damuwa ba face tarkon soyayya ko ba haka ba ne?."
Koda jin wannan batun sai kunya ta kama Sulairat ta sunkuiyar da kanta ƙasa tana mai cewa, "ki gafarce ni ya ummina, haƙiƙa na yi kuskure da na ɓoye maki gaskiyar abin da yake damuna."
Suhaimat ta dafa kafaɗun 'yarta Sulairat da hannayenta biyu ta ce, "Ya 'yata ki yi sani cewa ba wai zan hana ki ki yi soyayya ba ne, sai dai ina gargaɗin ki da ki kiyayi so, domin babu komai a cikinsa face tsantsar wahala da takaici."
Cikin alamun matuƙar mamaki Sulairat ta dubi mahafiyarta ta ce, "Ya Ummina shin ta ya ya so zai zama tsantsar wahala da takaici, bayan cewa rayuwar ɗan adam tana tabbata ne idan akwai so."
Suhaimat ta yi lallausan murmushi mai taushi a gareta ta ce, "Kwarai kuwa maganarki gaskiya ce amma da a ce kin karanta hikayar manyan sarakunan duniya uku dake cikin KUNDIN HIKAYA haƙiƙa da kin gasgata abin da na faɗa miki."
Da jin hakan sai mamaki ya kama Sulairat ta tambayi kanta a cikin zuciyarta tana cewa, "Shin me ya faru da manyan sarakai uku me so ya zamo masu a rayuwa?"
Amsar tambayoyin da Sulairat ta kasa bawa kanta kenan kawai sai ta ɗauraye hannunta da ruwa a cikin wani ɗan ƙaramin akushi, sannan ta je inda shimfiɗarta take ta kwanta, domin ta huce gajiyar da ke tattare a jikinta, amma sai ta kasa rintsawa, ba komai ne ya haddasa hakan ba face tsananin bege da tunanin bawa Himlas, domin duk abin da ta kalla a kogon dutsen sai ta ga fuskar bawa Himlas take gani yana yi mata murmushi mai taushi, haƙiƙa Sulairat ta yi zurfi a kaunar bawa Himlas wacce ba za ta taɓa jin kira ba, haka ta kasance a cikin wannan hali har barci ya yi awon gaba da ita. Wannan shi ne abin da ya faru da Sulairat bayan ta dawo daga ziyara izuwa birnin Sin.




BABI NA GOMA


A can brinin Sin kuwa, washegari tunda duku-dukun safiya fadar Sarauniya Abidat ta cika ta batse da jama'a maza da mata yara da manya, duk inda mutum ya kalla kawunan bil'adama ne rututu babu masaka tsinke tamkar dandazon kiyasai.
Abin tambaya anan shi ne ko me ya sanya jama'ar barin gidajensu suka halarci wannan fada tunda duku-dukun safiya haka?.
Ba komai ne ya sanya hakan ba sai domin a yau ne sarauniya Abidat za ta yankewa baiwa Sunaifa da bawa Himlas hukuncin kisa ta hanyar sare masu wuya.
Bisa wani BOYAYYEN AL'AMARI da ta gano a cikin halarar tsafinta a daren jiya, abinda ta gano din kuwa shi ne.
Ba wani abu bane ya sanya bawa Himlas yake wannan murmushi a jiya a lokacin da suke tafiya a cikin kasuwa ba har ya dai na jan keken dokin da take kai ba face arba da ya yi da Sulairat, har suka kamu da soyayyar junansu.
Abin da zai ƙara tabbatar maka da hakan shi ne idan ka yi duba izuwa ga waɗansu manyan diraku da ke tsakiyar fadar, za ka yi arba da bawa Himlas da baiwa Sunaila ɗaure cikin sasari na baƙin ƙarfe hannu da ƙafa.
Fiye da tsawon rabin sa'a jama'a na cece-kuce kowa na faɗin albarkacin bakinshi bisa jinkirin fitowar Sarauniya Abidat.
Ana cikin wannan hali ne sai aka jiyo bushin algaita haɗe da bugun tambura daga cikin gidan sarauta alamar ga Sarauniya Abidat nan tana gab da bayyana.
Jim kaɗan sai ga Sarauniya Abidat

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login