Showing 6001 words to 9000 words out of 55178 words

Chapter 3 - KARUWAR GIDA BOOK COMPLETE NA MAMAN JABIR.txt

29 Nov 2024

3371

kyautata mata,baya son yaga wani abun da zai 6ata mata zuciya ko ranta, kullum a gida yake kusan yini ko gurin sana'arshi bai ciki fita ba yana manne da ita"fahintar da ZAINAB tayi na cewar RABI'U d'anson biyan buk'atane da jin dadi daga mace, wannan ce ta bata damar daura dammarar yi masa duk abinda yake so shima," ko kadan bata nuna gajiyawarta akanshi wajan jure masa akan duk wata buk'atuwa tata zuwa gareshi"ko kadan shima RABI'U baya gajiyawa da jikin na ZAINAB domin kuwa hakan yafi so tunda yanxu babu wani abu da zaiyi masa birki 'ya ce an dauke ta,tana hannun kakanninta, abu kamar wasa dai ZAINAB batayi wata biyu da yaye MARIYA ba wani cikin ya sake shigarta haka ta fara amaye_amaye kamar dai lkcn da tasami cikin MARIYA" nan fa RABI'U ya fara jin haushinta had'i da cin zarafinta" kullum fada da masifa babu kama hannun yaro" Haka RABI'U ya dinga gara ZAINAB,daga kashe ya bijiro mata da cewar lallai sai ta zubar da cikin jikinta" ZAINAB kin yadda tayi da kudirin RABI'U" shi kuwa ya fita harkarta" ganin hakan tasa ZAINAB ta shirya ta je gidan iyayenshi domin sanar musu da halin da suke ciki ita da mijinta, koda ZAINAB taje kasa gaya musu tayi duba da yadda dan nasu yake kyauta ta musu tasan idan tagaya musu ba lallai su yadda ba kuma kamar ta ragewa kanta k'imane a idon surakan nata,duk da mu'amalar da yake nuna mata daban wacce yake nunawa iyayenshi daban" wannan ce tasa ZAINAB ta rasa kwarin gwiwar gaya musu komai"sai da yamma likis ta koma gida yammar da bazata manta da ita ba a rayuwar ta ,tana komawa gida ta tsinci kanta a wani irin yanayin mai ban tausayi domin kuwa wani irin jiri ta ringa gani hadi da ciwan kai mai tsanani har wani Kore_Kore take ganin garin yana juya mata, da k'yar ta k'arasa shiga d'akinta ta sami guri ta kwanta,tana faman kiran sunan ALLAH, batafi mutuna goma da shiga wannan halin ba sai ga RABI'U ya dawo gida" yana shigowa ya sameta a wannan halin yi yayi kamar bazai bata agaji ba domin gani yake kamar karya take ganin ciwan nata yana qara ta'azara ne yasa ya budi baki ya tamabayeta ko lfy?" Amsawa ZAINAB tayi da cewar batada lfy hadi da sanar mishi irin yanayin da take ji" sannu kawai yace mata ya sake kada kanshi waje ya fita" koda ya fita chemist ya wuce yaje ya sayo mgunguna ya kawowa ZAINAB yace ta tashi tasha" a gwaugwauce tasha maganin ido rufe domin ji take kamar ranar zata bar duniya" ALLAH sarki ZAINAB shan maganin nata ke da wuya baifi mitin biyu zuwa uku ba ciwo ya k'ara tsananta tun tana iya fahintar inda kanta yake har ta daina ganewa" tana cikin wannan halin ne jini ya yanke mata ya fara zuba ganin zubar jinice ta kara rikitar da jikin ZAINAB kamin kace wani Abu tuni ta sume a inda take ko motsi ta daina!" ganin halin da ta shigane yasa RABI'U fita daga gidan a gurguje yayi waje ya samu motar da zata kaita asibiti cak ya dauke ta ya fitar da ita zuwa kofar gida ya jefata jikin motar da ya samo ba tare da ya sanarwa kowa ba"da zuwansu aka kar6esu cikin gaggawa duba da irin halin da su kaga ZAINAB na ciki" nan da nan likitoci suka zo kanta aka fara kokarin ceto rayuwarta, cikin k'aramin lkc" koda ZAINAB ta farfado batayi mamakin ganinta a asibiti ba domin tasan komai zai iya faruwa da ita, koda kuwa mutuwa ce a yadda ta tsinci kanta,"ba wani ciwo da yake damun ZAINAB illa rashin kwarin jiki da takeji ko da ta farfado" Da sauri RABI'U ya k'araso kusa da gadon da ZAINAB take kwance yayi mata sannu!" Amsawa tayi ba tare da ta kalli fuskarshi ba tace yawwa! Ta mayar da kallonta xuwa ga silin din dake saman d'akin, suna cikin wannan halin ne wata nurse ta shigo dauke da faranti wanda yake cike da allurori ta k'araso inda ZAINAB take kwance tayi mata sannu hadi da yi mata nunin ta gyara zata yi mata allura" amsawa ZAINAB tayi tare da gyara wa lkc guda,"Nurse din tayi mata allurorin har guda biyu,bayan ta gamane ta kalli ZAINAB da RABI'U a tare ta fara yi musu tambayar menene dalilin da yasa zasu zibar da ciki wanda a sakamakon haka da kyar suka sami ceto rayuwar ZAINAB din?" Kallon2 suka fara a tsakanin su wanda yasa ZAINAB kasa jure hakan domin batasan amsar Da zata bayar ba" shi kuwa RABI'U da yasan komai shima kasa bud'e bakinshi yayi, ya yiwa Nurse bayanin shine ya bawa ZAINAB k'wayoyin da yasa ta cikin ya zube,wani gumine ya fara karyo masa tare da bayyana fargabarshi na furta shine ya bawa ZAINAB maganin a sarari" jin basuda niyya bata amsa yasa ta fara yi musu masifa tare da yiwa ZAINAB gargadi hadi da Jan kunne da nuna mata idan bata son ta dauki ciki kar ma ta bari ta dauka bare har taje tana shan maganin da zai k'arar da rayuwatar"tun kamin takai k'arshen maganarta ZAINAB ta saki salati hadi da wata irin k'ara tana fadin RABI'U ka cutar dani idan baka sona ka sakeni na huta ba sai ka kasheni ba ,ka kashe abinda yake cikina ba!!!" Jin wadan nan kalaman da suke fita daga bakin ZAINAB yasa Nurse din ta tabbatar bada sanin ta cikin ya zube ba, rarrashin ZAINAB ta shiga yi da nuna mata muhimmancin yadda da kaddara" kukane yaci k'arfin ZAINAB da take kwance a kan gado mai ban tasauyi da rikita zuciya" wannan dalilin ne ya hana RABI'U ko motsi a inda yake yana dai kallon su yana kuma sauraron duk abinda yake wakana" banda kugin kukan ZAINAB babu abinda yake tashi a d'akin" jin hakan ne yasa Nurse din tayiwa RABI'U nuni da tafiya waje" amsawa yayi kawai da toh ya fita." bayan fitar shine ta k'ara gyara murya ta kira sunan ZAINAB a hankali" ZAINAB ta dan saurara da kukan da tayi ta amsa da mata" jin dadin hakan Nurse tayi da taga ZAINAB din har ta kawo hankalinta gareta sai ta k'ara yi mata nasiha hadi da rarrashinta da bata shawarwari akan yadda zata kauracewa duk wani abu da zai daga mata hankali dangane da irin hakan idan ya taso, ta nuna mata abu mafi mahinmmanci shine idan kinsan zaki sami ciki da mai gidanki yazo yana baki k'wayoyin da zasu jefa rayuwarki cikin hadari to karki fara daukan cikin ma sai ki dauki matakin daukan baki daya,duba yadda rayuwar nan ta sauya mafi akasarin maza basa buk'atar haihuwa gaskiya abinda nake so na sanar miki kenan ina fatan zaki karbi shawarata?" kai kawai ZAINAB ta daga mata domin kuwa jinta kawai takeyi tunda ta fara maganganunta ita ba fashimta take ba sabida tsananin bugar zuciyar da take ji" fuskantar hakan da tayi daga ZAINAB yasa ta ci gaba da bata bakin tayi hakuri akan duk abinda ya faru da ita"toh kawai ZAINAB ta cewa Nurse din ta kara kwantar da kanta gefe tana cigaba da zubar da hawaye" jin zainab tayi shiru ne yasa nurse ta k'ara tambayar ZAINAB ko tana jin wani ciwo?" A'a zaina tace kawai " hakan ce tasa nurse din fita daga d'akin inda tayi kacibus da RABI'U ya k'osa ya shigo domin kuwa ya kosa a wajan da ya fita shima" Domin kuwa gani yake kamar Nurse din zata matsa ma ZAINAB da tambayoyi shine dalilin kosawarshi"murmushi Nurse din tayi masa hadi da cewar ka gaji ta jirana ko?" Amsawa yayi da cewar ko kadan likita" sake murmushin tayi a karo na biyu da cewar bari na dawo ai yanzu zamu sallameku duba da yadda abin yazo da sauki kuma tace min babu wani ciwo da take ji a halin yanzu wannan dalilin yasa zamu sallameku yanxu amman jirani k'adan dan Allah ina zuwa" toh RABI'U yace cike da gwarin giwar jin kalaman Nurse din" yasa kai ya shiga d'akin fuska a sake kamar bai aikata komai ba" ganin haka yasa ZAINAB tamke tata fuskar a gareshi" yi yayi kamar bai san tanayi ba ya k'ara matsawa kusa da gadon da take kwance hadi da kamo hannunta" fizgewa ZAINAB tayi had'i da dakatar dashi da dayan hannun da cewar dakata MALAM bakada wata magana da zaka gayamin maha'inci kawai" hakan shine yayi dai2 sallama Dr tare da nurse da sukaji yasa tayi shuru amsawa RABI'U yayi fuska a sake" k'arasawa Dr yayi jikin gadon ZAINAB ya duddubata sosai sanna ya karbi katin ta a hannun Nurse din take biye dashi yayi rubuce2 da zaiyi sanna ya mik'awa RABI'U" karba yayi jiki na rawa hadi da yiwa Dr karin godiya" Dr ya amsa hadi da mika masa hannu sanna ya kara jaddada masa cewar lallai yasa yi magungunan da ya rubuta musu sanna ya ringa saya mata kayan fruit wadanda zasu kara mata jini"amsawa RABI'U yayi da insha Allah" sanna Dr ya koma kan ZAINAB da bayaninshi da cewar ta ringa yawan shan abu mai dumi banda mai Sanyi koda wankane kar tayi da mai Sanyi har sai bayan sati biyu ta kuma daure ta ringa shan magani duba da yadda ta zubar da jini mai yawa"toh kawai ZAINAB ta cewa Dr" shima bai jira yaji wani k'arin bayani daga bakin ZAINAB din ba tunda ya fuskanta tana cikin wani yanayi na rashin jin dadin zuciya" kallon RABI'U ya k'arayi da cewar babu komai kwa iya tafiya idan ta Dada hutawa" godiya RABI'U yayi da cewar toh likita mungode da shawarar ka" OK kawai Dr yace suka juya suka fice daga dakin. Suna fita ya sake komawa jikin gadon da ZAINAB take kwance yace mata ta tashi ta shirya kamin ya samo mota su tafi" shiru tayi kamar bata ji shiba ta cigaba da zubar da hawayen da tacigaba dayi tun bayan fitar Dr" bata k'ara cewa komai ba, kallonta yayi hadi da zama daga gefen gadon ya kamo hannunta da cewar magana nakefa kinmin shiru" yi tayi kamar bazata amsa ba" sai ji tayi ya k'ara kama hannunta had'i da dago kanta da cewar haba ZAINAB me yasa kika kasa fahimtar abinda nakeso ne? Kinsan ni dai ba mutum ne mai damuwa da haihuwa ba amman kin kasa ganewa wallahi ZAINAB ina matukar kaunarki da zaki yadda ki gane hakan da lfy k'alau zamu zauna muyi rayuwa idan har kika bi abinda nakeso zan nuna miki duk wata kulawar da ta dace" koda yazo dai2 nan sake d'aga masa hannu tayi tana magana cikin shashekar kuka tace ya isa MALAM nidai nace ka sakeni daga nan ma na wuce gidan iyayena" wani irin kallon rashin fahinta yayi mata da cewar ZAINAB kece kike fad'an wannan kalmar da bakinki? Toh bari kiji yanzu na shirya zama dake dan kiji kuma babu inda zaki daga nan da ya wuce gidana" fasa fita yayi ya samo motar kawai ya mike ya tattara duk wani abun da yake nasu ya fizgi hannunta kamar yarinya yayi waje da ita,ganin da gaske yake ga rashin kwarin jiki da yake damunta gashi daga fitowarsu daga d'akin da aka kwantar da ita har mutanen dake gefensu sun fara lekowa shine yasa tace ya sakar mata hannu taji zata iya tafi ba sai yajata da karfi ba"ganin hakan shima yasa ya biye matan ya saki hannunta suka jera a hankali har suka isa bakin get din asibitin bai tsaya jiran mota ba ya tarar musu kafi babur suka hau suka nufi gida. Da Isar su gida ya hau gaganiyar dorawa ZAINAB ruwan wanka duk tana jinshi har yayi ya gama sannan ya shigo daki ya Sameta a kwance tana faman zubar hawaye ya sami guri ya zauna daga gefe, ba tare da yace mata komai ba, hannunshi yasa ya tallafota hadi da dora kanta a kan cinyoyinshi, itama ZAINAB din zamewa tayi ba tare da d'aga ido ta kalleshi ba. Bai wani tsaya jin sautin kukanta ba ya kara cewa haba ZAINAB sai hawayenki ya kare? Ina sai nake ganin duk abinda Allah ya kaddara babu makawar ketareshi ina mai baki hakuri bisa duk abinda nayi miki wallahi, wallahi ZAINAB dan bakisan yadda nakejin kukan nan naki ba har cikin zuciyata amman kin kasa fuskanta hakan sai k'arawa ma kikayi ko?" Shiru ZAINAB tayi kamar wacce ruwa ya cinye sabida bata san amsar da zata bashi" ganin batada niyyar cewa komai yasa RABIU tashi ya kara komawa kitchen ya zauna sai da ya tabbatar ruwan yayi zafi dai_dai wanka ba tare da ansurka ba ya kai bayi ya hada mata komai na wankan sannan ya dawo ya cewa ZAINAB ta tashi ya rakata tayi wanka kar tayi wasa da jikinta"wani irin kallo ta bishi da shi ba tare da tace masa komai ba" ganin batada niyyan tashi yasa ya dauke ta chak yayi bayi da ita, sannan ya shiga cire mata kaya" sake d'aga masa hannu tayi da yabar mata kayanta ita zata cire da kanta" babu yadda ya iya haka yabarta a cikin bayin ya fito"..........






~AMENAT KABER KIRU~












*KARUWAR GIDA*






*STORY WRITEEN BY✍*




*AMENAT KABER KIRU*


*SADAUKARWA GA:*


*HAJIYA ZALIHA YOLA(MMN AHMAD)*





*TSOKACI*


*wannan labarin bai shafi wata ko wani ba,na rubuta shine domin ganin yadda rayuwar mata ta sauya a wannan zamani duba da yadda kwadayi da son zuciya yayi yawa a zukatan ku,ba nayi ne dan son yad'a bad'ala ba zanyi ne saboda na zak'ulo wasu halaye da suka shiga gidan aure.*




*🅾4⃣*




Ya na fita ya rufeta, ta waje yasaka makulli domin gudun kar tayi yunk'uri guduwa daga gidan. kayan ciye2 ya sayo mata da duk wani abu da zata buk'ata wanda yasan tana so ya haďo mata da magungunan da Dr ya rubuto musu ya dawo. Koda ya dawo sai ya iske ZAINAB tayi bacci haka ya aje komai ya shirya duk wani abu da yasan ba gurin zamansa bane a d'akin sannan ya tashe ta daga bacci yace taci abinci." wani irin kallon tuhuma ZAINAB ta k'ara binsa dashi ta mayar dakai ta koma" baiyi zuciya ba ya shiga rarashinta kamar wata yariya ganin ya nace yasa ta tashi ta ci komai kadan2 ta ture duk da yunwar da takeji amma haka nan tabar masa kayanshi ya cinye wadanda yake ganin zasu lalace kamin safiya.
"tunda RABI'U ya fuskanci ZAINAB tana fushi dashi taki sakin jikinta yaita faman bata kulawa babu ji babu gani komai shi hatta birni da wasu aikace2 gida ya hanata tayi, ko fita yayi baya dadewa yake dawowa gudun kar ZAINAB ta sami damar fita bada saninshi ba ko wani yazo ta sami damar gaya masa." Lamfa ZAINAB tayi wa RABI'U da nuna mishi ta hakura da duk wani wulak'anci da yayi mata a baya har jikinta ya warke sarai" ganin haka shima RABI'U sakin jikinshi da'ita kamar babu wani abu da ya shiga tsakaninsu hakan ce tasa ZAINAB bayan ya fita wajan neman kudinshi ta shirya kayana tsaf ta gudu gidansu a karo na biyu" koda ta isa gida kuwa babu sa'a kamar zuwana na farko domin tun kamin ta k'arasa gida ta hange MALAM yana fitowa daga gidan nasu da alama fita zaiyi.tana hangoshi kuwa gabanta ya fara daukan uku2!!"yi tayi kamar ta yasar da akwatin da take rike da shi a hannunta ta juya da gudu ganin irin kallon tuhu MALAM din yake mata tun kamin ta k'araso inda yake tsaye chak,"durkusawa tayi haďi da cewa" ina kwana MALAM baki na rawa" "ya amsa tare da cewar muje ciki" "tashi ZAINAB tayi tsam ta shiga MALAM na yabi bayanta" tana yin sallama d'akin mahaifiyarta ta shige hadi da sallama" mahaifiyarta dake cikin dakin tana ninke kayan wanki ta amsa" shiga ZAINAB tayi ta sami gefe guda ta zauana tare da akwatinta a gefe ba tare da tacewa mahaifiyar tata komai ba"itama bata tambayeni ta ba taji dalilin zuwanta gidan ba" MALAM ne yayi sallama suka amsa a tare" sanna ya shigo ya wuce gefen gado ya zauna sanna ya dubi ZAINAB da cewar lafiya? Amsawa ZAINAB tayi da cewar eh MALAM" sakae kefa mata wata tambayar yayi da cewar ina zaki da kaya toh?" Ji ZAINAB tayi bakina yayi nauyi da tambayar MALAM din" shiyasa tayi shiru kamar wacce ruwa ya cinye, bude baki tayi yana rawa da cewar MALAM wallahi na gaji da halin da RABI'u yake min ne" MALMA ya amsa da uhumm" tun kamai takara cewa wani abu ya sake cemata kashe auren kikayi" girgiza kai ZAINAB tayi kawai da cewar A'a" toh mekike nufi da tahowar da kikayi?" Shiru ZAINAB tayi" domin ta rasa rasa ta inaza zata fito da maganar abida RABI'U yayi mata ,ganin haka yasa MALAM ya dinga yiwa ZAINAB fada ta inda ya shiga ba tanan yake shiga ba, jin ZAINAB bata kwakwaran dalili yasa MALAM ya cewa ZAINAB ta tashi ta koma inda ta fito" jin haka yasa mahaifiyar ZAINAB saka bakin cewa haba MALAM!" Ai yana da kyau mu tsaya muji ta bakinta duk da karin maganar 'yan Hausa suna cewa (karfe daya baya amo) amman yana da kyau mu saurareta don jin salin dalikinta na zuwa garemu".Katseta MALAM yayi da cewar dakata HALIMA baki isa ba!! Domin na ciki sanin wacece ZAINAB tun daga yarintar ta har zuwa girmanta, kuma nafiki sanin me duniya take ciki domin ina yawo lungu da sak'o ina ganin matan da suke gantali a titunan garin nan babu aure, kanaso ta zama d'aya daga ciki ne?" Girgiza kai mahaifiyata tayi da cewar a'a ba haka nake nufi ba yana da kyau da ka duba"amsawa yayi da cewar ni ba shashan uba bane wanda da 'ya'yansa sun gaya masa magana ya hau ya zauna, na fuskanci da saka hannunki ta taho gidan ma kenan" amsawa mahaifiayar ZAINAB ta sakeyi da cewar babu saka hannu na,amman dan Allah MALAM ka saurareni yana da kyau ka san cewar zamani ya sauya akan komai musamman

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login