Showing 27001 words to 30000 words out of 55178 words
Chapter 10 - KARUWAR GIDA BOOK COMPLETE NA MAMAN JABIR.txt
dan ke kaide" sai da tazo nan sannan ZAINAB ta d'ago idona wadda tuni ya cika da hawaye tace k'awara ya zamuyi hakan Allah Karki damu" hmmm kawai RUKAIYYA tace" sanna tace ai damuwa ta zama dole domin kuwa sabo akewa kuka"itama ZAINAB ta dangane ne domin a sarari taga damuwar RUKAIYYA tunda tasan duk wani abu da take ji bai wuce akanta ba, amman ai mijinta shine mafi mahimmanci a gareta, banda abin yazo haka da tasan babu wani abun da zai rabasu sai mutuwa" wanna dalilin ne yasa ta danne nata tashin hankalin domim ta bata damar shiryawa tabi mijinta cikin kwanciyar hankali domin hakan shine zaisa taga ta yi mata sakaiyya ta kwarai" ba" ba ZAINAB ce kade ta fashinshin RUKAIYYA ba ita kanta tasan karfin hali ZAINAB din take, dan taga ta faranta mata rai amman tasan cikin zuciyar ZAINAB d'anfare take da tashin hankali kala2 sai dai babu yadda zasuyi da kaddara ubangiji, shine ya tsaro hakan"duk wata magana da ZAINAB taje da ita domin gayawa RUKAIYYA haka ta barta a zuciyarta ta hakura da gaya mata komai, tunda ma abin yazo da haka a cewarta idan ta fadama babu wata mafita tunda duk wata gamana daga yau ne, domin gobe zasu rabu" wanna ce ta k'ara SA ZAINAB a cikin matsananci tashin hankali domin kuwa ko tantama babu tunda har zata rasa RUKAIYYA akusa da ita tata tazo k'ashe tabbas bakin cikin RABI'U ne zai kasheta nan zancan zucin da takeyi ashe har ya fito sarari"da sauri RUKAIYYA ta k'ara dago da ZAINAB da cewar wanne subatu kikeyi haka yar uwata?" Shiru ZAINAB tayi ta cigaba da yin kukan da takeyi" nan RUKAIYYA ta tattara duk wani hankalinta da nutsuwarta ta fara yiwa ZAINAB nasiha ankan yadda da k'addar da hakuri a kar6weta yadda tazo, hakan shine cikar mumuni na gari" karki manta da duk wani baki da Allah ya hallita shine yake hore masa yadda zaiyi ya rayu ba tare da dabararshi ba ko wayonshi dan haka ki yadda da Allah ki rikeshi sau da k'afa sai ya iyamaki domin hausawa sunce dogaro ga Allah jari ne" haka dai RUKAIYYA tsira bin ZAINAB da nasihohi masu ratsa jiki da zuciya,har sai da taga ZAINAB din ta dan saki jiki sannn ta tashi ta tayata hada kayyayakin da takeyi." RUKAIYYA da kanta ta ware kaya masu yawa na sawa da na mafanin gida da ku dade masu yawa ta bawa ZAINAB tace ta rik'e ta bar mata kamin taje garin da aka turasu taga yanayin zama da zarar taga hanya zata ringa zuwa tana ganin ZAINAB tana komawa" ZAINAB ta karba tayi mata godiya, sunsha kuka kamar basu daina ba,lkc da RUKAIYYA ta rako ZAINAB gida motarta ta da duk kayan da tabata sannan ta rubuta number wayar ta ta bawa ZAINAB da cewar gashinan duk lkc da take da buk'atr wani abu ta buga mata ta sanar mata, insha Allah zata sami hanyar da zata ringa yi mata sako" godiya ZAINAB tayi hadi da k'ara fashewa da kuka"da kyar RUKAIYYA ta rarrasheta tayi shiru" sannna suka damu damar da sukayi sallama da cewar gobe da sassafe RUKAIYYA zata zo su k'arayin sallama." Toh ZAINAB tace mata suka k'arayin sallama sannan ta tafi. Ita kuwa ZAINAB ta kashe duk kayan da RUKAIYYA ta bata da kudaden ta Adana, sanna ta shige d'akinta ta cigaba da aikin kukan da ya zame mata jiki, har yara suka dawo daga islamiyya ta basu ambinc tana ta kallon hanyar dawowar RABI'U amman shiru" haka dai ta sake zaman ba tare da ta runtsa ba har aka fara kiraye2 sallah asuba bata ritsa ba mikewa tayi ta tafi ta tafi ta daura alwala tazo tayi nafiloli, da baya ta mike ta kawo farillah bayan ta idar ta kwanta ta rintsa kadan ta fara baccin kenan taji ana bugun k'yauron kofar gida, a firgice ta tashi ta fito ta nufi kofar gidan,tana zuwa ta bude bata jira tambayar waye ba ta bude,ganin wanda yake a tsaye ne a kofar gidan bayan ta bude gidan yasata cikin firgice, domin kuwa shi kanshi a gigice yake lkc da ta ganshi ba wani bane sai UMAR dan mijin RUKAIYYA ne a tsaye ido jawur yace kuka ga murya ta disashe ya ce baki na wara yace AUNTY ......"amsawa ZAINAB tayi da cewar lfy UMAR?" Da kyar ya budi bakin cewar AUNTY na ce Allah ya karfi rayuwata, ko jira batayi ya kara fadeba taci kwallarshi da cewar karya kake wallahi RUKAIYYA ta bata mutu ba garin yaya zaka ce ta mutu menene ya Sameta ka gaya min gaskiya nace ka gayamin gaskiya!!!" ganin ta gigicene yasa ya cire hannuta daga kan kirjinshi, cikin kuka yace wallahi da gaske nakeyi ta rasu !!!!a dalilin bugawar zuciya da yasameta cikin daren jiya!! bayan nadawo daga gurin abokaina ne nashiga domin sake tayata harhade kayan da bata k'arasa hadawa ba shine na sameta akwance tana wani irin nishi da fitar da dafara daga bakinta ,nayi korin kiran likitan da zai dubata ta kamin yazo ta rigamu gidan gaskiya" koda likitan yazo shine ya tabbatar min da dalilin mutuwar tata,tun a daren aka sakarwa da kowa da kowa dangin na kusa da na nesa wasu tuni sun hallara a gidan, ganin ban ganki a gidan ba yasa na taso yanzu na zo gaya miki" wani irin kuka ZAINAB ta sake saki tare da ihu wanda hakan har sai da ya taso makwaftanta suka fito domin jin ihun kukanta, haka suka ringa bata hakuri da" shi kuwa UMAR tunda ya gama mata bayani ya juya gida domin komawa su yi Jana'izar RUKAIYYA( ALLHU AKBAR KABIRAN)." Komawa cikin gida ZAINAB tayi ta tashi su MARIYA tace suje makwafta su jirata zataje gidan rasuwa RUKAIYYA ce Allah ya karbi rayuwarta" su Kansu yaran da suke kananu sai da suka koka bisa maganar da sukaji na rasuwar aminyar mahaifiyar tasu." Amsawa sukayi da toh cikin kuka" itama ta shirya ta fita zuwa gidan rasuwa koda ta k'arasa kofar gidan ta tarar ya cika mak'il da jama'a da kyar ta sami hanyar da ta ra6a ta shiga cikin gidan tana zuwa ta tarra da gawar RUKAIYYA lallibe da zani a kwance a tsayar falon ta" tana budawa ta fada kan kirjita ta na wani irin kuka mai ratsa zuciya, hakika ZAINAB ta gigice da ganin gawar k'awarta ta sosai ta girgiza mutar ta domin kuwa gani take tamkar ita kade akayiwa mutuwar" nan fa mutane da yan uwan RUKAIYYA suka janye ZAINAB da kyar sannan a ka dauke gawar akayi mata wanka aka hada ta domin kaita makwancin ta,sai da aka dauke gawar aka fitar da itane ZAINAB ta k'ara yinkewa da maganar mutuwar RUKAIYYA gaskice domin da duk gani take tamkar mafarki take" wanna ne ya k'ara hasgitsa tunaninta da nutsuwarta domin gani take itama tata tazo k'arshe tunda ta rasa iyayenta bata kallon kowa a matsayinsu sai kawarta RUKAIYYA yau itama Allah ya amshi kayarshi," subatu ZAINAB ta riga yi mai ban tausayi babu wanda bai tausayawa ZAINAB ba a gidan mutuwar nan" domin kuwa kaiwa take tana kawowa tana surakatai tana juya hannu kamar wacce take shirin zarewa" ganin haka ne yasa wasu daga cikin matan da suke gurin suka kama ZAINAB suka zaunar da ita aka dinga yi mata nasiha da bata hakuri har ta ta lafa da subatun da takeyi" amman sam taki daina kukan da takeyi yaki tsayawa domin kuwa jinta take tamkar tsirara take a rayuwata ta duniyar yanzu" haka dai tacigaba da kuka mai tsuma zuciya da ban tausayi matuka" ana ta bata bakin tayi hakuri"...............
~AMENAT KABER KIRU~
*KARUWAR GIDA*
*STORY WRITEEN BY✍*
*AMENAT KABER KIRU*
*SADAUKARWA GA:*
*HAJIYA ZALIHA YOLA(MMN AHMAD)*
*TSOKACI*
*wannan labarin bai shafi wata ko wani ba,na rubuta shine domin ganin yadda rayuwar mata ta sauya a wannan zamani duba da yadda kwadayi da son zuciya yayi yawa a zukatan ku,ba nayi ne dan son yad'a bad'ala ba zanyi ne saboda na zak'ulo wasu halaye da suka shiga gidan aure.*
*GAISUWAR BAN GIRMA*
*_TA MANYAN HAMSHAK'AI MANDIYOYI BILKISU ABBAS SA'ID KIRU DA UMMU FATI MUTANE SAUDIYYA, BAN MATA DA KE BA UMMU ABDULLAHI KD,MMN AHMED KD (BAGOBIRA) MY SISTER UMMU MUHAMMAD, GA IRIN TAKU🤙_*
*1⃣1⃣*
Haka dai ZAINAB ta gaji har ta hakura. Tunda ta fara zuwa gidan karbar gaisuwa RUKAIYYA har sai da akayi sadakar bakwai da ita amman har a wannan lkc RABI'U bai dawo gida ba tun abin baya damuna har ya fara damunta haka tai ta rama da k'arewa a tsaye duka goma da goma" sai da RABI'U ya cika sati biyu Chif a waje ba tare da ya lek'o gida ba sannan ya dawo" koda ya dawo bai fasa halinshi ba haka zalika bai tausayawa ZAINAB halin da take ciki na rashin da ta shiga ba haka yayi ta kunsa mata taikaici na yau daban na gobe daban. Allah sarki duniya mai yayi haka ZAINAB ta kasance cikin rayuwar ban tausayi ga rashin kwanciyar hankali da miji"
Akwana a tashi RUKAIYYA ta cika wata hudu da mutuwa anan ne fa rayuwar ZAINAB ta k'ara tuzarta da wulak'anta domin kuwa idan ba kallon tsanaki mutum yayi mata ba zai ganeta ba duk da dacan din ma ba dadi take jiba amman da dama2" shiga d'aki tayi tana kwaso yan kayayyakin ta nasawa wadanda suka rage mata masu daraja a cikin werdrop dinta kawai sai ta arba da wata takada rubuce da number waya an rubuta HAFSAT AL'AMEN da sauri ta k'ara juyata takardar domin kuwa ta manta da ita tsawan lkc wanna da sauri ta janyo hijaf dinta ta ratayashi a wuya ta fita sai makwafata ta fada tare da yin sallama" makwafciyarta ta amsa" ko gaisawa ZAINAB ta jira sunyi ba ta tambayi makfciyarta ta ko wayarta da kati?" Amsawa tayi da cewar eh da kawai hadi da miko mata wayar kai tsaye" ZAINAB tasa hannu ta karba" tana karba ta fara latsa lambubin da suke rubuce a takardar da take hannunta cikin hanzari kamar wani zai kwance wayar tana gama loda lambobin ta tura kira hadi da karawa a kunneta,ta nasawa taji ta shiga sai tana k'ara amman ba d'aga ba har tagaji da gunji kiran ya yanke ba tare da an d'aga ba,haka ZAINAB ta sake kokarin sake tura kiran a karo na biyu har sai da ta kusa katsewa sanann taji an daga da cewar hello" jin haka yasa ZAINAB itama tayi sallama aka sake amsawa da tambayar wayem?" Da sauri ZAINAB tace nice ZAINAB ABDUL dan Allah ko da HAFSAT AL'AMEN nake magana?" Wata dariya taji an sakar mata da cewar eh itace shegiya kawata sai yau zaki nemeni ai nayi fushi"da sauri ZAINAB tace ko kadan wallahi tun lkc da kika bani number na rasa inda na jefa ta shine dalili yanzu ma da kika kirana wallahi banfi mutu biyu da ganinta ba cikin kayana shine dalilin da yasa na nace bari na gwada naji ko zata shigo" amsawa tayi da cewar OK karki damu ai komai yin Allah ne, yanxu gashi ya nufeki da ganinta kuma kinyi sa'ar ta shigo kashe na kiraki"ZAINAB ta katse layin" HAFSAT ta sake bugowa hadi da tambayar ZAINAB da cewe wanna ne layin naki na ajje shi" girgiza kai ZAINAB tayi kamar tana ganinta da cewar a'a banida wata ai har yanzu"wani tsaki HAFSAT ta saki da cewar ban gane ba, bakida ra'ayine ko kuwa lalacewa tayi?" A'a ZAINAB tace babu d'aya daga ciki banida ita ne gabaki d'aya"mamakin ya kama HAFSAT daga can bangaren da cewar daman har yanzu akwai wadanda basuda wayar hannun a wannan lk duk saukinta? haba kawata karki bada mata mana" murmushi ZAINAB ta yi da cewar k'awata kenan ai nima ba haka naso ba" tamabayarta HAFSAT tayi da cewar toh lefin waye gayamin? Da kina da ita ai da gaisawa batayi wuya ba.sun dade suna hira anan ne ZAINAB ta sanarwa da HAFSAT rasuwar RUKAIYYA nan HAFSAT ta jajantawa ZAINAB bisa rashin da sukayi da cewar insha Allah gobe zatazo da yamma da zarar ta gama uzuririkanta" ba karamin dadai ZAINAB taji ba domin kuwa hakan ya nuna a sarari" amsawa tayi da cewar babu damuwa Allah ya kaimu goben"HAFSAT ta masa da amen"sannan sukayi sallama juna ta yanke wayar ta."itama ZAINAB ta mikawa makwafciyarta wayarta tayi godiya"ta amsa da babu damuwa"ZAINAB ta fito ta koma gida zuciyarta cike da farin cikin albishir din da taji daga bakin k'awarta wacce suka rabu tun tsawan lkc. Haka dai ZAINAB ta zauna tana ta jiran kashe garin ranar tazo kamar ta k'arawa lkc gudu,har dare haka takai tana jiran tsammanin gari ya waye." A wanna daren ne kuma ZAINAB ta k'ara fadawa tsaka mai wuya domin kuwa a cikin daren ne ANAS ya farka da wani irin mugun ciwan ciki haka yayi ta murkusu!!"ba ZAINAB ba hatta MARIYA da take yarinya sai da ta kokawa ANAS din" sakamakon yadda taga yaron yana wata irin zambarma hadi da koka mai ban tasauyi"ga gida babu namiji domin kuwa yanzu RABI'U sai ya ga dama yake zuwa gida ya dubasu babu abinda ya damesu da a wanne hali suke yana can yana sharholiyarshi ba tare da yasan halin da iyalanshi suke ciki ba." Haka dai ZAINAB da MARIYA sukayi kwanan zaune ba tare da d'ayansu ya ritsaba,a ranar ZAINAB taci kuka kamar idonta zai tsiyaye sabida tsakanin kuka da tunanika iri da kala, domin kuwa a daren RUKAIYYA ce ta bijiro mata domin kuwa tasan ita kayiwa mutuwa ba kowa ba,hakika da tana raye tasan tashin hankalinta kadane koda zatayi bazai kai kamar wanda take ciki ba" haka dai tai ta tuna al'kairin RUKAIYYA gareta lkc da take raye." A haka har gari ya dauko waye was sannan ANAS ya samu ciwon ya dan lafa masa yayi bacci" ganin ya rintsane yasa ZAINAB tashi ta gabatar da sallolinta sannan ta dawo tacewa MARIYA itama taje tayi tata sallah" toh tace sannan ta mike ta fita"bayan ta dawo tayi sallah itama ta koma ta kwanta ta koma bacci domin ta dan rintsa." Ita kuwa ZAINAB tashi tayi bayan ta gama lazimi ta shiga kitchen ta huwara wuta domin Samar musu abin kalaci a gurguje"bayan ta gama ta daura musu ruwan wanka,ta koma ta tashesu ta sannan ta fito da ANAS ta fara yi masa wanka"bayan ta gama masa ta umarci MARIYA da taje tayi nata wanka" toh tace" ta fita cikin k'aramin lkc ta dawo" ZAINAB ta hada masu abin kari sannan ta fita ta yi shara itama ta shiga nata wankan batafi muti sha biyar ba ta fito ta dan goga mai kadan sannan ta saka yan kod'add'un kayanta ta zauna tana nazarin yadda zatayi da ciwan ANAS duk da ya farka jikin nashi da sauki amman dai ta firgita matuk'a domin kuwa ko kudin chemis batashi bare na motar da zata hau taje ta kaushi suga likita" haka dai ta zauna tana ta sake2 a zuciyata babu amsa daga k'arshe dai ta mika wuya ga Allah tana kallon hanyar domin sauraron zuwan bakuwarta."
Karfe goma dai2 HAFSAT ta yiwa gidan ZAINAB tsinke domin kuwa kugin tsayawar motar HAFSAT ce tayiwa kunne ZAINAB tsine koda bata leka ta gani ba amman tasan babi wanda zaizo kofar gidan ta a wannan lkc da mota har kofar gida, domin kuwa mai zuwa da motar da can RUKAIYYA ce kuma Allah ya karbi kayarshi" da sauri ta mike tsaye daga inda take zaune tun tsawan lkc domin kuwa Jin sallamar HAFSAT tayi a tsakar gida" cikin farin ciki da murna ta fito ta tafi da gudu ta rumgume k'awarta ta,hadi da yi mata sannu da k'arsowa"amsawa HAFSAT tayi hadi da daukan kafadar ZAINAB da cewar yimin a hankali k'awata kar ki kayar dani" murmushi ZAINAB tayi da cewar wace ni? Na kayar da manya irinku" dariya HAFSAT tayi da cewar ke kuka bakya ganin takalman da na sako ne?" Sai a wannan lkc ZAINAB ta kula da uban tsinin takalmin da yake kafar HAFSAT domin kuwa tsininshi ya kai tsini matuk'a gashi da kyau da walwali kalashi daya da yar karamar jakar hannuta wanda ta cikashi da awarwaron gold da zubuna suna duk na gold kai tsayawa ma lissafa tsaddadun kayan jikin HAFSAT 6ata lkc ne." ZAINAB ca tacewaw ZAINAB oh yi hakuri ai sam ba kula ba kisan abinka da wanda idonshi ya rufe da ganin k'awarshi sam bazai kula da abida yake a gabanshi ba" murmushi HAFSAT ta k'ara yiwa ZAINAB da cewar ai na lura kin shiga da yawa k'awata farin cikin ki yaki 6uyuwa a fuskarki naga alamar hakan" amsa ZAINAB tayi da ko? Toh mushiga daga d'aki man,kya cigaba da yankata k'awata" amsawa HAFSAT tayi da cewar ba wani yanka muje dai" ZAINAB ta shiga gaba HAFSAT na biye da ita a baya tana k'ara yiwa gidan kallon tsanaki tana mamakin yadda ZAINAB take iya rayuwa a cikinshi kuntattace ga rashin iska ga wani irin kauri da take Jin yana taso mata kamar ana k'ona taya ga wasu tarin kayan wanki daga can gefe abu dai babu dadi kallo" ZAINAB ta lura da irin kallon da HAFSAT takewa gidan amman ta share har suka shiga d'aki ta shifida mata sallaya tace mata ta zauna"nan fa HAFSAT ta k'ara tsinkewa da lamarin da ZAINAB take ciki sai da taga d'akin da take ciki babu uwar komai sai tari shirgin tsumo karan da suka cikashi" zama HAFSAT tayi akan sallaya ta kalli ZAINAB da cewar k'awata ya kwana biyu toh?" Amsawa ZAINAB tayi da cewar sai kairan ,hadi da cewar bari na debo miki ruwa duk da dai har yanzu da sauran safiya" amsawa HAFSAT tayi da cewar a'a basai kin debo ba wallahi na gode, zauna muyi hirar ta abota ta kalli ZAINAB" zauna ZAINAB tayi tana fuskantar HAFSAT da cewar k'awata wallahi nayi mamakin ganinki a wanna yanayin domin kuwa da wani ne ya gayamin cewa zanyi k'arya ne ke kuwa yaushe kikayi auren da har zaki mayar da kanki tsohuwar dole? haba k'awata karki bayar da mata mana, ina RABI'U yana