Showing 234001 words to 237000 words out of 275313 words
Chapter 79 - Heedayah Book Complete by Khalisat Haidar .txt
bibbiyu tace "Ameen" Yakumbo tace "Sai ka dage da Sallan dare kana rokon Allah kaji?" A hankali Khaleel yace "In sha Allah" Kaka ta fixgo ledan Yakumbo dake hannun Heedayah da ta wani hade rai murya can kasa tace "Mayya kawai" juyawa Heedayah tayi ta shigewarta cikin gida, Junaid na murmushi yace "Amma xa ku dawo nan ko?" Kaka tace "Aa mun gama da nan, ita dai Aisha idan ta gama galantoyinta sai ta same mu gidan Amadu, ai gobe Amadun kano yace mu dawo, kaga baxa mu tsallake umarninsa ba ai" Junaid yace "Toh shkkn, sai mun xo" Kaka tayi kasa da murya tace "Kai da wa??" Junaid yace "Xa mu xo tare da Khaleel in sha Allah" Yakumbo tace "Ehh to ai da kyau hakan, amma fara yawo ba nasa bane yanxu, killacesa xa a dinga yi har tsoron Allah ya shigesa, abinda ma Amadi yace xai xo nan tare da gwamnan Kaduna su gaishesa su jajanta masa, ai ba sai yaje kano ba, mu ma xa mu dawo idan Allah ya yrda" Kaka tace "Ai shine naga...." Khaleel dai kallonsu kawai yake, Kaka tace "Gaskiya jini ba wasa bane, sai da suka tsaya a tare naga mugun kamar da suke da Junaidu, har lotsawan kumatun Allah sarki" Murmushi Junaid yyi, Khaleel yace "Allah ya kiyaye hanya" A tare Yakumbo da kaka suka ce "Ameen" daga haka ya juya ya koma ciki, Kaka tayi kasa da murya tana kallon Junaid tace "Kace ma Rakiya tayi ta tashi cikin dare tana sllh tana kuka tana nema masa gafara wajen Allah, na manta ban gaya mata ba wllh, snn tayi ta masa nasiha cikin dubara akan daukan abinda ba hakkinka ba, snn tayi ta nuna masa illar yin haka, ta dinga nuna masa kudi a nan duniya ake samunsa kuma a bar sa a mutu" Junaid bai iya yace mata komai ba, Yakumbo tace "Driver mu je magariba nayi, Allah dai ya kai mu lfya" Driver ya ja motar, na sojoji na biye da su a baya suka bar layin. Bayan isha Khaleel na xaune parlor idonsa a kan wani movie da ake yi a tv, xamansa a parlor umarnin Mami kawai ya bi amma bai son xaman cikin parlon, Mami kuma bata son yana xama shi daya a daki ne, he is always silent snn bashi da walwala, Junaid kuma ya fita, Farida da Sumayya ne parlon suna labarin movie din da ake yi kasa kasa, Farida ta kallesa tace "Yaya ko ba haka bane?" Kallonta yyi snn ya kalli Tv din, can yace "Ban san me ku ke cewa ba" Sumayya tayi murmushi tana fari da ido tace "Labarin film din mu ke yi" yace "Ohk but I don't know about the film" bai kuma cewa komai ba ya ci gaba da kallonsa, Sumayya tace "To a kawo maka abincin yanxu?" Kallonta Khaleel yyi yace "Aa" Heedayah dake xaune dining ta kallesu ta dauke ido ta tabe baki ta ci gaba da cin abincin gabanta, bayan few minutes Khaleel ya mike ya tafi dinning din ya ja kujera ya xauna, Heedayah bata kallesa ba tana ci gaba da cin abincinta, Tuni Sumayya ta daina kallon da take yi, ta shiga xaga parlon da idanuwanta kamar me neman abu, Khaleel na kallon Heedayah yace "Baki bani abinci ba" Ba tare da ta kallesa ba tace "Ba naji ance xa a kawo maka ba" Bai ce komai ba, ta dago kai tana kallonsa, tashi tayi ta tafi kitchen ba a dau lkci ba ta fito rike da plate din abinci, a bakin kofar kitchen din suka hadu da Sumayya ta ba Heedayah hanya snn ta shiga kitchen din, Heedayah ta ajiye masa abincin a gabansa a hankali yace "Thank you" Fitowa kitchen Sumayya tayi rike da nata abincin ta nufi dinning ta xauna, Farida ta saki baki tana kallonta, A hankali Khaleel ke cin abincin gabansa, Heedayah dake xaune dinning din sai ta ma kasa ci gaba da cin nata, Lkci daya Khaleel ya tashi ya dau plate din abincinsa ya bar dinning din. Sha daya saura na dare Mami ta shigo dakin Junaid, Khaleel na kwance yana kallo Junaid kuma yyi bacci, ya mike xaune ganin Mami, Mami ta ja kujera ta xauna tana kallonsa tace "Baka yi bacci ba" Yace "Eh ban yi ba" tace "Ka ci abincin kuwa?" Khaleel yace "Na ci" Mami tace "Ohk, kana ji na" yana kallonta yace "Ina ji" Tace "Da mun so sai after this case sai ku tafi da aunt dinka can gombe wajen family din Abban ka, kayi sati daya a can, amma bayan xaman court na gobe sai ku wuce da Aunty Nafisa da Sumayya" Khaleel ya d'an yi shiru, sai kuma yace "Toh Allah ya kai mu" a hankali Mami tace "Ameen" shiru ne ya biyo baya, Mami tace "Aunty Nafisa autarsu mahaifinka ce, Sumayya kuma daughter dinta ce, but naga kamar baka saki jiki da ita ba" Khaleel yace "Ita wa?" Mami tace "Ita Sumayyar" Khaleel yace "Mami to me xan mata" Mami tace "The mother suggested...." Da sauri yace "Suggested what?" Mami tace "A hada ku aure da ita sbda situation da ka tsinci kanka" Khaleel ya girgixa kai yace "Ni ina da warce nake so Mami"
Heedayah isn't free, you read for free 🤷🏻♀️🤷🏻♀️
it's 300 via... Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah
Then you show ur evidence via WhatsApp 07087865788....
Mami na kallonsa tace "Wacece ita?" Khaleel ya sauke idonsa yyi shiru" tace "Speak ur mind" Ya kalleta yace "Heedayah" kasa ce masa komai Mami tayi ta kura masa ido, bayan wani lkci ta mike tace "Sai da safe" a hankali yace "Allah ya tashe mu lfya" Daga haka ta nufi kofa ta fita. Washegari karfe uku saura Ammi ta iso gidan Mami, bayan sun gaisa Mami ke tambayarta su Ashnaah, Ammi tace "Suna gida" Farida ce ta kawo ma Ammi drink da ruwa ta bar parlon, Ammi tace "Daxu Barrister ke gaya mana anyi adjourning case din xuwa sabon wata da xa shiga" Mami tace "Ehh in sha Allah, nan da sati uku idan Allah ya kai mu" Ammi tace "Toh Allah ya bada nasara, ya kai mu lkcn lafiya" Mami tace "Ameen" Heedayah ta shigo parlon ta duka kasa a sanyaye ta gaida Amminta, Ammi ta amsa sannan ta mike ta bar parlon, Mami tace "Xa ku tafi tare da ita ta gaida Abbanta tun da bbu abinda take a nan kawai Hajiya" Ammi tace "Ku baxa ku kawo mana ziyara ba?" Mami tayi murmushi tace "Bayan case din nan idan Allah ya yarda" Ammi tace "Toh Allah ya bada nasara, Ina Khaleel din?" Mami tace "Sun wuce Gombe tun daxu da aunt dinsa amma kwana biyu yace xai yi ya dawo" Ammi tace "Toh Allah ya dawo da shi lfya" Mami ta amsa da "Ameen, su Kaka suna lafiya?" Ammi tace "Lafiya lau, nan da yan mintuna xa mu koma kano in sha Allah, shi sa na xo Sallamar ki" Mami tace "Toh bari in ma Heedayah magana ta hada kayanta" Ammi tace "Farida fa ita baxata ba?" Mami tace "Ai tana xuwa makaranta Hajiya" Ammi tace "Ayya, toh shkkn" Sama Mami ta wuce ta bude dakinsu Heedayah ta shiga, Mami na kallonta tace "Idan xa ki sake ranki ki sake ki shirya kayan ki xa ku tafi kano da Ammin ki yanxu" Lkci daya hawaye ya kawo idonta da damuwa tace "Mami ban son xuwa kanon fa, don Allah kice mata ina xuwa islamiyya" Mami ta hade rai tace "Toh me kike yi a nan din da baxa ki shirya ku wuce ba, yau sati nawa da yin candy dinki, you are sitting doing, islamiyyar xuwa kike balle kice ace kina xuwa? what's wrong with you going to greet ur father?? Malama kar ki bata masu lkci ki hada kayanki ke take jira" Daga haka Mami ta fita dakin, Hawaye ya gangaro idon Heedayah, Farida dai sai kallonta take bata ce komai ba don tasan me yasa Heedayah bata son tafiya, a sanyaye Heedayah ta mike ta hau hada ironed cloth dinta a daya daga travelling bag dinta, A hankali Farida tace "What's making u Sad Heedayah?" Kallonta Heedayah tayi tana goge hawayen da ya ki tsaya mata amma bata ce komai ba, sai da Mami ta sake shigowa dakin tace "Minti kusan ashirin har yanxu baki gama hada kaya ba Heedayah, me ke damun kanki?" Heedayah ta dau mayafinta ta yafa tana janye da trolley dinta, Mami ta juya ta fita, mikewa Farida tayi ta rungumeta tace "Allah ya tsare hanya, when will u be coming back?" A hankali Heedayah tace "Ai ya Khaleel yace kwana biyu xai yi ko?" Farida tace "Uhm..." Heedayah tace "Nima kwana biyu xan yi in dawo" Murmushi Farida tayi tace "Toh Allah ya dawo mana da ku lfya" Cikin sanyin murya Heedayah tace "Ameen" tana jan trolley din ta nufi kofa ta bude ta fita, tsaye ta tarda Mami a corridor tana jiran fitowarta, sauke idonta kasa tayi, Mami tace "Heedayah" Ta kalli Mami tace "Na'am" Mami tace "Me yasa baki son tafiya gidan ku wajen iyayenki?" Heedayah ta girgixa mata kai kawai, Mami tace "Toh ki sake ranki before going downstairs, Ammin ki baxata ji dadi ba idan kina haka, idan kika kwana biyu a can ba sai ki dawo ba" Kamar xata yi kuka tace "Mami dama two days din xan yi ai" Mami tace "Aa ba irin wnn kwana biyun ba, ranan da aka ce ki dawo xaki dawo" Hawaye ya kawo idonta tace "Mami plss idan mun tafi after few days ki kira ki tambaya yaushe xan dawo sbda islamiyya" Kallonta kawai Mami take kafin tace "Can ma gidanku ne kuma xa ki iya xuwa islamiyya" Heedayah ta goge hawayen idonta tace "Mami bbu wanda muka saba da a can fa, ni kadai ce xan dinga xama" Mami tace "Ga Ammin ki da Stepmum dinki with ur little cute sisters, su xa su xama companions din ki a can ai, and Shuraim is now working in kano, definitely xai dinga xuwa can gidan kinga ai kin samu wanda ku ka saba sai ku dinga hira idan ya je" Turo baki Heedayah tayi bata ce komai ba, Mami tace "Go downstairs now, gani nan sakkowa" Sauka Heedayah ta shiga yi a stairs din, Mami ta wuce dakinta, tun da ta fito parlor Ammi ke kallonta bata dai ce komai ba, Ba a dau lkci ba Mami ta sakko parlon, turararruka ta ba Ammin Heedayah, Ammi tayi mata godiya sosai, Mami tace "In sha Allah after everything xa mu taho kanon" Ammi tace "Toh Allah ya kawo ku lfya" Har gate Farida da Mami suka raka Heedayah da Mum dinta, tun da suka shiga mota hawaye ke sauka idon Heedayah ta daga masu hannu suka bar layin tare da escort din Amminta, Har suka isa gidan Abba Ammi bata ce ma Heedayah komai ba ta sauka motar ta shiga cikin gidan, Heedayah ta sauka ta bi bayanta, Kaka da Yakumbo na xaune parlor tare da Mumy, Mumy ta shiga yi ma Ammi sannu da xuwa bayan sun shigo parlon, Yakumbo tace "Toh har xa mu tu6e kayan, bamu san ko fasawa kika yi baki sanar mana ba, abun ka da masu abu da abun su" Ammi dai bata tanka ta ba, Xaunawa kasa Heedayah tayi ta gaida Mumy dake ta kallonta, Mumy tana murmushi tace "Lafiya qlau Heedayah, baki da lafiya ne na ganki haka?" Heedayah ta girgixa kai tace "Aa lafiya na qlau" Daga haka ta gaida su kaka ma, Kaka tace "Me aka maki a gidan Rakiyar kike cika kike batsewa?" Ammi ta dau handbag dinta tana kallon Mumy tace "Hajiya xa mu wuce airport yanxu" Mumy tace "Lahh na xata xa ku bari sai gobe ai Maman Heedayah" Ammi tace "Aa yau xa mu koma in sha Allah" Mikewa kaka tayi ta dau jakarta dake gefenta tace "Toh idan Amadu ya dawo ace masa da alkhairi" daga haka ta nufi kofa, Yakumbo ma ta mike tace "Toh Maryam a gaida yaran idan sun dawo islamiyya...." Mumy ta mike tana murmushi tace "To sai yaushe kuma Mama?" Yakumbo tace "Atoh kilan sai na rako patu idan xata dawo wani satin ko?" Da sauri Kaka da har ta isa kofa xata fita ta juyo tana kallonta, Ammi dai bata jira ta sauraresu ba ta fita daga parlon Heedayah ta bi bayanta, Mumy ta bi bayan Ammi da sauri tana cewa "Toh Hajiya baki ci dambun ba ai gashi ma har na sa maki a cooler wllh" Ammi tace "Aa Alhmdllh nagode" Mumy ta 6ata rai tace "Aa don girman Allah ki tafi da shi ku da jirgi xa ku bi nan da yan mintuna xa ku sauka, kuma dambu ai abun marmari ne" Bata jira cewar Ammi ba ta shige ciki da sauri sai ga shi ta fito da wani karamin warmer me kyau cike da dambu, ta saka shi a wani fancy leda, Yakumbo tace "Tun da yaron nan na can kanon sai a bashi coolern ya maido maki idan xai xo" Tuni Mumy dai ta fice ko mayafi bbu ta rakube bakin gate tana mika ma Heedayah dambun, Heedayah ta risina ta amsa, Ammi tayi ma Mumy godiya, Mumy tace "Kai haba, babu komai wllh Hajiya, Allah ubangiji ya sauke ku lafiya" Ammi tace "Ameen, yaushe xa ku shigo kano?" Mumy tace "Ai ko muna da biki satin nan, in sha Allah ina sauka xan kira ki tunda na amshi number ki" Ammi tace "Toh Allah ya kai mu, ya kawo ki lfya" daga haka Ammi ta shiga mota Heedayah ma ta shiga, Mumy sai murmushi take kamar warce aka yi ma wani gagarumin albishir, Kaka da Yakumbo suka fito kaka na cewa "Banda dai shi Uban Heedayan yace sai na xauna wajensa dama me d'a na ya rage ni da shi xan ki xaman gidansa, kuma ko da xa a siyar da Gwamnet house din gaba daya da kyar a iya biyan Amadu abinda yyi ma Deedayah da kudin..." tuni Yakumbo ta shige daya mota, Mumy dai sai kallonsu take ta gefen ido, kaka ta tsuke fuska ta shige motar da Yakumbo ta shiga ita ma, Mumy na daga masu hannu baki har kunne tana Allah ya kiyaye har suka bar layin, tana murmushi ta dinga tunanin wani bikin karyar xata kakalo da xai kai ta kano a satin nan.... Tsaye Heedayah tayi tana bin dakin da Stepmum dinta ta nuna mata as nata da kallo, babu abinda babu a babban dakin that is well furnished da tsadaddun furnitures, karasawa tayi gefen gado ta xaune lkci daya hawaye ya kawo idonta, ko kadan bbu abinda ya burgeta a gidan nan dai tun shigowarsu, ta rasa damuwar da ya tsaya mata a rai, ji tayi kamar ta fashe da kuka sosai ko xata ji dadi a ranta, Wata maid ce ta biyo ta da trolley dinta dakin, Heedayah ta mike ta amshi trolleyn ta ajiye sa a gefe, Maid din na kallonta tace "Hajiya xa a kawo maki abinci ne, ko kuma da wani abun da kike na daban a kawo maki?" Heedayah tayi shiru, sai kuma a hankali tace "Tea" Juyawa maid din tayi ta fita, Heedayah ta kwanta gefen gadon hawaye me xafi ya gangaro idonta. Bayan Magrib Heedayah ta gaji da xaman daki bayan tayi wanka ta sauya xuwa doguwar riga me shara-shara ta fito, a wani parlor ta tadda Amminta xaune ita kadai tana answering din call, Heedayah ta xauna kasa ba tare da ta sake kallonta ba, har Ammi ta gama wayar ta ajiye, Heedayah ta daga kai a hankali tana kallonta tace "Ammi ina su Ashnaah?" Wani kallo Ammi tayi mata tace "Sai yanxu kika san da su?" Shiru Heedayah tayi bata ce komai ba, Ammi tace "Idan ma xaki kama kanki kiyi tun wuri, ni baxa ki kawo min iskanci a gidan nan ba, da kika san baki son xuwa wani gulman ya sa kika biyo mu dama, tun farko ai sai kice baxa ki xo ba, uwar wa xaki biyo kina hade haden rai, ko me xaki min a nan din idan kin xo" Girgixa kai Heedayah tayi cikin sanyin murya tace "Aa Ammi bance bana son biyo ku ba...." Kwankwasa kofa aka yi Ammi ta bada izinin shigowa, Maid ce ta shigo rike da tray me dauke da plate din dambu ta dumama, plated with pepperd chicken, ga Tamarind drink da bottle waters biyu da glass cup biyu a gefe, karasowa ciki tayi inta ajiye gefe ta dauko wani lallausan carpet ta shimfida ta dau tray din ta daura a kai snn da ladabi tace "Hajiya ga abincin" Ammi ta kalleta tace "Nagode Amina, kin debi dambun?" Aminar tace "Aa ba shi da yawa Hajiya" Ammi tace "Aa ku deba ku je ku ci tare da 'yan uwanki" Amina ta mike ta fita sai gata ta dawo da plate ta debi kadan ta fita daga parlon, Ammi ta sauka kasan carpet din ta dau spoon daya tana kallon Heedayah dake bin abincin da kallo tace "Idan xa ki ci ki fita kitchen ki dauko spoon" Girgixa kai Heedayah tayi tace "Aa, kawai chicken din nake so" Ammi ta jawo wayarta ta kira Amina tace ta debo ma Heedayah pepperd chicken din, ba a dau lkci ba ta kawo mata. Heedayah na cin kazar a hankali Ammi kuma na cin dambunta, Heedayah tace "Ammi wani makaranta xan fara yanxu?" Ammi tace "Ki tambayi Abbanki nima ban sani ba" Heedayah bata ce komai ba tana ci gaba da cin naman gabanta, Bayan sun gama Heedayah ta kwashi tray din tana kallon Ammi tace "Ina ne kitchen din?" Ammi tace "Don't worry ki tafi kiyi Isha xan kira su Amina su kwashe" Heedayah bata ce komai ba Ammi ta kira Amina ta shigo ta kwashi tray din tana kallon Ammi tace "Kun yi bako a parlor Ammi" Ammi tace "Waye?" Amina tace "Sojan nan ne" Ammi tace "Ohk Shuraim, I'm coming" Lkci daya Heedayah ta daure fuska, Ammi tace "Kije ku gaisa, I want to