Showing 210001 words to 213000 words out of 275313 words

Chapter 71 - Heedayah Book Complete by Khalisat Haidar .txt

26 Nov 2024

26821

din, ba musu Heedayah ta koma ta cire snn ta dawo, gaba daya bata da walwala, motar sojoji guda ne a layin tun xuwan su Amminta gidan Mami jiya, Heedayah dai na xaune bayan mota tare da Yakumbo, Farida kuma ta shiga gaba suka bar layin. Suna isa gidan Abba mai gadi ya bude masu gate, driver ya shigar da motar yyi parking, Heedayah ta sauka snn Farida, Yakumbo ma ta sauka tayi hanyar cikin gidan suna biye da ita... Mumy ta fito daga kitchen kenan suka shigo parlon, ganinsu ta baje fara'a a fuskarta tace "Sannun ku da xuwa" kallo daya Yakumbo tayi mata ta nufi kujera tana cewa "Ina patun take?" Mumy na ta murmushi ta karaso cikin parlon tace "Ta je gida, Amma yanxu xata dawo" Yakumbo tace "Ya mai jikin?" Mumy tace "Da sauki Alhmdllh, yana cikin daki, Heedayah rakata dakinsa" sosai Heedayah tayi mamakin abinda Mumy tace, ta dai gaisheta tare da Farida, Mumy ta amsa tana washe baki tace "Ki kai ta dakin Shuraim" mikewa Heedayah tayi ta nufi dakin Shuraim Yakumbo na biye da ita a baya, ta bude kofar dakin ta tsaya nan bakin kofa ta ki shiga, Yakumbo ta shige dakin tana kallon Shuraim dake kwance yyi rub da ciki yana bacci, he looks so sick and tired, Yakumbo tace "Toh kai kuma ya da kwanciyar 'yan wuta, cuta ai ba mutuwa bace" Shuraim ya bude ido a hankali, ganinta tsaye dakin ya mike xaune da kyar, Yakumbo tace "Sannu, ya jikin?" Ya gyada mata kai yace "Da sauki, ina kwana?" Tace "Lafiya lau, me ke damun ka haka?" Murya can kasa yace "Na ji sauki" Ta xaro ido tace "A haka?? Toh Allah ya sauwake, amma wnn kam ai kana jin jiki...." Ya daga kai ya kalli Heedayah da ta ki shigowa har sannan, suna hada ido ta sauke kanta tace "Ya jiki" Bai amsa ba ya cire Duvet din jikinsa ya saukar da kafafuwansa kasa, Yakumbo tace "Tana maka ya jiki" ya daga kai ya kara kallonta yace "Fine" Yakumbo ta kyabe baki ta nufi kofa tana cewa "Ita ma ai bakin halin gareta" da sauri Heedayah ta bi bayanta bayan ta fita ta kullo masa kofarsa suka koma parlor, Mumy tuni ta ajiye ruwa da lemo har da abinci a kasa kusa da kujeran da Yakumbo ta fara xama, Yakumbo na kallon abincin tace "Aa mu mun ci abinci kafin mu fito, kamar dai ana yunwa" Tana fadin haka ta matsar da abincin gefe ta xauna tace "Me ke damun shi Aliyun haka?" Mumy tayi kasa da murya tace "Wllh bamu sani ba, ya ki fadi...." Yakumbo tace "Toh ba a je asibiti bane?" Mumy tace "Yayan Abbansa ya xo daxu yyi masa allura ma, toh shine yake ta bacci tun daxun, yana dai complain din ciwon kirji" Yakumbo tace "Toh Allah ya sauwake, ita patun yanxu xata dawo kuwa?" Mumy tace "Ehh taje yi masa girki ne kafin ya tashi wai, na ma ce ta barsa gashi nayi amma ta ki saurarata" Yakumbo tace "Toh ai da kince mana yana bacci da bamu tashe sa ba yyi baccinsa isasshe" Mumy dai sai murmushi take bata ce komai ba, Farida dai idonta na kan TV da gaba daya bata san abinda ake ba, Mumy ta mike ta wuce kitchen, ba a dau lkci ba sai ga ta ta dawo da cup din shayi ta nufi Heedayah dake xaune ta mika mata tace "Tunda ya tashi gashi ki kai masa, tun safe bai ci komai ba, Allah ya sa ya sha wnn din ma" Heedayah ta d'an buda ido tana kallonta, ganin mika mata dai Mumy ke yi ta amsa ta kalli Farida dake kallonsu, Yakumbo tace "Toh ko baxa ki kai masa din bane tunda kunya bai isheki ba, sai Farida ta amsa kawai ta kai ita" Heedayah ta d'an hade rai ta mike ta nufi dakin, Farida ta bi ta da ido, a hankali ta bude kofar dakin tana kallon ciki, xaune ta gansa yanda suka barsa ya rike kansa da duk hannunsa biyu, jin an bude kofa ya dago sai dai bai kalli kofar ba, ta shigo dakin ta ki kulle kofar, kamar warce aka tilasta tafiyar ta isa inda yake xaune tace "Mumy tace in kawo maka" Jin yyi shiru ta durkusa ta ajiye masa cup din tea din, ta mike xata fita taji yace "Heedayah" tsayawa tayi amma bata juyo ba gabanta na faduwa, bayan few seconds ta juyo a hankali tana kallonsa.... Bayan tafiyarsu Heedayah kafin azahar Ammi ta dawo gidan, Mami na kallonta tace "Amma dai bbu tafiyar ta ku yau ko?" Ammi tace "Ehh wai Aliyu bashi da lafiya daxu Abbansu Islam ke gaya min, kuma Yakumbo ma taje can gidan ko?" Mami tace "Ehh tana can da su Heedayah" Ammi tace "Dole sai gobe kenan xa mu tafi, anjima daddare xan je dubasa idan Allah ya nufa" Mami tace "Allah ya kai mu, xan d'an fita in dawo yanxu Maman biyu" Ammi tace "Toh shhkn Allah ya tsare hanya" Hijab Mami ta sa har kasa ta dau wasu files Ashnaah ta fara kuka xata bi ta, Mami ta kama hannunta suka fita, Abba take son kai ma files office kamar yanda ya bukata, bayan tayi warming motarta ta fita gidan tare da Ashnaah dake xaune front seat.... Mami na fitowa daga layin, aka sauke glass din wata farar mota dake parke nesa da layin, Oga Manga ya kalli Zayyad dake gefensa cikin motar yace "Ita ce wancan?" Zayyad yace "Aa...." Wani naushi Manga ya kai masa yace "Ba matar nan muka tarar asibiti a Abuja ba??" Zayyad yyi shiru a ransa yana mamakin me yasa Khaleel yyi ignoring din message din da yyi passing masa ta waya da safe, Wani naushin Manga ya kai masa, Zayyad yace "Ita ce" tada motar Salim yyi suka bi hanyar da Mami ta bi a guje kafin Wani barrier ya shiga tsakaninsu, Mami na isa office din Abba tayi parking waje ta dau wayarta ta kirasa don ya fito ya amshi envelope din hannunta don baxata shiga ciki ba, Ashnaah dake xaune tace "I want to ease my self..." Mami ta kalleta tace "Ohk" daga haka ta bude motar ta sauka ta rufe ta xagayo ta inda take ta bude motar ta sakko da ita, A bayan motarta su Manga suka tsaya da tasu motar, duk da ta ga motar bata kawo komai ba ta xata client din Abba ne, Manga na kallon Fago yace "Kayi attacking yarinyar karama first...." Fago ya dira motar ya nufi Mami da ke daga kayan Ashnaah, lkci daya ya fiddo bindigarsa ya daura mata a kai yana kallonta da masked face dinsa, Xaro ido Mami tayi tana kallonsa kafin tace komai ya fixge Ashnaah daga hannunta xai koma motarsu ta bisa a rikice yana ganin haka ya bude motar ya jefa ma Manga Ashnaah, Manga na kallonta yace "Ki shigo idan kina son yar ki da rai...." Ai Mami bata san lkcn da ta shiga motar ba, ta shiga tashin hankalin da ya wuce misali, a rikice take cewa "Ku fadi abinda ku ke so daga gareni amma ku rufa min asiri kar ku tafi da 'yar mutane..." tuni Fago ya rufe motar ya shige gaba Salim ya tada motar suka bar wajen a guje, Zayyad dai ya sunkuyar da kansa ya kasa dagowa, Ashnaah ta haye jikin Mami a tsorace tana kuka sosai don gaba daya fuskarsu a rufe yake, Mami ta rungumeta har ranta taji farin cikin ba Ashnaah kadai xa su tafi da ba har ita....




Heedayah isn't free, you read for free 🤷🏻‍♀️🤷🏻‍♀️


it's 300 via... Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah


Then you show ur evidence via WhatsApp 07087865788....








Khaleel na kwance saman 3 seater a parlonsa, yyi nisa tunanin da yake idonsa na kan pop din parlon, a hankali ya juya yana kallon wayarsa da yyi vibrate a gefensa, ganin me kiran nasa ya ki dauka har ya katse, sake kira aka yi, ya mike xaune da kyar ya daga kiran yace "You called bana jin ka daxu kuma ka kashe waya gaba daya, What's up?" Muryar Oga Arne ya ji yana dariyar bosawa, Khaleel yyi shiru ya sake kallon screen din wayar yaga number Zayyad ne ya katse wayar ya kashe gaba daya ya jefar nan gefensa ya koma ya kwanta ya lumshe ido xuciyarsa na bugawa.... Mami na kallon katti ukun dake kanta a tsaye cikin wani daki ko wannensu rike da bindiga, tana son magana amma ta kasa cewa komai sai hawaye, Ashnaah ma sai kuka take tana shigewa jikin Mami, fuskarsu dake boye cikin face mask shi ke kara tsorata yarinyar, cike da karfin hali Mami tace "Ku fada min me ku ke so daga gareni?" Bbu wanda ya tanka ta cikinsu da alama gadinta kawai aka ajiye su suyi, Ta rungume Ashnaah tana lallashinta tana karanto addu'o'i a xuciyarta na neman tsari da sharrinsu. Shuraim bai yarda ya hada ido da Heedayah dake tsaye tana kallonsa ba yace "Close the door" ta kalli kofar sannan ta kallesa, kin xuwa ta kulle kofar tayi kuma bata ce komai ba, ya kalleta suka hada ido yace "Baki ji me nace bane?" Tace "Toh saboda me?" Mikewa yyi ta koma gefe da sauri tana kallonsa kamar xata yi kuka, ya isa gun kofar ya kulleya juyo yana tsaye wajen yace "I want to ask you 2 to 3 questions" Ta d'an yi shiru, sai kuma ta gyara tsayuwarta tace "Ina ji" Ya jingina da kofar bai yrda sun sake hada ido ba yace "And promise to say the truth... Nothing but the truth" ita dai tayi shiru tana jin sa, yace "Kin tuna lkcn da Abba ya kawo ki gidanmu ko?" Ta gyada masa kai, yace "Good, daga lkcn xuwa ynxu shekara nawa kenan?" Still not looking at him tace "Shidda" Yace "Alright, a cikin shekara shiddan nan can you plss remind me ko na ta6a cutar ki?" Kura ma carpet din dakin ido tayi trying to digest what he just said, bata san lkcn da tayi murmushi ba don ba karamin dariya tambayar ya bata ba, yana kallonta ce "Ina sauraron ki" tace "Wani irin cuta kenan?" yace "Duk abinda a tunanin ki cuta ne" tace "Ni na manta" Yace "Baki manta ba, bani amsata" Tace "Toh idan ma conscience dinka na judging dinka ne sbda abubuwan da yasan kayi, duk da ni dai manta pass dina balle in tuna abinda aka min, to I've forgiven you" Yace "My conscience can never judge me don nasan ban maki komai ba duk Shekarun nan...." Tace "Toh me ya kawo maganan nan yanxu idan kai kasan baka ta6a min komai ba?" Yace "Like, kina min kallon kamar wanda ya cuceki a rayuwar da kika yi gidanmu, always frowning when ever u see me, and many of that" Da mamaki take kallonsa tace "To dama mun saba magana ne da kai balle kace Ina frowning? I've known you to be someone that don't bother about others, baka shiga harkan kowa, kowa ma baya shiga naka harkanka, to me yasa xaka yi tunanin xan dinga shiga harkan ka yanxu?" Shiru yyi yana kallonta, can yace "Kin fahimci haka nake yi ma kowa kenan" A takaice tace "Ba kowa ba, ai kana sake ma cousins dinka, ur sisters idan sun gaisheka kana amsawa, kana siya masu abubuwan da ya kamata...." Yace "Ke kuma fa?" Ta d'an kallesa tace "Do I need to tell you that" Yace "Bana maki abubuwan duk da kika lissafa kenan" ta buda hannu yace "You've said it" komawa yyi gefen gadon ya xauna yyi shiru, bayan minti uku tana kallonsa tace "Can I go" ya dago ya kalleta, a hankali yace "You can, one day you might understand all what happened during ur stay in our house" tace "Why not now?" Ya girgixa mata kai yace "One day" juyawa tayi ta nufi kofa har xata bude ta juyo tace "Sauran tambayar fa?" Ya girgixa mata kai yace "No need" fita tayi ta sake juyawa ta kallesa suka hada ido ta sauke nata idon ta kulle masa kofarsa ta koma parlor, Mumy sai kallonta take bayan ta fito, Yakumbo tace "Ya sha shayin kuwa?" Heedayah tace "Yana sha" Mumy tace "Toh kinga, tun daxu nake fama da shi ya ki sha, da ta kai masa ai gashi ya sha" Har kusan karfe biyar Khaleel bai yarda ya kunna wayarsa ba, yana ta kwance kan kujera sai juyi yake ya rasa me ke masa dadi, ga xuciyarsa yyi masa nauyi, sllh kadai ke tadasa daga kan kujeran yana dawowa masallaci kuma xai ci gaba da kwanciyarsa ko abinci bai ci ba throughout, bai ta6a tunanin Heedayah will be the first person to judge him ba, but ya mata uxuri coz she just have to, yana nan a haka har aka kira Magrib, ya mike xaune da kyar ya rike kansa, jin xa a tada sllh ya tashi ya shiga bandaki dake parlon ya dauro alwala ya fito ya wuce masallaci, ko da ya dawo makullin motarsa ya dauka yana tunanin yaje gidan Mami ko kar ya je, bai san yanda Heedayah xata kuma karbansa ba idan ya koma, amma ya ji bayan ita ma yana son ganin Mami ko xai d'an ji sauki, hira da ita na gusar masa da damuwarsa for sometime, mamakin Heedayah ya kasa barin ransa duk da uxurin da yyi mata, did he make a mistake telling her who he is? Gaba daya ya ma rasa takamaiman tunanin da xai yi ya ji sauki a xuciyarsa dake masa xafi sosai, ya jawo wayarsa a hankali ya kunna he need to share this with Zayyad, har yayi dialing number Zayyad ya tuna muryar Arne ya ji daxu maimakon Zayyad din, katsewa yyi xai kashe wayar gaba daya text ya shigo masa, number Zayyad ya gani, hakan yasa ya shiga text din yana duba content dinsa, mikewa yyi da sauri yana sake karanta message din xuciyarsa na bugawa, kunna datansa yyi kamar yanda aka umurcesa a text din ya hau WhatsApp bayan some minutes sai ga message din Oga Arne ya shigo ta WhatsApp din, ya bude yana xaro ido.... Video ya ga Arne ya turo masa, yana gama downloading video din ya ga Mami xaune kasa ta rungume Ashnaah dake ihu tana kiran Ammi, ya ji Muryar Arne yana cewa "Kina son sanin wanda ya bada umarnin dauke ki daga cikin iyalanki??" Mami dai bata ce komai ba hawaye kawai ke sauka idonta sosai, abubuwa da yawa ne ke dawo mata na shekaru masu yawa da suka wuce, rungume Ashnaah tayi sosai a jikinta tana Kuka, sai take ga kamar xa a kwace ta ynda aka ta6a yi mata, Arne yyi wani shegen dariya yace "Ki sa ma ranki salama, xaki ga wanda yasa aka dauko ki, sannan miliyan hamsin ake bukata na ransom" Mami ta girgixa kai tace "Ba mu da wnn kudin, bamu da dalilinsa, ku ji tsoron Allah ku ji tsoron gamuwar ku da shi...." Arne ya sake yin wani dariya sai kuma ya hade rai yace "Wa'axi xa ki mana, to kuwa xa mu aika ke da yarinyar barxahu yanxun nan...." Mami tace "Wnn sai lkcn mu yayi" Banda xufa bbu abinda Khaleel ke yi daga tsayen da yake yana kallon video din, exactly kalan tashin hankalin da ya shiga lkcn da Heedayah ta kwana gidansa da su oganninsa suka xo, Arne yyi video din fuskarsa dake lullebe cikin mask yana 6a66aka dariya yace "Sai ka xo Brainiac" Khaleel ya kalli time din da aka turo masa video din ya ga tun karfe biyun rana ne, bai san lkcn da ya suri makullin motarsa ba ya fice gidan almost running. Da karfi ya bude kofar parlon gidan da suke haduwa da oganninsa yana huci, Salim da Fago na xaune suna xuke xuke, Manga ya fito daga wani daki kamar an yi announcing masa presence din Khaleel, wani dariya duk suka saki a parlon kamar hadin baki, Arne ya fito daga wani dakin sannan Bala ko wannensu na ma Khaleel wani kallo yana murmushi, a nutse Manga yace "Welcome back after a year Brainiac...." Khaleel bai ce komai ba ya nufi sama don yasan a dakin sama Arne yyi video din Mami, Tsaye ya ga wani Ogan nasa a sama ya tare hanya da bindiga a hannunsa, Khaleel ya dakata xuciyarsa na bugawa, Arne yace "Ina kake tunanin xaka Brainiac? Snn me kake tunanin xaka yi?" Khaleel ya dawo gun Arne cikin tsawa yace "I've served you for many years, I've been loyal for many years, I need my freedom now, I need freedomm...." Naushi Arne ya kai masa a ciki ya fixgosa yana huci cikin tsawa sosai yace "Duk ranan da kake tunanin samun freedom daga garemu to mutuwa kayi Brainiac, we will be together till the end, you will continue serving us till the end, ko kana da wasu sama da mu a duniyar nan ynxu, nayi maka alkawarin a gabanka xan aika matar nan barxahu don hakan kadai xai sa kanka ya dawo dai dai kasan abinda kake yi...." Da karfi Arne ya tura sa ya nufi sama rike da bindigarsa yana huci, sanin halinsa da abinda xai iya aikatawa sarai yasa Khaleel ya taresa da sauri yace "Noo plss, bata da laifin komai Oga, ka gaya min yanxu me ku ke so daga gareni I promise to abide, don't harm her plss" Arne ya tsaya yana huci yace "Sharadi uku xan baka da xaka yi abiding to... Abiding to the rules kadai xai sa mu bar matar nan da ranta, wllh... Kaji har na rantse maka" Khaleel da xufa ke karyo masa daga sama har kasa ya dake yace "Ina jin ka...." Arne yace "Yanxu xa mu tafi gun ta a matsayin kai ne oganmu gaba daya a nan, I want it to look like kai ma kasa mu dauko maka ita, snn xa ka bukaci amsan ranson na miliyan 50 don naga da maiko sosai tare da ita, snn daren yau muna da operation


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login