Showing 159001 words to 162000 words out of 275313 words
Chapter 54 - Heedayah Book Complete by Khalisat Haidar .txt
see... shi ma a Abujan xai kwana yau kenan?" Tace "Aa yana da night duty, he is going back to Kaduna" yace "When?" Tace "Yau din nan" yace "Nasan yau din nan , karfe nawa nufina xai tafi" tayi shiru snn tace "Nima ban sani ba" yace "Are you still together with him now?" Tace "Yess" yace "If he is going ki gaya min, Kar ki manta...." tace "Saboda me xan gaya maka??" yace "Nothing, bana son in kira ki yana nan ya gani, so idan kika ce min ya tafi i can call anytime" ita dai bata ce komai ba, yace "Heedayah" tace "Ina ji" yace "Me yasa kika yi shiru" tace "Aa ba komai" yace "Ohk, gidan wa ku ka je a Abuja" tace "Gidan yayar mu" yace "Toh ki bani address din wajen" tace "Sbda me?" Yyi kasa da murya yace "Baki son ganina kenan!" Ta turo baki tace "Toh ni fa I still don't know why we are together, Ina ce parent dina xaka nemo min kace??" Murmushi yyi yace "Su xan nemo maki in sha Allah" Tace "You are not making effort, kawai dai kai kana son mu dinga haduwa ne" yace "Noo Heedayah, tunda ba tare muke dake ba ai you won't see my effort, you are only desperate to meet with ur parent shi yasa kike ga I am not making effort, but trust me dear tunda nace xa ki ga iyayen ki, xa ki gansu" ta d'an yi shiru kafin tace "Ohkk" yace "Good gal, send the address via Sms now" tace "Toh" katse wayar tayi, ta mike ta fita daga dakin, Farida na parlor tare da yayarta sai Fadil da wata yarinya da baxata wuce shekara uku ba suna wasa da Fadil dake xaga parlon a kekensa tana biye da shi da katon doll dinta, Maman Fadil na duban Heedayah tace "Kinyi sllhn?" Heedayah tace "Ehh na yi" Maman Fadil tace "Toh ga abinci an kai maku dining area, na samu labarin baki cin tuwo ko..." Heedayah tayi murmushi ta sunkuyar da kanta bata bata amsa ba, ganin ta nufi kofa Maman Fadil tace "Ina kuma xa ki?" Heedayah tace "Ina xuwa" Bin ta suka yi da kallo da Farida har ta fita, Can gun mai gadi ta nufa tana kallonsa ya mike ya bude mata gate din gidan, fita tayi ta duba address dake manne daga gefen gate, ta bi anguwar dake dauke da manyan gidajen gaske da kallo, lafiyayyen titi ne malale anguwar, ko wani gida da flowers xagaye da shi masu kyau, tsayawa kallon katon gidan dake kusa da na su Maman Fadil tayi, don gidan har ya fi nasu girma da haduwa, taji muryar Farida a bayanta tace "What are looking for outside Heedayah?" Heedayah ta juyo da sauri tace "Nothing" Farida ta rungume hannunta tace "Hope you are not trying to give anyone address to this house?" Heedayah ta bi ta gefenta ta wuce ciki tace "Not at all pls" daga haka ta nufi entrance din gidan Farida ta bi ta da kallo. Heedayah bata wani ci abincin kirki ba ta wuce sama xuwa dakin da suka sauka ta dau wayarta ta tura ma Khaleel text din address din gidan snn ta kwanta ta rufe ido kamar me bacci tana nan a haka har aka yi la'asar snn ta mike ta shiga bandaki tayi alwala ta fito, da sauri ta dau wayarta kafin ya katse, tace "Have u seen it?" Daga daya bangaren yace "Sure, Ina ta jira baki gaya min ko Yayan naku ya bar Abuja ba" Heedayah tace "He is not leaving today" yace "Why?" Tace "Haka nan kawai, may be tare xa mu koma" Jin Khaleel yyi shiru tace "Xan yi sllh, sai anjima" katse wayar tayi ta mayar cikin purse dinta, bayan ta idar da sllh ta sauka parlor, bbu kowa parlon sai su Fadil, ta karasa gun su da sauri ganin fada suke, ta riko Fadil tace "Me tayi maka Fadil? What happened??" Muryar Mum dinsa taji daga sama tana cewa "You've started fighting her ko, to gobe in ji kace a kai ka wajenta, baka da kirki wllh" kamar xai yi kuka yace "Mumy she is pushing my bicycle, why will she? did i push her fat doll??" Heedayah dai na rike da hannun yar yarinyar dake ta kallon Fadil hawaye makale idonta, ta dau hularta da ya fadi kasa ta rufe mata dogon gashinta da shi tana bata hakuri, yarinyar na nuna sa cikin rawar murya tace "You are not my frnd any longer" Maman Fadil ta sakko ta karbe hannunta daga na Heedayah tace "Yi hakuri kin ji Islam, don't cry" Farida ta shigo parlon tace "Aunty yarinyar waye wai, ban ta6a ganinta ba, yar me kyau da ita" Maman Fadil tace "Yarinyar makociyata ce, shi ke makale mata fa, amma idan ta shigo yyi ta mata walakanci, bini bini kya ji yace xai tafi gun islam" tuni Fadil ya wuce sama kamar Soja a dole yyi fushi, Maman Fadil tace "Heedayah ku kai ta gida da farida yanxu tana fara kuka bbu me iya lallashinta a nan" Heedayah tace "Wani gidan ne nasu?" Maman Fadil tace "Ku tambayi Mai gadi idan kun fita" Heedayah ta dau doll dinta ta mika mata yarinyar ta amsa sannan suka fita tare da Farida don kai ta gidansu, kiris din ya rage Islam ta fara kuka, bin su kawai take tana makale da doll dinta, suna fita gate Mai gadi ya nuna masu gidan nasu, suka kwankwasa gate Mai gadin gidan ganin tare suke da Islam ya bude masu yana kallon Heedayah suka shiga cikin gidan, shi ya nuna masu inda xa su bi, babban gida ne na gaske me dauke da duplex biyu, motoci ne a duk parking space uku dake compound din da ya kawatu da flowers ta ko wani angle, suka danna bell bayan few minutes aka bude kofar, gaisheta suka yi, ta amsa tana masu sannu da xuwa sannan ta amshi hannun Islam tace "Tana daya bangaren mamanta, Bismillah ku shigo yanxu xata fito" Farida tace "Aa, muna dai gaisheta, sai anjima" daga haka suka juya suka nufi gate suka bar gidan. Heedayah na xaune saman darduma ta idar da magrib jin wayarta na vibrate ta kalli Farida dake sllh, mikewa tayi ta bude purse din ta ciro wayar snn ta daga ta kai kunne, daga daya bangaren yace "Ina waje" ta xaro ido ta d'an kalli Farida, sai kuma tace "Ohk" katse wayar tayi ta ajiye, haka nan kawai taji kamar an cire mata tsoro a ranta, taji she is not even afraid of anyone, taji kuma she wants to meet with Khaleel, tana ta xaune dai har Farida ta idar da sllh ta mike ta fita dakin, sannan ita ma ta mike tana rike da gyalenta da ta linke ta sauka parlor, tsaye ta same farida inda take shiga ba nan take fita ba, yayarta dai na xaune tana feeding din Fadil tana kallonta, cike da fada tace "Kuma wllh idan ya koma da wayata baxan sake amsar wayar ba ko an bani, dubi fa yanda na wani xauna tun rana kamar marainiya ba waya, nasan kuma ana ta kirana, ba sai ya bari driver yaje ya amso min kayana ba dama idan ba niyyar tafiya yyi da shi ba" kamar xata yi kuka ta kare maganar, Maman Fadil tace "Toh bari a kara kiransa amma Ina jin bai tafi bane da xai tafi ai xai kira yace in turo driver haka muka yi da shi" Farida tace "Lallai baki san waye shi bane Aunty wllh da gangan ma sai ya iya tafiya da wayar don in ji haushi, ai kinga ita da ta janyo ya amshe wayar har yanxu bata ce min komai ba as if fault dina ne, kuma har komawa tayi gaban motar fa ban san me ya kai ta can ba ta xauna, kuma sai tace bata ga wayar ba a kusa da ita???" Heedayah dai ko kallonta bata sake yi ba tayi hanyar kitchen, Mai aiki ce ta fito kitchen din ta gama wanke wanke, Farida ta bi Heedayah da wani shegen kallo har ta shige kitchen din, Maman Fadil tayi kasa da murya tace "Ni gaskiya bana son haka Farida, xata ga kamar don ta biyo ki ne kike mata haka, tun rana sai masifa kike mata gashi ta ki kulaki, bata ce maki komai sai masifa kike, wnn bai yi ba dai" Farida tace "Wa?? Kin xata wai ta rasa abinda xata ce ne yasa tayi shiru, ai ko xan kwana ina yi baxata tanka ba kuma baxata bani hakuri ba, taurin kai ne da ita da kike ganinta haka, wllh nasan kila da gangan ta bar masa wayar dama naga sai wani shisshige masa take" Maman Fadil tace "Shisshige masa ta ya kuma?" Farida ta xauna fuska daure tace "Ohon masu" Murmushi kawai Maman Fadin tayi ta dau wayarta tace "Bari dai in sake kiransa" dialing Number Shuraim tayi ba a dau time yana ring ba ya daga, gaisawa suka yi tace "sai muka ji shiru Yaya Shuraim..." Ta gama sauraronsa snn tace "Toh shkkn ba matsala, Allah ya tsare" katse wayar tayi ta ajiye, Farida ta xumburo baki tace "Wai me yace??" Maman Fadil tace "Jarabbiya to yana hanya xai kawo maki ynxu" da mamaki Farida tace "Toh me yasa bai koma ba??" Maman Fadil tace "Kilan ya gaji ne, kamar ma bacci yake, Amma yace xai taho ya kawo ynxu" Farida ta tabe baki bata dai ce komai ba. A hankali Heedayah ta bude kofar dake kitchen da xai sada ka da bayan gidan ta fita snn ta jawo kofar very careful kar yyi making ko wani sound snn ta yafa veil dinta ta fara tafiya da sauri, ta jikin parking space ta raba har ta isa gate, ganinta mai gadi ya fito dakinsa da sauri yace "Fita xa ki yi Hajiya?" Ta gyada masa kai, ya bude mata gate din ta fita, tana fita ta juya ta kallesa don tsayawa yyi ya ki komawa ciki as if wanting to know where she is going, ta hade rai, sau daya ta kalli motar da ya tsaya shi daya a layin da hasken fitilu ya haska kamar ba dare ba, ta san Khaleel ne duk da ba motar da ta saba ganinsa da shi bane don wnn har ya fi wancan haduwa amma bata tsaya ba tafiyarta kawai take, can ta ji Mai gadi ya kulle gate din ta juya taga ya koma ciki, A hankali Khaleel ke tafiya har ya tsaya dai dai flowers din gidan da suka kai islam daxu amma ta opposite, Heedayah ta sake juyawa tana kallon gate din gidan da ta fito snn ta nufi motar, sauke tinted glass dinsa yyi ta xagaya ta bude front seat ta shiga ta rufe. Khaleel na kallonta murya can kasa yace "Hope u took permission before coming out?" Ta girgixa masa kai ba tare da ta kallesa ba, yace "Why?" Ta turo baki bata ce komai ba, yace "Heedayah" daga manyan idanuwanta tayi ta kallesa tace "Don a min fada?" Yace "Toh ai ba a gida kike ba, kuma yawanci xa ki ga aunties usual don't have much problem, da yawa idan mace na son haduwa da saurayinta kuma ba a barin ta fita a gida, ta kan hada baki da yayarta ko aunt dinta sai ta xo gidan aunt din nata su hadu, kuma bbu wanda xai sani sai daga ita sai aunt din, so wnn ma da kin gaya mata baxata hanaki ba" Heedayah ta wani kallesa tace "To kai saurayina ne?" Shiru yyi yana kallonta, can yyi murmushi ya girgixa mata kai yace "Aa" ta dauke kanta, yace "Amma duk da haka da kin gaya mata, ko da yake naga kin fiye tsoro ke din" Tace "Not when Farida is there xan gaya mata, Beside it's not as if mun saba sosai da ita, na fi sabawa da kanwarta Aunty Fatee" yace "Ohk wnn baki santa ba?" Tace "Aa na santa, tana xuwa once in many month tayi two days" yace "Ohk how about her husband?" Tace "Yana UK shi" Khaleel ya gyada kai bai ce komai ba, ya ciro wayarsa dake vibrate a aljihunsa, Zayyad ne ke kiransa ya mayar da wayar ya ajiye har ya katse, tun yana hanya Zayyad ke kiran nasa yaki dauka, ya kalli Heedayah yace "Hope kin ci abinci?" Ta nuna masa wayarsa da aka sake kira tace "Pick ur call" Ba musu ya daga ya kai kunne bayan ya rage call volume din, Daga daya bangaren Zayyad yace "You caused everything Khaleel, you just ruin everything, da ka bi mu wllh wllh duk wannan abinda ya faru baxai faru ba, and mind you Oga Manga na neman ka yanxu haka, just don't show up anytime soon..." Calmly Khaleel yace "Me ya faru?" Zayyad yace "Abinda ya faru shine an harbe Saif and he is dead, mu hudu muka fita dama, kuma we weren't early enough don har target dinmu sun wuce exact village din that's conducive for the operation, and u caused everything, so muna dai tafiya not knowing an kafa wani check point a gaba sbda robbery da aka yi a wajen da asuba har an kashe wasu, da mun san da check point din da baxa muyi attacking dinsu ba a particular area din da muka yi attacking dinsu, everything wasn't in our favor today, mun sha ne da kyar... It wasn't funny Khaleel, kuma duk kai ne ka ja komai, Oga Manga na nemanka yanxu haka" Khaleel da yyi shiru yana sauraronsa yace "Tough day indeed" daga haka ya katse wayar ya sa flight mode ya ajiye, Wani mota ne ya shigo layin ya haskosu, da sauri Heedayah ta dukar da kanta, Khaleel ya dage glass din motarsa yana bin motar da ido, dai dai gidan dake opposite dinsu motar ya tsaya Mai gadi ya wangale gate, a hankali Heedayah ta dago kanta motar ya shiga gidan aka rufe gate din, kallonta Khaleel yyi yace "Kin taba xuwa layin ne da kike boye fuskarki?" Ta girgixa masa kai, xai yi magana wani motar ya kuma shigowa layin, Heedayah ta xaro ido sosai tace "Yaya Shureen" rufe fuskarta tayi da gyalen jikinta, Khaleel ya dinga kallon motar har ya iso inda motarsa ke tsaye, Heedayah ta dago kai ita ma a hankali ta bi motar da kallo, dai dai gate din gidan Maman Fadil yyi parking, Heedayah na kallon Khaleel kamar xata yi kuka tace "Did he see me?" Girgixa mata kai yyi yace "Tinted glass ne ai" Ta juya ta sake kallon motar Shuraim ta ga ya sakko daga motar sai da ya fara kallon motar Khaleel snn ya tafi ya kwankwasa gate din gidan, Heedayah ta marairaice tace "Kila ya gan ni fa" Khaleel yace "How? is he having tinted eyes?" Tace "Ni dai mu je gaba to" driving din motar yyi yana tafiya a hankali har ya bar layin gaba daya. Kallonta yyi yace "Ina xa mu je" tayi shiru gabanta na faduwa, sai kuma ta ji kamar an cire mata tsoron gaba daya, ta jinginar da kanta da kujeran motar a hankali tace "Anywhere"
Heedayah isn't free, you read for free 🤷🏻♀️🤷🏻♀️
it's 300 via... Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah
Then you show ur evidence via WhatsApp 07087865788....
Shuraim na shiga gate din gidan ya hadu da Farida xata fita ita kuma, komawa baya tayi ganinsa, ya mika mata wayarta, ta amsa kamar dai baxata ce komai ba sai kuma tace "Thanks" juyawa yyi xai fita, har xata yi magana sae kuma tayi shiru sai da taga ya fita gate din sannan ta leka waje, da ido ta hau surveying din street din, mamaki ne ya cikata ganin bata wani ga alamar Heedayah ba, to ina ta tafi, suka hada ido da Shuraim da ya bude motarsa ya shiga, ta dauke kai ta shigo cikin gidan tana kallon Mai gadi tace "Don Allah warce muka xo gidan nan daxu tare ta fita ne?" Mai gadin yace "Ehh ta fita" Farida ta fita gate din gaba daya tana sake bin layin tun daga saman sa har kasa da kallo, banda motar Shuraim bbu wani mota dake waje a wajen bbu kuma alamar mutum a layin, ganin kallon da Shuraim yake mata daga cikin mota ta juya xata koma ciki, taji yace "Come here, who are you looking for??" Shiru tayi bata son ce masa Heedayah take nema ta ja mata, can ta kallesa a takaice tace "Nobody" bata jira cewarsa ba ta shige ciki. Gun yayarta dake xaune parloe ta koma tace "Aunty ban ganta ba fa" Maman Fadil ta mike da mamaki tace "Baki ganta ba kuma, to ina ta tafi?" Farida tace "Wllh ban sani ba kuma me gadi yace ehh ta fita gate" Kasa cewa komai Maman Fadil tayi tana kallon Farida, Farida tace "And ni ban ga kowa a layin ba" Maman Fadil ta xaro ido tace "Toh kar dai bin wani tayi tunda kince kinji tana waya da saurayi" Farida ta girgixa kai tace "Noo Heedayah will neva follow him, ni na santa baxata yarda ta bi sa ba" Maman Fadil tace "Yau Naga ikon Allah, to idan ba bin sa tayi ba guduwa yyi da ita? Waye shi din, ke kin san sa ne?" Cike da damuwa Farida tace "Ni ban wani san sa ba wllh, kuma fa bbu wanda ya san ya bata waya, nima bata gaya min ba kawai gani nayi tana ta boyewa, I am just confuse, ina Heedayah xata je da daddaren nan" Bude baki Maman Fadil tayi tace "Na shiga uku ace a gidana, ita Hadiyar dama haka take? Daga xuwa garin mutane sai ki bi saurayi ku yi tafiyar ku, duka duka nawa take da xata aikata wnn aiki, ko kece kika bi saurayi daren nan ba sai Mami ta kusa balla ki ba balle ita, ni yanxu matsala xa a ja min kawai wllh, ta ina xan fara wani bayanin yanda aka yi, kamar wasa kawai a nemi yarinya a