Showing 84001 words to 84608 words out of 84608 words
Chapter 29 - Wa Zai Furta Book Complete by Zainab Dahiru Wawo.txt
Yar dariya lafiya Lau kuxo ga break din can......
Sai kusan azahar suka bar sashen ta dan sake kadan....
Suna shiga ya rikota zo ki gani..... Yabi da ita wani corridor suka shiga wani falo ya ce nan ma naki ne fa, ya bude bedroom din sai ga wasu irin set na gado royal masu kyau gefe jakun Kuna ne set talatin da shidda ya ce ga lefen ki Zaki gani Yanzu ko ba Yanzu ba?
Ta sunne Kai jikin sa kawai.... Ya danyi dariya *Bilkisu kunya*...............
Ya kamota ya zauna a kujera ita Kuma tana bisa cinyarsa.
Gaskiya kin saka ni farinciki Bilkisu naji dadi jiya har mutuwa nayi na dawo..... Bata San lokacin da ta kyalkyace da dariya ba .... Shima ya Kama dariyar ya ce Allah kinji nayi magana? Ai kasawa nayi.
... Next week zamu tafi Dubai a can zamu zauna Ina da gida a can, sadeeq zai ringa taking care na business din Nigeria tare da taimakon su Suleiman...... Ni Kuma Zan ci gaba da duba na sauran countries din nida su Alhaji murtala..... Kina son Zama Dubai?
Ta danyi murmushi ta ce um.Daga nan Zaki dauki Yan aiki ko kina son na can?
Duk yanda ka gani.... Yayi murmushi.
Zan baki appointment idan result ya fito kema kina amsar albashi kin San hausawa na cewa *Da namu gwamma da nawa* ya karasa maganar Yana dariya.... Kin San duk wakokin bikin Nan nafi son wakokin da *Aliyu nata* yayi Mana?
Ta danyi dariya gaskiya ya iya Waka, ya ce sosai ga babu zagi, ba habaici babu maganar banza yaron ya zo da basira Mai tsafta Shi yasa ake rububinsa..........
Ya Dan taba cikin ta Allah yasa jiya Yara sun shiga...... Ta soke Kai jikinsa..... Ya kyalkyace da dariya.............✍🏼
*KARSHE*
Allah ya bada zaman lafiya da zuri'a dayyiba.
Muna rokon Allah ya karemu daga cututtukan zamani.
Abinda muka karanta Allah yasa mu amfana da lesson din ciki na Shi mutunci Riga ne, ya kamata mu sani kunya na daya daga cikin abinda ke daga darajar mace a duk inda take.
Kwadayi baya Kai mutum ko Ina sai tushen wulakanci da Kuma nadama.
Mai kudi da talaka duk bayin Allah ne, masu kuci da ke nuna Basu iya rayuwa tare da talakawa ku sani rayuwar dasu bazai rage ku da komai ba sai dai na ku Kara samun daukaka, mutuncin ku zai karu, zaku Sami lada a wurin Allah. Akwai fa'idoji da dama masu amfani akan Haka. ..... Abinda na hakake a labari shine Jan labari ba shine ba, matukar sakon da kake son isarwa zai je to a layi biyu ma ya wadatar...... Kadan Mai albarka yafi Mai yawa yuyuyu.
Rubuta batsa, maganganun banza da rashin kunya ga labari ba shine ke kawo wa mutane kwarjini ga labari ba. Ma'anar labarin , tsabtar sa da Kuma kyautata rubutu saboda Allah. Duk abinda muka rubuta zamuyi depending din sa a wurin Allah. Ya Allah kada ka kamamu da laifin da mukayi bisa ga tunanin munyi da kyakkyawar niyya. Allah ka yafe Mana ka shirya Mana zuri'a.
Qalubale ga itaye, ku daina tura yaran ku makaranta ba tare da binciken abinda sukeyi ba, ku ringa Kai masu ziyarar bazata Kuna saka ido ga yaranku musamman mata, mazan ma abin kula ne Yanzu.
Yan Mata ku sani bin namiji ka nuna kana sonshi bance haramun bane Amma ku sani kunya ma cikon Imani ce, duk abinda musulunci yazo dashi muna daukarshi da muhimmanci .
Allah ya sada mu da alkhairi.
Wanda labarin bai mawa ba sai yayi hakuri.
Sai mun hadu a wani sabon labarin bayan sallah idan Allah ya kaimu.
*Zainab wowo*💖
*MAMAN AL'AMYN, AMINATU AND ABDALLAH*a