Showing 78001 words to 81000 words out of 84608 words

Chapter 27 - Wa Zai Furta Book Complete by Zainab Dahiru Wawo.txt

25 Nov 2024

4017

ware muyi magana....
Batayi gardama ba .... Tana shiga daki ta zauna sai tace ...Ina ji.
Bilkisu nasan kina da hankali, nasan kina da ilimin addini, Ina so Dan Allah kiyi hakuri duk da abinda mijin ki yayi ba laifi bane wata kila hakan ya Sanya ki shiga wani Hali.... Sadeeq gaskiya Anwar na mun abinda bana so, da bakin sa ya ce zai ba daddy mamaki abinda ke tayar mun da hankali shine duk ranar da daddy yaji Ina Haka da Shi wallahi bazai taba yarda cewar ba ni na sanar dashi akwai Aure ba.
Ya kasa gane hakan..... Na sani Bilkisu, ya kalli Anwar kallon da ke nuna ```kaga abinda nake Gaya maka ko```...... Yaci gaba da cewa, kiyi hakuri ya mun alkawarin bazai Kuma ba..... Baya iyawa, na Fara planning kawai Zan koma gida ne sai ya mun transfer kamar yarda ya..... Ya fizge wayar.... Billahil azim bazan Kara ba kiyi hakuri Bilkisu.
Tayi shiru Jin shine ya karbi wayar.... Yaci gaba da magana.... Wallahi nayi hakan don ki saki jiki dani ba Wai..... Shikenan ya wuce.
Yayi murmushi, na gode Dan Allah kizo lecture two kinji ko?
Shikenan. Ta fada.
Thank you...... Ta ajiye wayar kawai ba tare da ta karasa ji ba.
Ya kalli sadeeq Yana dariya yace, ta kasa Yi mun fada .... Murmushi kawai yayi ya barshi wurin ya koma gun Anas.......
Gaban ya Fadi ganin dalleliyar mota ajiye kirar Toyoto 2019 Fara.
Ita da Maryam suka fita, kamshi kawai ke tashi a motar .... Me yasa baku fadan ya kawo motar ba?...... Sadeeq yace muyi shiru Kar mu fada.
Ta ce hmmm kawai.
....... An kafsa fadan ne ko?
Murmushi kawai tayi cikin nikaf Mai sauti..... Daga nesa ya hango motar ya saki ajiyar zuciya ya shiga class Yana jiran isowarta.
Har ta zauna bata lura dashi ba wurin taga tsaye sai bayan da tagan Shi tsaye kusa da ita..... Matsa na zauna. Ya fada a dake!
Ta matsa Yana Zama ta ce.... Ina wuni.
........ Keni ba lafiya ba. Ya hau masifa, idan na Miki laifi I prefer ki mun duk tsiwar da Kika iya da fada amma bazan iya daukar this type of your punishment ba...haba. kwana uku? You switched off your phone, you skipped class, I believe ko zuwa nayi Zaki gudu daki ki kulle Haka akeyi ma miji horo?.... Nidai shikenan.... Ta fada a hankali..... Ba shikenan ba, wallahi idan Kika Kuma kashe wayar ki idan na Miki laifi zakiji ni baibai.... Sai kawai ya bata dariya ta duke tanayi...... Au dariya ma na baki ya balle bottle din rigarsa na sama ji kasusuwa kamar ba hakki na nabi ba?
Shikenan nidai..... Kiban hakuri Dan wallahi kin sani cikin damuwa fa..... Kayi hakuri ta fada tana murmushi cikin nikaf.... Cire nikaf din ya fizgeshi..... Fuskar ta mishi wani fayau, ta Dan dake saboda bata son a gane tana blushing.......... I missed my baby wallahi. Ya fada..... Zai Kara magana malamin ya shigo....
Yana gamawa ya fita ya koma bisa table ya zauna gabanta..... Kunyar ki tayi yawa Bilkisu.
Zaka Fara ko?
To ki kalleni Mana Wai sumke sumken na menene?
Ta danyi murmushi,
........ Jiya sadeeq ya rabawa Yan class din nan twenty thousand each though sun gane kudin daga wurina yake fa..... Kunyi kokari Allah ya Kara arziki Mai albarka, rigunan fa?
Na bayar ayi a kamfanina da ke Paris zasu fi kyau daga can ko kuwa?..... Karaf suka hada ido ya sakar Mata murmushi, ta danyi dariya ta mike ..... Ina zakije?
Ba tafiya zamuyi ba?
No! Ki jira nayo sallah yau muna nan sai dare...... Nima zanje masallaci....ya Dan kalleta Yana Yar dariya me zakiyo masallaci? Kuma Yanzu nayi magana kice zakiji kunya.....Hajiya ki jirani anan Ina dawowa Zan sallami kattin can ko kuwa?......
Dama ai Kai ka damu dasu..... Eh dole su kula dake ...ke din ce bazaki gane ba ya fita Yana kwance agogo.....
Ta bishi da kallo ta zauna ... Watau yasan bani sallah. Kai Anwar case ne...... Hajiya ke bazaki je sallah ba?
Ta sakar Mata murmushi habawa Helen....ai duk kallon ku nakeyi Yan class din Nan Yanzu kowa sai shareni yakeyi kunyi dai dai wallahi ...... Ba Dole ba, kina son Anwar ya sa a kashe mutum ko?.... Kisa Kuma Helen.... Yes ko mace baya so ya zo gurin ki bakiga guards din da suke binki... Mtsew forget about guards zasu hana abota ne?
Hmmm, Bilkisu you won't understand.
Ehe Bilkisu... Tayi kasa da murya is it true you both got married????
Who told you?.... Abeg .
Tayi murmushi yes is true amma ba'ayi bikin ba kawai an daura Aure ne...... Jesus..ta fada da karfi.
Bilkisu ta kyalkyace da dariya.
You are lucky Bilkisu.... Anwar ya bada mamaki..... And he is that young Nigerian billonaire Bushara... Bilkisu ta Kara kyalkyacewa da dariya Helen Zaki kasheni, Bilkisu you are lucky ooo he gave us 20k and our shirts and jacket will come soon free for everyone....... Hango shi sukayi Yana magana da guards ta mike da sauri please tell him I'm your friend too we will keep talking any time Sha.....ta wuce da sauri tana waigen ko ya taho..... Bilkisu ta duke tana kyalkyatar dariya har ya karaso ...... Ke da waye haka?
....... Ta rike ciki Helen..
Yayi murmushi tana Miki hauka ko? Jiya naso kina class din nan kiga hauka ni Dole na fita nabar sadeeq da shirmen su...
Ya figo Jakarta yamcici nasan ba Kya rabo da Malaki.... Ya Ciro short bread biscuit da bounty.
Ka fiye neman magana ta fizge jakar.
Ya harareta pad kike gudun kada na gani Kuma na ganta dai.
Ta danyi dariya kaiiiiiii Allah ya shirya ka.... Tare da ke da zuri'ar mu baki daya...... Ki ce Amin...
Ta danyi murmushi na ce a zuci..... Ya sauko da hannun rigarsa da ya nade yana sanya links ....kin San jiya da daddare kamar Zan kurma ihu?
Ta dan kalleshi ta gefe... Yaci gaba da magana Yana murmushi.... Dana tuna kin kashe waya Kuma saboda ni sai naji kamar inta ihu ana jina a gari..... Ta danyi dariya .. kina yarda kike so ai.
Kayi hakuri ta fada tana murmushi.
...ai Dole in ma banyi ba nine masha wuya.
...... Anwar bana gane Alfa and bitas din ga na econometrics ... Ya danyi murmushi....Kuma basu da wuya fa.
Wannan drivation din ka ganshi.... Ya karbi littafin ya sauko kusa da ita ya Fara rubutu Kinga yanda yake......
A hankali a hankali yakeyi yanda zata gane.... Anwar marshene komai ya hada.
Duk inda ya shige Mata sai da yayi kokari yaga ta gane duk firar ta koma karatu hakan yasa ta saki jiki sosai shima kuma sai yaji dadi ganin ba wani sumke sumke ta saki jiki.
Ana Kiran magrib ya ce muje ki ajiyeni gida zanyi sallah masallacin unguwar mu. ... Shi yaja motar.
Tun daga ranar ya daina zuwa gidanta, abinci shike aikawa ana karbo mishi ko ta tafi dashi suci school, duk firar su a school sukeyi ya dake ya cije baya nuna zalamarsa fili.
Anayin hutu tare suka tafi Abuja Amma bai kwana ba ya koma Kano kwanan sa biyu yabar kasar......
Koda aka koma school bai samu ya dawo ba, topic din sa na project ta email suka ringa communication da supervisor din sa, Bilkisu itama da akayi accepting nata ya ce ta tura mishi Shi ya ringa yo wa Yana turo Mata, ita Kuma da sadeeq suna tura mishi lecture da akayi. Wuni sukeyi video call, ko meeting yakeyi wani lokacin sai ya latsota,
Duk CA din da akayi Shi sai da yazo exam aka mishi,satin sa daya akayi hutu suka tafi da yake course shidda ne...... Abun ya Kara rikicewa saboda hutun sati daya ne, gashi final semester ga daddy yasanya bikin su bayan sun Gama da sati.
Anwar baya zama Nigeria ko kadan, ya Kuma hana su dady fita ko Ina Wai kada ayiwa Bilkisu soyayyar komai.... Shirye shirye ya kankama, sadeeq ma baya zaune.... Koda suka koma makaranta ita kadai ce, lectures sun ragu, course hudu sukeyi kacal, project kuwa Shi ke turo Mata,
Wannan da wuri ya dawo exams saura sati uku, yazo da jackets din su day shirts ko wane da size dinsa, jacket din dark blue da ratsin harsh anyi tambarin fudma ( logo ), kowa da sunan sa bayan rigar, sai white shirt ta yin signing da wando dark blue.
A bayan rigarsa an rubuta *Bushara* Bilkisu Kuma *Mrs Bushara* ya siyo Mata Tommy skirt dark blue Mai wasu irin flowers rose dark blue a jiki kana iya taba ko wace flower ya hadu iyakar haduwa..... Bai Bata ba sai ranar last paper yace ta saka da gyale ya yafe ..... Ga takalmi hills tayi kyau matuka..... Yazo da ledoji na i.v din su ko wace Leda da ticket da gate pass na tafiya bikin.... A ka dauko kattin speakers suna gamawa aka Fara ihu da kidi..... Bilkisu na fitowa Yana tsaye ya ware hannu ta rugo da gudu ta fada aka dau ihu...... Sun birge kowa, ya bude Mata gaban rigarsa ta rubuta *Mrs Bushara* shima ya rubuta Mata *Anwar* a tata sannan ya duka aka yi ta mishi rubutu.... Ita kuwa Mata kawai yace su rubuta kada shegen da ya taba mishi Mata .... Akayi ta dariya...
Nan aka Fara watsin lemuka, ana hotuna..... Anwar na makale da Bilkisu ya Fara watsin dollars.... Makaranta ta rude aka Fara wawaso..... Kawai ya hango mufeeda can ana niyyar danneta wurin kwasar kudi ya zunguri Bilkisu ya nuna Mata Yana murmushi.....ta karbi sauran dake hannun sa ta karasa kawai sai dai mufeeda taga an sunno Mata dumshin kudi...ta dago da sauri tana ganin Bilkisu sai kawai ta riketa tare da sakin kuka...... Duk ta ji tausayin ta. Mufeeda daina kuka Mana... Ta Mika Mata kudin kawai ta juya....
Bata ga Anwar ba, sai ta hangoshi can shida Suleiman Yana sunna mishi wani abu da alama kudi ne baya son kowa ya gani.... Tayi murmushi Bata karasa inda yake ba...... Yana murmushi yayi godiya. Amma ban fadawa mutuniyar ka tare zamu tafi ba .... Au haba.
Allah kuwa. Na ce Mata kawai zamu tafi da wasu Abuja yau saboda Shirin biki sauran tunda akwai ticket sa taho..... Ai kunyi kokari Allah yasa albarka da zuri'a dayyiba..... Amin Suleiman. Sai ku shiga mota idan sun karaso bana son muyi dare kasan rigimar Bilkisu..... Duk sukayi dariya. Jaka ta na daki ta Kaya...... Kayiwa murtala magana ya tafin maka da ita kawai can akwai kayanku..... Ya wuce yabarshi gurin ya nufi inda Bilkisu take.
Motocin sa suka shigo a guje school din... Bushara 1, Bushara 2........ Bushara 10.
Nan wuri ya Kara rikicewa....... Shi da Bilkisu mota daya, sadeeq da Anas mota daya, Suleiman da Ahmad motar su guda......... Suka fice garin duk sun bar mutane da magana a Baki........ Abuja tayi dauka Kuma za'a Fara Shirin shagulgulan biki........


*ZAINAB WOWO MAMAN ABDALLAH*πŸ’–πŸ’–πŸ’–.




*ALLAHUMMA LAA SAHLAN ILLA MAA JA'ALTAHU SAHLAN WA'ANTA TAJ'ALUL HAXNA IZAAHHH SHI'ITA SAHLAN...."* MU ringa karantawa saboda wannan an🀐 *WA ZAI FURTA?*🀐
2⃣9⃣


*Tukuici ne ga Aunty Rabi ( Hajia Rabi badawi Kano maman Ibrahim ), Allah ya Kara arziki ya shirya Miki zuri'a ya Kara Miki tsawon kwana. Amin.*




*KINA RAINA MAMAN WEEDAD*


*Domin ki...... beloved sister Khadija Dahiru wowo miji na gari I pray*


πŸ‘‰πŸΌπŸ’žπŸ’•πŸ’• *RUKAYYA BAKO DAN BATTA I love you so much, remember this always*πŸ₯°πŸ˜πŸ˜˜.


******************
*ABUJA NIGERIA*
Suna Isa daddy ya ce maza Anwar yazo Yana son ganin sa.....
Su biyu a falo daddy bisa kujera Shi Yana zaune a kasa, yayi yayi ya hau kujera amma ya ce hakan yayi..... Ba karamin dadi yakeji ba irin Respect da kunyar Anwar din duk rawar kansa idan Yana gaban daddy bai iya ko kwakkwaran motsi..
... Abinda yasa na kiraka anan Ina son mu tattauna wasu maganganu, na farko akan kayan dakin bilkiyne, Anwar bisa ga Al'ada irin tamu ta hausawa kasan cewa duk diya da Kuma iyayenta suna son suga abinda suka saka ma yarta a gidan auren ta Amma Kai kace sammm baka da bukata, shine muka yi shawara zamu tura maka kudi a madadin kayan...
Na biyu, ta fada mun ka ce lefenta sai taje gidan ka, wannan tsari ya Mana dadi matuka....
Na karshe kuwa da zance shine, programs din da zakuyi tayi yawa ka mayar dashi party daya kwal! Kuyi Shi a jibi don in shaa Allah Ranar juma'a Zan dauketa da kaina in kaita daki bana son duk wadannan bidi'o'in.... Ya dago Kai da sauri ya kalli dadyn suna hada ido ya sunkuyar da sauri.... Yayi Yar dariya Kano zaka ajiyeta ko nan sannan ka hadani da mutum daya Wanda zai mun jagora don juma'ar bacin Kai da na fadawa mahaifiyar ta kadai tasan wannan tsarin nawa.
Ya Kara kasa da Kai yace toh.... A Kano zamu Fara Zama in shaa Allah.
.......madallah. Ina ga shikenan kana iya tafiya.
Ya Dan sosai keya Yana son magana Yana Jin nauyi...... Yaya akwai wata magana ne Anwar?
Ya danyi murmushi.... Ranar juma'a din da karfe nawa?....... Ka turon Wanda zai mun jagora gobe don in shaa Allah anan zanyi sallar juma'a bayan na dawo kaita....... Ya dankara kasa da Kai tare da zaro ido..
Ya rusuna Allah ya Kara girma mun gode....ya Mike.
Ya kalleshi account number zaka bayar kenan?
Ya danyi murmushi ya koma ya zukunna, ayi mun aikin gafara daddy bazan karbi kudi ba, amma idan ko hankali bazai Sami natsuwa Kan hakan ba, to a turawa Bilkisu tunda daman ko kayan akayi mallakin ta ne fatana a Sanya Mana albarka a ciki addu'ar kadai ce zata fi duk wani kayan masarufi ko kudin quality...... Daddy ya kura mishi ido Yana jinjina tunani da hankali irin na Anwar.
Yana tafiya suka Fara shirye shiryen hada party don cewar Anwar sai fa anyi.
Abokan sa na kasashen waje duk sun iso masu kudin Nigeria kuwa abokan huldar sa wurin kasuwa kawai ake jonewa Amma duk wani sha'ani na yarinta da 'ya'yan su Anwar keyi sune abokan.....Amma wannan bikin sun Alkawarin halartar partyn da za ayi a national conference Hall dake presidency a cikin Villa.
An kayata wurin mawaka duk sun hallara hada yaron nan matashi Dan katsina Mai tashe Yanzu watau *Aliyu nata ( Aure martaba )*
Iyaye da abokan arziki sun hallara wurin, dangi da duk wani Mai alaka da bikin kowa ya kure adaka.....
An tsantsara ma Amarya kwalliya suna saman bene za a shirya ta aka shigo da wata matsiyacitar *Gown* maroon color *Innalillahi* bana iya describing rigar saboda rigace akalla idan zuwa zakayi shago ka siyo zata haura millions, duwatsun jikin rigar kansu diamond ne, musamman aka mishi ita special da wasu laces da materials Wanda ya ware don party kawai Amma Yanzu daya zata saka.....
Kilibabbu magulmata wadanda ba a rasa irin su a kowane dangi Baki yayi gummm, saboda suna ta korafin duk kudin Bushara bikin sa ba lefe...... sunfi awa shida wasu abokansa a waje cikin motoci suna jiran fitowar Amarya bayan shiga da rigar saboda ganin rigar yasa dole aka canza pattern na kwalliyar.
Tunda ta Fara saukowa ake daukarta hoto, gidan ya rikice,Yan sanda da sojoji gewaye da ita sunki yarda ma a rabeta...... Su mommy da kawayenta na babban falo ana fama da ita Kan zuwa wannan party Amma tace sammm baza ta je ba.
Suna hango fitowar su ya fito mota dasauri...... Ya Sha farar shadda ta karshen karshe Yana isa duk aka dare kawai ya rungume ta.....wuri ya dauki ihu kanka yane cikin gyale sai da suka shiga mota ya daga Shi ya leka....... Ya tallabo fuskar...... tsarki ya tabbata ga mahaliccin Bilkisu..... Ya Kai bakin sa ga nata tayi saurin fadawa jikin sa ta na murmushi..... Ya danyi dariya.... Ke wallahi dadi na dake Yar garin mu ce, ya dagota ba da yawa zanyi ba please......ta Kara komawa jikinsa..... Ya kyalkyace da dariya kaiii Ni Kuma tawa ta sameni daga ni kada ki batan Kaya da Jan Baki toh, nasan karamin aikin ki ne...... Yayi juyin duniya taki yarda ta dago don tasan halin sa tunda yace zaiyi kissing dinta sai fa yayi.....
Ya Kama dariya ya rungume a sosai, ga son jiki ga Kuma tsoro sai a daga ni tunda ba'a son tukuici.
Yana shafa bayanta Yana magana a hankali wallahi nasan rigarnan dole ta Miki kyau. Tunda wasu suka ji labarinta an Fara damuna..... Ya dago ta da karfi Kuma sarkar nan ta hau kayan ko?
Sosai, ta fada tana murmushi.... Wuf! Yakai bakin sa ga nata sai kawai ta tafi jikin sit luuuuu tayi baya.......
Tsayuwar motar yasa Shi sakinta a hankali, tayi kasa da Kai ya danyi dariya na shanye Jan baki ya kura Mata ido ta sunne Kai kawai....... Ya shafi gefen fuskar ta Yana murmushi *shy girl*
Wuri ya dauku, Shi kansa bai taba tunanin ganin wasu mutanen ba Amma sun mishi surprise.
Rike yake da hannunta suna tafiya a hankali Kota Ina Yan daukar hoto ne, abokan su na bakin kofa suna jiran isowar su.
Kawayen Bilkisu sun Sha Anko na light pink lace da blue head sun hadu sun Gama haduwa abinda ga fresh and young graduates.
Daga ciki wani sound na kidi ya Fara tashi kawai Anwar yaga Yan matan nan sun Fara rawa iri daya Nan da Nan wuri ya dauki ihu da sowa...... Rawa sukeyi ta birgewa Anwar nata dariya ya tallabo kugun Bilkisu ya Dan duka ya Mata rada hada chorography kuka hada haka?
Tayi murmushi kawai. Rawar sukeyi sosai har suka raka su mazauni Anwar na Zama ya janyo Bilkisu ta fada bisa cinyarsa lokacin da take kokarin Zama wurin ya Kara rikicewa......
Yan matan suka ja layi tare da canza salon rawa hall din yayi tsit kidan kawai ke tashi an masu kuri da ido ba Wanda ke son ko kiftawa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login