Showing 75001 words to 78000 words out of 84608 words

Chapter 26 - Wa Zai Furta Book Complete by Zainab Dahiru Wawo.txt

25 Nov 2024

4007

sit din da ya taso.... Basai ka fizge ba two ce kai nasan nine kaci don ma baya bada cikon da tabbas ten zaka ci....... Inji waye ya fada Yana murmushi....ta zumburo Baki nidai fiddo naga Ni...... Ya Mika Mata Yana murmushi.... Kamar jira ake taje hannun Bilkisu aka Fara rokonta ta bada ayi snapping.... Ta Mika musu.
Mutumen can na daga mun hankali bana kaunar Dan iska.... Yayi dariya Kuma duk da Haka Baki taba faduwa course dinsa ba ko?
Ta harareshi Amma da yake akwai nikaf bai gani ba tace da hawan jini, da na ruwa ko?,ya kyalkyace da dariya, toh eh Mana,duk sai ya gama tayar Mana da hankali tukun Kuma *E* din nan dai ce ko *D* ..... Ina laifi ai yafi carry over ko?...... Zatayi magana malamin ya shigo..... Ya fiddo waya ya dan Mata magana a hankali..... Shiga WhatsApp...
```kinyi barci jiya?```


Ta maida mishi da ```me zai hana?```


```ni kuwa kasawa nayi saboda tunanin ki```
Ta kasa cewa komai


```kinji```
Ta ce ```Hmmm```


```smiles kin zo mun da tuwon?```


```yana mota```


```ina zamuje naci```?

```ina fa, anan waje ko?```


```Bana son waje is too open let's go to the field or new lecture rooms side I need quite place okay?```


Tayi shiru.


``` kinji ko?```


Ta maida hankali gun lecture.... Ya zunguro ta da hannu ....dole ta rubuta mishi


```naji```


Yayi murmushi.


``` sai Anja mun aji?```


```Ka bar mu muji lecture Anwar```


.....```ke ni ban wani ganewa ki Bari kawai zamuyi tutorial```


```Hmmm```
Malamin na lura dasu,
Yana gamawa ya ce tear a sheet of paper write your number only......


*Mun shiga uku ka ga abinda nake gudu ko?*
Ya sumke Yana Mata dariya.


Kina da black biro?.....
Banda Shi ta fada cikin tsiwa.
To kiyi sauri ki wanka ko na rubuta miki,?
Kawai kayi na kwafa idan Kuma ya tayar Dani shikenan.....
Yayi murmushi....
Ya Fara dictating questions based on what he discussed.
Ta Kara tsure Mata tana magana kasa kasa ... Wallahi kana ja mun wannan semester din..... Yayi shiru Yana murmushi Yana rubutu.
Tana kokarin Jan layi ya turo Mata takarda har ya Gama Daman two questions ne. Ya ci gaba da rubuta nashi Yana layin karshe kawai malamin ya ce hands up...... Amma sai da ya karasa Kai Anwar karshe ne......ta galla mishi harara cewa zakayi kasan abinda ka taka, yayi dariya to meye acikin nan cubweb theory din ke da wahala?


Ta ce hmm, duk ya Gama birgeta, gunguni kawai ke tashi cikin ajin.
Yana zuwa layin ya karba ya dan harari Anwar din ya wuce ....
Yana fita sadeeq ya taso kaga mutumen Nan ko?
Yayi murmushi bana fada ma ba, gaskiya naji dadin bayanin jiya... Ta kalleshi da sauri au Daman kunyi wannan din?
Sadeeq ya ce wallahi jiya kamar wasa ya koyan Kinga da yau naci kaniya ta...... Ta ce hmmm kawai,
Anwar ya kalleta kema yau zamu Fara karatu kiyi hakuri..... Na fito karfe hudu kenan?
A'a ki Bari sai after Isha zanzo gidan....
Gabanta ya Fadi, na marecen nake ga zaifi ko kuwa?
No!, Bana son yawan fita inba lecture akeyi ba, kawai ki jira zanzo kinji ko?
Toh, ta ce a hankali.
Ya Mike muje....
Ka Kira sadeeq muje yaci..... Zan rage mishi ..
Anwar meye Haka? Wasa tare ci banban.... Ya danyi dariya yarinya kawai kice kina son wani kusa kada muje na cinyeki Ni kadai.... Laaaa ni ba Haka nake nufi ba..... Sadeeq!!! Ya kwala mishi Kira....
Ya karaso Yana murmushi ya akayi?
Tuwo aka kawon Wai bazan ci ni kadai ba sai tare da Kai... Yawwa Bilkisu Allah dai ya biya kin San kuwa yunwa nakeji wallahi.... Ya banka mishi harara Kuma Kai baka wuce tayi ko?
Ban wucewa kin ganshi Nan ko ruwan zafi bai iya dafawa .... Duk suka kwashe da dariya.
Ina zamuci tuwon?
Field... Anwar ya bashi amsa.
Okay kuyi gaba Zan biyo ku da mashin.
Ungo nidai kaja motar Dan Allah..... Ya wurga mata harara ya fada gaba ya zauna kawai.
Dole ta shiga ta ja motar a hankali.... Duk inda suka gitta sai an bisu da kallo.. ba karamin kashe zuciyoyi sukeyi ba a school din suna bada *Plus*
Sadeeq na gama ci yabar wurin yace zaije aski.
....me Zaki dafa mun da dare?
Abinda kake so, ta fada..... Ke daga nikaf din nan na ringa ganin idonki.... Ya karasa maganar Yana yakice Shi .... Ta yi kasa da Kai tana murmushi..... Ya shafa gefen fuskar ta Yana fadin ```lemme see this baby face``` ... Ta to dariya ta ce kaiiiiiii.....
Yes, ya fada Yana Kara kallonta,
Me Zaki dafan?
Abinda kake so, ta Kara maimaitawa.
Kiyi mun chips mana.
Toh, ta fada a hankali.
Babban fridge din nan Kinga akwai kaji da naman rago da kawuna ko?
Um, ta ce.
Idan kina bukatar kifi kiyi mun magana a kawo Miki Shi kinsan baya da dadin ajiya saboda karni ko?
Gaskiya fa.
Me yasa baki taba rokona wani Abu ba?
Ta kyalkyace da dariya kaiii Anwar... Yabi fuskar da kallo..... Yana murmushi.
```Bilkisu kin San cewa ke din ta daban ce kuwa?```
Na sani Mana... Ta fada tana murmushi.
Ya akayi kika sani.....
Tayi dariya saboda *Bushara na Sona*..... Ya kyalkyace da dariya for the first time kin kirani *Bushara* Dole na Miki kyauta yau Zan canza Miki motar Nan...... Dan Allah ka barta Ina sonta....... Karki damu ai ba rokona kikai ba, Ina son ki bar tarihi FUDMA a ringa kwatancen mu..
.. Yanzu ma anayi.
In tambayeki???
Ta ce um,
Yaushe Kika Fara Jin kina Sona?
Ta yi kasa da Kai tana dariya.....
Kunya kike ji?
Ta Kara murmusawa..... Okay rubuta mun ta WhatsApp..... Ka Bari Zan fada maka..... Yaushe?.
Tayi shiru tana murmushi.
Kunyar ki tayi yawa Bilkisu....
Muje ki ajiyeni gida .
Ta tayar da mota,
Har ciki ta shiga yau, ya ki fita ya tsareta da ido sai kuma ya ce affff.... Ki jirani Ina zuwa please ya shiga gidan da gudu.....
Ta bishi da kallo tare da sakin ajiyar zuciya a hankali....
Ya dawo dauke da Yar leda Mai kyau a hannunsa, ya leko ta taga, it might be Baki zo da English wears ba ko?
Kisa wannan anjima.... Ta zaro ido...
Ya Kara sunkuyawa ba abinda Zan Miki Allah kuwa kawai Ina son ganinki cikin su matsala daya za a Samu idan kika Fara wannan kunyar taki lallai Zaki janyo ma kanki na taba ki.... Ban Baki a boye ba, just wear it and feel free okay????
Ta daga Kai a hankali.... Yayi murmushi that's my babe...... Tayi baya da motar ta fita a hankali duk jikinta yayi sanyi duk da bata ga kalar kayan ba.....
Yabi motar Yana murmushi... Ya ce tsoron ta yayi yawa gaskiya. Ya zuki iska ya fesar ya wuce ciki.
Ta zabga uban tagumi daki ita kadai ta zuba ma kayan ido, doguwar riga ce Mai kame jiki da hannun vest, daga kasa akwai tsaga har kusan guywa maroon ce Dana da wani katon belt bisa kugu, da jefi jefin flowers jikin rigar red. Aisha ta taimaka Mata sukayi farfesun kaji, sannan suka soya chips din kaskon karshe ta shiga tayo wanka tabar Aisha ta karasa ta feshe jikin ta da turaruka masu kamshi ta gyara gashinta Amma ta mishi gammo ta nade tare da zumbula katuwar hijab.... Tana fitowa taci karo da Aisha bakin kofa zata shigo ....Wai duk meye kikeyi haka ga Anwar can yazo.... Gabanta ya bada ras!.... Shida sadeeq ne?
A'a Shi kadai ne gaskiya... Kin saka ma coconut juice din ice ?
Eh Yana fridge muje na Kama Miki.... Barshi baya son haka, ta katse ta.
Yana zaune kasa ya Mike kafa Yana ta latsa waya sanye da farin boyel Mai laushi kansa ba hula.
Ta ajiye plate din chips din da cooler farfesun ta ce ... Ina wuni?
Ya Dan dago sai Shan kamshi yakeyi ya ce ... Bilkisu ya kike?... Na Sanya ki aiki ko?
Ba komi, ta fada tare da mikewa... Ya bita da kallo duk kamshin turarenta ya kashe Masa jiki.
Ta dawo da sauran kayan ta zuzzuba mishi Yana satar kallonta da wutsiyar ido, da tazo dagowa sai ya basar.
Tana gamawa ya tura Mata Wanda ta zuba mishi ya janyo sauran da ke cooler gaban Shi ya ce wallahi sai kin cinye duka Koda zakiyi amai.... Ta dago Kai da sauri ,.. ya hade girar sama da kasa yasha mur ...
Dole ta dage ta Fara ci sai da tafi Rabi yaga da gaske turawa takeyi sannan ya ce mikon dankalin na Kara bai isheni ba.... Ta tura mishi da sauri ya cinye... PeppΓ© soup din Nan yayi dadi fa.
Jeki Kai kayan kizo da books din da zamuyi ba dadewa zanyi ba.....
Ta mike da sauri ya bita da kallo sai kawai yayi dariya.... Tana dawowa ya Kara hade fuska.... Kina jira na ce ki cire hijab din????
A hankali tayi sama da ita.... Tsikar jikinsa ta bada Yarrrr, ya hadiye wani tsinkakken miyau sai kawai yayi kasa da Kai ya Fara budo littafin da ta Miko....
Tunda ya Fara bayani bai dago ba ..... Tun tana Jin kunya da tsoro har ta fahimci Sam ba ta ita yake ba gashi sai wani Shan mur yakeyi.....
Tana ganewa sama sama har sukayi course biyu.
Duk ta makure... Ya dago Kai kina ganewa kuwa?
Um, ta ce da sauri, saura kadan yayi dariya.
Yau barci nayi da Rana sosai...
Wai kin San cewa an gano nine Bushara school din Nan?
Ta danyi murmushi, nasan za a gane Kam...
Saboda me Kika ce haka?
To Anwar ko wadannan kattin da ke Bina da wadanda ke gidanka yaci asan Kai waye.... Ya danyi dariya inji waye kawai tsabar sa ido ne.
Naji class din mu za a yi jacket da shirt na graduation Ina ga ni Zan dauki dawainiya ko?
Ya dai kamata. Ta fada kanta kasa.
Yayi murmushi, Nima Ina son yiwa yaran Nan alheri me kike ga Zan raba musu?
Kudi, ta fada.
Kudi Kuma?
Eh, Mana kudi zaifi saboda kowa yasan meye damuwan sa Kuma kudi ke maganin komai ko kuwa?
Kuma fa, Shi yasa nake sonki wallahi saboda kina da hankali...kamar nawa Zan basu?
Yanda kayi niyya Kuma ai kafi kowa sanin iya karfin ka.
Ya kura Mata ido, ki fada mun Mana ai Yanzu shawara mukeyi nida ke ko?
Ka dai kiyasta Ni ban San nawa zance ba ko kayi shawara da sadeeq..... Da ke zanyi. Nawa kike ga ya Dace na raba masu?.
Tayi shiru... Ka Bari zanyi tunani toh.
Okay, sai na jiki tashi ki karon ruwan in Sha... Ta Mike ya bita da ido, kafin tazo kawai ya Mike kamar Mai neman wani abu,
Tana kokarin Miko mishi ya mameta ya kamo sai kawai taji ya hada bakin sa da nata, ta saki ruwan kasa..........βœπŸΌπŸ˜„πŸ™ˆ


*Zainab wowo mamar Abdallah*πŸ’–


*Mz , mz, mz Ina nufin ( salamatu Dahiru ) Allah ya Kara zumunci mother kina Raina koda yaushe.*




*ALLAH YABARKI DA ALHAJI NURA NA'IMA AMADU SPEAKER YAN ADAWA BAKU IYAWA MUNE AMARYA KUMA UWARGIDA MUTU KA RABA IN SHAA ALLAH*πŸ’žπŸ’žπŸ’ž






*Yauma page daya za'a samu Ina busy*🀐 *WA ZAI FURTA?*🀐
2⃣8⃣


*Tukuici ne ga Aunty Rabi ( Hajia Rabi badawi Kano mam in huhan Ibrahim ), Allah ya Kara arziki ya shirya Miki zuri'a ya Kara Miki tsawon kwana. Amin.*




*KINA RAINA MAMAN WEEDAD*


*Domin ki...... beloved sister Khadija Dahiru wowo miji na gari I pray*


πŸ‘‰πŸΌπŸ’žπŸ’•πŸ’• *RUKAYYA BAKO DAN BATTA I love you so much, remember this always*πŸ₯°πŸ˜πŸ˜˜.


```Bazan taba mantawa da ke ba Maryam Aliyu Yar adu'a ( M. Ali ) uwar Noor my in-law kina Raina Koda yaushe```


πŸ‘‰πŸΌπŸ’• *Mz ( salamatu Dahiru ) Ina Kara godiya Allah ya Kara dalili my mother*


*****************
*Federal University dutsinma*


....... Tun tana iya motsawa har jikinta ya mutu murus, duk illahirin kafafuwanta rawa sukeyi suna neman gagara daukarta, Jin tayi lakwas yasa Shi juyawa da ita ya zauna bisa kujera ita Kuma tana bisa kafafun sa..... Yayi iya gumin sa ya taba inda yake so, karkarwa jikinta kawai keyi duk ta firgita..... Ya saki ajiyar zuciya ya janye bakin sa a hankali..... Sai kawai ta tusa kanta cikin kirjinsa ta saki kuka... Yayi shiruuuu...
Zuciyar sa na mishi sake sake, shin ya biya bukatar sa ko ya ba dady mamaki?
Da ya motsa sai ta rikeshi gamm ta Kara sakin kuka.... A hankali yake fitar da numfashi.... Sai kawai ta bashi tausayi lallai ya Kara tabbatar wa kansa da Bilkisu yarinya ce karama.... Tunda har ta kasa supporting kiss kuma hakan ya bashi tabbacin this is her first kiss.....
Tayi Mai isarta, har lokacin jikin ta rawa yakeyi..... Da ya motsa sai ta Kara rikeshi.... Ya danyi dariya.. ``` To ki sakeni na tashi ko?```
Tayi shiru,


```Bilkisu```


Ya Kira sunan ta a hankali,


.... Ta Kara fashewa da kuka ``` Dan Allah kayi hakuri```
..... Ya Kara dariya naji sakeni Dan Allah ai ba Kya so ko?
Ta daga Kai cikin jikin sa...
Okay Zan tashi na tafi sakeni....
Ta Dan sakeshi.... Yana motsawa ta koma da sauri .... Ya kyalkyace da dariya da ya gane ba tsoro kadai ke addabar ta ba hada kunya..... Ni Kuma yau tawa ta sameni ni *Hamza*...... Bazaki sakeni ba? To gyara mu yi kwanciyar mu anan.... Ta sakeshi da sauri tare da soke kai cikin kujera..... Ya Kara dariya.... Ba rakiya kenan?
Tayi shiru..... Ya kawo hannu ya taba ta, saki kuka tare da kankame jiki..... Ya Kara dariya ya ce tohm na siyo ma kaina rigima da kudina..... Ya zukunna gaban ta, Shikenan daina kukan Zan tafi Amma Dan Allah ki dauki waya idan na Kira matukar bakya son na maimaita kinji ko?...... Saura kadan ta wawuro fuskarsa ta cije don takaicin kalmar ```kinji ko```.
Ya saki ajiyar zuciya ya mike sai da safe I will miss you honestly..... Ya fita da sauri.
Tafi mintuna ashirin a wurin kafin ta tashi zaune.... Ta Dora hannu a Kai *Na shiga uku ni Bilkisu idan Haka ne halin Anwar na gama banuwa* Shi baya da kunya?
Ashe abinda nake karantawa da abinda malaman islamiya ke fada gaskiya ne?
Ta Mike jiri ya kwasheta, ta koma ta zauna.... Ikon Allah, ta kalli hannuwanta sai kakkarwa sukeyi, tsikar jikinta tashi Yarrrr tana tuno abubuwan da suka faru... Namiji???? Shi har wata dariya yakeyi... Ta zumburo baki tare da zabga uban tagumi.
Yana shiga sadeeq yaji kamshin turarensa ya canja gashi cikin wani yanayi na nishadi .... Ya bishi da kallo kawai Shi Kuma ya fada toilet ya sakar ma kansa shawa.......
Duk su Aisha sun shige sun kwanta, ta shige dakin itama Kai tsaye kewayen ta fada......
Ta na rungume da qur'ani kiransa ya shigo..... Taji wani dammmmm a kirji.
Ta dauka Amma samm ta kasa magana....
Kinyi wanka?
Tambayar ta bata haushi ta mishi banza.... Kinji?
Um, ta ce a hankali.
Kin kwanta ne Yanzu?
Tayi shiru......
Ya ce kinji?
Ta ce um,
Yayi murmushi, Baki ya mutu ne?
Tayi shiru.......
Ya ce huh?
Da kyar ta ce hmmm.
Ya danyi dariya.
Thank you so much Bilkisu, wallahi naji dadi sosai Zaki Sami Lada Mai tarin yawa kin San Haka?
Tayi shiru...kanta sunkuye kamar Yana kallonta wayar ma kunya take Bata.
Ya Kara dariya Wai Baki magana?... Ko muyi video call........ Nidai a'a..... Ya tuntsure da dariya to kiyi magana inji, kiss kawai ya rikitaki haka Ina ga..... Zan kwanta Dan Allah..... Ta fada kamar zatayi kuka ya kyalkyace da dariya..... Shikenan sleep tight sweetie.... Ta latse wayar da sauri kirjinta na bugawa ..... Ai shikenan Ni Kuma tawa ta sameni ta fada a hankali.
Ta Dade barci bai dauketa ba har kusan karfe uku da Rabi..... Shi yasa ta rasa lecture karfe bakwai don Bata tashi ba sai Tara saura.
....... Sadeeq ya kalleshi ya Bilkisu bata zo lecture ba?..... Ya danyi dariya kawai...
Ya bishi da kallon tuhuma.... Me ka Mata?.... Ya daga hannuwa yana dariya wallahi ban Mata komai ba kawai kiss ne ....... Ai nasan baka iya ba daddy mamaki Anwar Kuma yasan abinda ka je ya dawo Kan yarsa akanka yasa ya yanke wannan hukuncin...... Allah Ina iyawa.... Me yasa ka taba ta toh?
Ya galla mishi harara halan ni katako ne da Zan tsaya da Aure Ina kallon matata haka zikau ai ko Dan romance din a daga mun kafa ko?
.... Sanya ma Rai koshi ke kawo yunwa Anwar a haka, ahaka zaka je inda baka son zuwa Dan Allah Ina baka shawara ka tausaya ma yarinyar nan ka Bari akai maka ita...... Kuma duk ta tsorata jiya kaga yanda jikinta ke Bari?
Ai dole ta tsorata, bacin islamiya da sai ince anya tasan me ake ce ma Aure saboda yanayin yarinyar na bani mamaki...... Wallahi yarinya ce sadeeq nayi mamaki jiya ta kasa daukar kiss...... Mtseww ai ka yi sauri...


Shin Zan kiyaye ai dai na Dana.... Ya mishi gwalo... Ai Kuma ka Dano ma kanka ko? don na tabbatar Yanzu ka siyo rigima da kudin ka..... Wallahi
kuwa, ko agabanta na fada jiya..... Amma fa na kashe bakin rigima Zan Sami sauki saboda ta tsorata da Ni...... Ya ce hmm.
Yaki zuwa gidan ranar ta kashe wayar ta...
Ta ce ma su Aisha zatayi karatu ne daki Koda sun jita shiru.
Kwana daya , biyu har uku Bata shiga school ba. Taki kunna waya kuma.
Hankalin sa ya Fara tashi, ya Sami sadeeq ya fada mishi suna tare da Anas ya Dan kebe shi.
... Yarinyar nan fa taki kunna waya kaga kuma Bata zuwa class.. nasan za a rina Anwar ai ka Mata shigar kutse da ka bari da Yan dabaru da hikima sai ka shawo kanta amma Haka zikau ai Dole ta firgita..... Ya kamata ka fahimceni ya zaka biye Mata ka dauki taking side.... Ya fada a hasale... Na sani amma Ina kwatanta maka ne...... Naji nidai kaje ka lallasar mun ita don Allah Kuma in shaa Allah bazan Kuma ba tell her this please.
Shikenan....amma Zan Fara magana da ita ta waya tukun..... Kana da wani layin nata bayan Wanda ta rufe?
Through Aisha...... Okkkay.
Yayi sa'a kuwa suna tare zasu ci abinci...... Ungo sadeeq na magana ta Mika Mata wayar ......bayan sun gama gaisawa ya danyi kasa da murya Anwar din na tsaye sun Sanya handsfree..... Idan babu damuwa ki Dan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login