Showing 6001 words to 9000 words out of 15008 words
sumar kanta tace:
“Layla... Nashwan zai turo iyayensa — amma ba yanzu ba, sai shekara mai zuwa.”
Layla ta zaro ido, ta rike hannunta cike da sha’awa da farin ciki:
“Shekara mai zuwa?! Subhanallah, ke wallahi wannan albishir ne! me kika ce masa?”
“Na ce zan jira shi duk da lokacin yana da nisa, amma kalmarsa ta daɗe da natsuwar sa sun saka na yarda. Soyayyarsa ta fi ni’imtar zuciyata.”
Layla ta fashe da dariya tana girgiza kai:
“Ke dai kina cikin naki duniya Amatu, Allah ya tabbatar da alkhairi. Wallahi Nashwan yana da kirki. Amma dan Allah... wato bazai yi tun da wuri ba kenan?”
Amatu ta nisa “Yace yana gyara wasu abubuwa ne. Na fahimta kuma na yarda. Na fi son abu ya zo da tsari da cikar mutunci fiye da sauri ba tare da shiri ba.”
Layla ta jinjina kai, tana murmushi:
“Toh ai Allah ya sanya alkhairi. Amma sai ki shirya kyau-kyau da addu’a. Zaman jira yana buƙatar haƙuri da jajircewa.”
“Na shirya,” Amatu ta amsa a hankali, “In har zan samu Nashwan a ƙarshen jirana — to na yarda da komai.”
Suka ci gaba da hira cikin nutsuwa da kwanciyar rai. Soyayya ta gaske ke kera zuciyar Amatu, tana girgiza tunaninta da fatan gobe. Kuma da ƙawarta Layla a gefenta, sai ta ji kamar rayuwar ta na gyarowa cikin salo mai tsafta da albarka...
SHIN WANAN JIRAR NA AMATULLAH ZAI HAIFAR DA ƊA MAI IDO
SHIN NASHWAN ZAI CIKA ALƘAWARIN SA.
LALLAI NASHWAN SHINE ZAƁIN ZUCIYA AMATULLAH
MUCEE GABA DA KASANTUWA ANA MIN UZURI DA RASHIN ISASSHEN POSTING A KOYAUSHE FATAN ALHERI 🥳🎊
https://chat.whatsapp.com/Iw0DqQGrB3UJg7MK20pgRC
💘 ZAƁIN ZUCIYA💔
THE HEART'S CHOICE
BY
NARNAH ƘANWAR SOJA
🎉 Happy Birthday to Me
July Girl Special 🎂✨
Na sadaukar da wanan littafin wa karan kaina kasancewar sa a watan haihuwa ta July..
Welcome to this journey... of love, of longing, of silence that speaks louder than words.
Let the novel begin... with a heartbeat. 💔💌
Love , Sad × Long-Distance × Hopeful * short story
DIAMOND 💎 GLOW PEN'S TEAM
PAGE 7 & 8
best on true life story
INTRODUCTION
19 /7/2025
"When the heart chooses, even silence speaks
WAYE NASHWAN?
Nashwan Ahmad saurayi ne mai kamala da nagarta. Kyakkyawan hali da sauƙin kai sun zame masa tufafi, zuciyarsa cike take da girmamawa da kula da wanda yake so. Tunanin sa mai zurfi ne, ba mai yawan magana bane amma idan ya furta kalma, zata dumi zuciyar mai sauraro.
Asalin sa daga jihar Kaduna, amma rayuwar sa ta kai shi ko’ina. A lokacin da Amatu ke secondary school, shine ya zo National Youth Service (NYSC) a makarantar su. Zuciyoyinsu sun haɗu a wancan lokacin — soyayya mai tsafta, mai nasaba da kulawa da mutunci ta kulla tsakaninsu. Daga wancan rana har yau — shekaru uku kenan — soyayyar nan na raye cikin nutsuwa da girmamawa. Ba su cika haɗuwa da juna ba, amma kowacce tattaunawa tana da ma'ana.
Yanzu Nashwan na da shekaru 30, yana aiki da wata Company mai zaman kanta dake Kaduna, kuma albashinsa na wata-wata na kai kimanin Naira dubu dari biyu (₦200,000). Duk da karancin ganawa da Amatu, Nashwan baya daina tura mata kyaututtuka, sakonnin ƙarfafa gwiwa da addu'o'in da ke tafiyar da rayuwar mace mai tsari.
Sau huɗu kacal ya zo gun Amatu cikin shekaru uku, amma kowanne zuwan yana cike da ma’ana, girmamawa da soyayya. Yana kula da ita fiye da yadda yawancin maza ke kula da matan da suke tare da su kullum a zuciyar Amatu, Nashwan shine hasken da ke tafiyar da daren rayuwarta, kuma soyayyarsa shine mafita da kwanciyar ranta.
BACK TO STORY
BAYAN WANI LOKACI
Karfe tara da mintuna goma sha biyu na dare. Amatu na kwance a kan gadonta, zuciyarta cike da fargaba da tambayoyi. Tana kallon last seen na Nashwan a WhatsApp – online yanzu yanzu ya sauka.
"Shiru? tun safe ba text, ba kira, sai na ganka online kana faman hira da wasu amma ni kamar ba na cikin rayuwarka..."
Tayi ajiyar zuciya, tana tura sako:
"Nashwan, gaskiya bana jin daɗi. Duk da ina ƙoƙari na fahimce ka, har yanzu bana ganin ka fahimce ni. Soyayya ba kyauta ba ce kawai, tana bukatar kulawa da kalma mai daɗi a rana, kirar da zata sa ranka ya lafa. Me yasa kana yin kamar babu ni?"
Bayan mintuna shida, sai gashi ya kira. Da ƙyar ta ɗauka. Murya ta cike da shakku da gajiya.
"My Amatu... na san ba kya farin ciki, amma wallahi aikin ne... bana da lokaci fa, kinsan aikinmu..."
"Ayyukan duniya ba su fi zuciyar da ke son ka ba!" Ta katse shi cikin murya mai sanyi da raɗa.
"Duk da nisan da ke tsakanin mu, ina tsammanin zan fi ka ƙauna — ba don kyauta ba, ba don suna ba — sai don ina ganin ka a zuciyata fiye da yadda kake kallona."
Shiru yayi, kamar yana narkar da kalmomin. Sannan yace:
"Kin fi karfin komai a rayuwata Amatu. Amma ba koyaushe nake da lokacin da zan yi magana ba."
ta numfasa, hawaye na gangarowa:
"Ba na son auren da zai zama kamar daɗaɗɗen suna ne kawai. Ina son rayuwa da wanda zai damu da rashin saƙona, ba kawai ganin saƙona ba. Nashwan, ka dawo da kulawarka kafin zuciyata ta gaji da jiranka."
Kamar wani yayi masa tsawa, Nashwan ya daɗe cikin shiru. Sannan ya furta:
"Zan gyara. Kuma zan tabbatar da cewa kina da gaskiya. Tabbas, kina da gaskiya fiye da shiru na."
Beep...
ya katse kiran. Amma a zuciyarta, tana jin zafi mai sanyi — na soyayya da yawan jira.
"Ina son Nashwan. Ina son sa fiye da yadda nake son ganin kaina cikin madubi. Amma duk zuciyar da ake soyayya da ita tana bukatar kulawa. Ina jira in ga ko zai cika alkawuran da yazo da su bayan wannan ƙorafi. Zuciyata na ƙauna, amma tana gajiya..."
Sati biyu kenan. Ƙwarya-ƙwarya.
Tun ranar da Amatu ta furta “Zuciyata na gajiya da jira”, Nashwan bai sake kiran ta ba, balle ya aiko da wani saƙo. Ba text, ba missed call — kamar soyayyar da suka ginaye akan lokaci da kulawa ta dusashe cikin iska mai sanyi da gajiya.
Amatu na zaune a ɗaki, zuciyarta a haɗe da wayarta. Sau dubu a rana tana duba ko Nashwan ya aiko da text ta kira sa ba adadi ta mai text shiru ta mai magana a online ya buɗe shiru ba amsar shiru shiru mai nauyi kamar dutse.
WhatsApp:
Last seen: Online 10 minutes ago.
“Yana lafiya? Ko yana tare da wani ne yanzu? Ko kuwa hakan kawai dabi’arsa ce – idan mun yi faɗa sai ya shude kamar ba mu taɓa soyayya ba?”
Zuciyarta na bugawa da ƙara. Kowanne tick na saƙon da ta sake karanta a baya kamar ƙarar dukan zuciya ne ke sake tuna mata da yadda ake ji idan ka fi ƙaunar wanda bai damu ba.
Tana kwance da fuska a mayafi, kwalla na ta faman gangarowa.
Sai ta furta a hankali cikin numfashi mai nauyi:
“Ina missing dinka, Nashwan... ko da baka missing dina ba.”
Tayi ƙoƙarin cire shi daga tunaninta, ta mayar da hankali kan aikin ta, sai dai duk inda taje, kamar murya da kamshin Nashwan na biye da ita ne.
Tana ganin sa a online, tana hango username ɗinsa, tana jin zuciyarta na amsa sautin sunansa — amma daga shi, shiru… shiru mai cike da tambayoyi.
"Shin da gaske so ya tsaya ne? Ko yana kokarin hukunta ni ne da shiru? Ko kuwa... ya gaji da ni? Amma me nayi da har sai haka?”
SOYAYYA GAMUN JINI
NANARH KANWAR SOJA ✍️✍️✍️✍️
https://chat.whatsapp.com/Iw0DqQGrB3UJg7MK20pgRC
💘 ZAƁIN ZUCIYA💔
THE HEART'S CHOICE
BY
NARNAH ƘANWAR SOJA
🎉 Happy Birthday to Me
July Girl Special 🎂✨
Na sadaukar da wanan littafin wa karan kaina kasancewar sa a watan haihuwa ta July..
Welcome to this journey... of love, of longing, of silence that speaks louder than words.
Let the novel begin... with a heartbeat. 💔💌
Love , Sad × Long-Distance × Hopeful * short story
DIAMOND 💎 GLOW PEN'S TEAM
PAGE 9 / 10
best on true life story
21 /7/2025
"When the heart chooses, even silence speaks
Kwatsam, zuciya ta gama jurewa. Amatu ta kama wayarta da hannu mai rawar zuciya ta danna sunansa. Bayan ƙarar kira sau biyu, ya ɗaga.
“Hello…”
Muryarsa kamar ba daɗin ji. Ita kuwa ba ta tsaya gaisuwa ba, sai dai ƙorafi mai sa kwalla:
“Nashwan, me na maka ne har three weeks baka kira ni ba? Me nayi da zaka rika yin online amma ba zaka tambaye ni lafiyata ba? Ko zuciyata bata da daraja ne a gurinka?”
sai shiru ya biyo baya.
daga can Nashwan yace a sanyaye:
“Amatu... aikin nan da nake ciki ba sauki bane. Wallahi kullum ina yinta har dare. Amma gashi yanzu na tura miki dubu goma, don ki Hai napep zuwa asibiti
Sai transfer alert ya shigo. Gaskiya, ya turo.
Amatu ta lumshe ido, zuciyarta ba ta cikin kudin. Sai tace da wani yanayi mai cike da taushi da zafi:
“Ni ba kudi nake so ba Nashwan, ina so ka bani lokaci. Ko da minti goma ne kullum, ka tuna da ni. So na ba sabulun wanka bane da zaka manta idan ka fita.”
“Ni ina son ka Nashwan, fiye da karfina ma. Amma kamar ina soyayya da bango. Zuciyata na ƙonewa.” shi kuwa ya sake shiru. Sai yace:
“To... zan duba, zan gyara. Ki bani lokaci.”
Washegari
Da safe kamar kullum tana jiran kira ko sako, sai gashi ya kira. Da farko ta ɗauka farin ciki zai biyo, amma...
“Amatu, na baki minti biyar. Duk abinda kike da shi a ranki, ki fadi yanzu. Ina aiki ne.”
Zuciyarta tayi wani irin nauyi. Kamar ta furta:
“Ina son ka Nashwan… amma bazan iya soyayya da mutum da agogo ba.”
sai ta fara magana cikin kuka mai saukar hankali...
“Zuciyata Ba Takarda Bace”
Yana cewa “Amatu, na baki minti biyar. Duk abinda kike da shi a ranki, ki faɗi yanzu. Ina aiki ne.”
Amatu ta dafe kirjinta kamar zuciyarta na neman tsagewa. Amma ta ja numfashi, ta fara da nutsuwa:
“Nashwan, ka tuna lokacin da muke tare a makaranta? Kana bani lokaci fiye da abincin ka. Ka tuna da kalaman da kake faɗa min? Ina ƙaunar ka Nashwan, har yanzu. Amma yanzu kamar ni ce kadai nake tafiyar da soyayyar nan…”
“Kullum sai dai ni na kira, ni na yi rubutu. Ka shiga online, amma ko ‘Hi’ ba zaka turo ba. Wannan ba soyayya ba ce, Nashwan. Ni ma ina da zuciya. Bana son mu rabu… amma ina jin kamar ni kadai ce a cikin wannan dangantaka.” Shiru.
Can kuwa… ihun Nashwan ya buga a kunne kamar karar roka.
“To me kike so ne yanzu? Kina takura min ne fa, Amatu! Ko ina aiki ba zaki fahimta ba? Sai kace ni bawa ne naki?! Wai wannan ce soyayya? Ko fursuna kike son ni na zama??”
Wayar ta dauki tsawa kamar hayaki yana fita daga kunne.
Amatu ta kasa magana. Kamar rana ta ɓace daga duniyarta.
Daga nan sai “call ended”. Ya katse wayar.
ta sunkuyar da kanta, hawaye suka gangaro kamar ruwan damina.
“So na ba ya isar da ni gareka… amma kuma ka manta ni mutum ce.”
-
“Ni Ma Mutum Ce”
"Meye laifina?"
"Laifina kawai shine ina son shi?"
"Ni ma mutum ce, ba dutse ba. Macce ce mai rauni, da zuciya mai sauƙin kamuwa da so."
"Sai don na nuna mai so na, shi ne zai ce min minti biyar nake da su? Minti biyar! Kamar ina roƙon lokaci daga wani wanda ya mallaki numfashina yana jan min tsaki a waya ."
"Shin haka soyayya take? ko kuwa ni ce ban dace ba?"
"Yanzu sai na fuskanci cewa soyayya tana da laifi idan mace ce ta fara nuna gaskiya."
"Yana online, yana dariya da duniya. ni kuma ina nan ina fama da ƙuncin da soyayyarsa ta jefa ni."
"Ko da ace na yi kuskure, ba zan cancanci wannan wulakanci ba."
"Wani lokaci nakan tambayi kaina, idan son shi laifi ne, to me yasa zuciyata ke dukan shi ba kowa ba?"
Tunda suka yi fadan nan, Amatu ta soma jin wani irin ƙorafi daga zuciyarta—na so da na zafi. Duk lokacin da ta ga Nashwan online, zuciyarta na harbawa, idonta na kallo cikin fatan cewa wataƙila zai turo saƙo ko ya kira, ya ce “Ina sonki, na tuba.”
Amma babu. Shiru.
Sai ta yanke shawarar cewa zata ja baya.
Soyayya ba wai azaba bace da za a cigaba da jurewa ba tare da kulawa ba. Ita ma tana da daraja.
A ranar Laraba, ta ga missed call nasa guda daya. Da niyyar komawa kira, sai ta tsaya. “Idan har ni kadai ke ƙoƙarin ceto wannan dangantaka... to ai ni ba itacen gicciyewa bace.”
Ta share kiran.
Ta tafi asibiti kamar kullum. Tayi murmushi da ma’aikata, ta yi aiki da gamsuwa. Amma duk da haka, a zuciyarta akwai rana mai yawan guguwa da ƙura—ƙuruciyar soyayya ke hura mata ƙonawa.
Layla ta lura.
Ta juyo ta ce mata da salo mai tausayawa:
“Amatu, kin fara zama kamar wacce ke cikin soyayya da namijin da ya manta da ita.”
Amatu ta yi murmushi, ya cika da hawaye.
“Ni dai Layla, soyayya ta kai ni ƙololuwa... amma rashin mutunci bazan jure ba. A zuciyata har yanzu ina sonsa—amma bazan bar kaina na ci gaba da wulakanci ba. Ni mace ce, mai daraja.”
Layla ta matso ta rungume ta.
“Kina da kyau, hankalinki kwarai da gaske. Idan soyayya zata ci ki—ki ci gaba da ja baya. Idan zai gane kuskurensa, zai dawo. Idan kuma ba haka ba... Allah zai baki wanda yafi shi daraja da kulawa.”
SHIN KUNA TUNANIN AMATULLULAH TAJA BAYA DAGA MASOYIN TA
WAI SOYAYYAR NISA HAKA YAKI DA AZABA
SHIN KUN TAƁA HAƊUWA DA MASOYI YANA WANI GARI KINA WANI GARI DISTANCE RELATIONSHIP YA ZAMA MATSALARKU
SHIN NASHWAN ME KE FARUWA DA ZUCIYAR SA AKAN AMATULLAH DUK DA CEWA YASO TA SOYAYYA MAI TSANANI
MUJEEE ZUWA BARE MUGA DA GASKE KO AMATU TAYI HANKALI ZATA JAH CLASS NATA INA TSORON KAR CLASS NIN DAI YA ZUBE
NARNAH ƘANWAR SOJA ✍️✍️✍️
Welcome to this journey... of love, of longing, of silence that speaks louder than words.
Let the novel begin... with a heartbeat. 💔💌
Love , Sad × Long-Distance × Hopeful * short story
Kwatsam, zuciya ta gama jurewa. Amatu ta kama wayarta da hannu mai rawar zuciya ta danna sunansa. Bayan ƙarar kira sau biyu, ya ɗaga.
“Hello…”
Muryarsa kamar ba daɗin ji. Ita kuwa ba ta tsaya gaisuwa ba, sai dai ƙorafi mai sa kwalla:
“Nashwan, me na maka ne har three weeks baka kira ni ba? Me nayi da zaka rika yin online amma ba zaka tambaye ni lafiyata ba? Ko zuciyata bata da daraja ne a gurinka?”
sai shiru ya biyo baya.
daga can Nashwan yace a sanyaye:
“Amatu... aikin nan da nake ciki ba sauki bane. Wallahi kullum ina yinta har dare. Amma gashi yanzu na tura miki dubu goma, don ki Hai napep zuwa asibiti
Sai transfer alert ya shigo. Gaskiya, ya turo.
Amatu ta lumshe ido, zuciyarta ba ta cikin kudin. Sai tace da wani yanayi mai cike da taushi da zafi:
“Ni ba kudi nake so ba Nashwan, ina so ka bani lokaci. Ko da minti goma ne kullum, ka tuna da ni. So na ba sabulun wanka bane da zaka manta idan ka fita.”
“Ni ina son ka Nashwan, fiye da karfina ma. Amma kamar ina soyayya da bango. Zuciyata na ƙonewa.” shi kuwa ya sake shiru. Sai yace:
“To... zan duba, zan gyara. Ki bani lokaci.”
Washegari
Da safe kamar kullum tana jiran kira ko sako, sai gashi ya kira. Da farko ta ɗauka farin ciki zai biyo, amma...
“Amatu, na baki minti biyar. Duk abinda kike da shi a ranki, ki fadi yanzu. Ina aiki ne.”
Zuciyarta tayi wani irin nauyi. Kamar ta furta:
“Ina son ka Nashwan… amma bazan iya soyayya da mutum da agogo ba.”
sai ta fara magana cikin kuka mai saukar hankali...
“Zuciyata Ba Takarda Bace”
Yana cewa “Amatu, na baki minti biyar. Duk abinda kike da shi a ranki, ki faɗi yanzu. Ina aiki ne.”
Amatu ta dafe kirjinta kamar zuciyarta na neman tsagewa. Amma ta ja numfashi, ta fara da nutsuwa:
“Nashwan, ka tuna lokacin da muke tare a makaranta? Kana bani lokaci fiye da abincin ka. Ka tuna da kalaman da kake faɗa min? Ina ƙaunar ka Nashwan, har yanzu. Amma yanzu kamar ni ce kadai nake tafiyar da soyayyar nan…”
“Kullum sai dai ni na kira, ni na yi rubutu. Ka shiga online, amma ko ‘Hi’ ba zaka turo ba. Wannan ba soyayya ba ce, Nashwan. Ni ma ina da zuciya. Bana son mu rabu… amma ina jin kamar ni kadai ce a cikin wannan dangantaka.” Shiru.
Can kuwa… ihun Nashwan ya buga a kunne kamar karar roka.
“To me kike so ne yanzu? Kina takura min ne fa, Amatu! Ko ina aiki ba zaki fahimta ba? Sai kace ni bawa ne naki?! Wai wannan ce soyayya? Ko fursuna kike son ni na zama??”
Wayar ta dauki tsawa kamar hayaki yana fita daga kunne.
Amatu ta kasa magana. Kamar rana ta ɓace daga duniyarta.
Daga nan sai “call ended”. Ya katse wayar.
ta sunkuyar da kanta, hawaye suka gangaro kamar ruwan damina.
“So na ba ya isar da ni gareka… amma kuma ka manta ni mutum ce.”
-
“Ni Ma Mutum Ce”
"Meye laifina?"
"Laifina kawai shine ina son shi?"
"Ni ma mutum ce, ba dutse ba. Macce ce mai rauni, da zuciya mai sauƙin kamuwa da so."
"Sai don na nuna