Showing 3001 words to 6000 words out of 15008 words
daddadan sanyin iska ya lullube garin su uku suka fita wajen gida domin ɗaukar aikin safe kamar yadda suka saba.
A cikin shirin tafiya aiki, Amatu ta shiga bayi tayi wanka, ta fesa turaruka masu daɗin ƙamshi, sannan ta zaɓi kaya farare—suit mai sauƙi da lafiyayyen hijabi.
Da ta fito sai shape ɗinta ya bayyana da salo: ta cika cika ta kwanta kwanta, amma cike da modesty da kamun kai a gabanta na madubi, ta tsaya tana kallon kanta, hannunta na dafa ƙirji kamar tana tambayar zuciyarta ita wacce ce.
WACCECE AMATULLULAH...?
Amatullulah ’yar mace mai kamun kai da imani ta fito daga gida na natsuwa da tarbiyya, amma rayuwa ta koya mata yadda ake zaune da hawaye a fuska da dariya a zuciya.
tana da murmushi da zai iya warkar da zuciya mai ciwo, da idanu masu taushi kamar ruwa mai nutsuwa.
ba ta da hayaniya, ba ta da surutu, amma idan ta kalle ka da idonta, zaka fahimci cewa akwai sirri da zurfi da ta ɓoye.
tana aiki a asibiti, ƙaramin matsayi ne – health care assistant – amma zuciyarta girma take da tausayi da kulawa.
A duk ranakun da take fuskantar wahala, bata taɓa fushi da Ubangiji ba. Soyayyarta da Nashwan wata labari ce ta silent devotion, tana iya hakuri da komai saboda shi.
Amatu ba mace bace da za ka gane da fari, dole sai ka tsaya ka zurfafa—sai ka fahimta a hankali. Akwai wani abu a cikin shigarta, cikin tafiyarta, cikin yadda take kallon madubi tana tambayar kanta: “Shin ni ce ta cancanci soyayyar sa?”
Toh, ita ce.
Amatullulah ce.
Wacce Nashwan ke mafarki da ita wacce rayuwa ta so tayi wa rauni, amma zuciyarta ta ƙi karɓar karyewa.
AMATULLULAH YUSUF LABARAN
Amatullah Yusuf Labaran, kyakkyawar budurwa mai cike da nutsuwa da kunya, ta fito daga karamin gida mai tarin daraja da tarbiyya. Ita ƴar asalin Borno ce, daga unguwar Gwange, wato ɗaya daga cikin tsofaffin unguwanni masu cike da tarihinta da rayuwar talakawa a birnin Maiduguri.
Unguwar da take cike da ɓoyayyun daraja—duk da talaucin da ya bayyana a bango da ƙofar gida, akwai arzikin zuciya da girmamawa a cikin iyalanta. Unguwar da ko ruwan famfo ya ƙi fitowa, mutane ke da zuciyar taimako da hakuri da juna.
Malam Yusuf Labaran mahaifin Amatu, mutum ne mai ilimi da ɗabi’a. Ba shi da yawa a aljihunsa, amma ya cika da basira da tarbiyyar da ya tura wa ‘ya’yansa. Ma’aikacin gwamnati ne—malami a makarantar sakandire ta gwamnati. Rayuwar malam Yusuf ba mai cike da kwaɗayi ba ce; sai dai koyarwa da addu’a da fatan ‘ya’yansa su rayu cikin nasara da tsoron Allah.
Yana da yara uku:
1. Mahir Yusuf
Shi ne babba a cikin ‘yan uwansa. Yana da shekaru 23 a duniya.
Dalibi ne mai hazaka a jami’ar University of Maiduguri, sashen Computer Science. Kamar mahaifinsa, yana da nutsuwa da hangen nesa. Slsai dai Mahir ya fi son ya fita daga ƙungiyar talauci da ɗan karen aikin gwamnati—yana mafarkin kafa IT Company ɗinsa, domin ceto iyayensa daga wahalar rayuwa.
2. Amatullulah Yusuf
Tana cikin matsakaicin shekaru, shekarar ta ashirin kenan ɗiyar da malam Yusuf ke alfahari da ita.
Budurwa ce mai hankali da kamun kai, tana aiki a babban asibitin gwamnati – General Specialist Hospital, Maiduguri – a matsayin karamar nurse (healthcare assistant).
Ta saba da sanyi da zafin asibiti. Idonta ya saba da ganin hawaye, amma zuciyarta bata saba da bari ta bayyana nata ba. Tana da kwarjini, da hali mai jan hankali. Duk wanda ya sadata da ita yana gane cewa akwai zurfin hankali da farin ciki mai ɓoyuwa a cikin sirrinta. Shi ya sa Nashwan bai gushe da soyayyarta ba – ko da yake zuciyarta tana cike da shakku da mafarki.
3. Safiya Yusuf
Ta fi kowa ƙuruciya. Yarinya ce mai shekaru 15, tana cikin shirin zana Junior WAEC.
Safiya yarinya ce mai wayo da surutu, tana da dariyar da ke sa uwarta ta manta da gajiyar duniya. Ita ce abar birgewa a gidan malam Yusuf. Tana sha’awar ilimi, tana kuma alfahari da Amatullah—wani lokaci har tana kwatanta kanta da ita a gaban madubi.
Gidan Malam Yusuf ba kawai alfarma ya ƙunsa ba, sai darajar mutunci.
Gidan da ko da turmi da tabarya ke yi da ƙyar, ana ci da albarka, ana kwana da aminci. Wani guri ne da so da addu’a su ke wakiltar arziki.
Amatullulah ce farar goro a cikin ruwan dare.
Ita ce zuciyar mahaifinta ke alfahari da ita.
Ita ce tauraruwa a cikin gidan da ba ya da wutar lantarki amma ke da hasken zuciya.
Ita ce jini da numfashin labarinmu.
Bayan Amatullah ta fito daga ɗakin su, ta shiga tsakiyar gidan tana gyara ɗan gyambon hijabinta. Mama Rabi ta dubeta da murmushi, ta furta mata addu’ar fatan alheri da karewa daga sharrin hanya da mutane.
“Allah ya tabbatar da alkhairi a yau, ya tsareki da alkawarin sa, Amatu,” Mama ta ce cikin muryar da ke cike da ƙauna da kulawa.
Amatullah ta lumshe ido, ta amsa da "Amin Mama," sannan ta shige ƙofar gida cikin nutsuwa da sanyin safe mai daɗi, fuskarta a lullube da kwarjini na mace tagari.
Ta tsaya bakin titi tana duba gefen hanya don samun abinda zai kaita hospital. Cikin sauri sai wata karamar napep mai kyalli ta tsaya gabanta, ɗan saurayin dake ciki ya leƙo da fara'a da sallama:
“Assalamu Alaikum kyakkyawar halitta daga Ubangijin halitta amince ya tabbata a garinki.”
Amatullah ta tsaya cak, zuciyarta na karanto sunan da bata ji ba tukuna, amma muryar da kunnenta ya tsinta ya janyo ta juya da hanzari.
Ta sakar da dan guntun murmushi Habibu
Saurayin da kullum baya gajiya da bin diddigin soyayyarta, kamar yaro da kuka yakan cusa kansa a cikin zuciyarta. Yana da shegen kawaici da zafin so, wanda ke jan hankali ko da a hankali take tafiya.
“Lafiya dai Yaya Habibu?” ta ce cikin ladabi da kasaita, tana mai gyara jakar ta a kafada.
“Lafiya kalau, nurse Amatu nace na kawo ki aiki yau, ko?” Ya ce yana ƙoƙarin bude kofar gefen napep ɗin cikin ladabi.
Ta daga hannu cikin girmamawa amma da takama, “A’a Yaya Habibu, na gode wallahi. Ka daina wahalar da kanka, ni dai na saba zuwa da kaina.”
Habibu ya dan sunkuyar da kai, ba tare da nuna damuwa ba, sai murmushi yayi da cewa:
“Ai in har wahala ce ke kawo ganin fuskarki safe da safe, wallahi zan ɗauke ta a matsayin ni’ima ne daga sama.”
Amatullah tayi dariya kadan, ta kauda kai cikin jin nauyi, sannan ta ce:
“Nagode Yaya, Allah ya saka da alkhairi.”
Sai ta juya cikin nutsuwa, ta nufi wata babbar motar haya da ta tsaya daga nesa. Habibu kuwa ya bita da kallo har sai da ya fice daga gani, yana kallon fuskarta kamar ana rubuta soyayya da alkalami a zuciyar sa.
Tana cikin motar, fuskarta a window, tana kallon yadda iska ke jefa ganyen bishiyu cikin sanyi da natsuwa. A cikin zuciyarta, kalmomi ne ke yawo, kamar ana karanta su daga wani ɗan karamin littafi da ba kowa ke da damar budewa ba.
"Ina ma ace Nashwan yana bani lokaci kamar yadda Yaya Habibu ke bani. Ina ma ace duk wata mace zata samu namiji daya damu da ita da zuciyarsa gaba ɗaya… to da kowacce mace daɗin rayuwa ne nata."
Ta sauke ajiyar zuciya, sannan wayarta ta fara ringing. Ta zaro ta daga jakarta – Baba ne Sai ta dan lumshe ido kafin ta ɗaga ta kara a kunne.
“Baba, barka da safe,” ta ce cikin natsuwa.
“Kin fita ne kenan Amatu?”
“Eh Baba, ina hanya yanzu.”
“To Mama tace kana bachi , Zan dawo da wuri sai muyi magana.”
“To ‘yata, Allah ya kiyaye hanya.”
Ta katse wayar tana murmushi, zuciyarta na taune ƙaunar da iyayenta ke nuna mata – soyayyar da ke da tsafta da fatan alheri.
Bayan ta isa asibiti, ta sauka a hankali, ta gyara veil dinta sannan ta nufi gaban babban ofishin su. Da zarar ta sa kafa a ciki, sautin murya da gaisuwa ya karade ofishin:
“Happy birthday Amatu!”
Kawayenta da abokan aikin ta suka taso suna rungumeta da murna da dariya. Ta ce da sanyi: “Oh my God! Kun tuna? Thank you so much everyone... Wallahi I didn’t expect it.”
Daga nan sai su zauna tare da ƙawarta ta fi kusa da ita – Layla – wacce ko da yaushe tana tsaye mata kamar ‘yar uwa. Layla ta ce:
“Wallahi yau sai mun saka miki wani abu, Amatu. Enough of this modest birthday every year!”
Suka fara hira, cike da dariya da zolaya, kafin su nufi reception don karɓar jerin sunayen marasa lafiya da za su duba.
“To Layla, yau ni da ke jan jini, ko?” Amatu ta ce tana gyara gloves ɗinta.
“Eh mana, ko kina ta birthday, ai jinin mutane ba zai tsaya ba,” Layla ta amsa da dariya.
Bayan an kammala duba marasa lafiya, Amatu ta miƙe da gajiya amma fuskarta na ɗauke da murmushi mai nutsuwa. Ta cire gloves ɗinta, ta wanke hannunta sannan ta ɗauki jakar ta a hankali, tana nufar ƙofar fita daga asibitin. Yayin da take tafiya, tana jin sauyin iska da hargitsin zuciya—saboda shi.
Ta zaro wayarta domin kira. Sunanta biyu: “Nashwan”.
Ta matsa kiran farko... ringing... babu ɗauka. Ta kara na biyu... "Missed call".
Zuciyarta ta dan yi sanyi, kamar ruwa mai sanyi da aka jika makera. "Wai me yasa yake nesa da ni haka? na cancanci kulawa..."
Bata gama tunani ba sai wayarta ta kara, Habibu ne—kamar kullum, girmansa a cikin zuciyarta bai wuce soyayya ba amma bai da gajiya da ƙoƙari.
Sai kawai ta danna ɗaya cikin kiran goma da ya shigo a da. Muryarsa mai taushi ta karade kunnenta:
“Assalamu Alaikum Amatu, ya aiki?”
“Lafiya kalau yaya Habibu, sannu da kokari...”
“Na dade ina kiran ki ne, ina so in gaida ki kafin ki koma gida.”
“Ah, ai gani nan zan taho, Allah ya saka da alheri.”
Ta kashe wayar tana jin tausayi. Habibu mutum ne mai hakuri da nuna kauna, sai dai zuciyarta bata nan gaba ɗaya a wurin sa. Tana son wani, amma wanda bata da tabbacin ya fi son ta.
Da ƙarfe shida da rabi na yamma, lokacin rana na neman bacewa da iska mai sanyi tana hura gefen veil ɗinta, ta fito daga asibiti da takunta mai cike da natsuwa da ɗacin zuciya.
Sai kawai ta hango Habibu a bakin titi, yana tsaye a gefen napep dinsa kamar yadda ya saba, idonsa cike da kulawa da kaunar da bai iya ɓoyewa.
“Bismillah Amatu,” ya ce da ɗan murmushi.
Ba tare da musu ba, ta shiga. Babu hayaniya a tsakanin su, sai sanyi da nutsuwa da ke bayyana daga kallon sa. Yana tuka napep ɗin da hankali kamar yana ɗauke da zoben zinariya a ciki.
Ya kai ta har kofar gidansu, ya tsaya, ya ce:
“Allah ya hutar da gajiyar ki, ki huta lafiya Amatu.”
Ta kalli shi tana murmushi, da murmushin da ke tsakanin gaisuwa da alhini, sannan ta ce:
“Na gode sosai, Allah ya saka da alheri, yaya Habibu.”
Ta juya ta shige gida cikin nutsuwa, amma zuciyarta ba ta da kwanciya. Daya yana nuna ƙauna, ɗaya yana ɓacewa kamar hayaki cikin iska......
Amin uzuri don Allah na rashin posting da rashin time na buɗe group da reply a private message a chigaba da haƙuri in sha Allah komai zai dai dai ta na gode
https://chat.whatsapp.com/Iw0DqQGrB3UJg7MK20pgRC
💘 ZAƁIN ZUCIYA💔
THE HEART'S CHOICE
BY
NARNAH ƘANWAR SOJA
🎉 Happy Birthday to Me
July Girl Special 🎂✨
Na sadaukar da wanan littafin wa karan kaina kasancewar sa a watan haihuwa ta July..
Welcome to this journey... of love, of longing, of silence that speaks louder than words.
Let the novel begin... with a heartbeat. 💔💌
Love , Sad × Long-Distance × Hopeful * short story
DIAMOND 💎 GLOW PEN'S TEAM
PAGE 5 & 6
best on true life story
INTRODUCTION
16 /7/2025
"When the heart chooses, even silence speaks.
Bayan sallar Ishaa, gidan ya lullube da natsuwa da sanyin dare. Safiya na gefen Mama suna gyara kwanon abincin da suka ci tuwon masara da miya kuɓewa mai ɗan yaji, wanda Amatu ke matuƙar so.
Baba na zaune a jikin kujera yana duba littafin karatun sa, zuciyarsa cikin shiru, kamar yana nazarin wani abu. Sai kawai Amatu ta fito da ƙaramar jaka daga cikin daki, ta buɗe ta fito da zunzurutun kuɗi na Naira dubu hamsin, ta miƙa masa da girmamawa da murmushin ƙauna:
“Baba, ga wannan. Dan Allah ka karɓa, nasan zaka yi amfani da shi da albarka.”
Baba ya karɓa yana kallon kuɗin da ta miƙa, sai ya ɗan jinjina kai da murmushi.
“Wannan duk name Amatu? Ina kika samo kuɗin nan haka kamar mai albarkar hatsi?”
Amatu ta ɗan yi ƙasa da murya tana murmushi cikin jin kunya:
“Nashwan ne Baba. Ya turo min a matsayin kyautar birthday. Kullum haka yake min, ba ya taɓa barin ranar ta wuce haka kawai.”
Baba ya kalli Amatu sosai, kamar yana nazarin fuskarta da zuciyarta a lokaci guda, sai ya furta:
“Ikon Allah. Shi Nashwan kam baya gajiya. Kuɗin da ya aiko miki da su, wallahi shine albashi na gaba ɗaya a wata. Na yaba da irin karamcin sa. Amma…”
ya tsaya yana jinjina kai sannan ya ce da tsantsar tausayi da damuwa:
“Sai dai me, ke Amatu... sai yaushe zai turo kansa? Ina jin tsoron kada wannan juyin zuciya ya zame miki juyin rayuwa. Idan har yana sonki da gaske, me zai hana ya taho ya gabatar da kansa? Ya zo ya gaishe mu, mu san iyayensa, su san mu? Ni nake fatan hakan... ba wai zuba ido muna jiran sakon waya da alert ba.”
Amatu ta yi shiru, zuciyarta cike da ruɗani. Tana son Nashwan fiye da kowa, amma tambayar Baba tana da nauyi har yanzu, Nashwan bai taɓa fitowa fili da maganar aure ba ya cika da kyaututtuka da kulawa, amma shiru kan abinda take mafarki da fata...
Baba ya ƙarasa da faɗar cikin murya mai sanyi:
“Na fi son yazo ya ce min da bakinsa, ‘Baba na zo neman Amatullah, ku bani dama’ — haka kawai zuciyata zata huta da murmushi.”
Amatu ta ɗan sunkuyar da kai, tana wasa da yatsun hannunta, zuciyarta na faɗin: “Ya Allah ka shiryar da Nashwan ya gane muhimmancin hakan...”
Ta koma ɗaki, lokaci ya kusa da ƙarfe goma na dare. Tana cikin shirin kwanciya, rigar bacci jikinta, fuska a gajiye amma zuciya na yawan tunani. Wayarta ta yi tsit, sai kawai ta hango missed call ɗin Nashwan har sau biyu. Ta ɗan jiyo numfashinta cikin damuwa, tana mamakin dalilin kiransa a wannan lokaci.
“Ina ma ba za’a gama da kiraye-kirayen dare ba...” Ta furta a hankali, sai kawai wayar ta ƙara ringing. Da kyar ta ɗaga, muryarta cike da gajiya da sha’awar bacci:
“Hello…”
agefe guda, muryar Nashwan ta karade kunne da sanyi da nutsuwa, kamar mai ɗauke da busar sarewa mai sanyi da tsantsar natsuwa.
“My Amatu, kin tashi lafiya? Na gaji da rana, wallahi sai yanzu nake samun kansa.”
Amatu ta lumshe ido, murya a sakakke:
“Lafiya lau, na ga missed call naka. Nayi zaton ka manta dani ne…”
ya ɗan murmura, muryarsa na ɗauke da raɗa:
“Kamar ya manta dake? Ai ke ce zuciyata. Kawai ne nayi busy sosai yau, kin san aikin nan... amma a duk inda nake, wallahi ke na ke tunani.”
Sukayi hirar da bata fi minti biyar ba, amma kamar zasu baje da soyayya. Sai Amatu ta nutsu ta faɗa masa:
“Baba ya karɓi kuɗin da ka turo, kuma ya ji daɗi sosai. Yace duk da farin ciki da jin dadin karamcin ka, yana tambaya sai yaushe zaka gabatar da kanka.”
Shiru ya biyo bayan kalmarta na ƴan dakiku. Sai daga baya Nashwan ya sauke ajiyar zuciya sannan ya furta da gaskiya:
“Soyayya ta da ke ba wasa ba ce, Amatu. Wallahi da gaske nake. Amma akwai abubuwa da nake gyarawa yanzu, sai dai insha Allahu—nan da shekara mai zuwa, zan turo iyayena. Zan zo da kaina, mu gama magana cikin mutunci.”
Zuciyar Amatu ta cika da farin ciki da fargaba a lokaci guda. Shekara guda? Haka za ta jira? Amma a lokaci guda, ta ji kwanciyar hankali da yadda ya furta kalmomin, ba da wasar magana ba, ba da ɗoki na banza ba. Da karamin murmushi ta ce:
“Na yarda. Na karɓa. In Allah ya yarda, zan jira har sai lokacin nan.” Nashwan ya ce da ƙayatarwa:
“Kuma har lokacin nan, soyayyata ba zata gushe ba. Na fi ƙaunar ki fiye da na kaina, Amatu.” ta saki ajiyar zuciya, murya a raɗa:
“Ni ma ina son ka Nashwan... fiye da yanda zan iya faɗi.”
Wayar ta kashe ne da salati da addu’a daga gare shi. Ta zuba wayar a gefe, ta lumshe ido da murmushi a fuska. Zuciyarta ta nitsar da wani irin sanyi — sanyi mai ɗauke da fata, ƙauna da alkawarin gobe...
Washegari...
Tun karfe bakwai da rabi Amatullah ta tashi, jikinta na da sauƙi, zuciyarta cike da kwanciyar hankali da farin ciki na soyayya. Tana gab da isa bakin titi sai Habibu ya zo kamar yadda ya saba da napep nasa. Ta shiga ba tare da wata damuwa ba, amma a zuciyarta tana jin sanyi... Nashwan dai ya saka haske a rayuwarta.
Da suka isa asibiti, ta faɗa Layla rai a ɗumɗum. Bayan sun gama shiryawa a office, suna cikin sassanyar rana, suka zauna a gefen taga suna ɗan hutawa kafin fara aikin rana. Layla ta lura da murmushin Amatu, da wata annuri a fuskarta da ba kasafai ake gani ba.
“A’ah ke dai yau kamar an baki labari mai daɗi. Me ke faruwa ne da wannan murmushin sirri?” Layla ta tambaya tana ƙara matsowa kusa da ita.
Amatu ta lumshe ido tana ɗan kallon taga, sai ta juya da ɗan shafa