Showing 15001 words to 18000 words out of 43747 words
Chapter 6 - Zumuntar kenan Book 2 by Sumayya Abdulkadir Takori Kabara.txt
shi ba ta hannunsu balle su kwance ko su warware. Duk wannan kakabi da zagi da tashin hankali ba nasu bane, ba su ya kamata ki yiwa ba tsakaninki da Fa’iz ne can. Amma ina ruwan Ummi, Hajjah ko Zanirah?”
Na galla masa harara na ce, “To shin ina na ganshi balle in yi mishi Yaya Aliyu? Ni kam yadda nake ji a zuciyata baki dayan A.B nake jin haushi. Har kai din wallahi”.
Murmushi ya yi, ya rausayar da kai, “Ta ina laifin wani ke shafar wani? Har da Yaya Aliyu? Fa’izah” Fa’eez shi ya nemi aurenki da kansa domin gyara zumuncinku da ya gurbata a baya”.
Ban san sanda na lailayo ashar ba na ce, “ZUMUNCIN me? In dai wannan shi ake kira gyara zumunci to ba shi bane, sai dai kara lalata shi. Na ji zan iya yafewa Fa’iz dukkan abin da ya yi mani, amma ba ta hanyar aure ba. In dai har an yarda a raba auren nan in auri Dr. N na YAFEWA FA’IZ DUK ABIN DA YA YI MANI A BAYA!”
[6/3, 4:13 pm] Takori: Aliyu ya ce, “A da har an tayar mani da hankali da aka ce dani wai “Fa’izahna ta haukace! Ashe lafiyar kanwata lau. To share hawayenki ki bar ta da hakarkari tunda kin ce haka shi kenan. Yanzu abin da za ayi Fa’iz za ki yiwa wannan bayanin ta lallama da salama da kwantar da kai. Kin san an ce..... mai nema shine a kasa har kullum.
Don haka kada ki ji komai don kin roki Fa’iz wani abu wannan hakkinsa ne a yanzu. Shi ke da ikon yi ko ki. Don haka dole ki aje rawanin kiyayyar gefe ki roki Fa’iz.
Yanzu Fa’iz ya canza, ba shi da wannan muguwar azzalumar fuskar da kike fadi, ke tsoronki ma yake ji! Kin san an ce abin da ya baka kuka wata ran shi zai baka dariya. Haka abin da ya baka tsoro wata ran shi zai baka dariya. Baki ga ya kasa zuwa ba? Amma ina ruwan su Zaneerah, Ummi da tsohuwar Allah HAJIYA HADIZA?”
Na girgiza kai hawaye na zuba na ce, “Yaya Aliyu kai kadai ke sona a cikin gidan nan tunda har ka goyi da bayana ka gane abin da nake so su gane suka kasa ganewa, wato Fa’iz ba mijin aure bane, ba masoyi bane abin neman tsari ne. Don haka na dauki shawararka, ka je ka baiwa su Hajjah hakuri domin na zage su sosai”.
Aliyu ya yi murmushi ya ce, “Har na ji dadi, ni Aliyu Baban Fa’izah! Allah yasa nima tawa Fa’izar ta yi min biyayya haka tamkar mai sunan ta. Share hawayen nan duka A beg...”
Nasa habar zanina na share hawaye tas, duk jikina rawa yake da karkarwa. Aliyu ya ce, “Kada ki damu da su Hajjah, su tunaninsu kin samu motsi a kanki ne. Don duk kuka suke miki na tausayawa. Ni kam na san babu yadda za ayi Fa’izata ta haukace a kan Fa’iz, faruwar hakan na nufin kenan FA’IZ ya yi galaba a kan FA’IZAH!”
Na ce, “Never. Idan har na yi hauka saboda Fa’izu na ji kunya na fadi babu nauyi, kuma ban haifu cikin Maimunar da yake zagi ba tunda ban rama komai ba, tunda na bar Fa’iz cikin nasa hankalin. Wata ma zai je ya auro wadda ta fini ya ci gaba da rayuwarshi normal ni ko in kare a pyschiatric da Asylum”.
Cikin murmushi sosi Yaya Aliyu ya ce, “Yauwa, ashe dai kin gane. Amma in ya baki takarda kika yi auren ki da Dr. Nazir kinga ai kin tusa mishi haushi ko baya sonki zai ji kishi, tunda akwai igiyar aure da ta taba gittawa a tsakanin ku, ko ya ya ne. In hakan ta faru da kyar ma zai iya zaman kasar ko ya kika ce?”
Na yi murmushi da kumburarriyar fuskata na ce, “Shin Yaya Aliyu ina zan ga FA’IZ BAMALLI?”
Yaya Aliyu ya ce, “Fa’eez na cikin kasarmu mai dimbin albarka yanzu haka. Za ki ganshi yau, gobe, jibi ko gata. Muddin ranakun nan suka wuce baki ga Fa’eez ba, to kirayi auren ku da suna tabbatacce na muddin rai. Domin sune ranaku na karshe da za a kammala bikinku a kai ki gidansa kina so ko bakya so. Don haka ki yi duk kokarin da za ki yi ki ga Fa’iz cikin kwanaki uku”.
Na yi zugum ina kallon sa, na ce, “Shin don me ka boye min tun a daren ranar Yaya Aliyu? Wallahi-wallahi da duk yadda za ayi ba zan bari a daura auren nan ba......” Na ci gaba da kuka.
Aliyu ya rasa me zai ce mini? Shi kam dabararsa ta kare kuma. Sai ya ce, “Ni kaina Fa’izah yanzu ba na ce miki ga hakikanin inda Fa’iz yake ba, rabona da shi tun ranar da ya dawo”.
Da lallami da ban baki gami da dabara irin na Yaya Aliyu yasa na tashi daga store na je na kwanta a gadon Hajjah. Daga Ummi har Zaneerah babu wanda ta yi gigigin shigowa don kam su tsorona ma suke ji. Yarinyar da za ta bude baki ta zage Hajjah cikin A.B ai abar tsoro ce, balle nasu iyayen karan-kada miya. Yau da Baban ABU ya ji kalaman nan da na kade har ganyayyakina.
Cikin daren na dinga shesshekar kuka ni kadai ina watangaririya a kan gadon Hajjah, daga wannan gefe zuwa wancan. Na turza na turza cikin kowanne lungu na zuciyata wurin bin shawarar Yaya Aliyu ta ki amince min da hakan, wato in kwantar da kai in roki Fa’iz Allah-Annabi amma na kasa.
Ya ya zan iya zub da mutuncina ga Fa’iz in nemi wani abu daga gare shi, ashe ma ya isa kenan! Never (fau-fau). Dole ne ma ya bani, in ba ta tsiya ba ta tashin hankalin da bai taba gani a rayuwarsa ba! Shima ya sani ko a lahira ba zamu yi makwabtaka ba balle zaman inuwa daya a duniya ko a lahira!!!
Wai ta ya ya ma Fa’iz zai nemi aurena, kamar yadda Yaya Aliyu ke cewa? Ni fa Fa’izah da ya tsana? Ni kazama dakikiya ‘yar Maimuna? Uhm! Ko don yanzu na yi idon gani na zamo abar kwatance cikin mata? Da da nake a ‘yar’uwarsa kankanuwar yarinya mai rauni da bukatar kulawar yayyu irin sa me ya hana ya kauna ce ni?
Ta ya ya yake tunanin ni Fa’izah zan mance kiyayyar da Fa’iz ya nuna mini tun ina ficiciyata har na kawo yanzu? Sanda yake aikowa su Ummi kayayyaki BAN DA NI. Ya tambayi lafiyar kowa BAN DA NI. Ya nuna banbaci kiri-kiri da fifiko tsakanina da sauran ‘yan’uwana...... Ya yabesu ni ya kushe ni..... ya zagi uwata a duk sanda ya so, ya dauko Ummi daga makaranta ni ya barni a jeji ko in mutu ko in yi rai ba damuwarshi ba ce. Ba don komai ba sai don saboda tsabagen tsana da kiyayya! Shin meye dalilin auren yanzu?
Don na yi girma na yi kyau na zama kyakkyawa..... Don na yi kwakwalwar karatu wadda a da bani da ita..... Don na yi kyawun da duk cikin A.B babu kwatankwacina balle tsarana! Kaico da masu halin son zuciya irin Fa’iz Giwa.
Wani da shan wahalar raino, ilmantarwa tare da real kauna ga Fa’izah shekara da shekaru bai samu ba sai shi. Wani da kwashe shekaru yana hidimtawa Fa’izah da inganta rayuwarta positively ba a bashi ba sai shi.
Ga masoyi na gaskiya irin Dr. N mai wuyar samu a wannan lokacin, mai sadaukarwa so da kauna dukkan hakkokin da Allah ya ce a basu bai samu ba sai shi. Tabbas muddin na yarda na zauna da Fa’iz ko na saurari wata kalma daga gare shi ko da guda daya ce na tabbata wadda ba ta san ciwon kanta ba, ba ta san darajar kanta ba, ba ta san darajar wadda ta dauki cikinta wata tara ta haife ta shayar cikin wahala da kakani-kayi. Muddin ban auri Dr. N ba na cika butulu duba da tarin kauna da soyayyar da ya mallaka mani, na zama mayaudariya.
Ya zama dole kenan in kaskantar da kaina ga Fa’izu ya warware igiyar da aka zarga a tsakaninmu? Juyawar da barin kaina yake yi ya tsananta cikin ‘yan dakiku, a yayin da zuciyata ta halarto min da cewa, rokon Fa’iz a bisa abin da bani da iko a kansa wannan dole ne! Kaskantar da kai ya zama dole gare ni, tunda durkusawa wada ba gajiyawa bane. Amma ba don ni ba illa don farin cikin Dr. Nazir Sani Galadanci.
****
A washe garin ranar idanuwana na bisa kofa, yinin ranar zungur ban ko leko falo ba, illa kunnuwana da na kasa suna zuko min duk mai shigowa da mai fita a gidan Hajjah ko zan ji muryar Fa’izun? Shiru! Har yamma. Kafin in ji Aliyu na ce da Hajjah “Fa’iz ya je Kano dauko Yaya Bashir”.
Hajja ta shigo dakin da nake kwance hannunta rike da kwano shake da gasasshen nama da ruwa-ruwan shi, an kuma barbade shi da yajin daddawa wanda ya ji kayan kamshin gargajiya mai dadi, ta zauna gefena a hankali da gani a darare take.
Allah sarki Hajjah! Duk zagin da ta sha bai sa ta yi fushi dani ba don ina ji da safe tana gayawa bakinta ‘yan taya murna da suka zo mata daga Zaria, kada wanda ya shigo ya ta dani barci nake a barni na huta.
Ita kanta ta fada fiyat! Kamar wadda ta tashi daga zazzabin kwana biyu. Ta ce, “Fa’izah ki yiwa Allah ki bude ido ki ci naman nan, na san kina jina ba barci kike ba, tun asuba nake aikin gasa miki don na san shi akdai za ki iya ci tunda kin ki cin komi tun jiya, shin baki tsoron irin ciwon Aliyu ne?”
Na yi mata banza na kara cusa kaina cikin filo na bude sabon kuka. Hajjah ta yi zugum da kwano a cinya, daga bisani ta aje shi a kasa ta ce, “In kin kin cin abinci wanka fa Fa’izah? Rabonki da wanka yau kwana hudu. Shin Fa’izu ya san wainar da kike toyawa ma, in don shi kike yiwa kanki wannan ukubar?”
Ban san sanda na zaro kai daga cikin filo ba na yi kutubal da shi na mike zauna, na ce, “Hajjah don na yi kyau, don na yi haske na daina kazanta na zama abin gani har a so ayi sha’awa Fa’iz ya ce miki yana son aure na ko? To daga yau duk wani abu da ya shafi gyaran jiki zuwa wanka na barshi har abada! Na koma Fa’izar da ya sanni a baya, kazama ‘yar Maimuna!!! In ce dai in na shiga warin hammata da warin baki ya ce baya so, ya je ya auro ‘yar Rasha ni kuma a barni da mai sona tsakani da Allah ba don wani abu da na mallaka ba....” Na ci gaba da kuka na gasken-gaske.
Hajjah ta ce, “Ayya Fa’izah, kin yi kuskure babba, zato zunubi ko da ya kasance gaskiya. Daga ranar da Hafizi ya bar Najeriya bai kara ganinki ba ko a hoto sai ranar da ya dawo bayan an daura muku aure”.
Da hanzari na tari numfashinta, “Tunda haka ne ki kwance auren mana ko dole ne? Na ji ko da ban auri Dr. Nazir ba na yarda na amince ki hada ni aure da Malam Hassan maigadin gidan Baban Kaduna, ko Isa direban gidan nann....”
Hajjah kam ta koma yi min dariya, ta ce, “Yo ai shi kenan, wannan abu mai dan karen sauki. Sai ki je wurin Hafizin ki amso takarda ki kawowa Ahmadu da ya kulla auren ku, ni kuma na yarda ayi aure da Malam Hassan maigadi tunda ai mutumin kirki ne bawan Allah, ko ba jinina bane na san asalinsa da tushensa, na zauna da shi tun ba a haifeku ba, babu cuta ba cutarwa”. Ta mike ta fice ta bar kwanon naman a wurin yana ta turiri da kamshi.
Na dade ina juya maganar Hajjah bayan fitar ta. Don me kowa na ce ya rabani aure da FA’IZU ABUBAKAR sai ya bude baki ya ce in amso takarda wurin sa? Bayan suna da masaniyar cewa ba zan taba iya rokon Fa’iz wani abu ba, ko kalma ta hadani da shi a kafatanin rayuwata?
Ni na kai masa auren da zan je na karbo ba su suka kai ba? Don me su ba za su je su karbo ba in har da gaske suke suna son gyara kuskure da laifin da suka yi mini wanda ba zan iya taba yafe shi ba ko in amince da shi? Don me sai na karbo takardar aure zai warware ina ce in an maidawa Fa’iz sadakinshi shi kenan aure ya warware?
Cikin kuka na fitar rai mai soya zuciya na ce da Hajjah, a lokacin da na mike na bita har uwar dakin barcinta tana shirin ta da sallar walha.
“To ki bani sadakin mana ki gani in ban mayar mishi ba?”
Tana kokawar sanya hijabin sallarta ta ce cikin alamun nuna gajiyawa da magana daya, “Shin ni Hadiza meye nawa ne cikin lamarin nan Fa’izah? Sadaki dai Barau ya karba, bayan daurin aure kuma ya dankawa ubanki na Zaria. Saboda haka su za ki je ki yiwa wannan tijarar da kike yi mini amma ni in kika sa min hawan jini Allah zai saka mini....”
Ta soma kokarin fashewa da kuka. Na juya na fice da gudu na bar mata dakin tun Allah bai jeho wani cikin ‘ya’yanta ya aika dani lahira ba tare da na kara sanya N.S a idanuna ba.
****
BIKI-BIDIRI
Ga al’adar mutanen Giwa da yammacin Laraba ne muke kamu, washe gari alhamis kuma ayi budar kai. Don haka ban yi mamakin jin hargowar jama’armu ba daga ko ina cikin garin Giwa, Zaria, Kaduna da makotansu sun cika A.B Estate. Masu kidan kwarya sun soma wasa korai da gyaran murya cikin lasifaka, masu guda na yi, maroka na ma Hajjah kirari duk inda ta gifta.
Na tabbatar dai al’amarin nan da nake dauka almara nema yake ya tabbata, za su hadani rayuwa da Ya Fa’iz ne ko babbaka su zan yi. Lallashin ma babu mai lokacin yi min shi, shima Yaya Aliyun tun ranar da yasa kafa ya bar gidan ban kara jin ko tashin muryarsa ba.
Ummi da Zanirah babu wacce ta kara shiga sabgata, na kan ga dai Fa’iza ‘yar Zanirah ta rarrafo dakin da nake tana wasanta, ta yi ta gaji ta fita ko sanin da halittar dan Adam bana yi a dakin, domin ruhina da kulliyar tunanina baya wannan duniyar tamu, yana cikin wata duniya ta kunci, azaba da tafasar zuciya da zabalbalar kwallah.
A yau na yi amanna da cewa, zan zama matar Fa’iz in na bari tsofaffin nan suka shafa min lalle. Na yi tunani iyaka tunani bani da mafita, bani da mai mara min baya, babu mai duban hujjata da idanun basira in dai a kan Fa’izu Abubakar ne. Wani yaro cikin ‘ya’ya da jikoki da suke matukar so duk da tarin aibobinsa. Don haka na yakewa kaina mafita ta karshe.
Na janyo (travelling bag) dina na shiga shirya kayana da ba za suyi min wahalar dauka ba a gurguje.
Adda Hanne kanwar Maman Kaduna da tawagarsu suka yane labule suka shigo da guda da sallama, duk suka cika dakin taf! Tsokanar duniya babu irin wacce basu yi min ba, in gadon dakin ya daga ido ya dube su to nima hakan. Kaya nake ninkewa daga sif ina dannawa a jaka.
Adda Hannatu ta yi kwafa ta ce, “Ke ‘yar tawaye, mun zo kama ki ne kinyi kamar baki ganmu ba saboda kin isa”.
A yayin da ta bincire hancin kwalbar turare “intimately beckham” suna ta raha suna darawa cike da unexpressable nishadi da farin ciki bayyananne a zuciyar su da fuskokinsu.
Na dago jajayen kumburarrun idanuna na yi musu wani kallo a kaikace ta kasa-kasan ido a hankali na ce, “Ku kama uwarku dai”. A yayin da na sunto dankwalin kaina na yi damara a kugu gashina dake daure cikin (bound) ya sunce gaba daya ya cika fuskata da wuyana baki daya, ban damu ba, ban kula ba, jikina har tsuma yake ina jiran mai kwarin kashin da za ta fara matsowa gare ni.
Adda Hannatu ta ce, “Eye! Dambe za ki yi damu Fa’izah! Lallai da aka ce kin haukace ashe ba ayi kuskure ba. To bismillah ma ga mai kwarin kashi tsakanin ni da ke”.
Zaneerah cikin zafin cewa da na yi su kama uwarsu ta ce, “Eh, uwarmu zamu kama mana, tunda dai babban Yaya uba ne kamar yadda matar babban Yaya ta zama UWA...... wadda za ta cika mana gida da ‘ya’ya ta sauke tukunya ta dora mana abinci...... ta sa mana kula ta sabe mana babbar riga ta yiwa ‘ya’yanmu tarbiyyah irin ta gidanmu ba irin tata ta rashin neman albarkar iyaye da son gamawa da duniya lafiya ba.......”
Daga haka suka shiga kwararo min turaruka ta ko’ina gaba da bayana har tsakar kaina zuwa yatsan kafata, har kuma cikin idanuna.
Ashe dama kowaccensu da guzurin abinta cikin mayafi, ba Adda Hanne kadai ba. Azabar turare cikin kwayar idona ta rudani ta gigita ni na soma kara ina murza idanun da dukkan hannuwana, ina fadin “Idona.... idona..... wayyo Hajjah sun fasa min ido”.
In sun fasa to ke da baki nan kin fasa karatun nan, sai dariyarsu suke. Kasa na sulale na kwanta ina birgima ina murzar ido dake neman tsiyayewa.
Sai da suka kusa karar da kwalabensu kana na sha duka kitif-kitif-kitif daga hannun kowaccensu, wai ban yi wanka da kwalliyar tarbarsu ba sai zagin da na yi musu guzuri da shi.
Kai wannan rana na ga wulakancin duniya da takaici da bakin ciki wanda ke kokarin fin karfin juriya da karfin halin da nake tinkaho da su. Nake amfani dasu ko yaya ne wajen ganin na kwato hakkina daga iyaye da dangina na A.B baki daya.
Sai da idanuna suka lafa daga zugin da suke yi min na kuma tabbatar da basu tsiyaye din ba kamar yadda nake tsammani. Na shiga toilet dinmu wanda dama like yake da dakin barcinmu na wanko fuska da ruwan famfo mai sanyi, tuni zuwa lokacin an kece da kidan kwarya mai dadin amo da dadin sauraro.
Wanda sautinsa ke amsa kuwwa cikin kwakwalwata yana zabalbalar min da ita. Ji nake shine amo mafi rashin dadin sauti da na taba