Showing 9001 words to 12000 words out of 43747 words
Chapter 4 - Zumuntar kenan Book 2 by Sumayya Abdulkadir Takori Kabara.txt
Kano”.
Ummi ta zare ido cikin firgici da kaduwa. Ni kuwa sai na rungumeta ina murna ina fadin “Don Allah Mama waye angon?”
Mama ta ce, “Da masoyinta mana mai sonta tun tana karama”. Babu wanda zuciyata ta kawo min sai FA’EEZ MUKHTAR ABUBAKAR BAMALLI GIWA!”
Ban san sanda na ce, “Amma a rasa wanda za a bawa Ummi sai Fa’iz?”
Sai bayan na fada ne na tuna cewa, UWA da UBAN da suka tsugunna suka haifi Fa’iz ne a gabana. Suna zaune ne idanuwansu cike da kauna, kuma suna son dansu kwatankwacin yadda kowanne iyaye ke son dan da suka haifa duk munin shi ko munin halinshi. Ya yin da ni nake kokarin aibata musu shi a gabansu.
A sanyaye na ce, “Allah ya sanya alkhairi”. Cikin sanyin jiki na wuce daki zuciyata cike da sake-sake. Wani bangaren tausayin Ummi nake ji. A ganina sun cuce ta sun aura mata mutumin da bai cancanci a hada auren shi alkhairi ba. Sai na tuna Ummi fa na son Fa’iz, kuma so hana ganin aibu.
Yadda nake son Dr. N da tabban da yake da shi, haka Ummi ke son Fa’iz da kowanne tabo mai alaka da shi da halinsa. Iyayenmu suka bini da kallon nazari ganin yadda yanayi na ya sauya gaba daya a lokaci daya.
Wajejen karfe hudu na yamma masu aikin gidan ke ta kaiwa da komowa sun kasa zaune sun kasa tsaye. Suna diban katon-katon na lemuka suna jerewa a firizan dake dakunan Baskwata (boys quaters) guda biyu dake like da juna.
Na dan matsa na leka, ko falon dan ‘Prince Charles’ sai haka. Kwata-kwata falon bai yi kama da sauran falukan da na saba gani ba a wurare daban-daban. Komai na falon cream colour ne in ka dauke kayan kallo bakake samfurin SONY, hatta ‘curtains’ (labulaye) cream colour ne. Haka sauran kayan alatun dake falon.
A.C har biyu, ta tsaye (standing A.C) da ta manne a bango (split), sai sassanyan kamshin (Bakhour) da Yahya ya sanya a dakin ke tashi. Kujerun (leather) ne suma cream colour masu laushi. Yadda wannan dakin yake, haka na kusa da shi yake komai da komai, sai bambancin kala. Na daya dakin ruwan makuba ne (grey).
“Shin Yahya Baba amarya ya yi ne?”
Sai ya kyalkyale da dariya, “Mama ce za ta bari Baba ya yi amarya?”
“Yo ina na sani? Na san dai ba naku bane, duk da gasu a Baskwata”.
Ya kara kyalkyala dariya, “Kin manta ne gobe su Yaya Bashir da Yaya Fa’eez za su dawo? Sai dai Bashir ya kammala, Fa’iz ma’aikaci ne ganin gida kawai zai zo”.
Na ce, “Hummm! Lallai. Ni za ni in kwanta, anjima in su Baba za su koma Giwa kasa a tashe ni don Allah”.
Ya ce, “Insha Allah”.
Na juya zuwa cikin gida zuciyata cike da sake-sake. Da mamakin kaunar da Baban Kaduna yake yiwa ‘ya’yansa (beyond comment) sunan wani ganyen shayi. Abin haushin dukkansu babu na gari, don gara ma Bashir din shi shaye-shaye kawai yake. Shi dayan munin hali har ba a magana.
Sai dai duk yadda na so in yi barcin Ummi ba ta barni ba. Hakika tana cikin farin ciki da ban taba ganinta cikin irin shi a duniya ba. Murnar auren ta da masoyinta Fa’iz Allah ya cika musu burinsu. Ta yi kukan dadi, ta yi na sosai. Duka dalilin daurin aurenta da Fa’iz gobe......”
Na yi murmushi na ce, “Ki yiwa Allah ki barni in yi barci, ki bari ya dawo sai ku yi tare tunda karfe daya baya amo. Ki barni da abin da ya dame ni fargabar zuwan iyayen Dr. N, don ban san irin tarbar da Hajjah za ta yi musu ba”.
Ta ce, “Matsalarki ce wannan”.
Karfe bakwai na magariba muka bi Baban Giwa sai Giwa, Yaya Mufty ya wuce Kano. Tun daga gate din A.B Estate gaba daya komai ya canza, an sake fasalin ginin an mayar na zamani sosai, haka cikin gidan Hajjah an canza komai sabo dal kamar gidan amarya. An sake fenti gida kamar ba a cikin garin Giwa ba kamar a Lagos ko Abuja.
Irin wannan sauyin na A.B Estate na faruwa ne a duk lokacin da A.B family za su yi wani gagarumin biki. Na ce, “Uhm! Ummi ana ji da aurenku tabbas”. Ta ce, “Fadi da babbar murya”.
Abin da ya bani mamaki yadda su Inna Kubra, Indo da su Kaltume da sauran kannenmu na Giwa ke min oyoyo da (AMARYA).... Ka ga amaren sai kyallin goshi suke.... ni dai murmushi kurum nake ina cewa cikin raina “Auren Ummi guda ai dole a kiramu Amare, tunda mune Amara kirazan biki”.
Idona bai hasko min kowa a falon ba sai Zanirah, rungume da buleliyar ‘yarta tana shayar da ita. Yaya Aliyu na gefenta yana waya. Habawa! Da Zanirah ta cizge ‘yar a nono ta dangware masa a cinya ta yi wani tsalle muka dire a tare muka makalkale juna bayan mun shararo a guje muka shiga juyi a tsakar falon Hajjah.
Wai! TAKORI ta ce, TUNA BAYA SHINE RIKO!
Yaya Aliyu ya mike rike da ‘yarsa ya hau Zanirah da fada..... “Wai ke baki da hankali ne? Kashe min ‘yar za ki yi? An girma ba a san an girma ba, kuna abu kamar kananan yara? Ko su Hanifa ba za suyi wannan shirmen da kuke yi ba....”
Zanirah aka kwantar da kai aka shiga lallashin maigida... “Haba Baban Fa’izah! Shekaru uku currr! Ni, Fa’iza da Ummi???”
Yaya Aliyu ya yi murmushi yana ci gaba da jijjiga Fa’izar don ta koma barcinta da hayagagar mu ya katse mata, don shi dama fadan shi baya nisa. Ya koma ya zauna ya ce, “Fa’izah ya karatu? Shi kenan an kare ko?”
Muka dubi juna ni da Zanirah da Ummi duka muka yi murmushi. Na mika mishi hannu ya bani diyata kuma takwarata Fa’izah. Na dauke ta na sumbace ta na kura mata ido. Allah kareem dani yarinyar take kama sosai, ko da yake dukkanmu kamar tamu daya ce.
Na ce, “Ya Allah ka raya mana little Fa’izah”.
Kowa ya yi murmushi ya ce, “Ameen”.
Yaya Aliyu kallona kawai yake, na san ba zai wuce mamakin kyakkyawan girman da na yi ba.
Na samu Yaya Aliyu a kofar gida kan fararen kujerun roba yana yiwa ‘yar shi wasa, na labarta mishi zuwan dangin manemin aurena Dr. Nazir gobe.
Yaya Aliyu ya yi shiru yana mai nazarin zancena. Akwai wani yanayi a tare da shi ya kada min ‘ya’yan hanji, wani yanayi da na kasa fassarawa. Yanayi ne mai nufin “BA ZAI TABA YIWUWA BA!”
Na yi zugum! Ina dubansa hannuwa a kumatu zuciya cike da taraddadi. Ya yi ta maza in ji mata ya ce, “Fa’izah kin yi babban kuskure da kika saka soyayyar Dr. Nazir a ranki, alhalin kina sane da cewa babu auren (na gani ina so) cikin zuri’armu. Balle auren bare, wanda ba a taba ko da wasan kwatantawa ba. Tun bayan na mahaifiyarki wanda ko shi tunda ran A.B ne.
Shin abin da ya faru a baya ni dake bai ishe ki ishara ba? Ki guji mu’amalar soyayya da kowa ki baiwa Allah zabi cikin al’amuran rayuwarki baki daya?”
Idona ya cicciko da kwalla kadan ya rage su shimfido a kundukukina, na ce, “Yaya Aliyu ka taimake ni ina son Naziru, ina tsoron halin da zan shiga in na rasa shi. Fadar A.B ba fadar Allah ba! Bani da wanda zai taimaka min ya shige min gaba idan ba kai ba. I cannot afford losing him...”
Yaya Aliyu ya zuba min ido na san mamakin halinmu na mata yake yi, a raina na ce, “Har an fika Aliyu Haydar?’
Ya saukar da kai bisa yatsun Fa’izah karama dake bisa cinyarsa, ya ce, “To ni dai Fa’izah babu abin da zan iya a kan wannan rigima da kika je kika jajibo. Zan yi dai iya kokarina in ga cewa ba a yiwa dangin Nazir wulakancin da za su tafi damu a baki ba idan sun zo. That is all. Ki jira hukuncin Hajjah a gobe”.
Tun daga nan jikina ya kara yin la’asar. Na tashi na bar Yaya Aliyu don a ganina ba shi da abin da zai iya yi min din da gaske kamar yadda ya ce. Karfe tara na dare na kira Maman Kaduna nake sanar da ita zuwan dangin Nazir a gobe, don na manta ban sanar da ita a Kaduna ba.
Na kare da cewa (cikin murya mai ban tausayi) “Mama na san ko da kowa bai goyi da bayan in auri Dr. Nazir ba, to ban da ke don ke uwa ce mai son duk abin da ‘ya’yanta ke so. A ganina lokaci ya yi da za a kawo CANJI a kan auren zumunci da ake tilasta mu yi, domin ZAMANI YA CANZA.
A duk lokacin da zamani ya canza, dolen al’umma ne ta tafi tare da canjinsa in har tana so ta ci gaba. Auren zumunci ba laifi bane amma idan akwai son ran ma’auratan, in ko babu na daya daga cikinsu ya zama auren MUGUNTA, domin dole za a zalinci daya.
Ke kadai kika rage min da zan kawowa kukana ki share min hawaye...... ki taimake ni Mama su amshi maganar Dr. Naziru da muhimmaci da karramawa. Wallahi ina sonshi Mama ba zan iya hakura haka in barshi ba a kan tsarin Hajjah... Ki taimake ni Mama don Allah, he’s the stranger that I’m always praying for!”
Mama shiru ta yi na lokaci mai tsawo, kamin ta aje wani gwauron numfashi wanda ya kara samun suspence ya sagar da gwiwoyina. Domin numfashin da Mama ta sauke na nufin ba za ki taba cin nasara a soyayya ba Fa’izah. Ba za ki cimma ko daya cikin burarrakinki a rayuwa ba.
A karshe ta yi tashin gwauron zabi ta murje jin nauyi da kawaici ta ce, “Fa’izah! Sai dai ki yi hakuri kam. Amma wannan yaron BA ZA KI AURE SHI BA! An riga an yi muku mazaje ba tun yau ba”.
Da maganganun Mama na kwana zuciyata jagule ta kasa sukuni. Wadanne irin mazaje Mama ke ikirarin an mana? Mu bamu sansu ba? Mama na nufin ba zan auri Nazir ba? Mama na nufin ba zan taba cimma burirrikan rayuwata ba? Ya ALLAH ka sa kada shima in rasa shi kamar yadda na rasa Aliyu-Haydar. Ya Allah kada ka nuna min wannan ranar..... ranar da za a ce shima Dr. N na rasa shi.
Ni sai yanzu ne ma na san ina son Dr. N, hankalina ya yi matukar tashi da al’amarin dake shirin faruwa dani. Ya ya zan yi iyayena su amshi Dr. N? Na yi tunani iyaka tunani bani da mai mara min baya cikin dangina kakaf, kowa tsoro yake kada in shafa mishi kashin kaji.
Na yi kuka na yi kuka har na ji babu dadi, idanuwana suka shiga yin wani yaji-yaji saboda kuka. Tunanin halin da Dr. N zai kasance in ya tsinci labarin ba za a bashi ni ba, da wanda nima zan kasance da abin da iyayena ke nufina da shi, shine babbar damuwata. Shin me ya mantar dani matsalar gidanmu tunda fari? Na yi zurfi a son Naziru? Me ya mantar dani rigimar gyatumar mu mai ran karfe? Babu ko tantama SO ne, SON NAZIRU ne.
Ya makantar dani ya kurmantar dani har bana iya tunanin me zai je ya zo, har bana tuna baya balle abin da gobe za ta haifar. A wannan rana na yi fatan a ce ina ma ban fito daga A.B family ba! Ina ma ban kasance cikin zuri’ar Abubakar Bamalli Giwa ba
[6/3, 4:13 pm] Takori: Surutun Hajiya kara kular da shi yake. A kufule ya ce, “To na ji Hajjah, in ta farfado din sannan ki san abin yi ko ba yanzu ba da lafiyarta ake nema ba komai ba”.
Hajjah ta wuce tana fadace-fadacen ta da mita wanda Fa’izu bai saurari ko daya daga cikinsu ba.
Pilot Fa’iz Giwa babu abin da ya gama shi da asibiti. Amma tsabar kishin kada Aliyu ya daukar mishi mata ya gwammace kada a kaita asibitin. Shi kam yanzu ya fara son Fa’izah ma da damarar rayuwa da ita. Sai dai ta mutu su je lahira suyi aure su zauna tare, amma Hajjah ta canza masa farat daya kamar ba Hajjar shi ba wadda ta fi kowa son shi a duniya including iyayenshi, ta fi shi son duk abinda yake so, ta fi kowa farin ciki da ya ce a aura mishi Fa’izah ba. Ta yi murna, ta sa mishi albarka har da kukan farin cikinta. Amma da ya dubi halin rai kwakwai mutu kwakwai da Fa’izar ke ciki sai ya yi mata uzri.
Firjin dake gefe ya bude ya fiddo ruwa mai sanyi ya zuba a kofi ya tsugunna ya karanto Ayatul-Kursiyyu, Falaqi, Nasi da Ikhlas. Ya karanto karshen Suratul Al-Imran wato daga (Rabbana faghfirl lana wa af-anna) ya karanto ayoyin karshe na suratul Hashri tare da addu’ar Yusuf (A.S) a lokacin da ya shiga kunci a kurkuku, da addu’ar Yunusa (A.S) duka ya tofa a cikin ruwan, duk wata addu’ar yayewar kuncin zuciya da ta zo bakinshi ya tofa a ciki.
Ya shafe min fuska da ruwan har cikin kirjina dai-dai santar zuciyata. Na lumshe ido a hankali amma ban motsa daga yadda nake ba, Fa’iz ya samu kanshi cikin tsananin rudewa da firgita, bai san sanda ya kwalawa Ummi da Zanirah kira ba.
Dama suna falo suna ta tsuma. Zanira a guje Ummi da sassarfa suka fado dakin. Ya ce, “Shi kenan da gaske ne ta mutu, ku ce da su Baba su zo su binneta....” Fa’iz kuka yake sosai da hawaye da zuciyarsa. Haka Ummi da Zaneerah. Ko kusa da Fa’izar sun kasa karasawa.
Aunty Hauwa ta shigo dakin da saurinta, da alama zuwan ta gidan kenan. Tana ta fada kamar ta ari baki, “Wane irin hauka ne wannan Fa’iz? In ka hana Aliyu kai Fa’izah asibiti me kenan ka yi? Ko meye ribar ka cikin hakan? Wai ma tukunna Fa’iz da na sani ne kuwa? Crying for the sake of Fa’izah’s unconsciousness?”
Ta yi murmushi, duk ita daya ta ciccibeni gaba daya ta yi waje. Fa’iz bai ce komi ba, illa rakamu da kyawawan idanunsa dake cike da hawaye sun kuma kada sunyi jair. Sai kuma ya tashi da hanzari ya bita. Aliyu ya yi dariya ya aje little Fa’izah ya bisu ya ja motar zuwa asibitinsu wanda ke bayan gidan duka cikin A.B Estate wato A.B Clinic and Maternity.
Likitoci biyu ne suka rufu a kaina suna kokarin ceto numfashina. Fa’iz ya shiga kai kawo tsakanin gabas da yamma, kudu da arewa. Ya yin da Aliyu ya jingina da kofar (Emergency Room) da nake ciki yana hango fuskata cikin (oxygen) da aka makala mini.
Aunty Hauwa ta yi tagumi a kan kujera ta rasa abin da yake mata dadi. A haka jama’ar gidanmu da ‘yan daurin aure duka suka taddamu wannan ya harari Fa’iz wannan ya tausaya mishi, babu wanda ya iya ce masa ko da sannu da zuwa bayan shekaru masu dama da suka kwashe basu sanya shi a idanunsu ba. Shi kam Babana kujera ya samu ya kame yana kallon kowa daya bayan daya.
A lokacin Baban Kaduna wato Alh. Mukhtar ya iso asibitin. Da Dr. Habib ya fito ya nemi son ganin daya daga cikinsu Baban Kaduna ne ya shiga.
Ya ce, “Muddin Fa’izah ba ta farfado ba nan da awanni uku, to zai yi wuya in ba coma bane ta shiga. Sannan jininta ya hau, mugun hawa kuwa, zuciyarta ta tabu. Kokarin da muke yi yanzu shine na jininta ya sauka, numfashinta da bugun zuciyarta su dawo dai-dai. Na roke ku idan an samu Fa’izah ta farfado ku guji gaya mata awkward incidence ba ta hanyar da ta dace ba. Domin sudden unpleasant shock ya kan harbi kwakwalwa har ya haifar da depression’.
Baba Muntari ya shiga sharar zufa, babu shakka ya shiga tashin hankali. Ya ce, “Ba komi likita, shi kenan ai in an samu ta farfado din shi kenan. Kuma ni ban san abin da aka gaya mata na tashin hankali ba, aurenta kawai aka daura da dan’uwanta yanzu-yanzun nan, bayan wannan ban san komai ba, dama can tana da makamancin ciwon hawan jini ko (something associate) ne bamu sani ba?”
Dr. Habib ya ce, “Lafiyarta kalau. Sudden shock ne wanda zuciyarta ta kasa karba kawai. To ko auren ne ba ta so?”
Baban Kaduna ya ce, “Mai yiwuwa. Biri ya yi kama da mutum, domin wasu daban sun zo neman auren ta. Bari in je in same su in ji”. Ya mike ya firto fuskarshi babu annuri sam.
Barau ya kira gefe suka yi magana don da shi ya fara cin karo, ya kuwa gaya masa komai a gurguje cewa, Fa’izah ba ta son Fa’iz tun tana kankanuwa, Fa’iz ya tsani Fa’izah, tunda aka haifeta basu taba zama a inuwa daya ba dai-dai da sakan daya. Aliyu ta so ta aura kuma da bata samu ba ta dangana saboda Zaneerah. Tun sanda Hajjah ta fara fito da zancen ya same ta cikin sirri ya ce kar a soma wannan kada gyara zumunci ya zama bata zumunci.
Su da aka yi musu haka suka zauna lafiya, to fa in babu soyayya a tsakani haka babu kiyayya, kuma su na jiya ne ba na yau ba, zamani kullum canzawa yake yi. Zai fi kyau a dinga karbar canjin da ya zo da shi idan babu sabon Ubangiji ko halaka a cikinsa”.
Jikin Baba Muntari sanyi kalau kuma ransa ya baci domin shi ba haka Fa’iz da Hajjah suka gaya mishi ba kafin ya karbi waliccin auren nan. Ya dauka cewa ko da hakan (doctrine) din su ne kuma umarnin Hajjah ne, to babu wani abu makamancin wannan tsakanin Fa’izu da Fa’izah.
Ofishin Dr. Habibu ya koma ya dauko takarda da biro ya fito ya doshi Fa’iz wanda ke tsaye gefe yana kallon su cikin dimuwa, don ya amince ba ALHERI Baba Barau ke gayawa Baban Kaduna ba, ganin yadda fuskarsa ma’abociyar kamala ke tattarewa tana yamutsewa.
Don haka ganin ya nufo shi da takarda da biro fuskarshi babu alamun rahama, sai ya ji hanjin cikinsa suna dunkulewa wuri guda.
Fa’iz ya daga dara-daran idanunshi da suka kada suka yi jawur ya dubi Baba kallon rashin fahimta, ya motsa baki zai yi magana amma ya rasa me zai ce ne.
Baba ya ce, “Karbi ka rubuta min saki uku yanzun nan Fa’izu”.
Fa’iz ya ja da baya ya soma hawaye ya ce, “Baba Fa’izah za ta farfado