Showing 39001 words to 42000 words out of 43747 words
Chapter 14 - Zumuntar kenan Book 2 by Sumayya Abdulkadir Takori Kabara.txt
kafarki-kafarshi zuwa Russia, wallahi nima na daina lallaminki, mu zuba mu dake aga wanda ya haifi wani. Dabba kawai, shashasha, mara hankali".
Na ce, "Ko uwar Rasha ne ba zani ba, wallahi ba zani ba ko gunduwa-gunduwa za'ayi dani".
Rabi tayi dariya, "Ai har uwar Rashar ma zaki, tunda matukin jirgi kike aure ina ne ba za'a saka ki a jirgi a kaiki ba?"
Na ce, "Koda na rasa bawan Allah Dr. Nazir, mai ilimin da ya amsa sunan ilimi, banga me zanyi da direba ba Ya Rabi. Kamar ni in kare a mutumin da bai da ilimin komai sai na tuki? Direban tasha, wallahi na yi asara!!!".
Rabi ta ce, "Kin kuwa yi asarar. Yanzu ke ko babur zaki iya tukawa ne balle aje ga mota zuwa jirgi? Ke kinga shegen bakin ki baya mutuwa, ni na gaji da magana don ba malamar jami'a bace. Ranar da ki ka bi Fa'iz daga ke sai shi na tabbata murus bakin zai mutu mu don kin raina mu ne ki ka cika mana kunne da babatu. Don haka sai anjima, mijina yana jirana. Sai mun zo rakiya filin jirgi...".
Tamkar ta soka min mashi a kirji haka naji.
"Ko kuma an aiko muku da sakon mutuwar danku kunzo zaman makoki ba? Ki sani, ranar da duk Fa'izu ya yi gigin sake sako kafarshi cikin gidanmu kamar yadda na dauke kafata daga nasu gidan, wallahi sai buzunsa Ya Rabi!".
Ta ce, "Ko? Lallai kin fitsare, inama ina nan za'ayi wannan (BOXING)? Kai da na kadawa (Winner) tuta. In kuma kanwar ta kar tsamin ne sai kiyo min waya inzo jinyarki".
***
Zaman Zaria fa yayi min zafi, Walida, Abdallah duk suna makarantar kwana. Kausar da Walid makaranta suke zuwa safe da yamma. Babu Ummi babu Zanirah balle tsohuwa Hajjah mai samu farin ciki. Ko da yake Hajjah ni na gujeta don a ganina ita ce ummul-haba'isin sanya rayuwata cikin halin kuncin da take ciki bayan shafa min bakin jini da hakan ya yi a idanun iyaye da 'yan uwana.
Daga uwata har ubana kowa fushi yake dani, Walida kadai ke kula ni a gidan, haka nan kullum Baba zai fita sai ya ce.
"Tunda haka kike so, wato ga dakin uwarki ga naki, inta wuce dakina ki bita da ido kina kissime-kissime ai sai kiyi ta zama".
Wannan magana ba karamin kona min rai take yi ba, tun ina kuka har na saba. A zuciyata kuwa Allah Ya isa ga Fa'iz tafi dubu biyar.
Na rame, na fige, na zama 'yar firit dama jikin ba wani jiki ba. Nayi niyyar komawa Giwa amma na kasa saboda kurarin da nayi a baya cewa ba zan sake zuwa gidan Hajjah ba. Wuri daya ne nake tunanin idan naje zanji sanyi, wato wurin Maman Kaduna, to amma in ina da kunya ai bana dosheta ba alhalin kiyayyar danta na neman zauta ni. Ko babu komi ranar da Fa'izun ya ga damar dawowa me na isa nayi mishi akan idon uwarsa? Gara dai ya kwaso jiki ya kawo namu gidan.
Haka Zanirah da Aliyu suka yo min waya wai hakuri suke bani abinda suka yi min ranar bikinmu a Giwa su wasa ne suke min. Tsaki nayi na kife wayar nayi tagumi da hannu bibbiyu.
Bayan kwana biyu kuma, sai Ummi da Bashir suma suka bugo, amma su ba hakurin suke bani ba, korafi suke wai naki inje inga gidansu, to inzo in raka Ummi awo tana da ciki dan sati biyu.
Na ce, "Sai ku bari ya cika wata daya tukunna mu fara zuwa awo, kunji ko 'yan abu kazan uba marassa kunya".
Ummi ta ce, "Da fatan (this very big) ashar (is for me alone not with my husband) don mu albarkar miji muke nema ba ma zaginsa".
Watanni biyu suka shude tun ana zuba ido har kowa ya gaji babu Fa'iz babu duriyarshi, babu ko wayarsa. Don haka na yanke shawarar tunkarar Baba da shawarar da na yanke, wato komawa karatuna a Kano.
Da farko baban ya fara ne da zunduma min zagi bayan ya gama saurarona, kana ya ce.
"Sai dai in karuwanci kuma za ki sannan in barki, tunda kin ki zaman aure. Sannan ina mai tabbatar miki muddin ya kasance wani mummunan abu ne ya samu Fa'iz sakamakon raunin da kika yi mishi da kwalba, to ki tabbata sai na rotsa miki kwalbar 7up a wannan kodaddiyar fuskar da kike tinkaho da ita. Kazalika in Fa'iz yayi zuciya ne yaga cewa gara ya fasa auren, sai na dauke ki ke da kayanki na kai mishi sadaka, ko aikace-aikacen gida ne kiyi masa.
****
A WALES (UK)
A bakin wani (swimming pool) dake cikin hotel din da suke ciki cikin birnin Wales din kasar Ingila, bisa fararen kujeru da ‘yar jar lema da tayiwa kujerun inuwa ta rage hasken hantsi daga idanuwan wadanda ke zaune cikinta.
Pilot Fa'iz Giwa ne da Maajid da Johari tare da wasu abokan su wadanda duka matuka jirgin sama ne ke zaune suna karya kumallo bayan sun fito daga (interview) din da ta kawo su kasar Ingila da British Airlines. Maajid na shan (tea) cikin wani kankanin kofi, amma hankalin shi naga Fa'iz dake faman juya cokali cikin (coffee) mai zafi idon shi na kan wata siririyar baturiya dake sanye cikin dan kamfe da 'bra' kadai, tana tafiya lange-lange kamar zata karye saboda rashin kauri da kumari ko kuwa kamar da an busheta da baki zata fadi don sirinta. Amma a zahiri, idan ka dubi cikin kwayar idanunsa ba ita yake kallo ba, idanunshi ne kawai a saitin da take, tsabar tunani ke jagwalgwala kwakwalwarshi wanda kuma ke neman fitar da shi daga duk wani jin dadi da yake ciki ya kuma zamo barazana kuma ga walwala da farin-cikin sa, harma da nutsuwarsa da hayyacinsa cikin duk al'amuran da yake gabatarwa tun barowarshi gida wanda ba wani abu bane face kanwarsa/matarsa FA'IZAH A.A GIWA.
Wadda damuwa da al'amarinta da neman sanin hanyar warwarewar damuwar al'amarinta da shi ya zamo wani abu kadai da ya tsaya ya yi karantsaye ya addabi rayuwarsa. Har yake neman zautashi ba don ya kasance jarumi akan komai ba musamman wajen shanye damuwa komin girmanta.
(Still) idanunshi na kan Ba'ireshiyar cikin rashin sanin abinda yake yi ya dauki attaruhun kwalba ba tare da ya ankara ba ya zuba cikin kofin Gahwarsa ga zatonsa sukari ne yake zubawa. Maajid na kallon shi bai hana shi ba sai ido da ya gwalo kamar za su fada cikin kofin shayinsa.
Pilot Javed Saddyqy ya dubi Maajid cikin yamutsa fuska tare da nuna Fa'iz din da abinda yake yi da baki. Maajid ya kada masa ido alamar ya kyale shi. Idon shi daina kan Baturiya wadda ke ta faman yi mishi gizo da Fa'izah surarta na rikidewa tana zama Fa'izah. Ya sake daukar cokali ya motsa shayin yana shirin kaiwa bakinsa. Anan ne Suhayl Khan mutumin India ya ce da Saddiqy wanda shima Ba'indiyen ne cikin harshen Tamil.
"Fa'iz ya samu makuwa ne halan?"
Alama Saddyqy yayi mishi ta yayi shiru ta hanyar daura dan yatsarsa bisa lebensa, a lokacin yana rike da kofin ne a hannunsa amma tsayin mintuna uku bai kurba ba idanunshi akan Baturiya. Anan sai Javed ya sanya kafa ya dan take mishi yatsun kafarshi dake kusa da tasa, ya ce.
"Ba zaka sha bane?"
Fa'iz ya kai kofi da azama bakinshi ya yi mishi kyakkyawar zuka. Ba shiri ya saki kofin a kan tebirin ya ce.
"Aaah!".
Suka kwashe da dariya gaba daya, wadda zafin gahwah da zafin attaruhu suka hadu suka hana Fa'iz jinta duk da karfinta (dariyar tasu). Maajid ya samu abinda yake so, ya buga tebirin da hannunsa da karfi yana fadin.
" Woman na nufin WO! MAN, ka shiga uku kenan. In har baka dauko Fa'izah ba kun zauna a garin nan tare Fa'iz kai ba namiji bane ungulu ne da kan zabo, duk wannan cika da batsewar naka
[6/3, 4:13 pm] Takori: ****
A ZARIA
A wannan rana wadda ta kasances asabar din karshen watan Agusta cikin 'Area One', Walida da Abdallah duka suna gida sunzo hutun karshen zangon karatu na biyu daga makarantun su daban-daban.
Ina kwance cikin dakin Walida wanda yanzu ya zama nawa tunda ita ba zaman gidan take ba, sanye da riga da zani na atamfa mai karshen tsada (Exclusive Sharaton) ruwan ganye mai ratsin hoda, kaina ban daura kallabin atamfar ba yana dai ajje gefen gadon, na hade gashin kaina cikin tafkeken 'hair-bound ina karanta sabon littafin Takori ne mai suna 'KWANA SITTIN'. Zuciyata ta tafi gaba daya cikin rayuwar (schezophrenic_Safeenah) mai tsananin ban tausayi. A wani bangaren, ba Safeenar nake tausayawa ba kamar Kabir Danbatta, na rasa shi da Dr. Dangi wa yafi dacewa da amsar ragamar rayuwar Safeenah? Kowannen su masoyinta ne na hakika.
Muryar oyoyon da Walida ke yi ya katse min karatun, na bi hadaddun jakunkunan da Shu'aib ke shigowa da su dakin namu yana dora daya kan daya da kallo ina kissimawa cikin raina, wane irin baki ne muka yi masu tafe da jakunkuna 'classic' haka kuma har dozen? To kwana nawa suke nufin za suyi a gidan namu?
Kamshin sassanyan turaren (212) na maza ya sirnano cikin hancina, wani irin kamshi da ban taba jin mai sanyi da dadinsa a duniya ba. Wadanne irin baki ne momi tayi haka? Abinda nake tambayar kaina kenan.
Daga inda nake kwance na jiyo muryar ma'abociyar ginshira, na tambayar Walida ina Momi da Baba?
Walida ta ce, "Momi na gurin aiki, Baba na cikin makaranta. Amma Yaya Fa'izar tana ciki tana karatu".
Da murmushi fal a fuskarsa ya ce.
"Karatu? Ko dai kuka Walida?"
Ta ce, "Wallahi karatu take, kullum ma karatu take, ta je kasuwa ta sayo littattafan TAKORI na da dana yanzu, su take karantawa kullum, ta daina kukan tuni...".
Muryar FA'IZ, FA'IZ GIWA, FA'IZ MUKHTAR ABUBAKAR BAMALLI GIWA!
Da kwarin gwiwarsa ya yi sallama a dakin cikin 'husky voice' din da Allah Ya yi musu baiwarta zuri'ar Abubakar Bamalli Giwa bakidaya. Ya samu wannan kwarin gwiwar ne daga labarin da ya samu a bakin Walida masu nuna na kwantar da hankalina tunda har ina karatu? Duk da kwakwalwarsa bata fahimci littattafan TAKORIN da Walida take bayani akai ba, ya dai fahimci NOVELS ne wanda ba zai ce na Hausa ne, na Turanci ko na Larabci ba, tunda bai san mene ne ma'anar TAKORIN ba, bai ma taba jin kalmar ba cikin kowanne yaren. Abinda ya fahimta shi ne TAKORIN 'is an author' tunda yaji ance NOVELS dinta. Banda wannan kwarin gwiwar da ya samu ya samu karin na Momi da Baba duka basa nan yadda zasu ji dadin babbaka juna a wuta idan ta kama. Babu mai ceton dayansu. Yau za ayita ta kare (he can no longer tolerate it anymore!!! Kamar yadda ya ce da Mama ne ya zo daukar aurensa (dead or alive) haka yake har zuciyarsa.
In har littafin labarin SAFEENAT MAHMOUD ALKALERI wato KWANA SITTIN na Sumayyah Abdulkadir ya amsa, to nima Fa'izar da ake yiwa sallamar na amsa. Ya shigo kansa tsaye Walida na biye dashi kamar bakinta zai tsage don murnar ganinsa ta iso har gadon da nake kwance, da murnarta take fadin.
"Aunty Fa'izah ga Yaya Fa'iz!".
Wani irin kallo nayi mata wanda nake jin tunda Momi ta haifeta babu mahalukin da ya taba yi mata shigensa, ba shiri ta juya har tana cin karo da (stool) din madubi, saura kadan ta kifa.
Da sauri Fa'iz ya riko hannunta ya rike gam.
"Ina zaki matas? Ke da nazo muyi zance? Zauna hira za muyi kafin su Momi su dawo". Walida a daburce take, ya jata suka isa har gefen gadon da nake kwance suka zauna har rigarshi ta rufe min kafa kadan. In banda kamshin sassanyan turaren shi ba abinda ke tashi a dakin. Ya bige da tambayar Walida sha'anin makaranta tana bashi amsa a darare, kokarin zamewa take ta barmu yana kara shimfido mata tambayoyi akanta da kannenta su Waild, Kausar da yayanta Abdallah da nasu karatun.
Ganin ba zai barta ta tafi ba ta ce, "Yaya Fa'iz bari in kawo maka ruwa da lemo in kaiwa yaya Shu'aib abinci falo".
Ya ce, "Kada ki damu Walida, na cika cikina a Kaduna, haka shima Shu'aib. Yaushe Momi za ta dawo?"
Walida ta kalli inda nake bamu hada ido ba, amma taga yadda kwayar idanuna suka kada suka yi jajawur, numfashina ke sauka da sauri-da-sauri har wani irin huci nake kamar mesa babu rahma cikin su dai-dai da kwayar zarrah.
Walida ta kara rudewa ta ce, "Na jona ruwa a (heater) Yaya Fa'iz ka barni inje in kashe kada ya kone fada Momi zata yi min".
Ya ce, "To kiyi sauri nima ba zama zanyi ba, sako zan baki wurin Momi sai mu wuce".
Ta ce, "Toh".
Da saurinta ta fice har tana sake tuntube da dokin kofa.
Ya girgiza kai ya mike ya sauke ido a kaina, tsayin mintuna biyu yana kallona kawai babu ko kiftawa. Nima kallonsa nake, wani irin kallo da ni kaina na kasa fassara shi, na takaici ne ko na kiyayya koko na gara da Allah Ya kawo ka? Ni kaina ban sani ba.
Daga ni har shi babu mai niyyar daina kallon, duk da shima na kasa fassara nashi kallon. Shi ba kallon so ba, ba na kiyayya ba, ba na jin haushi ba. Yafi kama da kallon iko da raini. Ta wani fannin tamkar kallon, "Baki da yadda za kiyi dani" koko kallon "Nafi karfinki da ke da duk abinda kike takama da shi.
(In another notion) kallo ne na "Yarinya na ci dubu sai ceto, kiyi duk abinda za kiyi" Sai da ya mula don kansa ya ce.
"To ni Aunty Fa'izah zan wuce Giwa, tunda na iso Hajjah bata ganni ba, lefenki na kawo miki, wanda kowa ya kasa kawo miki tunda kin zama Faskari, mai faskarawa mutane kai. Sai tsarabar da nayo miki a tafiyar da nayi, tunda babu gaisuwa ko ta Musulunci a tsakaninmu.
Daman nazo ne in shaida miki zaman nan ya isa haka! Ranar (monday) kwana ki shidda kenan masu zuwa ki kimtsa kayanki da duk abinda kike bukata za ki tare a gidanki kamar sauran 'yan uwanki, don gaskiya fisabilillahi kin takurawa su Momi da alama har su Walida kin takura musu, nima kuma kin takura min. Haka kawai ina da mata amma bani da maraba da gwauro. Gara mu kauce haka muma mu manta komi, da duk abinda ya faru a baya, mu fuskanci sabuwar rayuwar dake tunkaro mu, muka kuma bude ido rana daya muka ganmu cikinta. Wato rayuwar aure. Sai mu rungumeta, mu kasance cikin godiyar Ubangiji da neman dacewa duniya da lahira".
Da ace Fa'iz yasan tashin hankali da bala'in da kalaman dake fita daga bakinsa suke kara jefani da ko da wuka a makoshi bai yi gigin furta su ba. Domin kalamai ne da ban taba jin mafi muninsu a duniya ta ba. (Hada rayuwa ta har abada da shi FA'iZ-ABUBAKAR) koko ince makiyina. Mugun dan uwa da kullum ketowar alfijir da faduwar rana sai nayi dakacen INAMA ban hada jini da shi ba.
Wani kwayan mutum guda daya da ya maida mahaifiyata marainiyar wayonsa, ya maida ni kwallon takawarsa a duk sanda ya so, ko gare-gare abin wasan yara.
Mikewa nayi gaba daya na littafin KWANA SITTIN ya fado daga ruwan cikina, na ce.
"Da uwar wa zaka tafi wurin direbancin?"
Tsalle daya nayi sai gani a bakin kofar dakin nayi maza na rufe na murza 'key' na zare shi na cilla shi waje ta taga cikin wani irin zafin nama da ni kaina ban san inada shi ba.
Ya yi maza shima ya cafe mukullin cikin irin nashi (exceptional) zafin naman wanda yafi nawa kafin ya kai ga ficewa ta tagar. Ya shiga sosa keya da (key) din ya daure fuska sosai kamar ba shi ne ya gama maganar da yayi cikin raha ba.
"Meye haka? Gafara ki bani hanya na wuce".
Na ce, "Wucewa kam zaka yi ta, tunda har ka yi nasarar amsar mukulli. Amman fa bayan rubutun saki uku ris a gareni FA'IZA A.A GIWA".
Murmushi ya yi, "Wannan ne kuma ba zaki samu ba har abada Fa'izah, har kuma yaumil-ardhi. Domin ban aureki don in saki ba. In haka ne tun farko ba zan fara ba. Karewa ma, ni ba lallaminki nazo yi ba kamar wancan karon, UMARNI ne ki hada kayanki ranar litinin za ki tare a gidanki kamar kowacce mace mai aure. Ba kuma neman afuwarki ko kiyi min uziri nazo ba tunda ke abu ba ya karewa a wajenki kamar cin kwan makauniya.
Ki matsa na ce, tun hannuna bai kai fuskarki ya yi mata tabon da bata da shi ba...".
Sunkuyawa nayi kafin ya kai karshen maganarsa na dauko littafin da Walida ta kammala rubutu dasu, na yago takarda a ciki na mika mishi.
"Ko da can babu wani wasa makamancin 'game' ko 'April-fool' da ya taba shiga tsakaninmu balle yanzu da kowannen mu ya mallaki hankalin kansa. Za ka wuce din babu haufi, kuma babu makawa, amma fa bayan ka yi rubutun nan". Na sake mika masa takarda.
Fa'iz ya sanya (key) cikin aljihun kaftanin shaddar dake jikinsa.
"Kenan har wani hankali kika mallaka yanzun? Ko daya! Kina nan yadda kike; Jiya 'i yau, kazama, dakikiya, 'yar kauye, mummuna. Don haka daina cewa wani wai kin mallaki hankali, ina hankalin yake nan kana tura kanka cikin jahannama kana ji kana gani?"
Na ce "In shiga wutar mana, tunda ba tare za'a sanya mu ba ina ruwanka?"
Ya ce, "Naga alama abin naki nema yake ya wuce na rannan, to ba zan rubuta ba kiyi duk abinda za kiyi".
Anan kam dankwalina na janyo nayi dammara dashi a kuguna kamar wata sabon hauka, na doshi Fa'iz da takarda har na iso gabansa. Sai dai kuma zuciyata cike da taraddadin murdaddun damatsan Fa'iz da na hango ta cikin kayan jikinsa. Ina tunanin idan ya cafke ni da su wa zai kwace ni? Babu kowa a gidan sai yara na kuma kama kofa na kulle? Da alama shima ya shirya yau.
Idona ya kyallo min biro a aljihun gaban rigarsa, na cizgo shi, na matsa gabanshi sosai har muna iya jin hucin numfashin juna. Kallon zakaru masu shirin dambacewa muka tsaya muna yiwa juna. Sai na samu kaina da ganin wautata anan, shin in nayi duka ta ina zai shigi wannan 'giant' din? Fa'iz kato ne sosai mai tsayi da kauri, kaurin da ba kiba ke haifar dashi ba