Showing 15001 words to 16780 words out of 16780 words
Chapter 6 - Sanadin Boko Book 2 Complete by Halima I Mashi .txt
abinda
kikeson ayi, in yaso in nazo zan gani. Ya mike zan tafi
gida, ga yar tsaraba nan. Ya nuna mata lader. Cikin
doki tace, amma na gode. To yanzu har zaka tafi
bamuyi wata fira ba sosai. Wani lokacin in nazo zan
dade. Ta rako shi har bakin gate in da hashim yake
tsaye da jamilu yayan fadi. Suka gaisa da jamilu, inda
ya shiga jin jina masa da cewa ya gode da wanan
jahadin da yayi a gurin lamido, inda ya samo musu
yanci. Abubakar yace au! Kai ma kayi farin ciki ne?
Jamilu yace, ba dole ba, don yarinyar da nagani
zuciyata ta so ba yar zuri‘ar mu bace. Son yarinyar ya
shige ni a kudu muka hadu da ita lokacin da muka je (N
Y S C) Allah ya shi maka albarka bayan bukinka zanyi
maganar tawa. Abubakar yace Allah ya taimaka, mu
kam bari mu tafi.
sati 2 tsakani da zuwan shi kano, lamido ya kirashi to
kasan lokaci yana gabatowa, don ha sai kafadi inda
iyayen yarinyar nan suke saboda aje a kammala da su
suma. Zufa ce ta soma tsatsafo ma Abubakar, amma
sai yace, am.....dama mahaifinta yayi tafiya ne shi
yasa. Amma idan ya dawo sai in fada muku saboda ya
riga ma ya san da maganar, kuma su a shirye suke.
Lamodo yace, to cike da damuwa ya fito, dole ne ya
koma kano gobe sai sai ya takurawa hafsa don yasan
abinda take ikirari zai hana auren su. Ya kira phone din
hashim yace, ka shirya gobe juma‘a zamu shiga kano,
sai mujuyo ranar sunday. Hashim yace, to
*******
Nikam tun ranar da abubakar ya tafi na shiga halin
kunci da damuwa. Na rasa dan ragowar farin cikin da
ke tare dani. Ina zuwa makaranta da gurin aiki, amma
bana iya cin wani abu. Ban amince ina son abubakar ba
sai yanzu. Har shadad yafini hakurin rashinsa, duk da
cewa sun shaku matuka. In nayi kamar in kira lanbobin
da ya bani sai in fasa. Nace, kai gara in koyi yanda
zanyiwa kaina fada, in hori zuciyata ta saba da rashin
sa kada in zurma da yawa in kamu da ciwon zuciya a
banza. Don nasan babu mai hankali da zaya aureni. Kai
akwai daran da na rabashi ina kuka. Ba zance irin
kukan da na saba bane, wannan kukan son abubakar
ne. Yau satin mu 2 rabon mu dashi. Ina zuwa ne cikin
aji, duk da hankalina yana gurin malamin amma har
yayi ya gama ba zance ga kalma 1 da yake fadi ba.
Tunanin Abubakar sadeek kawai nake yi. Na san abaya
na so munnir amma ban shiga irin wannan ma
tsanancin halin ba. Wani irin abubuwa nake ji game
dashi, waddanda ba zan iya fasrasu ba. Kenan da ba
son mannir nayi ba. Kenan da shirme nakeyi. Ya
rintace tasa nake ganin kamar son shi nake. Karshe ya
cuceni, shima dama ba sona yake yi ba sha‘awa ce.
Gashi dalilin abin da yayi min yasa na rasa abubakar
sadeeek.
har aka watse cikin aji ban sani ba. Da yake ni ba kawa
ko aboki gareni a makaranta ba, babu wanda ya kulani.
Kasancewar ko yaushe cikin daure fuska nake, masu
son kulani ma tuni sun watsar dani, saboda rashin
fuska. Ringing din wayata ne ya dawo dani daga
tunanin da nayi zurfi acikin sa. Jikina lakwas na dauka.
Nasan rahama ce, tunjiya take min nacin inje tana
nemana, ba tare da na duba fuskar wayar ba na kaita
kunnena. Muryar da tayi min sallama ce tasa naji na
watsake. Bansan na mike tsaye ba, ina cewa.
Wa‘alaikumus-salam. Yace, ina kike ne? Sai na samu
kaina da wani jan aji, ina tambayar wanene? Da sauri
yace, kina nufin baki ganeni ba ko? Nace, eh. Yace,
good! Ki fada min inda kike sai inzo in sameki. Nace,
ban gane kowanene ba ya za‘yi in fadi inda nake? Sai
kurum ya kashe wayar shi. Take naji haushin kaina,
mutumin da nake son gani ruwa a jallo amma yanzu na
tsaya salo. Da sauri na fita na nufi gida, ko in biya in
dauki shadad wai ina zaton yana kofar gidanmu. Ganin
bashi na juya da sanyin jiki na nufi makarantar su
shadad na daukoshi muka nufo gida. Hashim ya kali
sagir yace, kaima kazo muje mu 3 don mu sami
galabarta. Sagir yace, nifa shaknar hafsat nake ji, gashi
tana bani girma kada taga zamu matsa mata. Rahama
tace, ka daure kuje, kila ganin idonka ta sausauta.
Abubakar yace, nifa hafsat nasani tana sona. Dalilin da
take fadin cewa ba zai bari muyi aure ba shine nake
son ji. Sagir yace, to ku tashi muje. Suka mike yana
mitan cewa dan miskilanci irin na hafsa waima nine
bata gane ba yau. Hashim yace, kai dai wannan abu
yayi maka ciwo. Kasani ko kila bata gane kadin bane?
Sagir yace, wannan yanuna kai kadai kake sonta, ita
bata sonka kamar yanda kake zato. Abubakar yace
tabbas tana sona, amma ku muje dai.
Misalin karfe 8 na dare, Shadad ya yi barci, muna kan
tabarma a tsakar gida, ni kuwa lokacin zuciyata ta
kekashen idanuna sun bushe ina ta tunanin ina cewa,
"Ya Allah, dama haka so yake?" Na tashi zaune, na
mike tsaye, na jingina da bango duk banji dadi ba dai,
zuciyata tana tuhumata da cewa nice na bar dama ta,
me yasa na nuna ban gane shi ba? Sai kuma wata
zuciyar tace ki daina saka kanki cikin matsala, ba zai
aureki ba, keda kika yi cikin shege?!!!
Na koma na kwanta, hawaye na sintiri a idona daga
gefen idona zuwa kumatuna, so matsala ne, dama ban
san Abubakar ba, dama ban zo Kano ba, dama ban je
bikin Rahma ba.
Bugun kofar ne ya sani na dawo cikin hayyacina, da
sauri na mike cike da fatan shine, ba tare da na saka
takalmi ba na nufi kofa, ban bukaci na san waye ba na
bude kofa. Ganin shi tsaye ya sa na sauke wata
nannauyar akiyar zuciya, sai kuma Miskilanci ya motsa
na ce, "Daga ina? Ka canja ne ba kace ba zaka kara
zuwa ba?" "Au korata kike? To shike nan bari na koma."
Da sauri na ce, "Ni bance ba, ai ance bakonka
Annabinka, ka iya shigowa." Ya ce, "Zaki ji da gulmarki.
Hashim ku shigo." Na shimfida musu tabarma suka
zauna, shi kuma ya zauna kan tabarma ta kusa da
Shadad yana shafa masa kai, na kawo musu ruwa cikin
jug, na nemi kujera 'yar tsuguno na zauna. Na gaishe
su suka amsa, sai dai shi daya kafe ni da ido yana
kallona, duk da ba wuta sai hasken farin wata, ya ce,
"Ni ba zaki gaidani ba?" Na kalleshi irin hararar masoya,
na maida kaina kasa. Ya ce, "Shine na kiraki dazu wai
kike cewa baki gane ni ba." Shiru nai ban tanka ba Ya
ce, "Ka gani ko Hashim ta gane ni." Sagir yayi dariya,
"Kila bata gane ka din ba." Abubakar ya ce, "Bani aron
hankalinki nan. Shi yasa na kwaso abokaina dan su
zama shaida, da farko ina sonki, kuma ki ban amsa. Ta
dago ta ce Abubakar bana sonka, ba aibu bane dan
kince baki sona, in yaso sai sonki ya zama ajalina,
amma daga yau idan har kinki amince min ba zaki kara
ganina ba koda cikin mafarkine.
Gabana ke faduwa, na ce, "To ai ban ce bana sonka
ba." Hashim ya ce, "Pls Hafsa, magana daya zamu yi
tunda kina da hankali tin taba aure bai kamata mu
tsaya muna wasa da hankulan juna ba." Abubakar ya
ce, "Magana daya ce Malama, kina sona?" Kalma daya
ce da Hashim ya fada ta dagan hankali, wai na taba
aure? Inama na taba auren ai da bazan damu ba, sam
banji maganar da Abubakar yake min ba, su duk sun
dauka aure nayi na haihu, to tun kan na samu matsala
gwara na rabu da shi, sai dai sonsa ya zama ajalina, na
ma rabu da iyayena ballantana shi?
Tsawar da ya dakamin ita ta dawo dani daga tunanin
da nake ya ce, "Kin maidani dan iska ne ina magana
kin min shiru?" Hashim ya ce, "Ki yi magana mana
Hafsa."
Muryata ta soma rawa irinta masu kuka, "Lallai ina son
ka har ba zan iya kwatanta son da nake maka ba. .....
Zaharaddeen Shomar
whatsapp 08168575100
Sanadin Boko 2-08
Posted by ANaM Dorayi on 11:28 PM, 19-Sep-15
Under: SANADIN BOKO
Domin sonka ya shigeni ne a lokacin da nake tunani na
ha'ka dogon rami na saka so a ciki na rufe shi, ina fatan
kowa ya mutu ya huta. Amma abin bakin ciki sai da ya
fito har ya zo ya kama ni, a bisa adalci Abubakar bai
cancanta na zam matarka ba, matsayinka na kamili, kada
ka so kaji dalili ko ka matsa min na fada maka." Na kifa
kaina a tsakanin cinyoyina ina kuka irin wanda yake sa
jiki motsi, gidan ya yi tsit, gidan shiru kamar ba
mutane.Abubakar ya ce, "Malama ki nutsu ki fiddamu
daga tunani." Hashim ya ce, "Baiwar Allah ki nutsu ki
mana bayanin komai, da kin san irin son da wannan
bawan na Allah yake miki hakika da baki masa haka ba,
ni abokinsa ne kuma dan'uwansa ne na jini, Mahaifina
wan Mahaifinsa ne, tare muka taso kamar 'yan 2, ya san
sirrina haka na san nashi, tunda muke da shi ban taba jin
ya ce yana son 'yan matan da suke nacin sonsa ba, na
kosa na ganki mai sa'a." Na dube shi na ce, "Ina son sa,
kuma ina matukar farin ciki ace na samu mutum kamar
Abubakar ya zama Uban 'ya'yana, amma kash!!!" "Amma
kash me?" Sagir ya ce, "Dan Allah ki daure ki fada mana
Insha Allahu za'a samu mafita."
Na mike tsaye, "Ba wai ka aureni ba, da zarar ka ji
matsalar, sirri ne zan fada muku." Na yi shiru, na yi ajiyar
zuciya cikin kudurin gaya musu, "Amma ina so na gaya
maka Abubakar ina sonka, kuma duk lokacin da ka tuno
da ni ka tuna cewar na soka, zan ci gaba da sonka har
karshen rayuwata."
Na kalli Hashim na ce, "Za ka so dan'uwanka ya auri
karuwa? Wadda ta bar gidan iyayenta saboda cikin
shegen da tayi? Ta shiga duniya tana zaman kanta?"
Abubakar ya mike zumbur ya ce, "Cikin in, in, wa? Wa
kenan kina nufin ke karuwa ce? Cikin shege kika yi kika
haifi Shaddad?" Na ce, "Kwarai kuwa, ciki nayi."
Ban ankara ba naji saukar mari wanda idanuwana suka
daina gani na wucin gadi, ya ce, "Tur da haihuwarki, kin
cuceni da kika bar ni na fada son ki, Allah ya isa!" Ya
fice fuuu!!! Sagir da Hashim suka bishi.
Shadad ya farka a gigice sakamakon kukan da na fasa,
na zauna kasa ragwab, ya zo ya fado jikina muna kuka
tare da ina fadin "Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un.
Allahumma ajirni fi musibati wa'akhlifni khairan minha."
Mun yi kuka ya ishemu, amma har daga bisan Shadad ya
yi bacci, ni kuwa tuni zazzabi ya rufeni hakanan hawayen
idanuna bai kafe ba, abin da nake tsoro kenan rabuwa da
Abubakar gashi nan kuwa, Ya Allah! Ya ma aka yi na
fada masa zancen a baibai?
Kafin safe ko motsi na kasa yi don zazzabi da ciwon kai,
Ga fuskata ta kumbura sumtum saboda marin da
Abubakar yayi min, ga kuma kukan da nayi, haka muka
kawan gidan ko sakata ban iya samu na sa ba saboda
azabar ciwo.
Da asuba da kyar na iya tashi nai alwala, a zaune na yi
Sallah, Shadad ma Sallah kawai yayi dan ba zan iya yi
masa wanka ba, har 8 ina kudundune ban san me zai
biyo baya ba.
Shin Abubakar zai iya rabuwa da Hafsat? Ko Munnir yana
sane da cikin da yayiwa Hafsay? Baba fa da bangaren
Inna kuwa suna ganin Hafsa?
Duk amsar tambayoyin nan
Sae kun biyo mu a littafi na 3
Godiya gareku
Zaharaddeen Shomar
whatsapp 08168575100