Showing 3001 words to 6000 words out of 16780 words

Chapter 2 - Sanadin Boko Book 2 Complete by Halima I Mashi .txt

soma daukar shi,
sannan yaki kiran hashim ya fada mashi kamar daga
sama sai yaji an doki kafadar sa,
ya bude ido yaga hashim tsaye, yace har ka iso?
Hashim yace na iso ina? Ka fada min ne? Yanzu lamido
ya kira wayata yace ya yajimu shuru. Nace me yafaru?
Yace baka famun yana neman mu ba. Na kareka nace
ka fada min, nace na mantal yace ya bamu minti 20.
Abubakar yace kanme zakayi karya? Kawai kace masa
ban fada maka ba. Hashim yace tashi dai muje, amma
bari ka canja kaya, ya bude duriwar manyan kaya ya
ciro masa shadda waganbari bowa mai kalan sararin
samaniya. Hula baka minister, ta kalmi baki, yace tashi
dan Allah fadan lamido bashi da kyau, tunda in ya tashi
sai ya fara cin uban iyayen mu kafin ya dawo kan mu.
Abubakar ya soma sa kaya yana cewa, ni nifa kasan
Allah? Eh inji hashim, babu mai min auren dole. Sai irin
matar da tai min, mace 1 nakeso a rayuwata, kuma sai
na zabi duk wadda ta hada duk irin halayen da nake
son don bana son inyi mata 2 ko 3, 1 nan ta isheni.
Hashim yayi dariya, sanan yace niko har na hango
wace zan kara da ita fatana Allah karyasa lamido yace
wajenta zamuje. Abubakar ya dube shi kana nufin wai
lamido zai ce min in je gurin wata ne? Hashin yace
kaima ka sani, domin in baka manta ba juma‘a kamar
haka yace kasameni muje gunsa, mukaje yace muwuce
wirin shatu. Kana nufin munfika biyaya ne? Kada ka
manta mahaifiyar ka da a haifin ka yar mace da dan
namiji suke, kuma suma hadin ne. Abubakar yace duk
ina sane, hasim kanayi kamar baka san ABUBAAR
SADDIK ba, zaku sha mamakin zuri‘ata tashi muje
Hashim ya mike tare da ajiye kwalbar turaren da ya
kara fesawa a mazauninta.
Duk suna zaune gaban Lamido, wanda fuskarsa ke
take, yace Hashimu kuje gidan Baffanku Adamu, 'yan
matan gidan guda biyu ne, ka zabi daya da kanka ina
jiranku bayan sallar isha'I".
Hashim yace to, mun gode. Sai mun dawo. Suna mota
Hashim na tuki, Abubakar yana ta son tuna 'yan matan
gidan Baffa Adamu. Anya ya san su ma?
Hashim ya katse masa tunani da cewa, "Kai duk ruwan
idonka saika zabi daya daga cikin yaran gidan Baffa
Adamu." Abubakar yace ba dole bane su min. Hashim
yace Allah yasa kada ka canki wadda nake hari."
Tsaki Abubakar yaja, sannan yace tun kana yaro zaka
tara ma kanka gajiya, ka hada mata suyi ta maka
rigima kullum kuna fada Lamido, gashi kai ba dama ka
saki wata duk danginka irin gidan Yaya Sule gida sai
kace sansanin yaki."
Hashim yayi dariya harda dukan sitiyari, sannan ya ce
ni nan sai na gaji Lamido hudu nan sai na hada, Allah
ya taimaka inji Abubakar.
A kofar falon suka yi sallama, Yadikko ta amsa tare da
bude kofar, ganin su Abubakar ta fadada fara'arta, tana
masu sannu da zuwa cikin harshen fillanci.
Sun zauna a falon suka gaisheta, ta amsa tare da
tambayar mutanen gida, suka ce lafiya, cikin hanzari ta
nufi dakin 'yan matanta guda biyu, tace Maimuna ga
baki can falo su Hamma ne ku kai masu abin sha.
Jamila ta mike da hanzari, haka ita ma Maimuna
kowacce tana fatan gurinta yazo.
Tun fitowar su ya tsaida hankalinsa gurinsu, tabbas da
don kyau zaiyi aure da ya zaba, amma ba ra'ayinsa
kenan ba. Cikin yanga Maimuna ta gaishe su, yayin da
Jimila keta rawar kai gami da tsuga surutu.
Maimuna kam tun daga gaisuwa ta ciro waya tana ta
yin abinda bai sani ba, chattin ne ko game. Hashim
yayi kasa da muya yace wacce tayi? Kafin Abubakar ya
bada amsa, Jamila tace Hamma don Allah inga wayar
ka. Ba tare da ya bata wayar ba ya mike. Hashim tashi
lokacin sallah yayi, ya dube su ku kira ta muyi sallama.
Maimuna ta dube su har zaku tafi? Ko ruwan kai
Hamma baka sha ba. Yace zan sha wata rana, yau kam
na gode. Yadikko suka jero da Jamila nan dai suka yi
masu sallama, a hanya ne Hashim yake ta damun shi
da son jin wacce ya zaba, yace ni fa babu wadda tayi
min.
Hashim yace don me? Ga Jamila, Abubakar yace bana
som mace mai yawan surutu da rawar kai, gami da
bincike, wannan ya nuna in na aureta zata dinga daukar
wayata tana min bincike ko kuma tana min bincike a
daki.
Ya ce, Maimuna fa? Ita ma a'a ban cika son mace mai
shiru sosai ba, sai yawan danna waya, hankalina bazai
kwanta ba, domin zata iya share ni tayi ta mu'amularta
da waya. Hashim yace, tab, to wallahi bada ni za a
gurin Lamido an jima ban don haka kaje ka masa
bayani.
Abubakar yace tare zamu je, zaka ga kamar bazan iya
yi masa magana ba ko? Hum, bari mujem suna gaban
Lamido duk sun yi shiru, shi kanshi Abubakar yana jin
zuciyar shi na rawa, tamkar bazai iya bayani ba.
Amma ya daure yace babu wadda ya zaba, ya kawo
dalilansa. Lamido ya tsura masa ido, zuciyarsa na
zargin Abubakar nason kawo masa sabon salo ne cikin
zuri'a, amma sai ya danne yace naji. Hashim tun daga
gobe Asabar har zuwa rana irin ta yau, ku zaga duk
zuri'ar mu Abbab ya zabi wacce yake so in na Yola
basuyi ba ku tafi har Adamawa, kai har 'yan Kaduna da
Abuja da Kano kuje ya zaba.
Tsahon sati biyu na baku, ina jiran amsa. Abubakar
yace to mu gode sai dai a duba yanayi ayyukan mu.
Lamido yace wannan ya rage naku, ku zaku cire lokacin
da kuka ga zai dace ba tare da kun shiga lokacin aikin
ku ba, ku tashi kuje.
Sun ajiye bayan isha zasu dinga bin dangin kila a dace.
Sati guda suna zagaye gidajen dangi, amma ko ina sai
Abubakar yace bata yi ba, wannan yace kazama,
wannan yace zatayi rowa, wannan yace ta cika yawo.
Hashim yace to muje gidan mu ga kanne na, su kuma
yace basa jin magana, irin su daya da Rukayya
kanwata. Hashim yace haka ne amma fa bazaka samu
mace dari bisa dari da irin halin da kake so ba, su
dama da kashin hakarkari akayi su kaga kenan a
karkace suke, in ka dage cewa zaka mikar dasu sai su
karye. Abibakar yace, look bance maka dama ba, amma
irin matar da nake so nasan zan samu. Hashim yace
kasan me zamu yi? Tunda yau goma ga watan daya,
saura kwana biyar ayi family meeting mu jira ranar in
kowa yazo sai ka duba
Abubakar yace Allah ya kaimu
Duk shekara suke yin mitin na zuri'ar su, suna yin taron
ne a gidan tsohon wato Lamido, suna tattauna
matsalolin 'ya'yansu da su kansu a taron, duk wata
kowanne mai matsala yana fada ta kudi ko ta wani abin
da yake suna da asusun da suke tara kudi duk wata.
Sai a dauka ayi maganin matsalar da shi, tunda kuma
ba duk dangin bane masu kudi, sai dai masu kudin sunfi
talakawan yawa.
Tun ana gobe taron ake kada shanaye biyu saboda
yawansu, Lamido ke bada su, yayin da wasu daga cikin
manyan 'ya'yan zasu yi ta kawo kulolin abinci manya
kala daban daban, yan nesa irin su Abuja Kaduna tun
Juma'a suke dauko hanya.
Dada ta shiga dakin bayan ya amsa sallamarta, ta ta
ganshi kwance cikin bargo kasancewar lokacin sanyi ne
tace, ka tashi fa Abban ku fa ya tafi dasu Ummi da
Aliyu da Kasim. Usman da Umar kuwa na tabbata
yanzun sun tafi da iyalansu.
Shiri yayi tsaf cikin kayan alfarma, in ka ganshi zaka yi
zato cewa sarki ne, shi da Dada ne kadai. Gidan ya
cika makil, filin da aka saba yin taron tuni an shirya shi
da kujeru, gurin zaman iyaye daban, na 'ya'ya daban
haka ma na jikoki.
Dole su baka sha'awa, yanmata da samari ga sunan,
wasu dama anan suke hada kansu shikenan, Lamido
hakan na daga cikin abinda yake sashi jin dadi a taron,
gurin su Hashin Abubakar ya nufa, a gabaki dayan
tsararrakin sa babu wanda bashi da yara........
har saitin su usman da umar duk sunyi aure, hatta
usuma da umar suna da matansu matar usman tana da
tsohon ciki, ta usuman kuwa tana da danyen goyo,
dukansu suna aiki ne a kar kashin abubakar don mutun
ne mai adalci, kansu umma a hade yake. Hashim ya
soma yi mashi tsiyar cewa ya makaranta, salisu yace
ba dole yayi maka ba, tun da bashi da mai tashin sa.
Sani yayi tsagal yace, azumin nan mai zuwa sai munyi
mashi kidan tazuru, yace zakuyi ku gama. Hashm ya
turo mashi kujera zauna dai dai nan ka samu damar
kalon yan mata gasunan iyaka gininka. Ya zauna tare
da cewa ku tayani duba, sun bude taro da adu‘a kamar
yanda suka saba, sannan aka gabatar da marasa lafiya
dan ayi masu adu‘a sannan sauran abubuwan suka ci
gaba. Daf da karshene wanin baffan su mai suna yusuf
yace ya kamata kafin a tashi daga taron nan a saka
ranar abubakar, dan kowa ya san lokacin, duk iyayen
sun amince da hakan. Lamido ma yayi na‘am.
Abubakar dai zuface ta rufeshi, yayin da a bokan wasa
suka ta masa dariya. Sukuwa yan mata kowace tana
son taga wacece mai rabon nan. Shi kuwa tuni taron ya
gundire shi. Anci ansha samari sun sami yan mata
wasu kuma sunyi kari, amma abubakar duk basuyi
masa ba. Hashim yace gasu khalisat yayan baffa na
abuja, yace wadan nan yaran masu salon tsiya, barni
kawai.
Kamar daga sama yaji lamido na kiran shi tacikin abin
magana, Hashim yace to kaifa kila yau ta yan tatsuniya
za a yi maka, irin na 'ya'yan sarakunan nan ace mata
su jeru namiji yaje ya zabo. Abubakar ya mike ya mufi
gurin Lamido, yace ina so yanzun nan ka shiga cikin
'yan matan nan yanzu ka fitar da mata ka, nasa ranar
auren ka wata biyar daya ga watan.
In kayi lissafi zai zama wata hudu da kwana goma sha
biyar kenan, kafin lokacin kun fahimci juna." Nan da
nan dangi suka sheda suka shiga murna, shi kuwa gurin
zaman shi ya koma. Hashim yace tashi mu duba, yace
dan Allah ka bar ni ka ji."
Haka taron ya tashi ba tare da Abubakar ya zabi mata
ba, hakan ya kona ran mahaifansa da Lamido, daga
bisani kakarsa Gogwal kodai bashi da lafiya ne? A
bincike shi, sun tsare shi ya ce shi kam lafiyar shi lau,
amma bai samu kawai mai irin halayen da yake so
bane. Cikin bacin rai Lamido ya ce sun zura masa ido
amma ya sani rana baza a daga ba ko ya sami mata ko
bai samu ba, in lokacin yayi zasu daura aure da duk
wadda suka ga dama.
Abubakar kuwa ko a jikinsa, cikin hakan ne bikin
abokinsa Sagir ya taso a Kano, yaje yayi arba da
yarinyar da ya santa a Kaduna lokacin da yaje (Bautar
Kasa), tana talla mai yawan wasa, kusa shekaru goma
baya.
Yana son sanin abubuwa game da yarinyar kuma yana
jin wani abu a ranshi game da ita, sai dai abin tambaya
ta tara halayen da yake so matar shi ta kasance?
Ya iso gida daga gida Hashim, gaban iyayan nashi ya
zauna a kasa, Abban ya dube shi yau in ni na haife ka
ina son ka fada min nufin ka damu. Dada tace dazun
su Yafendon shi da suka zo dukan su kowa na cewa
yazo ya sasanta da 'yar gidanta, na ce masu dai kun
sanshi in ya yarda shike nan, amma fa ni bazan maku
alkwarin ko ya yarda ba.
Don haka ka fitar da mata kada ka hada ni da 'yan
uwana, Abba yace yama fada mana nufin shi kawai, in
yana da wata matsala ne sai ya kawo uzurin sa muji, in
ko lafiyar shi lau to raini ne da walakanci, baka jin
kunya kannan ka duk sunyi aure cikin dangi ko ina
lbarinka ake, fada min nufinka."
Ya danyi dim don yasan abinda zai fada yanzu zaya
girgiza su. Dada kayi magana mana. Ya dan numfasa
yace, naga wadda nake so." Abba yace, ko kai fa, fada
min wacece yanzu na sanar da Lamido ta waya." Yace
tana Kano." Suka hada baki gurin cewa, Kano? 'Yar
gidan Goggonka Furera?"
Ya ce a'a ba dangin mu bace. Suna hada baki gurin
cewa, ba dangi ba? Eh, ya dago ya dube su, ba zato sai
yaji saukar mari gefe da gefe, sannan ta rufe shi da
duka. Sunkuyar da kai kawai yayi tayi ta dukan shi.
Abban su kuwa sunkuyar da kai yayi ba tare da yace
Dada ta daina dukansa ba, har sai da ta bar shi don
kanta.
Cikin tashin hankali take cewa ba zaka jawo mim abin
fada a cikin dangi ba, kai ne mutum na farko da zai
kawo matsala a zuri'ar mu? Tur! Ba dani za a yi ba, ta
fice daga falon rai bace, yana nan zaune Abba yace
kasan dai kazo da abin da bazai yuwu ba ko? to ka cire
wannan tunanin a ranka in dai kana so kaci gaba da
zama danmu. ya mike shima ya fita dàga falon,
Abubakar yana zaune cikin halin da baza yace gashi ba,
yafi awa daya saññañ ya fito ya tafi dakinsa.
washe gari sam iyayen basu amsa gaisuwar sa ba,
wannan lamari ne mai girma. Ya zama dole ya faranta
ran iyayan sa, yasan idan tasu ne zai iya shawo kan
su, tsoron lamido da sauran dangi suke yi. Shi kuma
yana so ya kawo karshen wanan auran, domin wasu na
cutuwa, an hada su da wadanda basu so. Sannan ko
mai mace zatayi wa namiji ko shi yayi mata babu
rabuwa, yasan ba wai haramun bane auran zumuncin,
to amma yanda zuri‘arsu suka dauke shi tamkar ibada,
shine yake son su gane auren bare ma ba haramun
bane. Akan gadon shi yake ta juyi tare da neman
mafita, ya kalli agogo 11 a fili ya furta Allah yasa
hashim bai yi bacci ba, ya daga wayar sa yasa a kunne,
bayan ya laluba num hashim din. Tayi kuka har ta
katse ba‘a dauka ba, don haka ya ajiye wayar yana
miyar hashim har yayi bacci sai kace mace. Kusan
minti 30 wayarshi ta soma ruri, ganin sunan hashim ya
daga da wuri,ya soma korafi ka cika baci kamar mace.
Hashim yace ina tare da iyalina ban san tayi ringin ba,
duk da tana kusa dani in ka fahimce ni ka kira lokacin
ina duniyar ma‘aurata, bana tare da ku. Abubkar yace
ban tam bayeka ba, sannan Allah dai ya tsine ma mai
tona asirin iyalansa, don haka sai kai hattara. Kasanan
dalilin kiran da nayi maka? Hashim yace sai ka fada?
Abubakar ya gyara kwanciya sannan yace, kila kaji
mamakin cewa wadda nake so ba a cikin zuri‘armu
take ba ko?
me kake son fada mun? Hashim ya mike ya nufi falo
dan kada matarshi shatu taji abin da zasu tau tauna.
Kada kace zaka shugo da bidi‘a cikin zuru‘ar anan,
kasan hakan zai jamaka matsala kai da mahaifin ka?
Abubakar yace haba hashim kai fa ba jahili bane,
abinda kake kira bidi‘a ba haramun bane. To auren
zumunci sunna ne? Ka fada mun a matan monzon Allah
wacece yar uwarsa ko a kwai bata wuce guda 1 ba,
kuma duk matansa yan kabilar sa ne?Dashi fa muke
koyi, don haka matar da aura ina nufin ba haushiya ce,
ina zoton ma ba zawara ce, kaga kenan zanyi sunna.
Hashim yayi tsaki, wannan karan bana tare da kai,
matsawar baka canja tunani ba. Me hausa sukafi yaren
mu na fulani? Kyau ko asali? Abubakar yace look!
Hashim ka fahim ceni sosai, ba al‘ada ce a gabana ba,
addini nake son awa agabana, yarenmu suna da kyau
da asali da kuma tarbiyya, amma ban ga wadda tatara
irin halin da nake so ba. Ok inji hashim. Ita wannan ta
tara duk abin da kakeso? Abubakar ya tashi zaune, ba
zan saniba sai dai na ga 1 daga ciki, saura sai ta bani
dama mun zanta. Hashin yace kana nufin baku taba
zantawa ba? Abubakar yace ni ke sonta, ita bata san
inayi ba, domin bata so in kusanto ta, na dai taba sanin
ta da. Hashim dan Allah ka natsu, ina so ka taimaka
mun yanda zan shawo kanta, zanfi tsayuwa kan ra‘ayi
na inna tuna wanda nakeyi dan ita, ta san ina yi.
Hashim yace, abinda zai fi kaje ka fada mata nufinka,
ka ce mata kana sonta kuma zaka aure ta, na san zata
girmama zan cenka don matan da suka san abin da
suke yi, suna girmama zancen aure. In dai ba wani ya
riga ba. Abubakar yace ta tsani maza, ina zaton namiji
yayi mata laifi. Hashim yace kaje, in baku sasanta ba
ka sanar da ni, sai mu koma tare. Kai dai kasan yan da
zakayi mahaifanka kada su shiga fushin lamido. Yace
zan ga me zanyi. Sukayi sallama. Arana ta 3 ce daada
ta shigo dakin shi, da wowarshi kenan daga office, tace
ka sauya ra‘ayin ka ne ko kanan kan bakanka? Ya
kwantar da murya. Dada kiyi hakuri, wlh wace nake son
aura musulma ce mai tarbiyya. Tace amsa kawai zaka
bani, ba.
Tace amsa kawai zaka bani, bana son dogon turanci,
ya ce to duk yanda kuke so haka zanyi, tace uhm! Isa
da kai kaje ka cire mata a dangi, ta tausasa murya, da
zakaji tawa ma, ka sami lamido ka fada mashi ya zabo
maka. Na tabbata zaka wanke lefukan da kowa ke
ganin ka dashi. Muma zaka ciremu a zargin da lamido
ke mana, na san baka sami lbr mitin din da lamido ya
kira su abban kuba ko? Ya dube ta, na sami labari sai
dai ban san abun da aka tau tau na ba, duk da nasan
dan ni akayi shi. Tace to ya tara yayan shi maza ya
sanar dasu cewa bai yafe ba duk wanda ya bari dan sa
ya kawo bakon lamari a cikin zuri‘armu ba, yace za‘a
yanke mumunan mataki a kanshi da yayan ta hanyan
yanke zumunci da su


Zaharaddeen Shomar
whatsapp. 08168575100




Sanadin Boko 2-3
Posted by ANaM Dorayi on 07:34 AM, 19-Sep-15
Under: SANADIN BOKO
Abubakar yayi shuru, yayin da jikinshi yayi sanyi lakwas.
Al‘amarin mai girma ne, yace dada kada ki damu, zanje
gurin lamido amma ina so ku daina fushi dani. Tace to
mu dama fushin mu don kaki bin abin da muke so ne, da
kabi shi kenan mun huce. Yace to zanyi duk me kuke so.
Har zuciyar shi ya san ya amsa ne kawai, amma ba dan
zai je wajen lamido da batun a zaba mashi mata ba, zai
jene da batun wanda yake so amma sai yaje kano ya
dawo. Tun dare ya shaida wa mahaifan nasa cewa zai
shiga lagos a gobe, don tau taunawa da wasu abokan
kasuwan cin sa a bisa wata cinikayya da zasu yi. Sukayi
masa adu‘a da safe karfe 9 ya hau jirgin kano. Sai da ya
huta a masaukin shi sannan ya daga waya ya kira layin
sagir yace yana kamo don Allah ya kawo masa mota.
******* ******* *****
Tun dare zazzabin shi ya tsananta, kwana mukayi babu
bacci, gashi bani da ko parasitamol bani da kudin saya
cikin yan satitikan tsananin babu ta dameni, jiya ko girki
banyi ba. Da dadare garin rogo muka sha muka kwanta,
jikin sa ya tsanata sosai da safe har da safe har ta kai
numfashin sa na futa dai dai. Nace ka bari dai in watsa
ruwa sai mutafi asibiti tunda kan da kati, ko da bani da
na mota, ina saka hijab na lura ya mike idanun sa sun
kafe hakoransa suna datsewa, dukda ban san suma ba
tabbas suma ne wannan. Cikin matsanancin tsoro da
firgici na sunkuce shi da gudu nayi waje ina fadin
innalilahi wa inna ilaihir raju‘un! Kamar daga sama na
ganshi tsaye jikin mota, da gudu na nufeshi ina cewa, ya
mutu! Ya mutu!! Da sauri ya karbe

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login