Showing 6001 words to 9000 words out of 16780 words

Chapter 3 - Sanadin Boko Book 2 Complete by Halima I Mashi .txt

shi yasa a mota bai
jirani ba ya figi mota kamar dama abinda yake jira
kenan. Na koma cikin gida ina zagaya ina kai kawo,
kusan awa 3 sannan naji tsayiwar mota da gudu na fita,
shi kadai ne ya fita fiskar shi mur tuk, ko bai fada ba
nasan shadad ya cika.da gudu na juya cikin gida ina
kuka, hakika nayi rashi. Na zube kan katifa nayi kuka na
gode Allah, sai nace Allah yasa mai cetona ne. Ina
fitowa sai nagan shi jingine a bango, na daure nace ka
daukosh bari naje na fadawa su maman rahama. Yace ki
ce musu me? Ya rasu mana, yace inji wa? Na kara
matsawa kusa dashi me kake nufi? Yace ya far fado
nazo ne in kaiki gurin shi. Likita yace typort ne ya
kamashi da kyau. So, yanzu in kin gama kukan ki shirya
ki dauki duk wani abu da zaku bukata a can. Yan kayan
shi kawai na diba, sai nawa guda 2, da daudumar sallah
da alkur‘ani. Na fito yace kin dauki komai? Na ce eh.
Amma kafin muwuce bari na sanar da maman rahama,
kada suji shuru. Yace to ina jiranki a mota. Sai da na
kule gida sannan naje. Asibitin kudi ne mai tsari dakin
mu kadai ne har da kayan kalo ga na‘ura mai sanyaya
daki da taruwa. Na kafe shadad da idanu, duk ya rame
yanata bacci. Hawaye sai sauka suke a idanuna, yace
min yana zuwa. Bayan fitarshi likita yazo muka gaisa, ya
tambayi mai jiki nace da sauki, yace bai tashi ba ko?
Nace eh yace to idan ya tashi ki bashi abinci ko da
ruwan tea ne, sai ki bashi magungunan shi an siyo?
Nace banga ta kardar maganin ba ai, yace tana hannun
baban shi, yace dan Allah kada kiyi masa wasa da
magani, nace to. Yana fita na soma tinanin ina zan sami
kudi? Gashi ko abincin da zan bashi bani dashi in ya
tashi. Nace oh Allah na gode maka a wanan hali da kasa
ni, Allah ina mai naiman sauki a gareka. na dauki wayata
na kira Rahama na fada mata muna asibiti an kwantar da
shadad, tace taji gurin Abubakar, gasu nan zuwa dashi
da sagir ma. Kusan minti 25 da yin maganar mu sai
gasu. Rahama ce gaba dauke da katon kwando da
kulolin abinci da filas na ruwa zafi, Abubakar da Sagir
suka shigo da ledoji. Ya nufi yar durowan da ke gefen
gadon ya jera kalolin jus ne da ruwa. Sannan sai magun
gunan shadad ne ya zuba su a wani kwando dake jikin
gadon, kila an tanade shi ne dan zuba maganin dama.
Sagir ya koma ya shiga da dadduma mai girma, ya
shinfida ta can gefe suna fiskantar gadon, rahama ta
dauko kwandon ta zuba musu da fadukan shinkafa da
kayan lambu, sai farfesun kifi. Ta zo ta daukar musu
ruwa tana cewa bari na sashi a fridge saboda naji babu
sanyi. Ni dai sai bisu nayi da idanu. Rahama ta dube ni,
bari in sa mana, nace zuba dai dai cikin ki. Abubakar
wanda ya zauna saiti na da na dago fiska sai mu hada
ido, na daure fiska Rahama ta sani ni magana 1 nake yi
shiyasa bata matsa min ba, ta zuba nata ta juyo kujera
kusa dani, ina bakin gado ne ta soma ci. Ya kurbi ruwa
me yasa ba zaki ciba? Na dan tsuke fuska, sannan na
dube shi haka kawai. Ya kali kofar shigowa, kamar mai
nazari. Can ya sake duba na, amma ba don kin karya ba,
kuma ba don baki jin yunwa ba?ban karya ba kuma ni
bance bana jin yunwa ba. Rahama ta ce, Alhaji abubakar
dama ka barta, domin duk abinda tace tana nufin hakan.
Abubakar ya dubi Rahama, yace kina nufin bata
karyawa? Rahama tace a a ina nufin duk maganar da ta
fada ba zata canja ba, shi ne dalilin da yasa kaga da
tace ba zata ci ba, ban matsa mata ba. Ya ce ok. Duk
kamshi ya cika dakin sagir da Abubakar kasa kasa suke
hirarsu. Wayata ta shiga ruri, nayi tsam tare da son in
tashi taro da son inhasashi ko wanene, ina dubawa sai
naga number super markert din mu. Gabana ya fadi, sam
na manta da wani aiki. Ida nuna suka kai kan Abubakar,
ya kafe ni da ido da alama yana so yasan wanene ya
kirani? Nikam a zatona manaja ne, na daga da sanyin
jiki. Ba muryar shi ba ce, nace ishak ne ko musa? Yace
ishaq ne yace munjiki shuru ne kuma manaja yace baki
ce bazaki zo da yanma ba, tun dazu yace kina zuwa ki
sameshi ofis. Ya numfasa yace ranshi fa ya baci, wai shi
kin soma isarsa. Nace ishaq don Allah kace yayi min
uziri, yaro nane ba lafiya duk na rudene shiyasa ban tuna
da aikin ba, yanzu haka muna asibitin anbashi gado.
Yace to kikirashi ki fada mishi, dan kada ya gane nine na
kiraki. Nace to na gode. Na dafe goshi na, Rahama tace
ya akayi? Kin san cewa na manta da batun aiki? Shine
Ishak ya kirani. Na shiga dan na wayata ina son in duba
account dina, duk da nasan bani da kudi, ko ina ziro ziro,
nashi gshi bani da kudin ma da zan kira manaja sai in na
sa.
Rahama ta ce ga wayata ki kira shi, na harare ta kina
hauka ne, zan kira wani namiji da wayar ki, bayan kinyi
aure? Ta ce to menene, ba da nima Ogana ne ba? Nace
sam, da kika ce, ki tuna mijinki har canza maki layi yayi
don kada mutane su dinga kiranki, kuma hakan yayi
daidai, don ya nuna kishin ki.
Yanzu sai na kira Manaja? Alhalin yanzu baki da wata
alaka dashi?, tace to naji. Sagir wanda bansan suna jina
ba, yace a to fada mata gaskiya. Na dube su, idanun
Abubakar su suka sa na sunkuyar da kaina.Yace, "ga
wayata ki kira, na girgiza kai, ka barshi na gode, ya shiga
danna lambobi, ban sani ba sai naji yana cewa Manaja
yarinyar nan Hafsa tana da uzuri, don haka bazata samin
zuwa aiki ba sai bayan wani lokaci da bazata iya cewa
gashi ba, don haka tana son uzuri.Na tsura masa ido, a
raina ina cewa ji mutum zaya balgace min aiki na, bayan
dan shiru kadan da yayi sai yace, to shike nan. Ya dube
ni "menene na zare min ido? Ya yarda, nace na gode.
Amma ba haka ya kamata ka tambaya ba saboda
shugabanane a gun aiki. Ya ce yanzun nayi laifi kenan,
na girgiza kai alamar a'a, sannan nakai dubana ga
Shadad.Sai bayan munyi Azahar sannan ya farka, naba
bashi tea. Abubakar ya bashi magani, naji dadin yanda
ya bashi don ni idan na bashi kuka da su amai yake yi,
amma shikam ya bashi cikin lallashi kuma yasha. Amma
sai yace masa Uncle bazaka kara guduwa kabarni ba, ya
ce eh amma sai kasha magani.
Cikin rawar jiki yasha, na kanyi al'ajabin irin son da
Shadad yake yiwa Abubakar, domin ba shine mutum na
farko da ya fara masa magana ba, bai taba zuwa gurin
kowa ba sai shi.Sun fita sai ni da Rahama na kasa rike
abin da ke ciki na nace, Rahama wai me wannan abokin
mijin naki yake nufi da ni ne? Ta ce baki tambaye shi
ba? Na harare ta in ya bani amsa zan zo ina tambayarki
ne? Na jima ina tambayar sa bai bani amsa ba nifa
gaskiya bana son shishigin nan ki fada masa.
Ta ce ke me ya hana ki fada masa, ta gyra zama Hafsat
ki nutsu da kyau ki lura. Abubakar yana nemanki da
alkhairi ne, koda bai fada min ba nasan kila sonki yake.
Na dubeta da wani irin kallo cike da masifa nace sona?
Don Allah ki daina wannan sabon, in har yayi kuskuren
furta min kalmar so ai sai yayi nadamar yin hakan.Tace
maida wukar, tambayar ki zanyi. Cikin harara nace, ina
jinki, ta ce kina nufin laifin Munir ya shfi sauran maza?
Tsakani da Allah zaki bani amsa, na ce kusan haka ne, ta
ce kina dai da ilimin addinin musulunci, ance laifin wani
yana shafar wani? Na ce baya shafa amma na dade ina ji
a bakin iyaye na cewa maza ba yan goyo bane maza
rigar kaya ne, maza basu da tabbas, maza mugun ice da
dai sauran sunayen da ake kiran su da su, da ban yarda
ba sai gashi namijin yayi min, don haka ni layi guda na
ajiye su.


Zaharaddeen Shomar
whatsapp. ,08168575100












Sanadin Boko 2-5
Posted by ANaM Dorayi on 03:15 PM, 19-Sep-15
Under: SANADIN BOKO
"Amma wanda ya bada wannan shawara ya kyauta, dan
kai da Fadi kun dace, kuma ina zaton tana da wasu irin
halaye da kake so." Ya ce, "Na rasa dalilinku na cewa
mun dacen." Ya ce, "Ya kake son nayi da Hafsatu?"
Hashim ya ce, "Kun daidaita?" Abubakar ya ce, "Akwai
alamun nasara. Abba ne ya sani na dawo da gaggawa,
saboda wasu takardu. Sati na sama zan koma ko da
kwana daya ne, daga nan in mun daidaita zan kai ka ka
ganta. Amma ka shirya anjima zamu je gurin Lamido."
Hashi ya ce, "In dai kan yarinyar da zaka shigo da ita
cikin zuri'armu ne zaka masa to ka tafi kai daya ba zan
je ba." Abubakar ya ce, "Na rasa me yasa kuke tsoron
Lamido haka, shi ba dodo ba ba komai ba, ni Allah kadai
nake tsoron na sabawa ba mutum ba, zan je kuma zaka
ji sakamako." Har ya fita Hashim ya ce, "To yaushe
zamu je wajen Fadin?" Tsaki Abubakar yayi sannan ya yi
gaba.
Lamido ya tarbe shi cikin fara'a, ya ce, "Ubana ka iya
zabe, domin ko da ni ka bari to da wuya na zaba maka
irin wannan Babban kamu, lallai kun dace." Abubakar ya
sunkuyar da kai cikin daure fuska ya ce, "Ni fa ba nine
na ce ina son Fadi ba." Ya ce, "Duk wanda ya hada ku
yayi maka gata." Abubakar ya ce, "Ni wadda na zaba
daban, bana son Fadi." Ya ce, "To kila ka gaji
takwaranka Mahaifina kenan, tarihi ya nuna mana duk
cikin zuri'ar nan shine mutun daya taba auren mata 2
lokaci daya. Fada min wadda ka zaba ita ma yau akai
mintinta, rana daya duk a sa su a lalle." Abubakar ya yi
shiru, Lamido ya ce, "Duba, taso ka matso nan, ka fada
min wadda kake so." Abubakar ya matso, ya dubi
Lamido, "Wata yarinya ce a Kano, sunanta Hafsatu, bata
daya daga cikin zuri'armu....." Wani wawan mari Lamido
ya sakar masa da bayan hannu, ya mike tsaye cikin fada
mai tsanani yana cewa, "Tir da kai, ba zaka surka mana
Zuri'a ba, tunda muka taso zumunci iyayenmu suke yi,
don haka muma ba zamu daina ba har bayanmu, don
kana takama da boko, bokon banzanka, na yi tunanin
shine yasa kake zagaye-zagaye, kana juyamu kamar
waina (masa), to kaje da Iyayenka zan yi, don ina
girmamaka saboda sunan Ubana, zan ajiye uban a gefe in
kamata inci mutuncinka, baka wuce duka ba a gurina,
FITA!!!!!
Abubakar ya tashi ya fita.
Kafin wani lokaci ya kira dukkan manyan 'ya'yanshi ta
waya ya fada musu yana nemansu gobe da safe.
Abban Abubakar yana jin kiran ya sha jinin jikinshi kan
batun Hamma ne, domin Dada ta fada masa komai
game da abin da Abubakar ya ce.
Ummi ta shigo dakin yana ta sintirin kai kawo, ta ce,
"Hamma!!!" Ya dubeta ta ce, "Ka ja surutu cikin dangi,
ko a Makaranta surutunka 'yan uwa suke yi, wai ka
canja hali yanzu baka da biyayya, ni kam ka yarda da
Fadin mana."
Abubakar ya kama hannun Ummi ya rike kam, "Tun
farko ina rokon Allah ya bani macen da nake so,
zuciyata ta san da Fadima, amma ta kama son Hafsa
ranar da na fara ganinta, nasan kema zaki so ta
Ummi." Ummi ta ce, "Hamma ina son duk abinda kaima
kake so, sai dai bana son matsalar dangi, zaka yi kallon
halin da su Dada zasu shiga, tunda kace Lamido yana
nemansu." Ya ce, "Ki taya ni addu'a, so baya barin
mutum ya ji tsoro, ni da kaina na fadawa Lamido batun
Hafsa, jikina yana bani zan yi nasara, kullum cikin
mafarkin Hafsa nake." Ummi ta ce, "Allah ya amsa."
Lamido ya mike yana kai kawo a tsakanin 'ya'yansa
wadanda suke zaune akan kafet. Dukkansu manyan
mutane ne masu fada aji, domin wannan yana wane
wannan ne a kudi. Ya dubi Mahaifin Abubakar ya ce,
"Ibrahim dauki wayarka ka kira min danka Abubakar."
Nan take Abba ya aikata haka, shima Abubakar nan
take ya bar komai ya nufi gidan Lamido. Abubakar
gabansa ya fadi ganin daya yiwa Iyayanshi kamar masu
neman gafara. Dakin yayi tsit sai karar agogo, jiki a
sanyaye shima ya zube tare da sunkuyar da kai, sai dai
duk da haka bai ji a zuciyarshi cewa zai canja daga
batun son Hafsa ba.
Lamido ya ce, "Abubakar!!!" Cikin zafin rai ya ambaci
sunan. Abubakar ya dago da kai ya dube shi, Lamido
ya nuna su ya ce, "Su waye wadannan?" Abubakar ya
kalle su ya ce, "Iyayena ne." Ya ce, "Da kyau." Ya ce,
"To ina son ka fada musu abinda ka fada min jiya."
Abubakar ya sake dubansu gabanshi na faduwa,
musamman da suka hada ido da Baffa Magaji, Lamido
ya ce, "Ka fada musu nace." Abubakar ya kasa
magana. Ya ce, "OHO!!! ni ka raina kenan da ka zo ka
same ni kafada min saboda ba nine na haifeka ba?"
Baffa Magaji ya ce, "Ka yi magana mana, wane ne
sa'anka a nan?" Abubakar ya ce, "Dama kan batun
yarinyar da nake so ne, wadda ba 'yar cikin zuri'armu
ba." Dukkansu suka hada baki gurin tambayarshi, "Me
ka ce?" Illa Babanshi da ya sunkuyar da kai cikin
matsanancin takaici. Baffa Magaji ya ce, "Kai ko
Shaidanin yaro ne, zaka kawo mana sabon al'amari
cikin zuri'a." Lamido ya daga ma Baffa Magaji hannu,
sannan ya ce, "Ban taraku kwanakin baya ba na gaya
muku cewar kar wani daga cikin 'ya'yayenku ya kawo
mana wani sabon al'amari a cikin zuri'armu ba?" Duk
suka ce hakane. Ya ce, "To lokacin ina zargin Abubakar
zai aikata haka, gashi zatona ya zama gaskiya. Don
haka yanzu kai Ibrahim tunda ka kasa tankwasa danka
ba ka iya bashi tarbiyya ba, ina son ta bakin ka kafin
kuji ta bakina." Abba ya nisa ya ce, "Lamido Allah ya
huci zuciyarka, na jima ina fama da Abubakar akan
wannan matsalar, sam ya ki bin umurnina, don haka ina
son 'yan uwa da suke zaune ku zama shaida, daga yau
na cire shi daga cikin 'ya'yana. Ina son Lamido ya cire
shi daga cikin zuri'armu don girman Allah.
Baffa Sa'adu ya ce, "Ina rokon alfarma gurin Lamido,
da ya ba Abubakar dama muji uzurinsa kafin a yanke
masa hukunci." Lamido ya ce, "Gashi ga ku." Baffa
Sa'adu mai rike da sarauta a yanzun wato Mahaifin
Hashim ya dubi Abubakar ya ce, "Dana fada mana
dalilinka na son ka saki layin da ka same mu a kai?"
Cikin karfin hali ya ce, "Baffa duk ciki ban samu mace
mai irin halayen da kamannin da nake so ba." Abba ya
ce, "Ka ji ko? In ba rainin wayo ba ace duk zuri'armu
masu kyau da ilmi da tarbiyya amma ace ya rasa matar
aure? Sai ya je yayo mana rore-rore?" Baffa Magaji ya
ce, "Muna jin shi ai, ya fada mana irin matar da yake
so muji dame yake takama." Abubakar ya ce da su
Baffa, "Bana son macen da an kalleta za'a san
kyakykyawa ce, nafi son baka kuma zuri'armu kusan
duk kyawawa ne farare, game da batun halaye kuma,
nafi son mace da bata cika wayewa ba, sai wadda bata
cika buri ba, mai ilmi duka 2, mai tarbiyya da hankali da
natsuwa, sannan kuma 'yar talakawa wadda za taji
magana ta, ta girmama Iyayena da duk wani nawa, mai
tsoron Allah a duk inda take, mai hangen na kasa da ita
ba na sama da ita ba, wadda bata da rawar kai. Baffa
kada ku yi zaton na raina tarbiyyar 'yan matan
zuri'armu, ko ba za'a samu mai irin wannan hali a
cikinsu ba, a'a za'a samu matsalar daya ce, ina son na
auri wadda nake so kuma take so na, ba wacce take
sona ni kuma bana sonta ba, Manzon Rahama ya hana
auren dole, don yana da illoli, bana son a cikin
zuri'armu akwai dayawa wadanda zaman hakuri da
biyayya kawai suke yi, alhali babu biyayya ga abokin
zamansu, hatta dan sabawa mahalicci."
Baffa Magaji ya taso ya ce, "Wato auren zumuncin ne
sabawa Mahalicci? To sarkin iya magana fada mana
inda aka ce ya haramta?" Abubakar ya gyara zama,
"Aure bautar Ubangiji ne, a duk lokacin da aka hada
Ma'aurata dan dole ba so da kauna, to ba zasu yi
wannan bautar ba yadda Ubangiji ya ce, maimakon lada
sai kaga zunubi ya samu. Mu dauki misali da gidan
Yaya Saleh, duk family ba wanda bai san tashin
hankalin da suke ciki kullum ba, banda kuma sauran
dangi da ba'a sani ba." Baffa Magaji ya ce, "Lallai
Abubakar, boko ya sa ka fitsare idanunka, kana rigima
damu saboda aurenka." Abba ya ce, "Duk wannan
zantukan naka basu isa su zama hujja ba, tunda ba
littafin da yai hani ga auren zumunci."
Lamido ya ce, "Ikon Allah!!! Ashe tun ina da rai zan
samu wani a zuri'armu da zaya kalubatanceni akan
al'adarmu? Dole ne na dauki mataki, in ko ba haka ba in
na mutu zumuncinmu rushewa zai yi." Abubakar ya ce,
"Ku yafe ni, ba zan zama sanadiyyar rushe zumuncinmu
ba, haske na zo mana da shi cikin zuri'a, ku kwatanta
dani zaku gane nufina nan gaba. Ma'ana ku barni na
auri bare." Baffa Sa'idu ya ce, "Abubakar mene ne
dalilinka na cewa ba zaka auri mace mai kyau ba?
Alhalin shine burin duk wani namiji." Ya kalli Abba, "Da
ban san yin wannan batun ba, amma yanzu ya zama
dole na fada, dalilai 2 ne suka sa nace ba zan auri
mace dan kyau ba. Na 1 Yaya Mansur in baku manta
ba lokacin da aka ce ya nemi Waslia bai ki ba, ya ce ko
ba komai ai tana da kyau, da suka yi hadari fuskarta ta
lalace, har yau ba wanda bai san irin wulakancin da
yake mata ba. Abu na 2, lokaci mai tsawo daya gabata.
(Abba ka yafe min abinda zan fada, ina dan yaro
lokacin kun dan samu hargitsi da Dada, na ji kace mata
abu 2 ne suka sa kake zaune da ita, na farko biyayya
ga Lamido, na 2 dan kyanta da take da shi. Ta yiwu ka
manta, kayi min afuwa ban so na fada ba) A lokacin in
zaka tuna ina karami amma raina yayi matukar baci
kwarai, da muka je Makaranta nake fadawa Hashim sai
ya ce Ai shi jiya ya ji Dadarsu tana fadawa Abbansu
zaman hakuri kawai take yi da Abbansu, don ita ba shi
take so ba, daga lokacin na kudurce a raina bazan taba
aure ba, sai wadda nake so take sona. Ina son iyayena
ku taimake ni, ku duba hujjojina, in kunki ni zan hakura
in yi biyayya amma har abada ba zanyi farin ciki ba.
Duk jikinsu yayi sanyi, kuma sun tabbata kowannensu
yanada shigen wanan matsalar ko shi bai son matar ko
ita bata son shi, amma wanda suka hada kansu su
suna zaune lfy. Baffa sa‘adu yace, ina rokon lamido
yayi mashi izini yatafi, mukuma munyi shawara. Lamido
yace, ya iya tafiya. Abubakar ya mike cike da kwarin
guiwa ya fita. yasan adu‘a bata faduwa, don tashi yake
tun 2 dare ko 3 yana fadawa Allah matsalar shi.
Lamido ya dubesu daya-bayan-daya, kuna nufin kun
amince da batun sa? Baffa jume yace, a a sai yanda
kace. Baffa sa‘adu yace, da zai yuwu hujjojinsa sun isa
a duba lamarin, koda a gaban kotu ne. Amma in
zancena

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login