Showing 9001 words to 12000 words out of 16241 words

Chapter 4 - AZUMIN ILU (COMPLETE) BY MAMAN MAMY Maryam Muhammad Hassan.txt

mamaki liman ke amsawa tare da fadin wa Nike gani kamar ilun malam Allah dai yasa lfy ...murmushi ILU yayi tare da dukar da kanshi kasa irin na ladabin nan ..kai ILU ba karamin jairi bane ...
Aa lfy lau ya liman kawai yau nace dai bari inzo inmaka barka da shan ruwa ....sai kawai liman yahau washe baki yana fadin Allah dai yayi maku albarka yarannan ...basiru kam sai kumshe dariya yake....


Ameeen ya liman ILU ya fada tare da dakko lemu guda ya mika mashi... Ga wannan kadan sha da sanyinshi badai yawa..... Hannu na kyarma liman ya karba yanata was he baki ganin lemu sai zufar sanyi yake ....aa ILU hard a dawainiya


Aa ba komai ya liman ILU ya fada yana kara dukar da kanshi kasa ...


Nan take liman ya bude lemun ya fara sha sanyi na ratsa zuciyarshi ...kai ILU Allah yayi maka albarka ya kara daga lemu ya kwankwada... Ashe haka nan muke maka kallon mashirmanci Ashe kasan abinda kake ...ILU ne ya kalli basiru shima basiru ya kalleshi saura kadan su tuntsire da dariya mussamman basiru ya kara abar wurin ya yi dariyarsa mai Isar shi ....


Said a ya shanye rabi sannan ya kara kallon su... Waini ILU ya batun dorere yau dai karka bari kayi dorere ....nan ma gumtse dariyar ILU yayi... Ai insha Allah gobe bszanyi dorere ba sai wasu kuma....
Yar dariya liman yayi ai dorere ba dadi ILU liman ya fada yana kara shan lemu sanyi na ratsa shi...


Mikewa sukayi to ya liman mu zamu wuce... Inji ILU... A aha har zaku tafi ILU ...to nagode sosai Allah yayi maka albarka ga wani Dan kosai nan Ku tafi dashi ko zakuci anjima ....


Da sauri ILU ya dauka dama sai hararar kwanon yake... Godiya Nike ya liman... Sukayi mashi sallam a suka tafi....


Suna shan kwana basiru ya hau babbaka dariya harda faduwa kasa... Shi kanshi ilun dariya yake tare da fadin ....kai tsohon nan yasan dadi wai kaga yadda yake kurbar lemu yana yamutsa baki kamar an lasawa jariri Zuma .....
Cikin dariyar basiru ke fadin kai wllh ILU kai karshe ne ....


Kaga maza Muje ga maigari tun kafin ya shige gida.... Basiru na dariya suka bar wajen suka nufi gidan maigari...


Liman kau suna tafiya ya kwashe komatsanshi ya shige cikin gida ...yana shiga uwargidan shi talatu ta karbi kayan tare da fadin wannan ragowar namune ko mai gida ...


Fizge robar lemun liman yayi ...kai kudai mata kun cika kwadayi to Dana ILU ya kawomin saboda haka ba Wanda zai shashi.... Buzun buzun ya wuce dakinshi...


Dan murmushi talatu tayi... To liman asha lfy ta wuce kicin ajiye kwanoni...




Lokacin da suka isa gidan maigari har zai rufe gida... Aa wa Nike gani kamar ILU n malam... Eh nine ya maigari barka da shan ruwa ...yawwah ILU lfy dai ko...


Lfy lau maigari dama cewa nayi ya kamata inzo maku barka da shan ruwa.... Kai amma naji dadi sosai ILU ya malam da mutanen gidan....


Suna lfy ga wannan nace bari inkawo maka ba dai yawa...


Cikeda da faraa maigari ya karba ...yaji lemu karara..nagode sosai ILU kamar kasan Abu mai sanyi Nike bukata yanzu ...


Aa ba komai fa ILU ya fada... Mu zamu tafi said a safe.... To Allah ya kaimu ILU ngd sosai ka gaishe da malam...




Zaiji ya fada yana murmushi suka wuce ...tunda suka fito suke dariya har basiru yayi hanyar gida tare da fadin sai goben ILU nasan akwai bidiri garin nan.....




Yar dariya ILU yayi to basiru Allah ya kaimu ....




Tunda ya shiga gida yake dariya har iya da asabe suka fito dagadaki...




Iya ke fadin lafiyarka ILU ....uhm ai tunda kikaga ILU na wannan dariyar to akwai muguntar da zaiyi... Asabe ta fada tana Harar sa.....
















*Muje zuwa labarin ILU*
[6/20, 18:42] Maryam Muhammad Hassan Ce: *B.W.A*














😂😂😂😂😂😂
*AZUMIN ILU*
😂😂😂😂😂😂


*peg 16*
*MAMAN MAMY*....✍




```Allah yasa damu da alkhairan dake cikin wannan wata mai albarka```








Dan yake iya tayi ...to Allah yasa ba kanmu muguntar zata kare ba...
To ameeen dai inji asabe tana harararsa....




Shidai ILU baice komai ba sai dariyarsa yake abinsa.... Ya wuce daki ya fara cin kosan daya taho dashi daga gidan liman ....




Tofa jamaa liman fa bacci yake kasarika ...saura yan mintina akira sallah matan suka farka dama shine ke tadasu gaskiya.... Sunyi mamakin baccin liman na yau ...akayi akayi atadashi amma yakasa tashi sai buga minshari yake kamar tsohon sa...haka suka hakura suka kyaleshi ranar ma sai liman yayi sallar asuba...


Hakama bangaren maigari an tadashi an ta dashi yaki tashi haka aka kyaleshi yayita shara baccinshi ....


ILU kam anyi sahur yaci yaci abinci sosai saboda cewa yayi sai anhada mashi hadda na jiya da baiyi sahur ba ...cikeda farin cikin yadda zaiga liman da maigari ...


Tunda suka dawo sallar asuba malam ke mamakin rashin zuwan liman masallaci saboda baiyi mamakin rashin zuwan maigari ba saboda shidai dole liman ya fito ko baijin dadi ...sai dai inya fito yace wani yayi sallar ....


Shidai ILU baice komai ba yana ganin liman bai fito ba yasan cewa aikinshi yayi kyau ....


Sai misalin 10 ILU ya tashi yayi wanka ya fito da cazbaha a hannu ....iya ya duba dake yan share share ...wllh iya yau zaayi rana




Murmushi tayi kwarai kuwa ILU zaayi rana irin mai zafin nan.... Yawwah Allah haka nikeso ILU ya fada yana murmushi sannan yayi waje yana fadin yau akwai kallo kauyen nan ......




Yana fita ya nufi gidan su basiru kafin ma yakai suka hade... Tafawa sukayi tare da fashewa da dariya suka nufi wurin firarsu suna kara zantawa .........


Liman fa Abu ya kankama ko bacci n safe da kyar ya samu yayi ...gashi ana tsala rana irin maisa kishirwannan ....fito wa yayi da niiyar zuwa massalaci kiran sallah azahar duban matan yayi suna aikace aikacen su yaja dogon tsaki...


Yanzu duk cikinku arasa wadda zata tasheni ....wllh yau ukku ukku Nike ganin mutane ji ji nikeyi kamar ba yan hanji cikin cikina rabon da inyi dorere harna mance ....


Wllh wllh liman ba irin tadin da bamuyi maka ba kaki tashi... Uwargidan ce ta mayar masa da amsa tare da dukar da kanta kasa cike da tsoron abinda zai biyo baya ....


Bai kara cewa komai ba ya yi waje yana banbami ...Ashe bai lura ba takalman Kansu daban daban ne rigar kanta daban take da babbar rigarsa ...hatta rawanin ba yadda yake na dashi ya Nada ba ....


Tun daga nesa su ILU suka hangoshi me zasuyi ba dariya ba ILU hard a faduwa kasa.... Duk Wanda ya kalli liman saiya kara kallonshi cike da mamakin yadda ya koma....




Yazo wuce wa ne ILU ya kalli kafafuwanshi ya tintsire da dariya ganin takalma daban daban da alama liman baisan yayi gamin bauta ba .....


Ina yini ya liman ILU ya fada ...cike da galabaita liman ya dubi ILU ...lfy lau ilun n malam...


ILU ne ya kara kallon shi sama da kasa ....ya dai ya liman azumin ne.... Wani Dan nishi liman yayi ..bari kaidai ILU yau dorere Ashe haka kaji rannan wllh dishi dishi Nike gani....


Da kyar ILU ya kumshe dariya ....to ai Matsala r daya ya liman ita yunwa bata da hankali ...hakane ILU wllh na yarda yunwa ba tada hankali... Kaga bari inkarsa nasallaci indan huta kafin in fadi nan.... Buguzun buguzun ya wuce rawanin na Neman faduwa yana taroshi....


Aifa su ILU sai dariya suke suna maimaita yadda liman keyi... Can saiga maigari ya nufo masallacin sai yaken dole yake .....
Nan fa kallo ya koma kanshi ......












*Muje dai zuwa labarin ILU*
[6/20, 18:42] Maryam Muhammad Hassan Ce: *B.W.A*










😂😂😂😂😂😂
*AZUMIN ILU*
😂😂😂😂😂😂


*peg 17*
*MAMAN MAMY*......✍
09031711711 for comments


```har in bazakayi magana akan novel ba to karka dauki number nan plss```ngd


💖💖💖💖💖💖💖
*RAMADAN KAREEM*
💖💖💖💖💖💖💖


*Allah kasa muna cikin intattun bayinka Allah kayafemana zunubanmu badon yawan ibadun ba ya Allah*🙏🏻🙏🏻🙏🏻








Tun kafin ya iso inda su ILU suke ya hau balbalin masifa .....kai ILU bana hana fito da tabarmun masallaci a shimfida awaje a zauna ba... Wato kun raina arzikin mutane ko????




Basiru ne ya dubi ILU shima ILU ya dubi mudi cike da mamaki yake fadin mudi ina kaga tabarma anan iccen nan nefa da aka sare muka Dan baza ganyayenshi .....dariya basiru yasa wllh maigari najin azumin nan shifa da tsiya idanuwansa tabarma suke gane masa ba rairayi ba...


Aiko gaba daya suka kwashe da dariya ...dai dai lokacin maigari ya I so yana share zufa zai dasa wani balbalin masifar ya daga kai haka ya ga ba tabarma bace sukuti yayi yana kallon su.....


Da sauri suka dai daita Kansu da dariyar saboda sunsan halin maigari ba mutunci ne dashi ba....


ILU ne ya dubeshi ya maigari ka mance ne ka taho da but a ahannu ko ka mance nan masallaci akwai butocin yin sallah?? ILU ya fada yana kumshe dariya tare da kallon butar dake hannun maigari.....


Sai lokacin maigari ya dubi butar dake hannunshi ....lokacin da yayi alwallah ne sai ya mance bai ajiyeta ba ya taho da ita ....


Dan murmushi yayi ....kai dai bari ILU wllh alwalla nayi na mance ban ajiye butar ba nama rasa tunanin da nikeyi....


Yar dariya ILU yayi... To kodai azumin ne ya maigari??


Har maigari zaiyi magana aka kabbara sallah ...da sauri suka nufi masallacin gaba daya ba tare da an ida caftar ba...


Jamaa liman fa najin AZUMIN nan saboda karatun sallar ya fara gura gura ...inya karanta aya saiya Dan jima bai tuno ta gaba ba ...gashi sallar shaf shaf akeyinta wato yar faki inji yara ba yawa sai lada...


Jamaa sai mamakin liman suke ganin yadda ya rude yake Neman kasa yin Jam'i


Ahaka dai aka kammala sallar su ILU nata kumshe dariya ...


Bayan anfito ne dattawan garin aka tsaya ana tattaunawa ...malam ne ke tambayar liman lfy..


Uhm bari malam liman vya fada yana dafe ciki yau dorere nikeyi bansan ya akayi na makara ba ...duniya gaba daya ta zame min doguwa ...


Har malam zaiyi magana maigari ya rigashi ...to ai nima dorere nikeyi nikam wani irin bacci nayi da ban taba yin irinsa ba tun da Nike arywa ta ...


Subhanallah liman ya furta a wahalce ...to ai nima irin baccin da kake fadi nayi.. Wato ni kamar ma matattace na koma ...ikon Allah to wannan wace irin masifar bacci CE ta samemu ...ko kaima irin shi kayi malam??? Liman ya fada yana kallonsa




Azabure malam ke fadin ...aa nikam banyi irin wannan bacci n ba ..saboda tun lokacin da suka fara maganar ya fara zatgin da wani Abu akasa bare daya tuno kalaman ILU da safe da yake cewa.. Yau akwai kallo a kauyen nan ....




To Allah ya kyauta ...inji maigari yawwah malam dama inaso inyi maka godiya ...jiya ILU yazo yayi min barka da shan ruwa harda abin arziki gaskiya naji dadi ILU kam an fara hankali....




Liman ne ya karbe... To Ashe bani kadai yayi ma wannan abin arzikin ba ...nima jiya saiga ILU yazo min barka da shan ruwa da lemu mai sanyin gaske ...in gama ina gama shan shi da yan mintina na hau wannan mugun bacci n....


Kallon sa maigari yayi ..to ai nima ina gama shan lemun ko minti biyar baayi ba bacci mai nauyi yayi awon gaba dani ...


Malam ne sukaji yana babbaka dariya harda tafa hannuwa ...kallon shi sukai gaba daya lfy malam??


Uhm lallai sannunku ...ai kun shiga tarkon ILU Ashe Ku har yanzu Baku gama sanin waye ILU ba ...in banda abinku wake cin kudin ILU a kauyen nan bare har ya saya maku lemu mai sanyi ...


Shiru malam yayi saboda dariyar data kubce masa ...
Amma dai anyi jairin yaro wurin nan ..haba nidai nayi mamakin irin bacci n da nayi kuma na Dade INA tunanin kyautar da ILU yayi man ban sake shiga mamaki ba said a naji maigari yace shima ankai masa.. Oh! ILU ILU


Liman ya fada cike da takaicin abinda ILU yayi masa daga baya kuma sai dariya ta kubce masa tunowa da yadda sukayi da ILU da irin ladabin da yayi masa Wanda baisanshi dashi ba ....




Shi kanshi maigari dariyar yayi ..kaga jairin yaro yasa gaba daya na fita hayyacina saboda yunwa... Kila gara ni da liman .. Shifa liman takalman kafarsa daban daban ne saboda tsabar jin AZUMIN ...


Tuni liman ya turbune fuska wane irin gara kai ...maigari tun daga gida fa ka taho da buta ahannu da alama ba kasan ka taho da ita ba ....


Dariya malam yayi ...nidai yanzu don Allah kuyi hakuri ...ni kaina Dana haifi ILU bai ragamin ba in shegantakarsa ta motsa baiji bai gani ....


Aa ba komai malam ...to amma me yasa yayi mana haka ne ...liman ya fada yana shafe zufar dake keto masa ...


Uhm tun da kukayi masa dariyar dorere shine abin ya bashi haushi ni nasani yakace kuma sai kunyi ...ai arayuwar ILU ba abinda ya tsana irin kaGanshi cikin wani hali kayi dariya saboda haka saiku kiyaye....




Ikon Allah ...maigari ya fada.. Ba komai gobe ka turomin ilun da abokansa zan zartar masu da hukunci saboda in baa hukuntashi abinda zai rikayi kauyennan ba karami bane ....




Da dai ka barshi kawai ...liman ya fada saboda shi ya tsorata da lamarin ILU ...


Shidai malam baice kar a hukunta ILU ba...saboda ana iya ganin don yana dansa...


Amma yasan bazasu iya yimasa komai ba ...saboda ILU ya ishi kowa Riga da wando...




Ahaka sukayi ban kwana kowa ya nufi gidan sa ...


Malam na zuwa gida ya hau yima iya bayan I tayi dariya sosai suna cikin hakane ILU ya shigo yana fadin


WO! Ni ilu ilun malam wayace dani bani ba dara bataci gida ba .....


Malam ne ya dubeshi yana murmushi... To albishirinka jairin malam dara taci gidaje bama gida ba...














*hhhhhhh Muje zuwa labarin ILU donjin hukunci da maigari zai yanke masa anya maigari bai tabowa kansa ba*






*ni din daice maman mamy Nike cewa kunsha ruwa lfy*
[6/20, 18:42] Maryam Muhammad Hassan Ce: *B.W.A*










😂😂😂😂😂😂
*AZUMIN ILU*
😂😂😂😂😂😂


*peg 18*
*MAMAN MAMY*.....✍




💖💖💖💖💖💖💖
*RAMADAN KAREEM*
💖💖💖💖💖💖💖


*Allah ka yafemana albarkacin wannan wata mai albarka*🙏🏻


```barkanku da shan ruwa masoyan ILU ```😁




Cikeda mamaki ILU ya dubi malam ...bangane ba ya malam ILU ya fada yana gyara bajejiyar rigar dake jikinshi ....


Eh ai bazaka gane ba... Yanzu kai ILU ka kyauta kenan kasa bay in Allah dorere ba gaira babu dalili....wllh ILU kazo ka natsu kullum shekaru na gaba amma ba hankali ....


Yar dariya ILU yayi ..kayi hakuri ya malam ..ILU zaiyi hankali nan bada dadewa ba ...kuma daman ai hakane ya kamata da mai dariyar mugun ta bakaga da liman namin dariya jiya ba har wani dukewa yake ...


Kai ar jairi... Malam ya katse masa tunani ..towai ma me kasa masu a lemun ...


Dan kwanbare kafada ILU yayi ba wani Abu bane ya malam Dan maganin bacci ne irin mai nauyin nan ...sai kuma ya dubi iya ...wllh iya yau liman yana jin jiki Ashe haka limamai ke rudewa sukaji yunwa ...sai kuma ya babbake da dariya ...


Takalmin dake kafar malam ya cire ya jefe shi dashi ya kauce yana fadin tuba Nike ya malam..


Ajiyar zuciya malam ya saki ..ai gashi nan kajama kanka da abokanka gobe maigari na Neman ku ya zartar maku da hukunci dai dai da laifinku kuma wllh ban bashi hakuri ba kuma kasan halin maigari Allah dai ya kyauta ...daga haka maigari bai kara cewa komai ba ya mike ya shige dakinshi yana murmushi yasan ILU da tsoro ....


Ragwaf ILU ya zauna yana yake mai kama da dariya dariya ...uhm wllh iya maigari ya kuskura ya sani kiwon awaki cikin AZUMIN nan zaisha mamaki nasan karshen hukuncinsa kenan ...


Dariya iya tayi ..a to ai in mutum baaiji bari ba yaji hoho duk kuma Wanda baiyi sharar masallaci ba yayi ta kasuwa ...ai gara ya turaka kiwon dani nace kajemin kiwon bazaka jeba ....


Mikewa ILU yayi yana jujjuya wa dubi nifa iya babban yaro dani duk kauyen nan ba mai kyawuna ..sai ace in rika yin kiwo ...ai iya dani mai kudi ne wllh zaaga takama da iko ...


Hararsa iya tayi da wannan bajejiyar rigar taka zakayi iko da takamar ji cikin ka wane mai kudi zai zauna yayi katon ciki irin naka ....um ni kaga bari in tashi inyi sabgar gabana da wannan sokanar taka ..wai kudi ko yaushe zai yi kudin ..




Yar dariya...ILU yayi ya dubi iya data tashi ta nufi kicin tana dariya... Uhm insha Allah sai nayi kudi iya nasa an gyara maki kafafuwan nan naki da kike dungurawa ya kara babbakewa da dariya ....





ILU fa lamarin yayi masa kyau mussaman suke labe bayan gidan liman suna kwasar dariya saboda kofar gida ya baje yana dafe ciki kamar ba namiji ba ...




Daga karshe liman bai kara komawa massalaci ba sai gaf da zaa kira sallar magariba ya fita yayi zaune bakin massalaci yana Jan cazbaha gsanin ban tausayi .....










Bayan an sha ruwa ne liman ya tsare ILU sai nasiha yake masa kamar zaiyi kuka... ILU kam sai to yake
cewa in ta shiga tanan ta fita tanan ba alamun nasihar na shiga kunnuwansa baima gama nasihar ba ILU ya mike yana fadin ...ngd sosai ya liman Allah ya biya ..bai jira amsar dazai bashi ba ya kara gaba yana baje rigarsa..


Girgiza kai kawai liman yayi tare da fadin Allah ya shirya mana ILU ...


*nima dai nace ameeen*😂






Washegari ILU ankusa ma kara ...saiga iya da asabe da ILU na cin abinci kwano guda saboda basu ma tsaya wani kasa wa ba saboda karancin lokaci ...




Washegari da wuri maigari ya aiko kiran ILU da abokansa ....
Fito wa ILU yayi yana dariya to iya mu zamu fita Allah dai ya fidda ai ga rogo..
Dariya asabe tasa ...Allah yasa kar ta fita ai n ..


Dariya iya tasan ya harda dukewa.. Harara ILU ya zabgawa asabe ..ai asabe tuni na gano baki kaunata ...yayi waje yana fadin Muje ai maigarin ba Allah bane ...
Har ya kusa fita ya dawo ya dauki ashana ...ya dubi iya ki dakamana tasshi mai dadi ...




Cikeda mamaki iya ta dubeshi me zakayi da ashana da tasshi ...


Kila maigari zai soye ko ..asabe ta fada tana dariya... Binta yayi aguje ta shige daki tare da banko kofar...




Fita yayi yana haki... Zaki sani innadawo iya na tafi ...


To ILU Allah ya tsare ....




Said a ya biya ma basiru da mudi sannan suka dau hanyar gidan maigari ..basiru na fadin alkuran

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login