Showing 3001 words to 6000 words out of 16241 words

Chapter 2 - AZUMIN ILU (COMPLETE) BY MAMAN MAMY Maryam Muhammad Hassan.txt


*peg 5*


*MAMAN MAMY CE*.....✍
Nace Ku huta fans😍




*wannan peg nakune masoyan ILU acici mai cikin Zane*🀣🀣🀣🀣










Hakuri ta hau bashi ....na tuba ILU bazan sake ba... Ganin yadda ta tsorata yasa ya wuce abinsa yana masifa kamar shi kadai ke azumi kauyen ......




Misalin 6 na yamma ya fito sai dukewa kasa yake yana dafe cikin shi idanuwa sunyi jajir dasu ....malam ya hango ya Debi uban kosai aroba zai fita rabawa almajirai...


Da gudu ILU ya isa gaban shi ya riko robar kosan yana maida numfashi .....


Haba malam ya mu bamu koshi ba zaa kaiwa na waje kosan ya kalla ya kuma kalli sauran Wanda iya ke toyawa ....koni kadai zan iya cinye wannan kosan ban koshi ba shine kuma sai ahau rarraba dashi.....




Murmushi malam yayi ...haba ilun malam Wanda ka bada shine naka... Wanda kaci Masai zaije.... Yanzu kai anaka haukan ko barinka mukayi da kosan nan duka zaka iya cinye shi?????




Wllh tsab zan cinye shi har in nemi kari ...kuma da kace Wanda naci Masai zaya Ai nan ma wata sadakar nayi ma tsutsotsin dake cikin Masan tunda su zasu cinye kashin da nayi ...don Allah malam kayi hakuri kabar mana kosan mu in zan bar kosai guda yayi kwantai Allah ya tsine man ......




Dariya malam yayi ka fahimceni ILU ita sadaka ba lallai sai ka wadatu ba zaka bayar ....a musulunce anfi so ka bayar da abinda kafiso to Allah zai Baka lada sosai ....ka bada kadan Allah ya baka Wanda ya fishi ..sadaka maganin talauci duk mai sadaka Allah bazai taba barin shi cikin talauci ba zakaga da ya bayar Allah zai mayar masa da Wanda ya fishi sannan ga lada.. Bare cikin wannan watan mai RAHAMA .....ILU ka bari abada sadakar nan ni zan hada maka da nawa kason saika cinye ni nasha koko...




Sakin robar ILU yayi yana turo baki.... Abasu amma Allah da kasonka zan hada inaji ina gani bazaa kware niba .....murmushi malam yayi ya Ciro nera hamsin aljihunsa karbi wannan maza tashar alu ga kankara can ankawo ka siyo mana mu jika musha....






A wahalce ILU ya karbi kudin ya fita yana rangaji ..malam yabi bayansa da robar kosan da zai rabama yara ....saida ya tsaya ya gama Harar almajiran sannan ya wuce tare da fadin munafukan banza ......








Tun daga nesa ya hango Layin da ke akwai can ya hango basiru da mudi abokan sa nata bin layi ...dariyar mugunta yayi duk da uwar yunwar dake kwalkwalarsa .....






Can ya zagaya bayan mai sayar da kankara ya fara rada masa ....sannu da aiki bawan Allah dama maigarine ya aiko ni abashi kankara ....dubanshi mai saida kankara yayi ....yaga ILU yaci magani kamar bashi ba ....ba musu ya karbi kudin ya bashi kankara ukku harda kyautar daya gudu kenan....






ILU na dariya ya daga ma su basiru hannu yayi tafiyar shi .....


Lokacin daya isah har sun gama komai suna zaune sunata laximi ...mika masu yayi yai kwance kasa yana fadin... Astagafirrillah da karfin gaske.. Malam ne ya dubeshi ILU kayi cikin zuciya mana...












Aa malam bari inyi afili kunfi sanin halin da Nike ciki na yunwa....
















πŸ˜‚πŸ€£πŸ€£πŸ˜‚πŸ€£πŸ˜‚πŸ€£
[6/20, 18:42] Maryam Muhammad Hassan Ce: *B.W.A*












πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚
*AZUMIN ILU*
πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚


*peg 7*
*MAMAN MAMY CE*.....✍


Nace Ku huta πŸ˜†












Saida malam ya gara zama ...sannan Iya tayi mashi barka da shan ruwa asabe ma tayi mashi banda ILU ko kala baice ma malam ba sai zubawa uwar hanji yakeyi ......




ILU barka da shan ruwa ...malam ya fada cike da zolaya dai dai lokacin daya kai kofin koko bakin shi .....a haba malam duka yaushe nasha ruwan bare afarayiman barka tukunna dai...ILU ya fada yana kara dagwalo yaji ga kosai.....






Wasa wasa ILU ya kasa cinye Rabin kosan nan... Duk hadamarshi saiga ila na zare idanu gashi daya motsa sai cikin ya bada kululu alamar ruwa ya cika cikin...bare kunsan azumi Nada haka sai kaga kamar zaka Iya cinye Abu amma sai ka kasa






Malam yana kallon shi yanaso yayi dariya amma yaki yarda ta fito ....
Wai Iya kodai AZUMIN nan da nayi an rage min fadin cikina ne ...duka dubi Dan kosan da naci da koko n da nasha amma naji cikina ba sauran wuri gashi banci abinci ba ......




Dariya Iya tayi ...wa zai rage maka fadin ciki ILU... Kawai daga yin azumi sai ciki ya ragu ...uhm dama haka azumi yake sai kaita hadama amma abinda zakaci ba wani bane .....


Ikon Allah ILU ya fada yana satar kallon malam dake tamnar naman kaji Ashe sune a kwano ....




Tuni miyan ILU ya tsinke ..dubarace ta fado masa da sauri ya dauki kwanon kosan ya isa gaban malam ya dukar da kai kasa ...




Barka da xshan ruwa Babana.... Kasan soyayya ta da da uba bazan Iya cinye kosan nan da kason ka ba dama wasa Nike ma Iya ...Itakuma ta hada min da naka ..INA wane ni ...tuba Nike dattijo mai ran karfe .....




Wllh malam karka kulashi ..wayo ne dashi karya yake.. Ka tsare shi ya cinye shi tunda shi yace yaji ya gani ....asabe ta fada tana ma ILU dariya kasa kasa....




Kai kai wai asabe meyasa ke Yar bakin cikina CE duk gidannan kin tsani kiga INA warwasawa ...yinin yau INA lura dake kina min dariya to wllh ki shiga hankalinki dani .......


Ya isa haka malam ya dakatar dashi... Naji ni yanzu na koshi da kosai kaje ka ajiye anjima kaci naci guda biyu wurin salame ya isheni... Amma daka hana abada sadaqa da duk ina zaka kaishi ...malam ya fada tare da yagar naman kaza....




Kuttt! ILU ya hade miyau ...kai dai bari malam Ai gobe in zaka bada sadakar aba harda kaji ..ILU ya fada yana kallon naman kaza yana murmushin dole ....


Malam baisan sadda dariya ta kubuce masa ba... Duk yagama dago ILU... Kara cirar naman yayi ya mika masa kwanon ...ungo anshi ka diba ka basu sauran.....






Jiki na rawa ILU ya karba ya mike tsaye tare da fadin godiya muke ya malam... Saida ya yagi kafcececiyar tsoka sannan ya dubi asabe.....






Wllh asabe yau sai da naga kana nan malaikun mutuwa da manyan nagani da tuni na mutu.... Uhm ni ina ruwana koma waka gani ...nidai ka bamu kason mu sai kaci gaba da bamu labarin ......




Kash! Asabe kin cika kwadayi ki rage wllh ....wata tsokar ya kara yagowa ...asabe! Ya fada da karfi . .yau anyi rana yau naji ki shirya kamar ma banda makogwaro naji.... Oh! Ni salame.. Iya ta fada tana kallon ILU ...




Ai yi hakuri Iya karbi kason ki.. Kafafuwa ya miko mata ...taki karba tacigaba da hara rarsa ..ungo mana Iya abinda yasa na baki saboda na taba mafarki ...ance in tsaffi mata nacin kafar kaza to kafafuwansu za suyi kwari sosai ...kinsan ita kaza akwai kwarin kafa ...bare ke dazu da kina aiki kina dingisa su ji nayi kamar insa hama in bigesu kowa ya huta.....




Ai da kasa hammar ka dai daita minsu Iya ta fada tana dariya tare da amsar kafafun tasan karamin aikinsa ne ya hanasu duka.....




Ke kuma asabe ungo kai.. Ya mika mata kan kazar ...saboda na lura irin kanku daya da kaza ...kinga kin kara hankali ma ...wani dogon tsaki asabe taja wllh banci ...






Alhamdulillah ....shiyasa kike birgeni asabe biya ...komawa yayi zauna yaci gaba daci... Asukwane asabe ta warci irin bayan nan ta ruga daki ta turo kofa ....




Dariya ILU yayi haba yarinya bashi kikaci ...Iya kau da malam sai dariya suke tsokar dake hannun malam yaba Iya ta kara...




Kiran sallar ishai aka hau kira... Malam ne ya dubi ILU tashi kayi alwalla mu tafi masallaci.....














*Maman MAMY CE*
[6/20, 18:42] Maryam Muhammad Hassan Ce: *B.W.A*










πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚
*AZUMIN ILU*
πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚

*peg 8*
*MAMAN MAMY*.....✍








To malam ILU ya fada tare da yin wata mika ta mussamman... Iya ga kosai na nan a ajemin saura ki badashi sadaqa nasanki da tausayin Dan almajiri ....wa ni na isa in taba abinci ILU ...iya ta fada tana murmushi ....


Ahayye sama duniya tayi dadi!!! Haba ina amfanin yunwa da zan ganta ido da ido ...saina kashe ta ..koni ko ita wllh iya....


Har malam zaiyi magana sukaji ankwada sallama kofar gida... ILU fito mu tafi massalaci ..muryar basiru yaji daga kofar gida...


To basirun inna mai yan kunnuwa gani nan.... Lol! Wai ILU yaushe zaka daina radawa mutane suna ne ...iya ta fada..


Uhm kyaleshi yayi Ai ansha ruwa da dazu ne ko bakin shi bakiji sai idanu.... Aa malam wllh bani kadai nasha wahalar azumi ba ..tsaya kaji..sai kuma ya fara dariya ..ina ganin maigari dazu zai shiga gida saura kadan ya bige kai da alama bai ganin kofar gidan saboda yunwa πŸ˜†πŸ˜†


Dif wutarsu ta dauke mussaman malam da dariya ke cinsa ..ILU ba karamin sha kiyi bane... Saida ya gama kwasar dariyar sa sannan yace ....shi kuma liman dazu ana sallar azahar sau biyu karanta bisimilla ...nan ma wata dariya r ya saki .....


Ita kuma iya ...wani Dan karamin icce malam ya fizgo ya kaimashi bugu ya kauce ..yayi waje yana fadin muje basiru tun kafin tsohon nan ya kaini kasa....


Aida ka tsaya Dana koya maka hankali ...Ai dama nasan da yagama shsrrance yan waje zai dawo kanmu ...yana gamawa dake zai dawo kaina tunda shi jairine ....Ai ni garama ayita AZUMIN mun samu saukin ka ....


Yar dariya iya tayi ..uhm Allah dai ya kimtsa ILU v..kullum shirmensa gaba yake yi ....


Alwalla malam yayi yabi bayansu zuwa masallaci. .....


ILU fa ya mike duk ya ishi mutanan kauyen da tsokana ba Wanda yake ragamawa ba babba...koda aka gama sallah lulawa sukayi cikin kauyen daukar magana shida abokan sa ..bai dawo gidan ba sai wurin goma na dare ...




Sanda ta hauyi yadda kar malam yaji sadda ya dawo ....iya CE ta fito fi tsari saboda har sunyi bacci ..inwa tagani tsaye cikin razsna tasaki butar tare da fadin auzubillahi waye nan....


Da sauri ILU ya fito karta tona masa asiri ..nine iya ..kai kudai mata Allah yayi maku tsoro wllh kin kuma san ko barawo ne ko kallon arzuki baki Ashe shi ba....


Haka ya ratsata ya wuce yana mita saura inji zancen wurin malam wllh saina ballswa tunkiyarki kafa... Aa bazai ji ba ni na isa iya ta fada da karfi... Saboda tasan in ILU yace zaiyi Abu to sai ya aikata shi ....


Saida ya cinye sauran kosan da tuwo mai yawan gaske sannan ya kors da koko ya kwanta ....


Tun da suka tashi sahur asabe ke faman tada ILU amma yaki tashi saima gyara kwanciya yake ....


Malam ne yace ..kyaleshi asabe jekiyi sahur dinki.. Ai gobe ya sani yayi csahur din ma ya aka kare bare baiyi ba ...




Asabe kam komawa tayi taci gaba da sahur dinta ...iyace ta mike Umm bari inkara tada shi ni kadai nasan balain da zai mana gobe ....


Ki kyaleshi ya Dade baiyi ba laifin wa ..malam ya dakatar da ita.. Mikewa tayi aa malam nasan fitinar ILU kamar yunwar cikina bari dai in gwada .....




Iya ta tada ILU ta tadashi amma ILU yayi kunnen uwar shegu da iya haka ta hakura ta dawo taci gaba dacin abincin ta kafin lokaci ya kure .....
Haka dai suka gama suka kwanta ba tare da ILU ya tashi sahur ba..
















*muje zuwa dai fans.. Kunsan akwai bidiri ILU zai tashi da dorere*πŸ˜†
[6/20, 18:42] Maryam Muhammad Hassan Ce: *B.W.A*










πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚
*AZUMIN ILU*
πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚


*peg 9*
*MAMAN MAMY*..✍
Nace Ku hutaπŸ‘πŸ»






*wannan peg nakine zuzun Alkhairi ...Allah ya raya mana hafeez da hanan*🌹🌹








A firgice ILU ya tashi ji yayi kamar ana kiran sallah.... Da gudu ya nufi dakin Iya yana kwalamata kira... Iya Ku tashi wllh lokaci ya kusayi Ku tashi muyi sahur.. Gani yayi zuwama dakin Iya bata lokacine sai kawai ya wuce kicin da makekiyar rigarsa yana fadin....




Nidai duk Wanda bai tashi ba Matsalar shi CE ..nidai innayi sahur kowa ma ya gane sai ayita tadaku kunaji kuyi banza da mutane ...


Yana fitowa da kwanon abinci malam na fitowa dama sallah yake yanajin duk abinda ILU ke fadi.... Kardai ka kuskura ka ci abincin nan saboda lokaci yayi ...




Sakin kwanon ILU yayi woyyo Allah na shiga ukku ni ILU yanzu shine zaaki tadani wayyo Allah... Saiga ILU na ruwan hawaye ....
Iya CE ta fito da hijab jikinta ...haba ILU sai kace ba namiji ba don bakayi sahur ba sai ka ishemu da ihu sai kace Wanda ya rasa iyayensa ...


Kyaleshi yayi salame wane irin tadine ba a yi masa ba yaki tashi ...kuma dorere ba fashi akan shi tunda ba kanshi farau ba....


Aa malam ba kowane tadi aka yimin ba naki tashi.. Tsakani da Allah an watsa min ruwa anga ban tashi ba ko anturamin lomar abinci anga ban tashi ba... ILU ya fada cikin muryar kuka ...ni banma ga alamun anwani tadani naki tashi ba... Kawai dai kunaso yunwa ta kashe nine shiyasa ...




Eh yunwar ta kashe ka .....Ai wurin
[6/20, 18:42] Maryam Muhammad Hassan Ce: *B.W.A*










πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚
*AZUMIN ILU*
πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚
*peg 10*


*MAMAN MAMY*..✍


*fans Ku yafeni ganin peg 9 kadan wllh bisa kuskure ya tsaya haka plsss ayi hakuri*








Ai wurin ibada ka mutu... Kaga maza kaje kayi alwalla mu tafi massalaci kar mu rasa sallah ...wucewa ILU yayi yana fadin shikenan dai an cuceni wllh ancuce ni sai Allah ya sakamin ...


Salame dake gefe ..dariya tahauyi kasa kasa .....ahaka yayi alwallar suka tafi massalaci sai gunguni yake shidai malam bai kara CE mashi kanzil ba dama yasan zaa Rina ansaci zanen mahaukaciya ....


Bayan an fito salla h ne aka tsaya ana gaggaisawa liman ne ya lura da yanayin ILU ....aa mutumen lafiya na ganka haka... Daure fuska ILU yayi tare da dauke kai can sama baida alamar ba liman amsa... Malam ne yayi murmushi ..Ai liman yau mutumen ka baiyi sahur ba shine yake wannan tubukurin .. Saiga liman da maigari na dariya harda dukewa jin cewa yau ILU baiyi sahur ba sunsan cewa akwai bidiri kenan ...


ILU kau kara daure fuska yayi basu San cewa dariyar nan ta bata masa rai ba....liman ne ya dafashi haba namijin duniya ka nuna mana kai jarumi ne ba raggo ba ...duk da dai gaskiya bantaba yin dorere ba kusan shekara biyu kenan rabon da inyi dorere bansan wahalar shi ba amma nasan namijin kwarai lfy Lau zaiyi shi ba irinka ba ILU ..yana magana suna dariya da maigari malam ma murmushi kawai yakeyi ...


Wani Dan guntun murmushin mugunta ILU yayi harya hango ta inda zai rama dariyar da liman da maigari keyi masa ....


Tare suka jero da basiru ya baro malam can suna tattaunawa da mai gari ...wllh basiru inna yadda nayi dorere nan mutum hudu sai sunyi shi sunji yadda naji ...zaro idanuwa basiru yayi dawa dawa ILU...


Da salame da Iya suda suka ki tadani inyi sahur sai liman da mai gari da sukemin dariya bare liman har wani fadi yake rabon da yayi dorere anyi shekara biyu to wannan shekarar zaiyi shi ...abinda yasa bansa malam ba saboda shi dama wani lokacin ko ya tashi sahur din ba abinci yake ci ba sai dai yasha ruwa yacigaba da sallah ...


Kai ILU tayaya zaka hanasu tashi sahur.. Dariya ILU yayi tana kara gyara bajejejiyr rigarsa da tasha faci kala kala... Kai dai sa ido kayi kallo basirun inna... A haka sukayi bankwana kowa ya nufi gida shikam basiru baiyi mamaki ba yasan duk abinda ILU yace zaiyi tofa sai ya aikata shi ....






Misalin 8 na safe ya tashi yaufa ILU ba kanta ..tun lokacin ya fara jin yunwa ...fitowa yayi tsakar gida yayi tsaye gidan shiru kowa sai baccin shi yake hankali kwance ....wani takaici ne ya tokare ILU haushin baccin da yan gidan keyi ya keji shi kuma ya kasa yi ....




Ai wllh yadda banyi baccin nan ba bamai yinshi gidannan ..Ai yau an tokalo tsuliyar dodo.. ILU ya fada tare da nufar tumakan dake tsakar gidan ..ya hau kwance su ..maza kuyi xwaje ...


Saida ya korasu tsaf sannan ya leka dakin Iya ya hau buga masu kyaure ...Ku tashi sai bacci kuke ga tumakai can sun fice daji... A azabure Iya ta mike tare da fizgo wani yagaggen Zane ta rufa tayo waje harda bige ILU.. Ina sukayi ILU yau naga ta kaina ni salame ...da gudu Iya ta fita waje harda tuntube... Dariya ILU ya hauyi dama yasan haka zata faru yadda Iya keji da tumakanta shiyasa bata barin su fita koda yaushe suna cikin gida .....


Asabe CE ta fito da hijab ..haba ILU muje mana mu koro su sai kabar Iya ta fita Ita kadai ...hhhh hhhh kedai jeki asabe biya ina nan kuje Ku kuro su badai kunyi sahur ba yaci gaba da dariya ...hararshi asabe tayi haba nidai nayi mamaki ace gaba daya tumakai sun kwance kuma lokaci guda ..uhm wllh ILU kaji tsoron Allah yanzu don bakayi sahur ba sai kaita wahalar damu alhalin mun tadaka kaki tashi....




Malam ne ya nufosu da kara... Da gudu ILU yayi gefe yana dariya yi hakuri ya malam ...jeka Ku tafi akorosu dakai jairi maza Ku tafi tare kaima ka shawo wahalar da zasu sha wurin korosu ....


Da gudu ILU ya fita yana dariya ..lafiya lau malam aini dama yau rayuwata a wahala zata kare ....mutumen da baiyi sahur ba har an tambayeshi wahala ....
Asabe CE tabi bayan shi tana dariya taji dadin yadda malam yayi masa..


Girgiza kai kawai malam yayi ya koma daki ..dama yasan yau abinda ILU zaiyi ba karami bane ...


Saida suka wahala sannan suka samu suka hado kan tumakan ..zanen da Iya ta yafa saida ya dawo bisa kai saboda wahala kafafuwannan sunyi futu futu kamar basu taba ganin ruwa ba... Asabe CE ke fada mata ILU ne ya sake su..


Uhm Ai dama nasan wannan akininshi ne to Ai shima ya wahala tunda dashi aka korosu...


Dariya ILU yayi ...ba komai Iya don na wahala ni dama baccine banso kuyi gaba daya yadda yunwa ta hanani baccin safe to gara kowama ya tashi...




Asabe CE ta kalli Iya itama Iya asaben take kallo .....










*hhhhhh Maman MAMY ce duk Wanda ya karanta novel di nan baiyi dariya ba plss plss ya aiko min da sako zai iso gareni ..ni kuma zan bashi amsa ngd*🀣🀣🀣
[6/20, 18:42] Maryam Muhammad Hassan Ce: *B.W.A*










πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚
*AZUMIN ILU*
πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚


*peg 11*


*MAMAN MAMY*.....✍








Iya ce ta yi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login